Thursday, 1 January 2015
Ciwon-Suga ( Diabetes/Diabetes mellitus [DM])- A Takaice
Ciwon-suga (diabetes) cutace wadda suga (glucose) dake cikin jini yake haurawa sama - wato suga yayi yawa a cikin jini. Yawansa nada illa ga lafiya. Dalilin yawansa na faruwa ne sabili da jikin mutum baya samarda da wani sinadarin kemical mai suna 'insulin' ( = type 1 diabetes) , ko jikin ne baya amfani da 'insulin' yadda ake so, ko kuma ma jikin baya samar da 'insulin' da kyau [wato isasshe] ( = type 2 diabetes). Idan har babu 'insulin' tofa sugan 'glucose' zai cigaba da taruwa da yawa cikin jini har yayi illa ga lafiya. Sinadarin 'insulin' (a hormone), saifar 'dan adam ce ke samar dashi (pancreas). Amfanin sinadarin 'insulin' shine daukar sugan 'glucose' dake cikin jinin zuwa cikin 'kananan halittun da sukayi ginin jikin 'dan adam (cells) domin samun kuzari gare su da cigaban rayuwa. Idan babu 'insulin' ko baya aiki yanda ake bukata to suga fa zai cigaba da taruwa cikin jini yayi yawa har ya haddasa munanan matsaloli ga lafiya. Sugan zai iya yin illa ga idanu, koda, wasu jijiyoyin jini da kuma wayoyi/hanyoyin sadarwar kwalwa a jiki. Ciwon-suga zai iya haddasa cutar zuciya, mutuwar sashen jiki koma ya jaza yanke kafar marar-lafiyar. Idan ciwon yayi 'karami zai iya haddasa matsalar 'kashi da gabobi, matsalar fata, matsalar narkewar abinci, rashin karfin mazakuta, matsalar hakora da dasashi. 'Type 2 diabetes' ,wato nau'in ciwon-suga na 2 da mukayi bayani (wanda jiki baya amfani da 'insulin' yadda ya dace) shine nau'in ciwon-suga da yafi yawa ga mutane da dama fiye da nau'in ciwon-suga na 1: 'type 1 diabetes' (wanda mu kace jiki baya samarda da sinadarin 'insulin').Alamomin Ciwon Alamomin Ciwon-suga Nau'i na 1 (type 1 diabetes symptoms):
• Yawan jin kishirwa sosai
• Yawan yin fitsari
• Yawan jin yunwa ko gajiya
• Raguwar nauyin mutum ba tare da mutum yayi kokarin ragewar nauyin ba
• Dadewar ciwo/gwambo bai warke ba/warkewa a hankali
• Rashin gani da kyauAwon jini zai iya nuna idan akwai ciwon ko sabanin haka. Idan akwai irin nau'in ciwon , toh mutum zai cigaba da amfani da sinadarin 'insulin' da aka samar a asibiti, za'a bashi sinadarin a asibiti akan 'ka'ida da umarnin 'kwararren likita. Anfi yawan samun 'kananan yara da matasa da irin wannan nau'in ciwon-suga (Juvenile diabetes/Insulin-dependent diabetes)duk dadai cewa zai iya shafar mutane a kowani shekarun su na rayuwa. Alamomin Ciwon-suga Nau'i na 2 (type 2 diabetes symptoms):
• Yawan jin kishirwa sosai
• Yawan yin fitsari
• Yawan jin yunwa ko gajiya
• Raguwar nauyin mutum ba tare da mutum yayi kokarin rage nauyin ba
• Bushewar fata, kaikayin fata
• Mutum yaji kamar ba kafarsa ba ko jin tsira a kafafu
Yin awon jini a asibiti ko wata ingantacciyar cibiyar lafiya zai iya nuna maka ko kana da ciwon suga ko kuma akasin haka. Motsa-jiki (exercise), rage nauyin jiki yanda ya dace dace da koyarwar cikon lafiya, da kuma kula da tsarin cin abinci daya dace da ciwon lafiya, ko shakka babu , zasu taimaka sosai wajen shawo matsalolin lafiya na ciwon-suga. Cututtukan saifa, magunguna, kemikals, kamuwa da wasu cututtukan da gado daga mahaifan mutum na daga cikin dalilin da ake alakantawa da suke haddasa ciwon-suga. Allah ya bamu lafiya. AMEEN.
