Tuesday 27 March 2018

ƘARIN GIRMAN MAMA (BREAST ENLARGEMENT)

Mata da yawa na ganin ƙirjin mace  kimar ɗiya mace ne  kuma abin tinƙaho ne ga mace da jan hankali ga maza da kuma birgewa. Don haka  mata da yawa sun ɗauki gyaran mama wani muhimmin  abu, musamman bayan shayarwa ko faɗuwar nonuwan budurwa  a gida ko rashin girman sa.

Girman mama an alaƙanta shi  daga cikin abubuwa  wanda ke sa mace a ganta mai kyakkyawar halitta da ban sha'awa da birgewa ga maza kasancewar maza mafi yawa na son mata masu wannan yanayi.  Wannan lamari nada tasiri sosai ga tunanin mata da yawa,  ta yanda wasu ke jin alfaharinsu da tinƙaho  zai faɗi idan maman su ya faɗi ko suka bari ya canza daga sigar da ake bege. Shi dai nono wani dandazo ko cincirundon tsokar nama ne mai zagaye da kitse daya taso sama a ƙirjin mace baliga. Tsokokin suna canzawa lokacin balaga, haila, juna-biyu da lokacin shayarwa, da kuma lokacin barin al'adar mace (menopause). Waɗannan tsokoki kuma zasu iya buɗewa su ƙara girma saboda wasu magunguna ko tsirran magani.

Mata da yawa ne ke neman magani a kasuwanni domin gyaran mama kuma hanyoyin gyaran maman da ake bi suna da yawa amma amma a zahiri ingancinsu kaɗan ne, wanda sun hada da: ƙwayoyin magani, man shafawa, famfon iska na ƙara girman mama (breast pump), gari , ofireshin/tiyata (surgery)domin ƙara girman nono da sauransu . Wasu hanyoyin nada hadari ga lafiya, kuma sakamakon amfani da magungunan ko hanyoyin ya sha banban tsakanin mata masu ta'ammuli da magungunan, inda wasu sun sami nasarar  ƙara girman mamansu wasu kuma babu wani canji.

Anyi gargadi akan amfani da kayan turawa na kemikal (chemicals) wanda zasu iya haddasa cutar sankarar mama (ciwon daji/cancer), musamman man shafawa na turawa. Domin rage haɗarin dake tattare da yin amfani da magunguna barkatai wanda da zasu iya haddasa illa ga lafiya, MADINAH ISLAMIC MEDICINE mun yanke shawarar bayyana sirrin wasu daga cikin hanyoyi masu inganci kuma marar haɗari da mace zata iya  ƙara GIRMAN NONO ko CIKOWAR NONO idan ya kwanta. Bugu da ƙari, hanyoyin na  bada kariya daga cutar sankaran nono (breast cancer) kasancewar abubuwanda da za'a yi amfani dasu daga tsirrai ne na ɗabia (nature/natural). Abubuwan da za'a nema a ISLAMIC CHEMIST domin ayi amfani dasu sune:

1. HULBA (Fenugreek) da man ta (oil).
2. SHAMMAR (Fennel seeds)

Mai yiwuwa kin taɓa amfani da HULBA, kuma da kika ga hulba cikin abubuwa 2 da muka bayyana kya ce "Hmm. Ai nasan hulba , na jarraba amma shiru ne." Idan kina daga cikin masu irin wannan tunanin to akwai yiwuwar cewa baki yi amfani da hulba ba na tsawon lokaci kullum ko kuma baki yi amfani da ita ba yanda ya dace. Domin kuwa bincike ya tabbatar da tasirin yin amfani da hulba a halittar nonan mace. Hulba na sanya fata da tsokar dake zagaye da nonon mace su buɗe kuma nono ya ciko ɓulɓul  , musamman nonuwa wanda suna da girma amma ba'a miƙe suke ba, sun baje ko sun kwanta. Cikar nonuwan zaisa su miƙe su domin cika ƙirji da siga mai kyau.

SHAMMAR (fennel seeds) kuwa , shima ƴaƴan wani tsiron shuka ne masu kamar ƴaƴan  alkama ko shinkafa wacce ba'a cire ɓawon ba.

