Sunday 14 October 2018

Sabuwar Manjaha (application) ta Madinah Islamic Medicine a Playstore

Cibiyar MADINAH ISLAMIC MEDICINE dake a Katsina na farin cikin shaidawa alummah masoya masu mu'amulla damu da masoya mabiya shafin mu a yanar gizo cewa mun fito da sabuwar manhajar mu (APPLICATION) a PLAYSTORE. Application din na dauke da bayanan wasu matsalolin lafiya da suka shafi ma'aurata da hanyoyin magance wasu daga cikin matsalolin da kuma neman magani daga cibiyar. 

Ayi searching MADINAH ISLAMIC CHEMIST a PLAYSTORE ko a shiga wannan LINK kai tsaye ayi downloading: 
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.andromo.dev679836.app866696

Muna godiya ga Allah da Yasa wannan cibiya  ta zamo ta farko a Nigeria data kai ISLAMIC CHEMIST zuwa PLAYSTORE a cikin harshen HAUSA. Muna kuma godiya ta Musamman ga Muhammad Jafar Adam dake a Misra (Egypt) wanda yake shine kwararrre mai fasaha daya kirkiri wannan manhaja domin wanzar da cigaban wannan cibiyar lafiya. Allah Ya saka mishi da alheri.



Thursday 2 August 2018

ALAMOMIN MATSALAR FAIBIROD [ الورم الليفي / FIBROID]


Kafin bayanin alamomin,  mu fara da minene "fibroid"? Fibroid (الورم الليفي) wata matsalace a mahaifar mace,  wato wani yanayi ne da wani curin nama yake fitowa  kuma yana girma a mahaifar mace. Ƙululun naman mai cutar da lafiya  yana ɗanfare da wani sashen mahaifar (uterus) da wasu igiyoyinsa matakam. " Fibroid" kalmar turanci ce, domin sauƙin furuci da Hausa, zamu cigaba da amfani da lafazin FAIBIROD a cikin bayanin mu anan . Anyi ƙiyasi cewa cikin mata 100, kashi 20 zuwa 50 na matan suna da fibroid, musamman a shekarunsu na samun haihuwa - wato daga shekara 16 zuwa 50. Wani ƙiyasin kuma ya nuna cewa mata 30 zuwa 77 suna samun matsalar fibroid a lokacin shekarunsu na samun haihuwa, wato lokacin ƙuruciyar balaga zuwa lokacin tsayawar al'adar mace saboda manyanta ko tsufanta (menopause). Mafi yawan nau'in faibirod da ake samu bayada alaƙa da ciwon-daji / kansa (not cancer). Ƙululun ko ƙwallon irin wanda baya da nasaba da ciwon-daji ne (benign/non-cancerous). Yana iya fitiwo fiye da ɗaya a mahaifa, kamar guda uku, huɗu koma fiye da haka a wurare daban-daban cikin mahifa.

  TO MINENE ALAMOMIN MATSALAR FAIBIROD ƊIN?

Wasu daga cikin alamomin sun haɗa da:
1. Zubar jinin al'adah mai yawa, ko na tsawon lokaci
2. Zubar jini a baaƙin lokutta ko tsakanin lokuttan haila
3. Ciwon ƙugu, saboda ƙululun yana danne wani sashen jiki cikin mahaifa
4. Yawan fitsari
5. Ciwon baya daga ƙasan baya
6. Jin zafi /ciwo lokacin yin jima'i
7. Rashin jini saboda yawan zubar jini
8. Rashin jin dadi a mara, musamman saboda girman ƙululun a ciki
9. Basur maisa tsugunni a bayi saboda rashin fitar bahaya
10. Ciwon ƙafa
11. Girman ciki kamar mace tana da juna biyu amma ba juna biyu bane, musamman idan faibirod din ya girma
12. Koma rashin ganin wasu ko daya daga cikin alamamomin da muka yi bayani

  WASU MATSALOLIN DA FAIBIROD ZAI IYA HADDASAWA:

- Matsala wajen haihuwa/lokacin naƙuda
- Matsala yayin fama da juna biyu
- Matsalar rashin samun juna biyu / rashin ɗaukar ciki ga mace saboda ƙululun ya toshe/taushe ko danne wani  bangaren mahaifa
- Yawan bari/zubewar ciki
  Yana da matuƙar muhimmanci mai jin daya ko fiye daga cikin wadannan matsalolin yaje asibiti   domin binciki ko tana da matsalar faibirod ko akasin haka. Idan kuma kin riga kin sani to sai a nemi magani.

MINENE KE KAWO MATSALAR FAIBIROD?

Har yanzu dai masana ilimi a fannin lafiya na ƙoƙarin fahimtar cikakken dalilin daya sa ake samun fibroid. Saidai an gano cewa yawan sinadarin ESTROGEN (estarojin) a lokacin shekarun da mace ke iya samun haihuwa yana da nasaba da lokacin da mata ke samun matsalar faibirod. Daga shekara 16 zuwa 50 shine lokacin da sinadarin yafi yawa a cikin jinin mace. ESTROGEN daya ne daga cikin manyan sinadaran jikin mace, wato ESTROGEN sinadari ne na  jinsin mace dake tafiyar da girman jikin mace, rayuwar mahaifarta da yanayin halittarta daya shafi jima'i . A lokacin balaga sinadarin na taimakawa yasa nonuwa da gashin mara da hammata su fito, kuma shine ke saka sha'awa ko yawan sha'awa ga mace idan yayi yawa. A lokacin balaga ƙwayayan mahaifa (ovaries) zasu fara samar da sinadarin. Za'a iya kiran ESTROGEN da suna MAƘERIN ƳAN MATA , domin kuwa shine ke taimakawa wajen sauye-sauyen halittar jikin mace yayinda take girma. A taƙaice, ESTROGEN shine sinadarin da faibirod suka dogara dashi domin samun daɗa girma a mahaifa, wato makamasin faibirod. Faibirod zai cigaba da girma har sai lokacinda mace ta bar yin al'ada saboda girma (menopause), daga nan sai ya fara ƙanƙancewa.