Sunday, 13 April 2014
Amfanin Man-Zaitun ga Lafiya ( a takaice)
Sabili da muhimmancin itaciyar zaitun, Allah Madaukakin sarki, Mai -halittu ya ambace ta a cikin Al-Qur'ani Maigirma - Surat At- Tin da Surat An- Nur.
Man-zaitun nada amfanin sosai ga lafiyar 'dan adam. Binciken ilimin kimiyya ya nuna cewa yana da amfani kamar haka:
1. Yana 'karfafa garkuwar jiki ( domin yaki da kwayar cutar biras, bacteriya, fangas (fighting virus, bacteria, fungus etc.) da sauransu. Wadannan cututtuka suke haddasa matsalolin lafiya da dama, kamar irinsu ciwon-anta, tetanus da cin-ruwa.
2. Yana da sinadarai masu bada kariya daga kamuwa da ciwon daji (rich in antioxidant subtances).
3. Kariya daga cututtukan zuciya - yana rage yawan sinadarin kolestirol (reducing high cholesterol) wanda idan yayi yawa a cikin jini yake da illa ga zuciya.
4. Rage hawan jini (reducing high blood pressure).
5. Taimako ga masu ciwon-suga (helping diabetic patients).
6. Kariya daga ciwon jiki (sanyin jiki) dana gabobi (anti-rheumatism & arthritis).
7. Inganta lafiyar zuciya (improving heart's function esp. to older people whose hearts are weak due to aging) musamman ga tsofaffi wanda zuciyar su ta fara rauni wajen aiki saboda tsufa. Yana gyara zuciya da quruciya.
8. Kariya daga ciwon daji dake shagar fata ( protection from skin cancer).
9. Inganta lafiyar qashi. (improving bone health).
10. Inganta lafiyar kwalwa wajen koyon wani abu kamar karatu ko rike karatun, musamman ga manya (improving cognitive function) da sauransu.
Ana iya amfani da man-zaitun kamar haka:
~ Asha cikin babban cokali sau 2 a rana - safe da rana, cokali daya a kowane lokacin.
~ Ayi girki dashi a matsayin man girki ko a zuba cikin abinci bayan girki.
~ Manshafawa kamar sauran man amfani na jiki.
~ Giris ga ma'aurata (sex lubricant). Bugu da kari, zai kuma bada kariya daga cututtuka.
~ Ciwon-kunne, digo 2 ko 3 na man a cikin kunne.
~ Da sauran wasu hanyoyin na inganta lafiya.
Allah Ya bada sa'a.
Monday, 24 March 2014
AMFANIN ZUMA GA LAFIYA (A TAKAICE)
Don haka, zuma nada amfani ga lafiya kamar haka:
1. Tana kashe cutar bakteriya da fangas (bacteria & fungus) da kuma bada kariya daga kamuwa da ciwon-daji. Bincike ya nuna cewa zuma mai duhu-duhu tafi wannan amfanin.
2. Tana warkar da ciwo ko gyambo idan ana shafawa ko sha.
3. Tana taimaka ma mai-mura, tari , atishawa da sauran matsalolin sanyi.
4. Maganin gudawa ce.
5. Maganin gyambon ciki - Ulcer.
6. Tana karfafa garkuwar jiki.
7. Tana rage hadarin kamuwa daga cututtukan zuciya, musamman idan aka hadata da Kirfat (cinnamon).
8. Tana sanya kuzari a jiki.
9. Tana rage nauyin kiba. Shan ruwa mai-`dumi da lemun tsami tare da zuma kafin aci komi da safe zai taimaka wajen rage `kiba.