YANDA ZA'AI AMFANI DASU
A sami ƴaƴan hulba da  ƴaƴan shammar a Islamic Chemist  sai a niƙe su , a dake su sosai amma kowanne  daban-daban. Haka kuma za'a iya samun garin nasu a Islamic Chemist ba sai an sha wahalar daka ba. Sai a ɗibi cikin ƙaramin cokalin shayi na garin hulbar guda (1 teaspoon) a zuba a kofi , sa'annan a ɗibi garin  shammar ɗin shima cikin ƙaramin cokali guda a haɗe su a kofi ɗaya ( hulba + shammar). Sai a tafasa ruwan zafi idan ya tafasa sai zuba cikin kofin maganin a motsa da cokali sosai a sa'annan a rufe bakin kofin. Idan yayi minti 10 arufe - ya jiƙa sai a tace da rariya a zuba zuma ga ruwan da aka tace asha. Sa'annan a shafa man hulba ga mama safe da dare. Ashafa man a linda/luliya (massage)  ya shiga fatar nono sosai.  Za'a yi hakan (yin shayi da shafa man hulba) sau biyu (2) a rana - safe da dare har na tsawon wata daya. Za'a ga cikakken sakamako bayan wannan lokaci da yardar Allah. Daga zuwa wannan lokaci ko kafin lokacin mace zata fara jin nonuwanta sun kara nauyi, wanda alamace na girma da suke karawa. Kara girman nono ba abu bane dake faruwa cikin dare daya kamar yanda wasu ke tunani. Don haka akwai bukatar hakuri kamin aga sakamakon da ake bukata.

Man hulba yana da amfani idan aka jure ana amfani dashi.  Yana da amfani 2: Na farko, yana sanya gudanar jini da kyau wajen nono wanda zai taimaka wajen inganta lafiyar nono da kyawon fatar nono. Na biyu, yana buɗe tsokokin nono yanda zasu ƙara girma da ƙarfin fata (firming)  mai riƙe nono tsaye ba mai yawan taushi ba  wanda kesa mai sanya mama ya sunkuya saboda yawan taushi. A nemi man hulba ɗan Misra ko Hemani (Pakistani). Allah Ya taimaka.

Wadannan bayanan cikin harshen Hausa da muka wallafa a sama, na cibiyar MADINAH ISLAMIC MEDICINE (CAC :KT2557) dake Jihar Katsina, Nigeria.
Office Address: No. 34. Sabuwar Unguwa Dandagoro, Katsina, Jihar Katsina.

Www.madinahislamicmed.blogspot.com
Email: madinahislamicmed@gmail.com
Phone no.: +2348084028794 (kuma WhatsApp no.)



Friday 23 March 2018

YAWAN WASA-DA -AL'AURA DA ILLARSA GA ƘWALWAR MATASA : YAWAN MANTUWA



A ɗabi'ance  , a lokacinda mutum yakai shekara 30 da haihuwa kwalwarsa zata fara samun ja baya , ci bayan zai fara gudu a lokacinda mutum ya kai shekara 50. To amma a wannan zamanin ga alama cibayan zai iya zuwa da wuri kafin shekarun tsufan  samari yazo. Ko minene yasa haka? Amsar itace, "Zinar hannu" , wato wasa-da-al'aura (istimna'i) da ya zama ruwan dare bainar matasa, musamman saboda wayar salula da ake ƴada hotunan batsa da video wanda ke jefa matasa cikin matsananciyar sha'awa da aikata wasa da al'aura koma abu mafi muni zinace-zinace.

KO MINENE ALAƘAR ISTIMNA'I DA YAWAN MANTUWAR MATASA?

Kafin mu amsa wannan tambayar yana da kyau mu yi bayanin abinda ake cewa "Istimna'i" ko "wasa-da-al'aura".Wasa-da-al'aura dai ko wasa da gaba (Istimna'i [masturbation]) na nufin yin amfani da hannu, yatsa ko wani abu domin biyan bukatar jima'i ga mutum da kansa da tunanin saduwa da wata mace ko wani namiji , ga mace. Ana kiran wannan ɗabi'a "zinar hannu". Istimna'i dabi'a ce da take faruwa da yaduwa cikin mutane da dama - yara matasa, da manya mutane, musamman cikin matasa mararsa aure ko wanda aurensu ya mutu, koma rashin gamsuwar aure. Yawan aikata istimna'i (excessive masturbation/over-masturbation) na da illa ga lafiya sosai. Kuma idan ya zama ɗabi'ar mutum koda yaushe to yafi zama matsala ga lafiya da wuyar bari (addiction) wanda hakan zai jefa mutum cikin wani ƙalubalen lafiya mai muni.