WASU DALILAI DA KA IYA SA YIWUWAR MACE TA SAMU FAIBIROD:

- Gaado : Idan mahaifiyarki ko ƴar uwarki ta taba samun fibroid zai iya yiwuwa ki samu saboda gadon jini.
- Jinsin baƙar fata:  Mutanen Africa ko ƙasashen bakar fata, wato jinsin baƙar fata su suka fi kowanne jinsin mata a duniya samun matsalar faibirod. Kuma matasa mata baƙar fata sune suka fi samun matsalar a shekarunsu na matasa. A ƙasashen turawa, Indiya da Chana da sauran wasu ƙasashen, ba kaso ake samun matansu da matsalar ba.
- Amfani da hanyoyin tsaida haihuwa (ƙwayoyin tsaida haihuwa wani lokacin zasu iya sa faibirod ya girma), ƙiba, ƙarancin sindarin vitamin D, yawan cin jan-nama, rashin cin abincin ganye da yayan itatuwa,  shangiya da sauransu.
Hanyoyin asibiti na magance matsalar asibiti ya ƙunshi: aikin tiyata (surgery) domin cire ƙululun tare da cire wani bangaren mahaifa "uterus" [Hysterectomy] wanda zai hana samun haihuwa, sa'annan wani nau'in  aiki tiyatar [Myomectomy]wanda baya hana haihuwa a gaba, ƙwayoyin magani da wasu hanyoyin. Musamman idan ya girma aikin tiyata ne akafi yi domin rabuwa da matsalar.Girman faibirod na iya zama kwatankwacin girman dutse karami ko ƙasa da haka , ko girman lemun tsami ko na zaƙi, ko girman ƙwallo, girman jariri koma fiye da girman jariri, musamman idan ba'a cire shiba ko magance saba. Wasu likitocin naganin idan faibirod yakai girman inci 4 (4 inches/9-10 cm) to akwai buƙatar ayi aikin tiyata domin a cire shi.


Domin neman maganin gargajiya (herbal medicine) mai inganci akan wannan matsalar sai a kira +2348084028794 (kuma WhatsApp no. ce) ko email madinahislamicmed@gmail.com. Maganin musamman yana sanya FIBROID yayi ta ƙanƙancewa yana rage girma , ya maƙe har ya mutu.

Za'a iya neman maganin mu a ko ina kuke a Nigeria. Za'a iya biyan kudin magani kai tsaye ta account namu mai rigistar kamfani (corporate account) da suna MADINAH ISLAMIC MEDICINE (account name) a banki, mu kuma mu tura maka magani a duk inda kuke a Nigeria da cajin kudin mota ko Post Office mai sauki, kudin tura magani ta mota mafi sauki (amma banda kudin magani), kudin mota yana kamawa daga N2000, N1500, N1000 har zuwa N500 - a motar haya ko a Post Office idan garin da kuke ba'a Arewa bane. Ko azo office namu da yake a Katsina , Jihar Katsina.

Adreshin ofis: No. 34 Sabuwar Unguwa Dandagoro - kusa da solar Walu, Katsina, Jihar Katsina.
Adreshin mu: Titin Muhammad Dikko, Katsina, daura da makarantar sikandire ta K.C.K. (Katsina College Katsina), Shago na 5 , cikin shagunan Majalissar Malamai ta Kasa , reshin Jihar Katsina, Najeriya.
Kira +2348084028794
Go to:
www.madinahislamicmed.blogspot.com


Wednesday 25 July 2018

ALAMOMIN CIWON SANYIN MARA NA MATA / SANYIN MATA WANDA AKE YAƊAWA TA JIMA'I


Waɗansu daga cikin alamomin ciwon sanyin mata da ake samu ta hanyar saduwa da namiji ko mace mai  ɗauke da ciwon : (STD/STI):

1. Fitar ruwa daga farji, ruwa mai kauri ko silili, kalar madara ko koren ruwa daga farji.
2. Kuraje masu ɗurar ruwa da fashewa a farji , musamman wurinda pant ya rufe.
3. Feshin ƙananan ƙuraje a farji ko cikin farji
4. Raɗaɗin zafi a lokacin yin fitsari
5. Jin zafi cikin farji lokacin jima'i
6. Zubar jinin al'ada mai yawa ko zuwan jinin al'ada mai wasa, wato akan lokacinda ya saba zuwa ba
7. Ciwon mara
8. Zazzaɓi
9 . Ciwon kai
10. Murar maƙoshi/maƙogwaro
11. Kasala/raunin jiki
12. Zubar jini lokacin saduwa
13. Dakushewar sha'awa, ko rashin sha'awa ko ɗaukewar  ni'ima
14. Bushewar farji
15. Ƙaiƙayin farji
16. Warin farji (ɗoyi) mai ƙarfi
17. Kumburin farji da yin jawur
18. Gudawa
18. Ko rashin ganin wata alama daga cikin wadannan alamomin da muka bayyana a sama.

A can baya munyi bayanin ciwon sanyin mata na "toilet infection" (vaginitiies: Yeast infection &  Bacterial vaginosis) wanda cutar sanyin mara ce  wacce ba'a yaɗata ta hanyar jima'i - wato sanyin mara wanda mace bazata iya harbin mijinta da cutar ba, wanda akafi samu daga "toilet" (bandaki/bayan gari). Duk da haka , munyi bayanin wata nau'in cutar sanyi guda 1 (Trichomoniasis) a cikin waɗancan  bayanan da suka gabata, wacce cuta ce da mace ka iya sakawa mijinta ciwon (STD). A wannan karon kuwa zamu yi bayani ne kaɗai  akan ciwon sanyin mata  wanda akafi samunsa  ko yaɗawa ta hanyar jima'i (STD/STI).

Ciwon sanyi cuta ce da akafi yaɗawa ta hanyar jima'i, wato ta hanyar saduwa da mai dauke da ciwon, shiyasa ake kiran dangin cututtukan da turanci da suna SEXUALLY TRANSMITTED DISEASES/ SEXUALLY  INFECTIONS (STDs/STIs), wato CUTUTTUKAN DA AKE YAƊAWA TA HANYAR JIMA'I. Ciwon sanyi anfi yaɗasa ne ta hanyar jima'i kuma maza na iya harbin mata da ciwon ko kuma su matan masu ɗauke da ciwon su sakawa maza mararsa ciwon. Ciwon yafi yaɗuwa kuma anfi samunsa ga maza masu neman mata ko mata masu bin mazaje.
Haka kuma za'a iya samun cututtukan sanyi ta wata hanyar daba jima'i ba, kamar ta hanyar bada jini ga marar lafiya - jinin mai ɗauke da cutar sanyi daga wani mutum, ko haɗuwar jikin wani da wani - fata-da-fata ; wato idan fata mai ɗauke da cutar ta fashe zata iya harbin fatar wani mutum mai lafiya da cutar, ta jini ko ruwan jiki dake a jikin fatar mai cutar zuwa fatar wanda baya da cutar - wato idan akwai kafa buɗaɗɗiya komin ƙaƙantarta zuwa cikin hanyoyin jinin wanda baya da ciwon a fata zai iya samun cutar,  misali ta hanyar sunbata (kissing) ko tsotsar al'aurar mai ciwon (oral sex),  ko ta hanyar saka kayan sawar wata (pant) mai ɗauke da kwayar cutar mai rai, ko ta hanyar amfani da reza (razor blade) wanda wani yayi amfani da ita, rezar mai ɗauke da kwayar cutar mai rai, da kuma wasu hanyoyin na daban. Ataƙaice, ƙwayoyin halittun dake sanya cutar ana yaɗa sune daga wani mutum zuwa wani mutum, ta jini, maniyyi, ruwan farji ko ruwan jiki.

