Salam. A wannan karo zamuyi nazari akan
amfanin jima'i ga lafiyar ma'aurata. Hakika Allah
(S.W.A.) yasa albarka a cikin rayuwar aure. Toh
albishirinku ma'aurata da matasa masu shirin
zama anguna da amare. Aure nada muhimmanci
sosai ga rayuwar 'dan adam. Aure sunnar
Annabin muce (S.A.W.), ibadane, more
rayuwane, kwanciyar hankaline, mutumcin 'dan
adam da kuma kariya. Wadannan abubuwa da
muka zayyana akwai hanyoyin da akebi na
Musulunci domin a cimma nasarar samun su a
cikin aure, haka kuma bayanin kowanensu na
bukatar sharhi mai fadi na ilimi. Don haka sai
anemi bayanan malaman sunnah. Adaidai
wannan wurin, zamu takaita kan mu wajen
bayanai akan amfanin jima'i ga lafiya: ma'ana-
abunda zaka iya moruwa dashi na lafiya da
jima'i ke amfanarwa. Ko shakka babu, fahimtar
wannan mas'ala zai iya baka damar sanin
hanyar halas da zaka iya magance wasu
matsalolin lafiya ta hanyar saduwa da iyalinka.
Haka kuma, zaya sanya ka cikin mamaki da
fahimtar rahamar Allah madaukakin Sarki
akanka. Daga cikin wannan abubuwa da jima'i
ke maganinsu sun hada: rage hawan-jini (BP),
rage wahala, karfafa garkuwar jiki, gyara maniyyi
da sauransu.
1. RAGE HAWAN-JINI :
Abisa wasu bayanai masu inganci da muka
tattaro na wasu masana kimiyya, yin jima'i
tsakanin ma'aurata na taimakawa wajen rage
hawan-jini a lokacin da yake hauhawa.
2. HUCE WAHALA:
Idan maigida ya dawo aiki ya shawo wahalar
aikin ofis, ta kasuwa ko wata wahala mai wuyar
gaske kuma ya naso ya huta, toh sai yayi
wanka, yaci abinci, ya kuma sha ruwa ko lemu,
sa'annan ya sadu da iyalinsa. Ko shakka babu
zai samu wani irin hutu da bacci mai dadi da kuma
debe wahala. Jima'i na rage 'stress' da
'pressure' sosai.
3. KARFAFA GARKUWAR JIKI:
Binciken wasu masana kimiyya ya nuna cewa,
mutane (magidanta) masu yin jima'i akai-akai
sunfi yawan sinadarin "antibody" a cikin jikinsu
fiye da wanda basu yin jima'i kamar yawan
nasu. Shi dai wannan sinadari amfaninsa shine
kare jikin 'dan adam daga cututtuka (germs,
viruses and other intruders) masu kai farmaki a
cikin jiki su cutar da lafiya- wato garkuwane ga
jikin 'dan adam . Toh saidai yana da kyau
mutum ya yawaita cin abincin dazai kara masa
lafiyar jima'i kamar yanda muka bayyana a can
baya . Kuma mutum ya rinka hutawa don samun
cikakkiya lafiya da ni'ima.
4. GYARA MANIYYI:
Mutum mai saduwa da iyalinsa akai-akai, ilimi
ya nuna cewa maniyyinsa na kara inganci da
lafiya. Zaya samu sabon maniyyi ya zubda
tsohon maniyyi. Hakan zai iya taimakawa sosai
wajen saurin samun juna biyu ga iyalinsa. Haka
kuma, sabunta saduwa da uwargida na kara
mata sha'awa da ni'imar ruwa (vaginal
lubrication) domin saduwa da maigida cikin
sauki da santsi. Wannan rahotone daga wata
mai ilimi akan kiwon lafiya (Assistant clinical
professor of obstetrics and gynecology at
Northwestern University's Feinberg School of
Medicine in Chicago).
