Thursday 20 February 2014

Fitaccen Maganin Gargajiya na Kasar Sin - Ginseng

Ginseng da yaren turanci ko Rénshēn (人参/人蔘) a yaren Kasar Sin (Chana) , wata irin nau'in shukace mai ganye launin kore da jijiyoyi (sauyoyi) masu tsoka shigen irin na citta a yanayi da launi. Shukace mai tasawa ahankali-ahankali yayinda take girma. Ita wannan shuka ana samun tane kawai a yankin Amerika-ta-Arewa (North America) da yankin Asiya-ta-Gabas (Eastern Asia), kamar irinsu Koriya, Chana ta Arewa-Maso-Gabas, da sauransu. Haka kuma, shukar tana rayuwa ne a yanayin mai sanyi. Kuma tana da nau'i na daban-daban.

Ita kalmar "Ginseng" (furucin kamar haka /'Jinsen/) ta samu ne asali daga kalmar "rénshēn" wanda a yaren Chananci "ren" na nufin "mutum". Gudan kuma bangaren kalmar "shen" na nufin "jijiyoyi ko sauyoyin shuka" ta yanda idan ka hada kalmomin biyu zaka hararo wannan ma'anar, wato "jijiya mai yatsu wacce take kama da kafafuwan mutum." Ginseng sinadari ne da wadannan kasashe suke amfani dashi a matsayin maganin gargajiya tsawon lokaci mai yawa a tarihi , har izuwa yanzu. Akwai wannan sinadari a kasuwanni kuma ana sarrafashi ta hanyoyi daban-daban na zamani, kamar gari, lifton, abun-sha, kofee, sirof, kwayar-magani, da wasu amfanin. Ginseng na daya daga cikin magungunan gargajiya da akafi siya a duniya. Ana fitar dashi zuwa kasashen duniya da dama, wanda harda Najeriya.Ginseng nada tarihi mai-tsawo na amfaninsa wanda tun daga lokacinda aka fara rubuta amfaninsa (farko) a wani kundi lokacin daular "Liang" (Liang Dynasty 220-587 AD) har izuwa yanzu. Abisa wasu bimcike-binciken kimiyya na zamani, sinadarin Ginseng nada amfani sosai ga lafiya ,

kamar haka: 1. Yana sanya kuzari da hana kasala. Mutane da dama sunyi imani da hakan, kuma suna amfani dashi domin biyan wannan bukata.

2. Yana gyara kwalwa domin rike karatu da kuma kyautata hazaqa.

3. Yana qara ruwan-jikin 'dan adam, kamar irin na maniyyi (maza da mata).

4. Yana bayarda rigakafi daga kamuwa da ciwon-daji (kansa), da yardar Allah.

5. Yana taimakawa wajen magance matsalar rashin karfin-maza.

6. Yana maganin ciwon-jiki.

7. Yana qarfafa garkuwar-jiki.

8. Yana rage suga dake cikin jini da yawan sinadarin kolestorol dake cikin jinin.

9. Yana gyara jini da hana saurin tsufan jikin 'dan adam, idan Allah yaso. Yana gyara jiki da

quruciya. Sai a kiyayi cin haram don rayuwa tayi kyau, mutuwa kuma dole ce. Allah yasa mu dace.

10. Da sauransu.

Muna sayarda wannan sinadari a irin sifofin da muka zayyana ana sarrafashi da kuma samar dashi. Mai bukata sai yazo ya siya, a kuma  shawarci likita akan yanda ya kamata ayi amfani dashi.   Allah ya taimaka.

Medical Disclaimer: I am just a researcher & a herbal practitioner not a professional medical  doctor.