Alamomin ciwon sanyi ga mata sun sha banban tsakanin mata wanda ciwon ya harba. Hakan ya danganta ne da nau'in ƙwayar halittar cutar wacce ta haddasa ciwon  da kuma matakin da cutar ta takai a  jikin mace - ma'ana, alamomi ko matakin farko da kamuwar cutar ko alamomi na gaba bayan ta soma jimawa a jikin marar lafiyar. Haka kuma, suma yanayin alamomin sunsha banban ta fuskar tsanani ko sauƙinsu,  koma rashin ganin alama ko ɗaya duk da  cewa kau akwai cutar a jikin mace. A taƙaice dai, alamomin ciwon sanyin  zasu iya ɓuya amma gwaji a asibiti zai iya nuna akwai cutar ko akasin haka.

Alamomin ciwon sanyi na " toilet infection "  na iya kama da alamomin cutar sanyi da ake samu ta jima'i (STD/STI). Saidai banbancin shine hanyoyin samun cututtukan , kuma cutar sanyin "toilet infection" tafi saukin magancewa; ita kuwa cutar sanyin da ake yaɗawa ta jima'i (STD) nada wuyar magani da naci, musamman saboda wasu na'uin cutar daga kwayar cutar "virus" ne (kamar "syphillis" da "genital herpes"). Gwaji a asibiti shine zai iya nuna na'uin cutar da maganin da ya dace, imma "toilet infection" ko kuma cutar sanyin jima'i wacce tafi muni da wuyar magani.

MATSALOLIN DA CIWON SANYIN ZAI IYA HADDASAWA MACE:

a) RASHIN SAMUN JUNA-BIYU/ HAIHUWA: Cutar sanyi mai suna "Gonorrhea" (Gonoriya) , ƙwayar cuta ce daga halittar "bacteria" kuma zata iya laɓewa a cikin jiki ba tare da wasu alamomi ba. Itace mafi tsohuwar cutar sanyin da akafi sani. Gonoriya bata cika nuna alamun taba a jikin mace, musamman a matakin farko na shigarta cikin jiki, ba kamar ga maza ba wanda alamomin kan bayyana gare su . Mata da yawa basu san ma suna dauke da cutar ba a jikinsu. Duk da haka, tana iya zuwa da alamomi kamar fitar ruwa daga farji ko ɗan koren ruwa, mai kalar madara daga farkon cutar, yin fitsari da zafi da yawan yin fitsari,  yawan zubar jinin al'adah, murar maƙoshi/maƙogwaro, jin zafi a farji yayin jima'i, da sauransu. Idan ba'a lura da cutar da wuri ba kuma aka magance ta, zata iya sanya rashin haifuwa ga mace ko namji.  Tana shafar wani hangaren mahaifa da yi masa dameji, sai mace ta kasa samun juna-biyu.

Haka kuma itama cutar "Chlamydia" (kilamidiya), wacce kwayar halittar "bacteria" ke haddasata , na daga cikin game garin cutar sanyi wacce ke hana mace ɗaukar ciki. Hakan yafi faruwa idan mace nada cutar na tsawon lokaci  ko kuma ta samu cutar wasu lokutta na rayuwarta da dama. Idan an gano cutar kuma an magance ta da wuri zai rage illa ga mahaifar mace a gaba. Cutar "Chlamydia" maɓannaciya ce da take illa a ɓoye kuma mafi yawanci bata nuna wata alama a zahiri ga mai ɗauke da cutar. Ana samunta bainar mata da yawa fiye da maza. Mafi yawanci bata nuna wata alama sai haddasa rashin haihuwa.

b) RASHIN JIN DADIN JIMA'I , ƊAUKEWAR NI'IMA , KO DAKUSHEWAR SHA'AWA KOMA RASHINTA
Sanyin gaba mai zuwa da 'yan 'kananan kuraje cikin farji , na sanya mace taji zafi wajen jima'i yayinda zakari ke kai-kawo cikin farji, wanda sau da yawa masu kurajen basu ma san suna da kurajen ba cikin al'aura, saidai suce suna jin zafi lokacin saduwa. Kurajen suna fashewa saboda da gugar zakari, sai wurin ya zama rauni. Hakan nasa mata tsoron jima'i da ganinsa  abin azabtarwa gare su mai maimakon abin  jin dadi. Sau tari basu san abinda ya haddasa zafin ba, wanda kuma mai yiwuwa ciwon sanyi. Ciwon sanyi na iya dakushe sha'awar mace ko namiji. Ciwon sanyi na iya haddasa bushewar gaba (vaginal dryness) wanda alamunsa shine daukewar ni'ima da 'kaikayin gaba. Idan gaba ya bushe zaiyi wahala mace da miji suji dadin jima'i in banda zafi.

Wasu daga cikin cututtukan sanyin da ake samu ta jima'i da ƙwayoyin halittu wanda ke haddasa su (a yaren turanci):

a) CHANCROID (bacteria) , cuta ce wacce ke zuwa da yanayin gyambo wani lokacin tare da ƙululu a hantsa.

b) CRABS (parasite), 'yan ƙananan halittu sosai , yanayin kwalkwata, masu cizo da tsotsar jini mai sanya mugun ƙaiƙayi. Ana samunsu daga gashin mara inda suka maida gidansu, ana kuma iya ɗaukarsu daga gashin gaban wani mutum zuwa na wani lokacin jima'i. Ana kuma iya samunsu ta kayan sawa, gado da sauransu.

c) GENITAL HERPES (virus) , cuta wacce take zuwa da ƙuraje masu ɗurar ruwa a baki ko kan zakari,  ƙurajen masu kama dana zazzaɓin dare (fever blisters). Idan ƙurajen suka fashe sai su zama gyambo. Haka kuma za'a iya samun ƙurajen a ɗuwawu, cinyoyi, ko a dubura. Ciwon kai ko baya, ko mura (flu) mai ɗauke da zazzaɓi,  ko kaluluwa da raunin jiki/kasala.

d) SYPHILIS (bacteria),  anfi samunta wajen 'yan luwaɗi. Tana da matakai bayan shigarta a jiki. Misali,  matakin farko (1): fitowar wani irin gyambo (chancre), wannan gyambon shine wajenda cutar ta shiga jikin mutum. Gyambon mai tauri, mai zagaye marar zafi. Wani lokacin abuɗe yake kuma da lema, ko zurfi musamman a hular zakari, wanda zaka ga wurin ya lotsa. Ana samunsa a zakari ko dubura ko leɓe (a baki). Ana kuma iya samun gyambon a ɓoye wani wajen cikin jiki. Mataki na biyu (2): ƙuraje a tafin hannu ko ƙarkashin tafin ƙafa ko wani sashen na jiki. 'Yar mura, zubar gashi, zazzabi marar tsanani, kasala,  murar maƙoshi, ciwon kai ko ciwon naman jiki da sauransu.  Mataki na gaba: mataki na gaba ko ƙarshe shine  wanda cutar zata iya ɓoyewa a jiki, 'buya idan ba'a magance taba,  kuma zata iya sanya ƙululun kansa/ciwon daji (tumour), makanta, mutuwar sashen jiki, matsalar ƙwalwa, kurumta, ciwon mantuwa mai tsanani (dimentia). Ana iya magance cutar cikin sauki da idan an lura da ita,  da wuri, da yardar Allah.

