Sunday 17 February 2019

DALILAI 12 DAKA IYASA MUTUM GANIN JUWA/JIRI DA MAGANI


Ji ko ganin juwa alamace cewa jikinka  na maka magana wacce ba zaka iya ganewa ba, wato jikinka na gaya maka cewa akwai abinda ke damunsa wanda  likita ne kaɗai  zai iya fahimtar maganar domin kuwa kunnuwanka ba zasu iya gane zancen da juwa ke raɗawa likita ba.  Idan ka biyo mu a wannan rubutun da kake karantawa zamu baka aron kunnuwan likita da zaka iya fahimtar zancen da juwa ke raɗawa  likita game da lafiyarka.
---
Juwa ko jiri (dizziness/disequilibrium) , wani yanayi ne marar daɗi wanda mutum ke jin kansa na juyawa zai faɗi saboda ganin sararin da yake zagaye dashi yana juyawa,  wanda hakan nasa  rangaji kamar na maye, koma mutum ya suma ko  ya faɗi,  ko jin kamar mutum yana tashi sama. Idan juwa tana ɗibar mutum yakan ga duniyar da yake a ciki tana jujjuyawa , wanda hakan ba gaskiya bane a zahiri; ƙwalwarsa da idanunsa ne kawai suke yi masa dabo. Juwa ba cuta bace ita karan kanta, saidai wata alama ce da zata iya nunawa mutum wata matsala ko wasu nau'in matsalolin lafiya da mutum yake fuskanta ko shirin fuskanta.
---
Wasu daga cikin dalilan rashin lafiya daka iya haddasa ganin juwa ga mutum sun haɗa da:
---
1. Rashin jini
2. Saukar hawan jini kwatsam (drop in systolic blood pressure)
3. Matsalar zuciya
4. Ƙarancin suga a cikin jini , musamman ga masu ciwon suga.
5. Ciwon kunne
6. Rashin isasshen ruwan-jiki, musamman cikin zafi idan mutum baya shan ruwa isashshe
7. Yawan motsa jiki
8. Wahala ko yunwa matsananciya
9. Nau'in wasu magunguna da mutum ke sha, musamman na ciwon-damuwa da kwantar da hankali.
10. Ciwon kai maisa rashin gani da kyau (migraine).
11. Tsufa da magungunan da tsofi ke sha zasu iya saka ganin juwa
12. Matsalar tsoro da fargaba , da sauran wasu matsalolin da bamu ambata ba.
---
MAGANCE MATSALAR JUWA/JIRI
---
Magance juwa ya danganta da abinda ya haddasa juwar; misali, idan  yunwa ce ke cizonka to cin abinci zai kore ta, idan kuma rashin shan ruwa ne ko wahala to shan  isashshen kofin ruwa akai-akai da hutu mai yawa ya isa  yasa juwa ta rabu da ƙwalwarka data ke matsamawa. Idan kuwa matsalolin lafiya ne kamar na ciwon zuciya ko hawan jini, ciwon kunne ko ƙarancin jini to likita ne zai iya cecenka daga juwa, ta hanyar baka magani , shawarwari  koma ledar jini da za'a jona maka tiyo nata zuwa jikinka domin kashe jiniyar da juwa ke maka cewa baka da isashshen jini a jiki , domin kashe gobarar rashin lafiyarka. Duk wannan  zai faru ne bayan an gano dalilin juwar wanda  aikin likitane da wasu ma'aikatan lafiya. To dai mu taƙaita, ga wasu abubuwa wanda zasu iya magance matsalar juwa:
---
- Shan ruwa mai yawa , musamman a ranar
- Shan citta (ginger), musamman citta ɗanya ko busassa a shayi (tea) ko abinsha (drink), safe da dare koma sau 3 a rana
- Samun isashshen hutu da barci
- Shan lemun zaƙi da yawa ko lemun tsami a shayi
- Cin ganyen alayyahu a abinci
- Cin naman kaza, kifi da gyada
- Shan zobo a shayi ko abin sha , cin ganye, jan-nama, wake, naman kaji, musamman idan rashin jini ne dalilin juwar
- Ganin likita a asibiti ko ƙwararren mai maganin gargajiya

Call +2348084028794
madinahislamicmed@gmail.com
www.madinahislamicmed.blogspot.com