10. Tana saukaka narkewar abinci ga masu fama da rashin narkewar abinci.
11. Tana rage kumburi mai sanya waje yayi kalar ja da radadin ciwo.
12. Tana kyautata lafiyar kwalwa.
13. Tana gyara fata da rage kurajen fuska (pimples) idan ana shafa ta.
14. Da sauransu.
Saturday, 1 March 2014
KALUBALE GA MA'AURATA - KASHI NA 5
Thursday, 20 February 2014
Fitaccen Maganin Gargajiya na Kasar Sin - Ginseng
Ita kalmar "Ginseng" (furucin kamar haka /'Jinsen/) ta samu ne asali daga kalmar "rénshēn" wanda a yaren Chananci "ren" na nufin "mutum". Gudan kuma bangaren kalmar "shen" na nufin "jijiyoyi ko sauyoyin shuka" ta yanda idan ka hada kalmomin biyu zaka hararo wannan ma'anar, wato "jijiya mai yatsu wacce take kama da kafafuwan mutum." Ginseng sinadari ne da wadannan kasashe suke amfani dashi a matsayin maganin gargajiya tsawon lokaci mai yawa a tarihi , har izuwa yanzu. Akwai wannan sinadari a kasuwanni kuma ana sarrafashi ta hanyoyi daban-daban na zamani, kamar gari, lifton, abun-sha, kofee, sirof, kwayar-magani, da wasu amfanin. Ginseng na daya daga cikin magungunan gargajiya da akafi siya a duniya. Ana fitar dashi zuwa kasashen duniya da dama, wanda harda Najeriya.Ginseng nada tarihi mai-tsawo na amfaninsa wanda tun daga lokacinda aka fara rubuta amfaninsa (farko) a wani kundi lokacin daular "Liang" (Liang Dynasty 220-587 AD) har izuwa yanzu. Abisa wasu bimcike-binciken kimiyya na zamani, sinadarin Ginseng nada amfani sosai ga lafiya ,
kamar haka: 1. Yana sanya kuzari da hana kasala. Mutane da dama sunyi imani da hakan, kuma suna amfani dashi domin biyan wannan bukata.
2. Yana gyara kwalwa domin rike karatu da kuma kyautata hazaqa.
3. Yana qara ruwan-jikin 'dan adam, kamar irin na maniyyi (maza da mata).
4. Yana bayarda rigakafi daga kamuwa da ciwon-daji (kansa), da yardar Allah.
5. Yana taimakawa wajen magance matsalar rashin karfin-maza.
6. Yana maganin ciwon-jiki.
7. Yana qarfafa garkuwar-jiki.
8. Yana rage suga dake cikin jini da yawan sinadarin kolestorol dake cikin jinin.
9. Yana gyara jini da hana saurin tsufan jikin 'dan adam, idan Allah yaso. Yana gyara jiki da
quruciya. Sai a kiyayi cin haram don rayuwa tayi kyau, mutuwa kuma dole ce. Allah yasa mu dace.
10. Da sauransu.
Muna sayarda wannan sinadari a irin sifofin da muka zayyana ana sarrafashi da kuma samar dashi. Mai bukata sai yazo ya siya, a kuma shawarci likita akan yanda ya kamata ayi amfani dashi. Allah ya taimaka.
Medical Disclaimer: I am just a researcher & a herbal practitioner not a professional medical doctor.
Monday, 6 January 2014
ILLAR YAWAN CHOLESTEROL A JIKIN 'DAN ADAM
adam ke amfani dashi domin gudanar da wasu
ayyukan lafiya a cikin jinin mutum. Wasu daga
cikin ayyukan cholesterol a cikin jini sune: 1.
Sauye-sauyen halittar 'dan adam yayin da yake
balaga da kuma sarrafa sha'awar sa. 2. Daidaita
sukari a cikin jini 3. Kare mutum daga daukar
wasu cututtuka (infection) 4. Samarda VITAMIN
D (sinadari maisa 'kwarin 'kashi da hakora) da
sauransu.