5. RAGE CIWO:
Jima'i na rage radadin ciwo kamar irin na ciwon
jiki ko na baya da sauransu. A lokacin da mutum
yayi inzali, jikinsa na samarda wani irin sinadari
(hormone oxytocin), wannan sinadari yana
taimakawa sosai wajen samarda wani sinadarin
kuma (endorphins) wanda keda tasiri kamar na
maganin "aspirin" da "panadol" (pain relievers)
masu rage zafin ciwo. Jima'i magani me mai
karfi na ciwo. Idan mutum yanaso ya gane
gaskiyar wannan zance, a lokacin da yake jin
wani ciwo a jikinsa, ya saurara yaji idan akwai
ciwon lokacin yake kawowa (inzali).
6. GYARA ZUCIYA:
Masana kimiyya sun bayyana jima'i a matsayin
wani nau'in motsa-jiki (exercise). Motsa jiki
nada muhimmanci sosai ga lafiyar mutum. Yana
gyara lafiyar zuciyar 'dan adam da kuma kare ta
daga cututtuka masu kai farmaki. Yana sanya
gudanar jini a zuciya da sauran jiki yanda ya
kamata domin samun cikakkiyar lafiya.
7. RAGE KIBA:
Yawan jima'i nasa rama. Kada mu manta da
cewa jima'i wani nau'i ne na motsa-jiki.Yana
kone sinadaran kuzari (calories) wanda
taruwarsu da yawa a jiki ba tare da amfani dasu
ba ke jaza kiba (weight gain). Jima'i na tsawon
rabin awa na kone/amfani da kimanin 75 ko 150 na
sinadarin. Anyi kiyasin cewa mutum na kone sinadarin
kimanin 129 yayinda yake tafiya a kasa tsawon
rabin awa.Yawan kiba nada illa sosai ga lafiya.
Yana haddasa ciwuka kamar na zuciya, ciwon
suga da ciwon kafafu ko gabbai. Toh masu kiba
ga wata dama ta samu - Jima'i hanyace ta rage
kiba.
8. GYARA FATA:
Fata tayi kyau da kala mai kyau mai alamun
lafiya.
9. GYARA MAFITSARA:
Yana gyara lafiyar mafitsarar mata domin rike
fitsari da sauransu dai mutakaita.
Wadannan bayanai da suka gabata basa yin
nuni cewa mutum ya yawaita yin jima'i da
iyalansa. Yawan yin jima'i na iya sanya mutum
ya tsotse ya kuma rasa wasu sinadarai masu
muhimmanci a jikinsa. Nemi Karin bayani daga
malaman addini da kuma likitoci akan a dadin
yawan jima'i da mutum yakamata ya rinka yi a
sati don cikakkiyar lafiya da ni'ima. To amma adadin
yawan a sati yasha bamban tsakanin mutane ta
fuskar shekarunsu, yanayin halittar su da kuma lafiyarsu
da kuma wasu sauran dalilan na daban.
Ku biyo mu a KALUBALE GA MA'AURATA –
KASHI NA 5 domin jin amsoshin wadannan
matsaloli kamar haka:
1. Shin ko girman al'aurar namiji nada alaka da
gamsasshen jima'i ga matarsa?
2. Shin tsawo ko kaurin mazakuta ne yafi
muhimmanci?
3. Minene tsayin ko kaurin da ake bukata ga
maigida, kuma yaya ake awonsu don mutum
yasan nashi?
4. Toh minene mafita ga wanda yake da kasa da
abunda ake bukata na tsawo ko kauri(gwabi)?
umrah package 2017
ReplyDeletebinqasim travels present best umrah package 2017 at affordable price with best facilities.Now book your desireable umrah package in very cheap price,this ramzan book the journey of your life time with bin qasim travels.bin qasim travels offers best umrah package in karachi, you can see our packages at our website.
umrah packages, karachi, ramdan umrah