To tunda mun fahimci ko minene istimna'i , bari mu koma ga tambayar mu ta farko,  minene alaƙar istimna'i da yawan mantuwa wacce kesa dusashewar ƙwalwar matasa,  rashin riƙe karatu tun kafin tsufa yazo musu? Domin amsa wannan tambaya,  bari mu shiga jikin mutum mu ga abinda ke faruwa  kimiyyance kamar yanda masana suka yi bayani : A duk lokacinda jikin mutum ya fitar da maniyyi da yawa jikin na rasa wasu muhimman sinadarai (neurochemicals/acetylcholine) wanda ke kai saƙo ga kwalwa mutum , kuma su waɗannan sinadaran lafiya suna taimakawa wajen nazari, maida hankali da riƙe wani abu ko karatu a ƙwalwa. Mutumin da yake yawan yin istimna'i jikinsa na samun ƙarancin sinadaran. Sinadarin " acetylcholine" da wasu sinadaran gina jiki (proteins) suna raguwa. Ƙarancin sinadarin (acetylcholine) na sanya ƙwalwa rauni da mantuwa (memory loss/forgetfulness). Bugu da ƙari, ƙarancin na sanya yawan kasalar jiki, da rashin gani da kyau , wato gani buji-buji (blurry vision),  ko ciwon baya (back pain) da zubar gashi (hair loss). Matsalolin lafiya da yawan istimna'i yake haddasawa suna da yawa.

Mutane sunfi yawan alaƙanta yawan mantuwa da tsufa , wato ana ganin tsofaffi keda yawan mantuwa ba yara ba , to amma abin mamaki shine " Ana zaton wuta a maƙera amma sai gata a masaƙa". Yanzu ana samun matasa da yawan mantuwa , rashin hazaƙar ƙwalwa ko maida hankali wanda ke sanyasu wuyar karatun Islamiyya da na Boko. Don haka, yawan istimna'i na na shafar bangaren kwalwa mai kula da ajiye bayanai (hippocampus) daga ma'ajiya ta kusa zuwa ta nesa, da kula da karatu ko maida hankali. Akwai dalilan lafiya na daban da dama wanda zasu iya sanya yawan mantuwa ko ciwon mantuwa (dimentia), kamar haɗari da ya shafi ƙwalwa, gado ko wata cuta. To saidai mantuwar da istimna'i ke haddasawa matasa na daga cikin ɓoyayyun dalilan matsalar mantuwar matasa a wannan zamani.
Wasu illolin da istimna'i zai iya haddasawa  na daban wadanda basu shafi mantuwa ba sun hada:
kankancewar zakari da maraina, saurin kawowa ko rashin karfin mazakuta. Sauran matsalolin dazai iya haddasawa , sun hada da: ramar jiki ko 'karancin sha'awa, karancin maniyyi ko tsinkewar maniyyi da raguwar ingancinsa (wanda na iya haddasa rashin haifuwa) , raunin jiki, raunin garkuwar jiki, jin ciwon kai akai-akai, ciwon baya, fitar maniyyi daga zakari hakanan ba tare da mutum yayi niyya ba - ba tare da yayi istimna'i ba ko yayi jima'i, haka nan kawai.
Wasu illololin da zasu iya faruwa saboda istimna'i: bushewar fatar kan zakari ko illa ga fatar saboda gugar fatar da hannu, karkacewar zakari (penis curvature) ko sauya masa sigarsa ta asali, bugawar zuciya da sauri kurajen fuska.da sauransu.