Hanta (liver) tana daga cikin ma'aikata ta
gangar jiki dake samar da CHOLESTEROL mai
yawa. Haka kuma abincin da mukeci wanda yake daga dabbobi na samar
dashi (DIETARY CHOLESTEROL).
Wannan
sinadari yafi yawa a cikin abincinmu karmar: kwai
('kwanduwa), hanta, butter, kifi,
nama, madara, mai , kaza da sauransu.
Duk da kasancewar wannan sinadari yana da amfani ga jikin 'dan adam, ba'a so yayi yawa cikin jini. Yawan cholesterol a cikin jinin mutum nada
hadari sosai, yana haddasa cututtukan zuciya.
Cholesterol dai sinadari ne mai danko kamar
kitse. Idan yayi yawa a cikin jini yana likewa a
hanyoyin jini dake daukar jini (artery) zuwa
zuciyar 'dan adam. Faruwar haka na iya
haddasa toshewar fayif din hanyoyin jinin
(plague/atherosclerosis). Idan haka yafaru, yana
jaza matsalolin zuciya kamar haka:
1. Hanyoyin dake kawo jini zuwa zuciya su toshe
(Coronary artery disease). Daga nan sai a samu
"heart attack" (zuciyar mutum ta samu dameji
ko mutum ya mutu).
2. Zuciya ta kasa harba jini zuwa sauran
hanyoyin jini na sauran jikin mutum (heart
failure).
SHAWARWARI
Mutum zai iya rage yawan cholesterol a cikin jininsa
ta hanyar:
1. Motsa jiki (exercise).
2. Cin 'yayan itatuwa da ganye (fruits &
vegetable).
3. Zaka iya amfani da magani domin rage
yawansa (amma da izinin likita ). Haka kuma
yanada kyau mutum yaje asibiti domin a duba
yawan cholesterol a jikin sa, domin yana karuwa yayin
da mutum yake manyanta. Allah yasa mudace.
Ameen.
Wannan hoto da kake gani a sama yana dauke
da bayanan abubuwa biyu kamar haka: Nafarko,
jini yana gudana a cikin fayif din jinin zuciya
(artery) lafiya lau batare da wata matsala ba. Na
biyu, yana nuna yanda cholesterol ya toshe fayif
din jinin (hanyar jini) zuwa zuciya. Cholesterol
shine mai kalar 'dorowa.
Saturday, 28 December 2013
BASIR-MAI-TSIRO
wadanda wani lokacin suna samun matsatsi
da talala mai takurasu. A lokacinda suka
samu takurawa da yawa, sai su kumbura.
Kumburin wadannan jijiyoyin jini na kara matsi
da takura a garesu cikin dubura. Dalilin
wannan yanayi marar-dadi ga jijiyoyin, sai
kaga wani tsiro ya fito maka a bakin dubura
wanda jijiyar jinince. Zakaji ciwo, ko kai-kayi
koma zubar jini. Wannan lamari shine Malam
Bahaushe ke kira da BASIR-MAI-TSIRO
(Hemorrhoid/ Pile).
Wasu daga dalilanda ke haddasa shi sune
kamar haka:
1. Gaggawa wajen yin yun'kurin kasaye
abunda dake cikin mutum (kashi). Hakan na
takurama jijiyoyin dubura.
2. Yawan zawo(gudawa) ko 'kin fitowar kashi
maisa yawan tsugunni a ban-daki.
3. Yawan kiba, musamman wajen mara ko
duwawu.
4. Juna-biyu da nakuda (musamman wajen
yunkurin fito da jinjiri daga farji). Yana yima
dubura talala da matsi.
5. Jima'i ta dubura (haramun!). Masu jima'i da
iyalansu ta dubura da mafi yawan 'yan luwadi
na fama da basir mai tsiro.
6.Zama mai tsawo kamar na cikin mota ko na
tela, da sauransu.
7. Matsalolin zuciya kona anta na tsawon
lokaci wanda ka iya jaza talalar jijiyoyin jini.
