Monday 6 January 2014

ILLAR YAWAN CHOLESTEROL A JIKIN 'DAN ADAM

Cholesterol wani irin sinadari ne da jikin 'dan
adam ke amfani dashi domin gudanar da wasu
ayyukan lafiya a cikin jinin mutum. Wasu daga
cikin ayyukan cholesterol a cikin jini sune: 1.
Sauye-sauyen halittar 'dan adam yayin da yake
balaga da kuma sarrafa sha'awar sa. 2. Daidaita
sukari a cikin jini 3. Kare mutum daga daukar
wasu cututtuka (infection) 4. Samarda VITAMIN
D (sinadari maisa 'kwarin 'kashi da hakora) da
sauransu.

Hanta (liver) tana daga cikin ma'aikata ta
gangar jiki dake samar da CHOLESTEROL mai
yawa. Haka kuma abincin da mukeci wanda yake daga dabbobi na samar
dashi (DIETARY CHOLESTEROL).

Wannan
sinadari yafi yawa a cikin abincinmu karmar: kwai
('kwanduwa), hanta, butter, kifi,
nama, madara, mai , kaza da sauransu.

Duk da kasancewar wannan sinadari yana da amfani ga jikin 'dan adam, ba'a so yayi yawa cikin jini. Yawan cholesterol a cikin jinin mutum nada
hadari sosai, yana haddasa cututtukan zuciya.
Cholesterol dai sinadari ne mai danko kamar
kitse. Idan yayi yawa a cikin jini yana likewa a
hanyoyin jini dake daukar jini (artery) zuwa
zuciyar 'dan adam. Faruwar haka na iya
haddasa toshewar fayif din hanyoyin jinin
(plague/atherosclerosis). Idan haka yafaru, yana
jaza matsalolin zuciya kamar haka:

1. Hanyoyin dake kawo jini zuwa zuciya su toshe
(Coronary artery disease). Daga nan sai a samu
"heart attack" (zuciyar mutum ta samu dameji
ko mutum ya mutu).

2. Zuciya ta kasa harba jini zuwa sauran
hanyoyin jini na sauran jikin mutum (heart
failure).

SHAWARWARI

Mutum zai iya rage yawan cholesterol a cikin jininsa
ta hanyar:

1. Motsa jiki (exercise).
2. Cin 'yayan itatuwa da ganye (fruits &
vegetable).
3. Zaka iya amfani da magani domin rage
yawansa (amma da izinin likita ). Haka kuma
yanada kyau mutum yaje asibiti domin a duba
yawan cholesterol a jikin sa, domin yana karuwa yayin
da mutum yake manyanta. Allah yasa mudace.
Ameen.

Wannan hoto da kake gani a sama yana dauke
da bayanan abubuwa biyu kamar haka: Nafarko,
jini yana gudana a cikin fayif din jinin zuciya
(artery) lafiya lau batare da wata matsala ba. Na
biyu, yana nuna yanda cholesterol ya toshe fayif
din jinin (hanyar jini) zuwa zuciya. Cholesterol
shine mai kalar 'dorowa.