ILLAR ISTIMNA'I GA MACE

Mace zata iya samun wasu daga cikin matsalolin da mu kayi bayani a sama. Wasu matsalolin daka iya shafar mace sune: Rashin rike fitsari da kyau (ga mace) koYawan zuwa fitsari saboda saka wani abu cikin farji lokacin istimna'i, wuyar kawowa ga mace wajen jima'i (dalilin koyama jikinta da sai an taɓa wani sashen farji don ta kawo, wanda mai yiwuwa ne zakari baya taɓa wurin lokacin saduwa - a zahirin jima'i. Don haka istimna'i yana sa rashin gamsuwar jima'i ga mace - mijinta zai sha wahala wajen gamsar da ita. Jikinta ya riga ya koya, tayima kanta horo. Dalilin haka, mace zata ji dadin istimna'i fiye da jima'i , hakan kuma zai zamo mata matsala idan tayi aure. Zata ringa tunanin mijinta baya iya gamsar da ita ko mazaje data aura, saboda sabon da tayi da koyama jikinta hanyar gamsar da kanta fiye da hanyar da ta dace, wato jima'i a cikin sunnar aure. Ta canza dabi'ar ta. Da yawa zaka samu cewa mata masu yawan istimna'i basu jin daɗin jima'i sai istimna'i, koma basu gamsuwa sai sunyi istimna'i a bandaki bayan saduwa da mazajen aurensu. Wannan zai iya kawo babbar matsala a cikin aure. Bugu da kari, dadilan rashin gamsuwar mace wajen saduwa da mijinta suna da yawa. Don haka, bazamu iya cewa ba yin istimna'i kafin aure shine dalilin dake hana gamsuwa kadai ba. Akwai wasu dalilan na daban, wasu matsalolin nada alaka da bangaren mazajen.

Domin neman karin bayani cikakke akan illolin  yawan istimna'i ga lafiya da hanyoyin barinsa da kariya  sai a shiga wannan link kai tsaye (latsa) ko a kofa a liƙa a Google domin ayi searching:

http://madinahislamicmed.blogspot.com.ng/2016/11/wasa-da-alaura-da-illarsa.html?m=1

Ko a shiga Facebook (latsa LINK karanta) :

https://m.facebook.com/MadinahIslamicMedicine/photos/a.623324837696435.1073741826.621757857853133/1806983335997240/?type=3

Ko azo neman magani a Office Branch namu mai address kamar haka:
No. 34 Sabuwar Unguwa Dandagoro, Katsina, Jihar Katsina.
Kira: +2348084028794 (WhatsApp number)
E-mail: madinahislamicmed@gmail.com

Wednesday 21 March 2018

SAURIN INZALI DA MAGANI


Biyan bukatar namiji da mace wajen jima'i yasha banban ta fuskar tsawon lokaci. Kashi 68 cikin 100 na mata suna bukatar minti 8 su biya bukatarsu da mazajensu, haka kuma, kashi 45 na wasu matan na bukatar minti 12 yayin saduwa. Abin mamaki shine, kashi 75 na  maza na kasa jurewa su tsawaita lokacin biyan bukatarsu zuwa minti 3 ko 6, sabanin lokacinda wasu matan ke bukata don biyan bukatarsu. (Qinghai Province Xining City Ailida Biotechnology Company, 2012).

Saurin inzali ko kawowa (القذف المبك/Premature Ejaculation) yanayi ne da namiji yake saurin biyan bukatar  jima'i da zaran zakari ya shiga farji cikin 'yan daƙiƙoƙi ko mintuna kaɗan koma kafin shigar zakari cikin farji kasancewar namijin baya iya tsawaita lokaci ko jure dadin jima'in da yake ji na tsawon wani lokaci, musamman saboda matsannanciyar sha'awa ko kamuwa da yawa. Saurin inzali na faruwa ba tare da mutum yayi wata niyyar yin hakan ba. Jima'i a wannan yanayi na  karewa da zaran maniyyi ya fita daga jikin namiji. A wannan yanayi namijin baya iya yiwa sha'awarsa linzami ta fuskar rage sauri domin more jima'i na tsawon wani lokaci kuma baya iya gamsar da iyalinsa wacce saurin inzalisa ke hanata biyan bukatarta  , ko haddasa rashin gamsuwarta. Kasancewar mata na bukatar lokaci mai tsayi fiye da na maza mafi yawan lokutta.