8. Da sauransu.
Zaka iya maganin rashin fitowar kashi maisa
yawan tsugunni ta hanyar cin 'ya'yan itace da
ganye (fibre foods). Yana da kyau sosai ga
marar-lafiya ya rinka tafasa ruwan zafi ya bari
yayi 'dumi ya gasa basir nashi da auduga ko
kuma ya zauna cikin robar ruwan mai dumi
minti 30 sau 2 a rana, domin samun saukin
ciwo da kumburi. Bayan angama gasawa toh
sai asamu DETTOL a wanke wajen domin
gudun kamuwa da wata bakuwar cuta. Aje
asibiti neman magani. Haka kuma zaka iya
neman taimakon magani daga gare mu. Allah
ya taimaka, Ameen.
Akwai wani irin nau'in basir na cikin ciki maisa
zawo da jini wanda wata cuta ke jazawa ta
daban, wato DYSENTERY a turance. Haka kuma akwai "Fitar-baya" wato RECTAL PROLAPSE za muyi
bayanai akansu insha Allahu anan gaba.
Thursday, 26 December 2013
AMFANIN ZOGALE GA JIKIN 'DAN ADAM
(Moringa oleifera) itaciya ce mai ban mamaki dangane
da amfaninta ga lafiyar 'dan adam. Allah
(S.W.T.) yasa albarka da waraka ga
wannan itaciya. Zogale abinci ne mai romon sinadaran lafiya a bayan kasa, baza'a iya kwatanta shiba da sauran ganyaye ta fuskar amfaninsa ga lafiyar 'dan adam. Wannan dalili yasa wasu ke kiransa da suna ITACIYAR RAYUWA ( The tree of life). Ganyen zogale na kunshe da romon
sinadari mai yawa na VITAMIN A (wanda ke
karama idanun 'dan adam lafiya da gani) fiye da
VITAMIN A dake cikin karas har sau 4. Ganyen
zogale haka kuma yana da sinadari mai yawa na
CALCIUM (mai sanya qashi da hakoran 'dan
adam kwari da lafiya) fiye da yawan na cikin madara linki 4. Yana da sinadarin
VITAMIN C (wanda ke karfafa garkuwar jikin 'dan adam domin fada da cututtuka masu kai farmaki ga lafiyar mutum),
yanada wannan sinadarin mai yawa fiye da irin
wannan sinadarin dake cikin lemu har linki 7.
Haka kuma yanada sinadarin PROTEIN (sinadari
mai gina jikin 'dan adam), fiye da na cikin madara sau 2. Bugu da qari, yana da VITAMIN E
(sinari mai gyara fata da lafiyar fata). Masana ilimin kimiyya da bincike akan wannan itaciyar lafiya sun bayyana cewa ZOGALE/ZOGALA nada wadannan magunguna:
-Yana daidaita sukari cikin jini.
-Yana rage hawan-jini
-Yana taimakama mace mai shayarwa da ruwan nono.
-Yana kashe kwayoyin cutar bakteriya (bacteria).
-Yana saukake narkewar abinci a ciki.
-Yana wanke ciki, musamman idan aka cishi kafin aci komai.
-Yana kare lafiyar hanta da koda.
-Yana taimakawa da kuzari ga jikin mutum.
-Yana rage kiba.
-Yana gyara kwalwa.
Da sauransu.