e)  TRICHOMONIASIS (parasitic organism) , cutar sanyi maisa warin farji,  mace zata iya harbin mijinta da  cutar ko mijin ga matar. Idan ya kasance miji nada wata mata ko yana neman matan waje masu cutar ko kuma macen ta taba saduwa da wani mutum mai cutar daya samo cutar daga wata mace, to akwai yiwuwar ma'aurata su samu cutar. Mazaje ba kaso suke sanin suna da cutar ba kasancewar alamomin cutar basu cika bayyana ga maza ba. Yawanci sai idan ciwon ya kama matan su suna cikin neman magani a asibiti suke gano suna da cutar. Wasu daga cikin  alamomin cutar ga mata: zubar ruwa mai launin kore-da-dorawa - mai kumfa da wari, zafi wajen yin fitsari, rashin jin dadi wajen jima'i. Wannan cuta tana da hadari ga mace mai juna-biyu da abinda ke cikinta
f) DA SAURANSU, suna da yawa kuma alamomin wani ciwon na kama da na wani ciwon wani lokacin. Don haka bincike a asibiti shine zai nuna nau'in ciwon.

Ciwon sanyi anfi yaɗasa ne ta hanyar jima'i kuma maza na iya harbin mata da ciwon ko kuma su matan masu ɗauke da ciwon su sakawa maza mararsa ciwon. Ciwon yafi yaɗuwa kuma anfi samunsa ga maza masu neman mata ko mata masu bin mazaje. Haka kuma mutum zaya iya kamuwa da ciwon ta wasu hanyoyin na daban daba  jima'i ba. Kuma lallai ciwon nada wuyar magani , musamman idan mutum bai samu  magani ingantacce ba. Zai iya yin wuyar magancewa saboda  rashin samun sahihin magani ko daɗewarsa cikin jiki ba'a magance ba.  Sau da yawa zaka ga cewa mutane sukan sha magunguna domin kaiwa ciwon hari da sukar alluran likita amma hakan bai  razana ciwon ba  sai kaga  yana wa mutane jeka-ka-dawo tsawon watanni koma shekaru da dama ba'a samu waraka ba.

Domin neman magani mai inganci / waraka akan waɗannan cututtuka sai a kira +2348084028794 (kuma WhatsApp no. ce) ko email madinahislamicmed@gmail.com.

Za'a iya neman maganin mu a ko ina kuke a Nigeria. Za'a  iya biyan kudin magani kai tsaye ta account namu mai rigistar kamfani (corporate account) da suna MADINAH ISLAMIC MEDICINE (account name) a banki, mu kuma mu tura maka magani a duk inda kuke a Nigeria da cajin kudin mota ko Post Office mai sauki, kudin tura magani ta mota mafi sauki (amma banda kudin magani), kudin mota yana kamawa daga N2000, N1500, N1000  har zuwa N500 - a motar haya ko a Post Office idan garin da kuke  ba'a Arewa bane. Ko azo office namu da yake a Katsina , Jihar Katsina.

Adreshin ofis: No. 34 Sabuwar Unguwa Dandagoro - kusa da solar Walu, Katsina, Jihar Katsina.

Adreshin mu: Titin Muhammad Dikko, Katsina, daura da makarantar sikandire ta K.C.K. (Katsina College Katsina), Shago na 5 , cikin shagunan Majalissar Malamai ta Kasa , reshin Jihar Katsina, Najeriya.

Kira +2348084028794

Go to:
www.madinahislamicmed.blogspot.com

Thursday 21 June 2018

CIWON BURUSTAAT (PROSTATITIS/التهاب البروستات)


Wasu daga cikin alamomin ciwon:

1. Jin radadin ciwo wajen hantsa , kusa da dubura

2. Wuyar yin fitsari ko jin zafi yayin yin fitsarin

3. Rashin fitar fitsari (toshewa) ko rashin fitarsa da karfi

4. Fitsari mai duhu-duhu

5. Ganin jini a fitsari

6.  Yawan jin fitsari musamman a cikin dare sosai, ko tsoron yin fitsari saboda jin zafin fitsarin

7. Fitar farin daga zakari a lokacinda mutum yayi yunkurin bahaya/nunshi , ko bayan ya gama bahaya (kashi) ko bayan gama fitsari

8. Jin zafi yayin fitar maniyyi daga zakari

9. Dakushewa ko raguwar sha'awar namiji

10. Rashin jin dadi ko jin wani ciwo daga zakari ko maraina

11. Zazzabi

12. Alamomin ciwon mura, ciwon jiki (naman jikin)

13. Ciwon mara da hantsa ko ciwon baya daga kasan baya

14.  Fitar farin wani dan ruwa mai kauri akan zakari - wajen kofar fitsari, ruwan mai illa ga kan zakari da sanya jin radadin ciwo wajen fitsari

15. Rashin karfin azzakari

16. Ciwon kugu bayan jima'i

17. Yin fitsari mai wari

Wadannan suna daga cikin alamomin cutar burustaat - PROSTATITIS  (التهاب البروستات) - alamomin ciwon masu sauki da kuma wanda yayi kamari , duka a hade. PROSTATITIS dai cuta ce  dake shafar lafiyar PROSTATE  da kumburi mai ciwo(البروستات). TO minene PROSTATE (إذن ما هو البروستاتا؟)? PROSTATE (BURUSTAAT) wani sashen jikin 'dan adam, wato wata halittace  a jikin kowanne namiji mai shigen 'yar karamar 'yar kwallo wacce keda sigar "doughnut"  da huda ko rami a tsakiyarta. PROSTATE nada rami ko hanya a tsakiyarsa wanda bututun fitsari (pipe)  na zakari ya ratso cikin hudar, tayanda idan PROSTATE ya kumbura saboda wata cuta zai iya matse bututun fitsarin daya gitto ta cikinsa daga tsakiya, sai mutum ya dinga  jin wahalar fitar fitsari  da ciwo saboda matsewar hanyar fitsari (pipe din). PROSTATE yana nan a tsakanin mafitsara (bladder) da zakari - a gaban dubura , wato wajen hantsa daga ciki.