Shekaru da dabaru na yau da kullum saboda fahimtar jima'i tsawon lokaci a rayuwa  nasa maza su fahimci yanda zasu magance matsalarsu da kansu ba tare da wani magani ba wani lokacin.

ABUBUWANDA KE HADDASA SAURIN INZALI / KAWOWA

Haryanzu dai babu wani sahihin bayani ko dalili dake bayyana dalilin saurin kawowa ba, saidai wasu bayanai akan dalilan da ka iya bada haske gameda matsalar saurin kawowa ga maza (premature ejaculation). Sune kamar haka:

1. Matsalar rashin karfin mazakuta  (erectile dysfunction). Idan namiji baya da karfin gaba to akwai yiwuwar asami saurin kawowa lokacin jima'i , haka kuma,  idan akwai karfin zakari to akwai yiwuwar dadewar yin jima'i mai tsawo tsakaninin ma'aurata biyu. Saboda haka,  saurin inzali na iya zama wani lokacin alama ce ta rashin karfin zakari.

2. Yanayin halittar wasu mazajen. Wani haka Allah Ya halicce sa ko minti 1 baya iya yi da mace. Amma wannan baya nufin baza'a iya samun saukin yanayin ba. Za'a iya neman magani ko Allah Yasa a dace.

3. Samuwar hadari (accident) wanda zai iya shafar al'aurar mutum. Hadari wanda ya shafi lafiyar al'aura  na iya haddasa matsalar saurin kawowa.

4. Magungunan kayan mata/da'a da  mata keyi. Magunguna na matsi da mata ke sakawa cikin gaba domin matse/tsuke farji.  Idan mace tayi amfani da wani magani  gabanta ya tsuke/matse fiye da yanda maigidanta ya saba jinta zai iya sa maigidan yayi saurin kawowa saboda karuwar dadi ko dandanon jima'i.

5. Cututtuka masu shafar lafiyar jima'i, kamar cututtukan sanyin mara na maza da mata.

6. Ciwon damuwa ko fargaba na iya  haddasa saurin inzali. Misali, idan mutum yayi sabuwar amarya budurwa ko bazawara  , idan yana fargabar ko zai iya gamsar da ita ko damuwa akan wani abu, wannan tunani zai iya sanya saurin inzali a cikin saduwar su.

7.  Yin istimina'i da gaggawa ( quick masturbation) da wasu matasa keyi kamin  suyi aure, musamman yara don gudun kada a kamasu (wasa da al'aura ko zinar hannu). Yana shafar lafiyarsu, yana haddasa saurin kawowa lokacin jima'i.

8. Gado daga wajen mahaifan mutum (inherited traits). Akwai yiwuwar mutum yayi gadon saurin kawowa  daga mahaifinsa ko kakansa ko wani jininsa, wato tsatstsonsa. Wato haka duk "family" nasu suke amma bai sani ba.

9.  Matsananciyar sha'awar yin jima'i. Idan mutum ya kosa  yayi jima'i , fitinar sha'awarsa ko kamuwa da yawa zata iya sanya shi yayi saurin kawowa da zaran zakarinsa ya shiga jikin mace  ba tare da bata wani lokaci ba.

10. Rashin wasanni tsakanin ma'aurata kafin saduwa ta yanda macen zata iya fara biyan bukatar ta da wuri kafin maigida ya fara jima'i da ita ta gaba da gaba .

11. Sauyin abokiyar saduwa/ sabuwar amarya budurwa ko zawara. Yanayin sabuwar abokiyar rayuwa, wato sabuwar amarya ga maigida  nada tasiri ga kwalwar namiji, yana sanya namiji ya rikice ko ɗimauce da ɗauki wanda hakan zai sanya shi saurin kawowa. Bugu da kari, Binciken ilimi na kiyimiyya ya nuna cewa samun sabuwar abokiyar saduwa (mata)  na sanya maniyyin namiji inganci da kyau fiye da nada.

14. Canza salon kwanciyar aure, musamman mutum kada yayi kwanciya da iyalinsa wacce zata sa zakarinsa ya shige duka cikin gaban ta. Nutso (deep penetration) nasa saurin inzali.

13. Nau'in wasu magungunan. Akwai wasu magungunan da "side effects" nasu zai iya haddasa saurin kawowa ga mutum. Da sauransu, mu takaita haka.