Friday, 15 November 2013
KALUBALE GA MA'AURATA - KASHI NA 4
Salam. A wannan karo zamuyi nazari akan
amfanin jima'i ga lafiyar ma'aurata. Hakika Allah
(S.W.A.) yasa albarka a cikin rayuwar aure. Toh
albishirinku ma'aurata da matasa masu shirin
zama anguna da amare. Aure nada muhimmanci
sosai ga rayuwar 'dan adam. Aure sunnar
Annabin muce (S.A.W.), ibadane, more
rayuwane, kwanciyar hankaline, mutumcin 'dan
adam da kuma kariya. Wadannan abubuwa da
muka zayyana akwai hanyoyin da akebi na
Musulunci domin a cimma nasarar samun su a
cikin aure, haka kuma bayanin kowanensu na
bukatar sharhi mai fadi na ilimi. Don haka sai
anemi bayanan malaman sunnah. Adaidai
wannan wurin, zamu takaita kan mu wajen
bayanai akan amfanin jima'i ga lafiya: ma'ana-
abunda zaka iya moruwa dashi na lafiya da
jima'i ke amfanarwa. Ko shakka babu, fahimtar
wannan mas'ala zai iya baka damar sanin
hanyar halas da zaka iya magance wasu
matsalolin lafiya ta hanyar saduwa da iyalinka.
Haka kuma, zaya sanya ka cikin mamaki da
fahimtar rahamar Allah madaukakin Sarki
akanka. Daga cikin wannan abubuwa da jima'i
ke maganinsu sun hada: rage hawan-jini (BP),
rage wahala, karfafa garkuwar jiki, gyara maniyyi
da sauransu.
1. RAGE HAWAN-JINI :
Abisa wasu bayanai masu inganci da muka
tattaro na wasu masana kimiyya, yin jima'i
tsakanin ma'aurata na taimakawa wajen rage
hawan-jini a lokacin da yake hauhawa.
2. HUCE WAHALA:
Idan maigida ya dawo aiki ya shawo wahalar
aikin ofis, ta kasuwa ko wata wahala mai wuyar
gaske kuma ya naso ya huta, toh sai yayi
wanka, yaci abinci, ya kuma sha ruwa ko lemu,
sa'annan ya sadu da iyalinsa. Ko shakka babu
zai samu wani irin hutu da bacci mai dadi da kuma
debe wahala. Jima'i na rage 'stress' da
'pressure' sosai.
3. KARFAFA GARKUWAR JIKI:
Binciken wasu masana kimiyya ya nuna cewa,
mutane (magidanta) masu yin jima'i akai-akai
sunfi yawan sinadarin "antibody" a cikin jikinsu
fiye da wanda basu yin jima'i kamar yawan
nasu. Shi dai wannan sinadari amfaninsa shine
kare jikin 'dan adam daga cututtuka (germs,
viruses and other intruders) masu kai farmaki a
cikin jiki su cutar da lafiya- wato garkuwane ga
jikin 'dan adam . Toh saidai yana da kyau
mutum ya yawaita cin abincin dazai kara masa
lafiyar jima'i kamar yanda muka bayyana a can
baya . Kuma mutum ya rinka hutawa don samun
cikakkiya lafiya da ni'ima.
4. GYARA MANIYYI:
Mutum mai saduwa da iyalinsa akai-akai, ilimi
ya nuna cewa maniyyinsa na kara inganci da
lafiya. Zaya samu sabon maniyyi ya zubda
tsohon maniyyi. Hakan zai iya taimakawa sosai
wajen saurin samun juna biyu ga iyalinsa. Haka
kuma, sabunta saduwa da uwargida na kara
mata sha'awa da ni'imar ruwa (vaginal
lubrication) domin saduwa da maigida cikin
sauki da santsi. Wannan rahotone daga wata
mai ilimi akan kiwon lafiya (Assistant clinical
professor of obstetrics and gynecology at
Northwestern University's Feinberg School of
Medicine in Chicago).
5. RAGE CIWO:
Jima'i na rage radadin ciwo kamar irin na ciwon
jiki ko na baya da sauransu. A lokacin da mutum
yayi inzali, jikinsa na samarda wani irin sinadari
(hormone oxytocin), wannan sinadari yana
taimakawa sosai wajen samarda wani sinadarin
kuma (endorphins) wanda keda tasiri kamar na
maganin "aspirin" da "panadol" (pain relievers)
masu rage zafin ciwo. Jima'i magani me mai
karfi na ciwo. Idan mutum yanaso ya gane
gaskiyar wannan zance, a lokacin da yake jin
wani ciwo a jikinsa, ya saurara yaji idan akwai
ciwon lokacin yake kawowa (inzali).