Babban amfanin  PROSTATE shine masana'antar da ake samar da ruwa mai santsi (semen)  wanda yake ciyarda da maniyyi wasu sinadarai masu kare sa da kuma sufurin maniyyin zuwa hanyoyinsa a jiki. Yana jiqa hanyar maniyyi , wato bututun zakari wanda fitsari ke fitowa waje domin maniyyi ya samu ya sulalo da zaran an harbo sa daga maraina. Ruwan (semen) kuma na taimakawa maniyyi da zaran ya fita daga zakari har zuwa mahaifar mace - wato yana daukar maniyyi  har zuwa ga 'kwan mace a mahaifa,  tamkar wani kwale-kwale akan ruwa da yake daukar maniyyi cikin sauki ya sulala dashi zuwa marar mace har zuwa mahaifa. To kenan PROSTATE yana daga cikin bangaren jikin mutum namiji dake da alaka da lafiyar haihuwa? Wannan zance haka yake!
     
PROSTATITIS ciwo ne da 'kwayar cutar bakteriya (bacteria) ke haddasawa, kuma akwai CIWON DAJIN PROSTATE (prostate cancer) wanda baya da alaka da cutar PROSTATITS . PROSTATE CANCER wani ciwon ne na daban da baya da alaka da PROSTATITIS.

Mafi yawan matasa maza matasa  da manya masu shekaru da yawa (tsaka-tsakiya) suna fama da wannan ciwo na PROSTATITIS, kuma PROSTATE 'din mutum yana 'kara girma a lokacinda yake manyanta wanda shine yasa manyan mutane da yawa suke fama da matsalar fitar fitsari a lokacinda shekaru ke haye musu.

Domin neman magani mai inganci akan wannan matsalar sai a kira +2348084028794 (kuma WhatsApp no. ce) ko email madinahislamicm
ed@gmail.com. Zaka iya neman maganin mu a ko ina kake a Nigeria. Zaka iya biyan kudin magani kai tsaye ta account namu mai rigistar kamfani (corporate account) da suna MADINAH ISLAMIC MEDICINE (account name) a banki, mu kuma mu tura maka magani a duk inda kake a Nigeria da cajin kudin mota ko Post Office mai sauki, kudin tura magani ta mota mafi sauki (amma banda kudin magani), yana kamawa daga N2000, N1500, N1000  har zuwa N500 - a motar haya ko a Post Office idan garin da kake ba'a Arewa bane. Ko azo office namu da yake a Katsina , Jihar Katsina.

Adreshin mu: Titin Muhammad Dikko, Katsina, daura da makarantar sikandire ta K.C.K. (Katsina College Katsina), Shago na 5 , cikin shagunan Majalissar Malamai ta Kasa , reshin Jihar Katsina, Najeriya.

Adreshin ofis: No. 34 Sabuwar Unguwa Dandagoro, Katsina.
Kira 08084028794

Tuesday 27 March 2018

ƘARIN GIRMAN MAMA (BREAST ENLARGEMENT)

Mata da yawa na ganin ƙirjin mace  kimar ɗiya mace ne  kuma abin tinƙaho ne ga mace da jan hankali ga maza da kuma birgewa. Don haka  mata da yawa sun ɗauki gyaran mama wani muhimmin  abu, musamman bayan shayarwa ko faɗuwar nonuwan budurwa  a gida ko rashin girman sa.

Girman mama an alaƙanta shi  daga cikin abubuwa  wanda ke sa mace a ganta mai kyakkyawar halitta da ban sha'awa da birgewa ga maza kasancewar maza mafi yawa na son mata masu wannan yanayi.  Wannan lamari nada tasiri sosai ga tunanin mata da yawa,  ta yanda wasu ke jin alfaharinsu da tinƙaho  zai faɗi idan maman su ya faɗi ko suka bari ya canza daga sigar da ake bege. Shi dai nono wani dandazo ko cincirundon tsokar nama ne mai zagaye da kitse daya taso sama a ƙirjin mace baliga. Tsokokin suna canzawa lokacin balaga, haila, juna-biyu da lokacin shayarwa, da kuma lokacin barin al'adar mace (menopause). Waɗannan tsokoki kuma zasu iya buɗewa su ƙara girma saboda wasu magunguna ko tsirran magani.

Mata da yawa ne ke neman magani a kasuwanni domin gyaran mama kuma hanyoyin gyaran maman da ake bi suna da yawa amma amma a zahiri ingancinsu kaɗan ne, wanda sun hada da: ƙwayoyin magani, man shafawa, famfon iska na ƙara girman mama (breast pump), gari , ofireshin/tiyata (surgery)domin ƙara girman nono da sauransu . Wasu hanyoyin nada hadari ga lafiya, kuma sakamakon amfani da magungunan ko hanyoyin ya sha banban tsakanin mata masu ta'ammuli da magungunan, inda wasu sun sami nasarar  ƙara girman mamansu wasu kuma babu wani canji.

Anyi gargadi akan amfani da kayan turawa na kemikal (chemicals) wanda zasu iya haddasa cutar sankarar mama (ciwon daji/cancer), musamman man shafawa na turawa. Domin rage haɗarin dake tattare da yin amfani da magunguna barkatai wanda da zasu iya haddasa illa ga lafiya, MADINAH ISLAMIC MEDICINE mun yanke shawarar bayyana sirrin wasu daga cikin hanyoyi masu inganci kuma marar haɗari da mace zata iya  ƙara GIRMAN NONO ko CIKOWAR NONO idan ya kwanta. Bugu da ƙari, hanyoyin na  bada kariya daga cutar sankaran nono (breast cancer) kasancewar abubuwanda da za'a yi amfani dasu daga tsirrai ne na ɗabia (nature/natural). Abubuwan da za'a nema a ISLAMIC CHEMIST domin ayi amfani dasu sune:

1. HULBA (Fenugreek) da man ta (oil).
2. SHAMMAR (Fennel seeds)

Mai yiwuwa kin taɓa amfani da HULBA, kuma da kika ga hulba cikin abubuwa 2 da muka bayyana kya ce "Hmm. Ai nasan hulba , na jarraba amma shiru ne." Idan kina daga cikin masu irin wannan tunanin to akwai yiwuwar cewa baki yi amfani da hulba ba na tsawon lokaci kullum ko kuma baki yi amfani da ita ba yanda ya dace. Domin kuwa bincike ya tabbatar da tasirin yin amfani da hulba a halittar nonan mace. Hulba na sanya fata da tsokar dake zagaye da nonon mace su buɗe kuma nono ya ciko ɓulɓul  , musamman nonuwa wanda suna da girma amma ba'a miƙe suke ba, sun baje ko sun kwanta. Cikar nonuwan zaisa su miƙe su domin cika ƙirji da siga mai kyau.

SHAMMAR (fennel seeds) kuwa , shima ƴaƴan wani tsiron shuka ne masu kamar ƴaƴan  alkama ko shinkafa wacce ba'a cire ɓawon ba.