MAGANCE MATSALAR SAURIN
KAWOWA

Hanyoyin magance saurin inzali suna da yawa , wasu hanyoyin na yiwa wasu aiki, wasu kuma sabanin haka , don haka ga hanyoyi kamar haka da mutum zai iya jarrabawa domin neman dacewa:

a) Rage ƙosawa/ƙagara. Mai saurin inzali ya kamata ya cire tunanin jima'i daga ƙwalwarsa a lokacinda yake saduwa da iyalinsa. Matsanancin tunani ko kamuwa da yawa kafin fara jima'i  zai iya sanya mutum "ya ƙone tun kafin ya tafasa". Masana sun nuna cewa bujiro tunanin wani abu a cikin rai wanda ba jima'i ba marar daɗi a lokacin saduwa na ƙarawa mutum tsawon lokaci ba tare da ya lura da hakan ba. Ɗaukin jima'i baya biya, abinda zai taimakawa mai matsalar saurin kawowa shine, rage yawan tunanin jima'i ne yake aikatawa,  ko kuma ya bar yin tunanin cewa yana yin jima'i ne domin samun gamsuwa wacce  iyalinsa da yake sha'awa take biya masa. Kamata yayi  tunaninsa ya kasance cewa yana aikata jima'i ne domin ya biyawa iyalinsa bukata farko kamin tasa. Abin lura, ka ɗauka ma cewa ba jima'i bane kake yi a lokacinda kake tarawa da iyalinka.

b) A nemi kuɓewa ɗanya (okra) guda 5, a wanke sa'annan a yanke gutsun-gutsun a cikin tukunya, sai a sami kofi ɗaya na ruwa a zuba cikin tukunyar sa'annan a ɗaura akan wuta a rufe tukunya. Da zaran ruwan ya tafasa sai a sauke tukunya a tashe ruwan a kofin shayi , sai a zuba zuma  ta bada ɗanɗano , a bari ya huce kaɗan amma asha da ɗumi. Ayi haka sau 2 a rana har na tsawon kwana 10 ko fiye da haka. Kubewa nada sinadari mai amfani mai sanya jinkirin kawowa ga maza.

c) A nemi citta (ginger) musamman ɗanya, a wanke a kuma  karkare ta , sa'annan a dake ta , ayi shayi da ita , bayan an tashe ta a kofin shayi sai a zuba zuma ta bada ɗanɗano asha shayin da ɗumi. Ayi hakan safe da rana. Citta nada sinadari mai zafi na  "gingerol" mai sanya yawan gudanar jini ga laura , wanda hakan na sanya ƙarfin gaba da jinkirin kawowa.

d) A nemi man na'a-na'a (peppermint oil) mai kyau, musammman ɗan Misra ko na kamfanin Hemani (Pakistan) . A wanke gaba da ruwan dumi , a goge lemar sa'annan a shafa man ga  zakari ya shiga fata, ga kai (glans) da tsawon sandar zakari (shaft) , amma banda kofar fitsari (urethra). Musamman a shafa idan zakari yana mike,  sai  jira bayan minti 10 zuwa 15 sa'annan a sadu da iyali. Man na'a-na'a na rage "sensitivity" na zakari , wato rage kaifin ɗanɗano da zakari keji ta yanda zai hana saurin kawowa lokacin jima'i. Haka kuma za'a iya amfani da man kanimfari (clove oil) mai kyau a maimakon man na'a-na'a. Bugu da kari, man kanimfari na maganin karfin gaba.

e) Fita daga gaban mace na 'yan mintoci a lokacinda mutum yaji ya kusa kawowa, da kuma fita daga cikin farji da matse kan zakari da hannu (squeeze and pause technique/penis grip) a lokacinda mutum yake akan hanyar kawowa.

f) Bayan kawowar farko, kawowa ta biyu na zuwa da lokaci mai tsawo kafin mutum ya sake fitar da wani maniyyin a karo na biyu. Don haka idan mutum yana son  ya daɗe bai yi inzali ba to ya tari  jima'i a karo na biyu wanda zai bashi lokaci mai tsawo kafin yayi inzali.

g) Hanyoyin neman magani na musamman daga Likitan asibiti ko Malamin Islamic Chemist. Idan hanyoyin da muka zayyana basu yiwa mutum ba to sai yabi hanyar ganin ɗaya daga cikin wadannan mutanen domin neman taimako. Akwai wasu hanyoyi da dama na magance matsalar saurin inzali.