6. GYARA ZUCIYA:
Masana kimiyya sun bayyana jima'i a matsayin
wani nau'in motsa-jiki (exercise). Motsa jiki
nada muhimmanci sosai ga lafiyar mutum. Yana
gyara lafiyar zuciyar 'dan adam da kuma kare ta
daga cututtuka masu kai farmaki. Yana sanya
gudanar jini a zuciya da sauran jiki yanda ya
kamata domin samun cikakkiyar lafiya.
7. RAGE KIBA:
Yawan jima'i nasa rama. Kada mu manta da
cewa jima'i wani nau'i ne na motsa-jiki.Yana
kone sinadaran kuzari (calories) wanda
taruwarsu da yawa a jiki ba tare da amfani dasu
ba ke jaza kiba (weight gain). Jima'i na tsawon
rabin awa na kone/amfani da kimanin 75 ko 150 na
sinadarin. Anyi kiyasin cewa mutum na kone sinadarin
kimanin 129 yayinda yake tafiya a kasa tsawon
rabin awa.Yawan kiba nada illa sosai ga lafiya.
Yana haddasa ciwuka kamar na zuciya, ciwon
suga da ciwon kafafu ko gabbai. Toh masu kiba
ga wata dama ta samu - Jima'i hanyace ta rage
kiba.
8. GYARA FATA:
Fata tayi kyau da kala mai kyau mai alamun
lafiya.
9. GYARA MAFITSARA:
Yana gyara lafiyar mafitsarar mata domin rike
fitsari da sauransu dai mutakaita.
Wadannan bayanai da suka gabata basa yin
nuni cewa mutum ya yawaita yin jima'i da
iyalansa. Yawan yin jima'i na iya sanya mutum
ya tsotse ya kuma rasa wasu sinadarai masu
muhimmanci a jikinsa. Nemi Karin bayani daga
malaman addini da kuma likitoci akan a dadin
yawan jima'i da mutum yakamata ya rinka yi a
sati don cikakkiyar lafiya da ni'ima. To amma adadin
yawan a sati yasha bamban tsakanin mutane ta
fuskar shekarunsu, yanayin halittar su da kuma lafiyarsu
da kuma wasu sauran dalilan na daban.
Ku biyo mu a KALUBALE GA MA'AURATA –
KASHI NA 5 domin jin amsoshin wadannan
matsaloli kamar haka:
1. Shin ko girman al'aurar namiji nada alaka da
gamsasshen jima'i ga matarsa?
2. Shin tsawo ko kaurin mazakuta ne yafi
muhimmanci?
3. Minene tsayin ko kaurin da ake bukata ga
maigida, kuma yaya ake awonsu don mutum
yasan nashi?
4. Toh minene mafita ga wanda yake da kasa da
abunda ake bukata na tsawo ko kauri(gwabi)?
Friday, 2 August 2013
KALUBALE GA MA'AURATA - KASHI NA 3
Thursday, 1 August 2013
AMFANIN KANIMFARI GA LAFIYA
2. Za’a iya amfani dashi a matsayin abun wanke baki. Yana maganin warin baki (a tafashi a yawaita wanke baki dashi sau 2 ko 3 a rana).
3. Yana hana zubar hanci ga masu mura. A tafasashi da citta/jinja (ginger) a sha shayi.
4. Yana maganin cututtuka (infections caused by bacteria, fungi and virus ) na cikin jiki ko na bayan fata, kamar kuraje (spots and rashes), makero (ring worm) da kyanda (measles).
5. Yana maganin zawo da amai da zazzabin cizon sauro.
6. Yana saukake narkewar abinci a ciki.
7. Yana maganin ciwon kai. A shafa man kanimfari a goshi.Yana taimakawa wajen ciwon kai da mura kan jazawa.
8. Yana kara karfin mazakuta idan aka shafa mansa kadan ga mazakuta. Da sauransu.