YANDA ZA'AI AMFANI DASU
A sami ƴaƴan hulba da  ƴaƴan shammar a Islamic Chemist  sai a niƙe su , a dake su sosai amma kowanne  daban-daban. Haka kuma za'a iya samun garin nasu a Islamic Chemist ba sai an sha wahalar daka ba. Sai a ɗibi cikin ƙaramin cokalin shayi na garin hulbar guda (1 teaspoon) a zuba a kofi , sa'annan a ɗibi garin  shammar ɗin shima cikin ƙaramin cokali guda a haɗe su a kofi ɗaya ( hulba + shammar). Sai a tafasa ruwan zafi idan ya tafasa sai zuba cikin kofin maganin a motsa da cokali sosai a sa'annan a rufe bakin kofin. Idan yayi minti 10 arufe - ya jiƙa sai a tace da rariya a zuba zuma ga ruwan da aka tace asha. Sa'annan a shafa man hulba ga mama safe da dare. Ashafa man a linda/luliya (massage)  ya shiga fatar nono sosai.  Za'a yi hakan (yin shayi da shafa man hulba) sau biyu (2) a rana - safe da dare har na tsawon wata daya. Za'a ga cikakken sakamako bayan wannan lokaci da yardar Allah. Daga zuwa wannan lokaci ko kafin lokacin mace zata fara jin nonuwanta sun kara nauyi, wanda alamace na girma da suke karawa. Kara girman nono ba abu bane dake faruwa cikin dare daya kamar yanda wasu ke tunani. Don haka akwai bukatar hakuri kamin aga sakamakon da ake bukata.

Man hulba yana da amfani idan aka jure ana amfani dashi.  Yana da amfani 2: Na farko, yana sanya gudanar jini da kyau wajen nono wanda zai taimaka wajen inganta lafiyar nono da kyawon fatar nono. Na biyu, yana buɗe tsokokin nono yanda zasu ƙara girma da ƙarfin fata (firming)  mai riƙe nono tsaye ba mai yawan taushi ba  wanda kesa mai sanya mama ya sunkuya saboda yawan taushi. A nemi man hulba ɗan Misra ko Hemani (Pakistani). Allah Ya taimaka.

Wadannan bayanan cikin harshen Hausa da muka wallafa a sama, na cibiyar MADINAH ISLAMIC MEDICINE (CAC :KT2557) dake Jihar Katsina, Nigeria.
Office Address: No. 34. Sabuwar Unguwa Dandagoro, Katsina, Jihar Katsina.

Www.madinahislamicmed.blogspot.com
Email: madinahislamicmed@gmail.com
Phone no.: +2348084028794 (kuma WhatsApp no.)



Friday 23 March 2018

YAWAN WASA-DA -AL'AURA DA ILLARSA GA ƘWALWAR MATASA : YAWAN MANTUWA



A ɗabi'ance  , a lokacinda mutum yakai shekara 30 da haihuwa kwalwarsa zata fara samun ja baya , ci bayan zai fara gudu a lokacinda mutum ya kai shekara 50. To amma a wannan zamanin ga alama cibayan zai iya zuwa da wuri kafin shekarun tsufan  samari yazo. Ko minene yasa haka? Amsar itace, "Zinar hannu" , wato wasa-da-al'aura (istimna'i) da ya zama ruwan dare bainar matasa, musamman saboda wayar salula da ake ƴada hotunan batsa da video wanda ke jefa matasa cikin matsananciyar sha'awa da aikata wasa da al'aura koma abu mafi muni zinace-zinace.

KO MINENE ALAƘAR ISTIMNA'I DA YAWAN MANTUWAR MATASA?

Kafin mu amsa wannan tambayar yana da kyau mu yi bayanin abinda ake cewa "Istimna'i" ko "wasa-da-al'aura".Wasa-da-al'aura dai ko wasa da gaba (Istimna'i [masturbation]) na nufin yin amfani da hannu, yatsa ko wani abu domin biyan bukatar jima'i ga mutum da kansa da tunanin saduwa da wata mace ko wani namiji , ga mace. Ana kiran wannan ɗabi'a "zinar hannu". Istimna'i dabi'a ce da take faruwa da yaduwa cikin mutane da dama - yara matasa, da manya mutane, musamman cikin matasa mararsa aure ko wanda aurensu ya mutu, koma rashin gamsuwar aure. Yawan aikata istimna'i (excessive masturbation/over-masturbation) na da illa ga lafiya sosai. Kuma idan ya zama ɗabi'ar mutum koda yaushe to yafi zama matsala ga lafiya da wuyar bari (addiction) wanda hakan zai jefa mutum cikin wani ƙalubalen lafiya mai muni.

To tunda mun fahimci ko minene istimna'i , bari mu koma ga tambayar mu ta farko,  minene alaƙar istimna'i da yawan mantuwa wacce kesa dusashewar ƙwalwar matasa,  rashin riƙe karatu tun kafin tsufa yazo musu? Domin amsa wannan tambaya,  bari mu shiga jikin mutum mu ga abinda ke faruwa  kimiyyance kamar yanda masana suka yi bayani : A duk lokacinda jikin mutum ya fitar da maniyyi da yawa jikin na rasa wasu muhimman sinadarai (neurochemicals/acetylcholine) wanda ke kai saƙo ga kwalwa mutum , kuma su waɗannan sinadaran lafiya suna taimakawa wajen nazari, maida hankali da riƙe wani abu ko karatu a ƙwalwa. Mutumin da yake yawan yin istimna'i jikinsa na samun ƙarancin sinadaran. Sinadarin " acetylcholine" da wasu sinadaran gina jiki (proteins) suna raguwa. Ƙarancin sinadarin (acetylcholine) na sanya ƙwalwa rauni da mantuwa (memory loss/forgetfulness). Bugu da ƙari, ƙarancin na sanya yawan kasalar jiki, da rashin gani da kyau , wato gani buji-buji (blurry vision),  ko ciwon baya (back pain) da zubar gashi (hair loss). Matsalolin lafiya da yawan istimna'i yake haddasawa suna da yawa.