Wadannan bayanan cikin harshen Hausa da muka wallafa a sama, na cibiyar MADINAH ISLAMIC MEDICINE (CAC :KT2557) dake Jihar Katsina, Nigeria.

Office Address: No. 34. Sabuwar Unguwa Dandagoro, Katsina, Jihar Katsina.

Www.madinahislamicmed.blogspot.com

Email: madinahislamicmed@gmail.com

Phone no.: +2348084028794 (kuma WhatsApp no.)

Wednesday 7 March 2018

Amfanin Babunaj [بابونج/Chamomile] Ga Lafiya


Albabunaj/Babunaj  ganye ne da furen wata shuka mai albarka. Ana amfani dashi a matsayin maganin gargajiya. Furen Albabunaj magani ne daya shahara musamman wajen yin shayi dashi a kasashe da al'adu a duniya. A  America ya kasance shine fitattaccen abin yin shayi . Bincike da nszarin kimiyya ya nuna cewa yana da matukar amfani ga lafiya , kuma yin amfani dashi baya da wani cikas ga lafiya. Ana samun busasshen gari Albabunaj da kuma busasshen  fure nasa a Islamic Chemists a Nigeria. Ana kuma samun  mai nasa, amma a nemi mai kyau, musamman 'dan misra. Ga wasu daga cikin amfaninsa ga lafiya:

1. Yana inganta bacci da maganin rashin bacci . A dibi cikin cokalin shayi 1 [teaspoon] a tafasa ayi shayi dashi marar madara.  Ayi hakan safe da dare. Za'a iya kuma amfani da zuma, yana da kyau hakan.

2. Maganin mura (shima shayi za'ayi).

3. Yana maganin ciwon mara lokacin al'ada (shayi).

4. Maganin ciwon ciki (shayi).

5. Maganin huce wahala ko gajiyar kwalwa da damuwa (shayi dai,  malam ko malama). Za'a iya hadashi da kanimfari  ayi shayi.

6. Gyara fata da haske (shayi dai har yanzu).

7. Yana kashe kwayoyin cutar bakteriya da karfafa garkuwar jiki (shayi).

8. Yana maganin ciwon jiki - ciwon naman jiki (shayi).

9. Yana maganin kurajen fuska , da rage tabon kurajen (shayi).

10. Yana maganin amosanin kai [dandruff] - rabuwa dashi. A wanke kai da ruwansa  bayan an tafasa albabunaj an tace (wanke kai ba shayi ba).Sa'annan yana da kyau ayi amfani da man albabunaj ko man kwakwa bayan wanke kai - a shafa aka.

11. Yana rage saurin zufan jiki da fata (shayi).

12. Yana maganin bacin ciki ko rikicewar ciki.

13. Rage laulayin mai ciki da korar aljani daga jiki . Wannan bayani da amfanin an cirota sa ne daga likitancin Islamic Chemist.To saidai babu wani bayani a kimiyyance da ya nuna cewa Albabunaj baya da hadari ko cutarwa ga mai ciki. Don haka sai a nemi bayanan lafiya masu inganci kamin mai ciki tayi amfani dashi.  Masu ciki su guji shan wani magani idan bada izinin likita.

14.. Yana taimakawa masu ciwon suga - daidaita sukari cikin jini. (Shayi amma banda zuma fa, to kunji).

15.  Amfanin da yawa fa. To anan zamu sa aya dai.

Wannan bayanan cikin harshen Hausa da wallafa , na cibiyar MADINAH ISLAMIC MEDICINE (CAC :KT2557) dake Jazar Katsina, Nigeria.
Office Address: No. 34. Sabuwar Unguwa Dandagoro, Katsina, Jihar Katsina.
Www.madinahislamicmed.blogspot.com
Email: madinahislamicmed@gmail.com
Phone no.: +2348084028794 (Also WhatsApp no.)
Facebook: https://m.facebook.com/MadinahIslamicMedicine