Mutane sunfi yawan alaƙanta yawan mantuwa da tsufa , wato ana ganin tsofaffi keda yawan mantuwa ba yara ba , to amma abin mamaki shine " Ana zaton wuta a maƙera amma sai gata a masaƙa". Yanzu ana samun matasa da yawan mantuwa , rashin hazaƙar ƙwalwa ko maida hankali wanda ke sanyasu wuyar karatun Islamiyya da na Boko. Don haka, yawan istimna'i na na shafar bangaren kwalwa mai kula da ajiye bayanai (hippocampus) daga ma'ajiya ta kusa zuwa ta nesa, da kula da karatu ko maida hankali. Akwai dalilan lafiya na daban da dama wanda zasu iya sanya yawan mantuwa ko ciwon mantuwa (dimentia), kamar haɗari da ya shafi ƙwalwa, gado ko wata cuta. To saidai mantuwar da istimna'i ke haddasawa matasa na daga cikin ɓoyayyun dalilan matsalar mantuwar matasa a wannan zamani.
Wasu illolin da istimna'i zai iya haddasawa  na daban wadanda basu shafi mantuwa ba sun hada:
kankancewar zakari da maraina, saurin kawowa ko rashin karfin mazakuta. Sauran matsalolin dazai iya haddasawa , sun hada da: ramar jiki ko 'karancin sha'awa, karancin maniyyi ko tsinkewar maniyyi da raguwar ingancinsa (wanda na iya haddasa rashin haifuwa) , raunin jiki, raunin garkuwar jiki, jin ciwon kai akai-akai, ciwon baya, fitar maniyyi daga zakari hakanan ba tare da mutum yayi niyya ba - ba tare da yayi istimna'i ba ko yayi jima'i, haka nan kawai.
Wasu illololin da zasu iya faruwa saboda istimna'i: bushewar fatar kan zakari ko illa ga fatar saboda gugar fatar da hannu, karkacewar zakari (penis curvature) ko sauya masa sigarsa ta asali, bugawar zuciya da sauri kurajen fuska.da sauransu.

ILLAR ISTIMNA'I GA MACE

Mace zata iya samun wasu daga cikin matsalolin da mu kayi bayani a sama. Wasu matsalolin daka iya shafar mace sune: Rashin rike fitsari da kyau (ga mace) koYawan zuwa fitsari saboda saka wani abu cikin farji lokacin istimna'i, wuyar kawowa ga mace wajen jima'i (dalilin koyama jikinta da sai an taɓa wani sashen farji don ta kawo, wanda mai yiwuwa ne zakari baya taɓa wurin lokacin saduwa - a zahirin jima'i. Don haka istimna'i yana sa rashin gamsuwar jima'i ga mace - mijinta zai sha wahala wajen gamsar da ita. Jikinta ya riga ya koya, tayima kanta horo. Dalilin haka, mace zata ji dadin istimna'i fiye da jima'i , hakan kuma zai zamo mata matsala idan tayi aure. Zata ringa tunanin mijinta baya iya gamsar da ita ko mazaje data aura, saboda sabon da tayi da koyama jikinta hanyar gamsar da kanta fiye da hanyar da ta dace, wato jima'i a cikin sunnar aure. Ta canza dabi'ar ta. Da yawa zaka samu cewa mata masu yawan istimna'i basu jin daɗin jima'i sai istimna'i, koma basu gamsuwa sai sunyi istimna'i a bandaki bayan saduwa da mazajen aurensu. Wannan zai iya kawo babbar matsala a cikin aure. Bugu da kari, dadilan rashin gamsuwar mace wajen saduwa da mijinta suna da yawa. Don haka, bazamu iya cewa ba yin istimna'i kafin aure shine dalilin dake hana gamsuwa kadai ba. Akwai wasu dalilan na daban, wasu matsalolin nada alaka da bangaren mazajen.

Domin neman karin bayani cikakke akan illolin  yawan istimna'i ga lafiya da hanyoyin barinsa da kariya  sai a shiga wannan link kai tsaye (latsa) ko a kofa a liƙa a Google domin ayi searching:

http://madinahislamicmed.blogspot.com.ng/2016/11/wasa-da-alaura-da-illarsa.html?m=1

Ko a shiga Facebook (latsa LINK karanta) :

https://m.facebook.com/MadinahIslamicMedicine/photos/a.623324837696435.1073741826.621757857853133/1806983335997240/?type=3

Ko azo neman magani a Office Branch namu mai address kamar haka:
No. 34 Sabuwar Unguwa Dandagoro, Katsina, Jihar Katsina.
Kira: +2348084028794 (WhatsApp number)
E-mail: madinahislamicmed@gmail.com

Wednesday 21 March 2018

SAURIN INZALI DA MAGANI


Biyan bukatar namiji da mace wajen jima'i yasha banban ta fuskar tsawon lokaci. Kashi 68 cikin 100 na mata suna bukatar minti 8 su biya bukatarsu da mazajensu, haka kuma, kashi 45 na wasu matan na bukatar minti 12 yayin saduwa. Abin mamaki shine, kashi 75 na  maza na kasa jurewa su tsawaita lokacin biyan bukatarsu zuwa minti 3 ko 6, sabanin lokacinda wasu matan ke bukata don biyan bukatarsu. (Qinghai Province Xining City Ailida Biotechnology Company, 2012).

Saurin inzali ko kawowa (القذف المبك/Premature Ejaculation) yanayi ne da namiji yake saurin biyan bukatar  jima'i da zaran zakari ya shiga farji cikin 'yan daƙiƙoƙi ko mintuna kaɗan koma kafin shigar zakari cikin farji kasancewar namijin baya iya tsawaita lokaci ko jure dadin jima'in da yake ji na tsawon wani lokaci, musamman saboda matsannanciyar sha'awa ko kamuwa da yawa. Saurin inzali na faruwa ba tare da mutum yayi wata niyyar yin hakan ba. Jima'i a wannan yanayi na  karewa da zaran maniyyi ya fita daga jikin namiji. A wannan yanayi namijin baya iya yiwa sha'awarsa linzami ta fuskar rage sauri domin more jima'i na tsawon wani lokaci kuma baya iya gamsar da iyalinsa wacce saurin inzalisa ke hanata biyan bukatarta  , ko haddasa rashin gamsuwarta. Kasancewar mata na bukatar lokaci mai tsayi fiye da na maza mafi yawan lokutta.

Shekaru da dabaru na yau da kullum saboda fahimtar jima'i tsawon lokaci a rayuwa  nasa maza su fahimci yanda zasu magance matsalarsu da kansu ba tare da wani magani ba wani lokacin.

ABUBUWANDA KE HADDASA SAURIN INZALI / KAWOWA

Haryanzu dai babu wani sahihin bayani ko dalili dake bayyana dalilin saurin kawowa ba, saidai wasu bayanai akan dalilan da ka iya bada haske gameda matsalar saurin kawowa ga maza (premature ejaculation). Sune kamar haka:

1. Matsalar rashin karfin mazakuta  (erectile dysfunction). Idan namiji baya da karfin gaba to akwai yiwuwar asami saurin kawowa lokacin jima'i , haka kuma,  idan akwai karfin zakari to akwai yiwuwar dadewar yin jima'i mai tsawo tsakaninin ma'aurata biyu. Saboda haka,  saurin inzali na iya zama wani lokacin alama ce ta rashin karfin zakari.

2. Yanayin halittar wasu mazajen. Wani haka Allah Ya halicce sa ko minti 1 baya iya yi da mace. Amma wannan baya nufin baza'a iya samun saukin yanayin ba. Za'a iya neman magani ko Allah Yasa a dace.

3. Samuwar hadari (accident) wanda zai iya shafar al'aurar mutum. Hadari wanda ya shafi lafiyar al'aura  na iya haddasa matsalar saurin kawowa.

4. Magungunan kayan mata/da'a da  mata keyi. Magunguna na matsi da mata ke sakawa cikin gaba domin matse/tsuke farji.  Idan mace tayi amfani da wani magani  gabanta ya tsuke/matse fiye da yanda maigidanta ya saba jinta zai iya sa maigidan yayi saurin kawowa saboda karuwar dadi ko dandanon jima'i.

5. Cututtuka masu shafar lafiyar jima'i, kamar cututtukan sanyin mara na maza da mata.

6. Ciwon damuwa ko fargaba na iya  haddasa saurin inzali. Misali, idan mutum yayi sabuwar amarya budurwa ko bazawara  , idan yana fargabar ko zai iya gamsar da ita ko damuwa akan wani abu, wannan tunani zai iya sanya saurin inzali a cikin saduwar su.

7.  Yin istimina'i da gaggawa ( quick masturbation) da wasu matasa keyi kamin  suyi aure, musamman yara don gudun kada a kamasu (wasa da al'aura ko zinar hannu). Yana shafar lafiyarsu, yana haddasa saurin kawowa lokacin jima'i.

8. Gado daga wajen mahaifan mutum (inherited traits). Akwai yiwuwar mutum yayi gadon saurin kawowa  daga mahaifinsa ko kakansa ko wani jininsa, wato tsatstsonsa. Wato haka duk "family" nasu suke amma bai sani ba.

9.  Matsananciyar sha'awar yin jima'i. Idan mutum ya kosa  yayi jima'i , fitinar sha'awarsa ko kamuwa da yawa zata iya sanya shi yayi saurin kawowa da zaran zakarinsa ya shiga jikin mace  ba tare da bata wani lokaci ba.

10. Rashin wasanni tsakanin ma'aurata kafin saduwa ta yanda macen zata iya fara biyan bukatar ta da wuri kafin maigida ya fara jima'i da ita ta gaba da gaba .

11. Sauyin abokiyar saduwa/ sabuwar amarya budurwa ko zawara. Yanayin sabuwar abokiyar rayuwa, wato sabuwar amarya ga maigida  nada tasiri ga kwalwar namiji, yana sanya namiji ya rikice ko ɗimauce da ɗauki wanda hakan zai sanya shi saurin kawowa. Bugu da kari, Binciken ilimi na kiyimiyya ya nuna cewa samun sabuwar abokiyar saduwa (mata)  na sanya maniyyin namiji inganci da kyau fiye da nada.

14. Canza salon kwanciyar aure, musamman mutum kada yayi kwanciya da iyalinsa wacce zata sa zakarinsa ya shige duka cikin gaban ta. Nutso (deep penetration) nasa saurin inzali.

13. Nau'in wasu magungunan. Akwai wasu magungunan da "side effects" nasu zai iya haddasa saurin kawowa ga mutum. Da sauransu, mu takaita haka.

MAGANCE MATSALAR SAURIN
KAWOWA

Hanyoyin magance saurin inzali suna da yawa , wasu hanyoyin na yiwa wasu aiki, wasu kuma sabanin haka , don haka ga hanyoyi kamar haka da mutum zai iya jarrabawa domin neman dacewa:

a) Rage ƙosawa/ƙagara. Mai saurin inzali ya kamata ya cire tunanin jima'i daga ƙwalwarsa a lokacinda yake saduwa da iyalinsa. Matsanancin tunani ko kamuwa da yawa kafin fara jima'i  zai iya sanya mutum "ya ƙone tun kafin ya tafasa". Masana sun nuna cewa bujiro tunanin wani abu a cikin rai wanda ba jima'i ba marar daɗi a lokacin saduwa na ƙarawa mutum tsawon lokaci ba tare da ya lura da hakan ba. Ɗaukin jima'i baya biya, abinda zai taimakawa mai matsalar saurin kawowa shine, rage yawan tunanin jima'i ne yake aikatawa,  ko kuma ya bar yin tunanin cewa yana yin jima'i ne domin samun gamsuwa wacce  iyalinsa da yake sha'awa take biya masa. Kamata yayi  tunaninsa ya kasance cewa yana aikata jima'i ne domin ya biyawa iyalinsa bukata farko kamin tasa. Abin lura, ka ɗauka ma cewa ba jima'i bane kake yi a lokacinda kake tarawa da iyalinka.

b) A nemi kuɓewa ɗanya (okra) guda 5, a wanke sa'annan a yanke gutsun-gutsun a cikin tukunya, sai a sami kofi ɗaya na ruwa a zuba cikin tukunyar sa'annan a ɗaura akan wuta a rufe tukunya. Da zaran ruwan ya tafasa sai a sauke tukunya a tashe ruwan a kofin shayi , sai a zuba zuma  ta bada ɗanɗano , a bari ya huce kaɗan amma asha da ɗumi. Ayi haka sau 2 a rana har na tsawon kwana 10 ko fiye da haka. Kubewa nada sinadari mai amfani mai sanya jinkirin kawowa ga maza.

c) A nemi citta (ginger) musamman ɗanya, a wanke a kuma  karkare ta , sa'annan a dake ta , ayi shayi da ita , bayan an tashe ta a kofin shayi sai a zuba zuma ta bada ɗanɗano asha shayin da ɗumi. Ayi hakan safe da rana. Citta nada sinadari mai zafi na  "gingerol" mai sanya yawan gudanar jini ga laura , wanda hakan na sanya ƙarfin gaba da jinkirin kawowa.

d) A nemi man na'a-na'a (peppermint oil) mai kyau, musammman ɗan Misra ko na kamfanin Hemani (Pakistan) . A wanke gaba da ruwan dumi , a goge lemar sa'annan a shafa man ga  zakari ya shiga fata, ga kai (glans) da tsawon sandar zakari (shaft) , amma banda kofar fitsari (urethra). Musamman a shafa idan zakari yana mike,  sai  jira bayan minti 10 zuwa 15 sa'annan a sadu da iyali. Man na'a-na'a na rage "sensitivity" na zakari , wato rage kaifin ɗanɗano da zakari keji ta yanda zai hana saurin kawowa lokacin jima'i. Haka kuma za'a iya amfani da man kanimfari (clove oil) mai kyau a maimakon man na'a-na'a. Bugu da kari, man kanimfari na maganin karfin gaba.

e) Fita daga gaban mace na 'yan mintoci a lokacinda mutum yaji ya kusa kawowa, da kuma fita daga cikin farji da matse kan zakari da hannu (squeeze and pause technique/penis grip) a lokacinda mutum yake akan hanyar kawowa.

f) Bayan kawowar farko, kawowa ta biyu na zuwa da lokaci mai tsawo kafin mutum ya sake fitar da wani maniyyin a karo na biyu. Don haka idan mutum yana son  ya daɗe bai yi inzali ba to ya tari  jima'i a karo na biyu wanda zai bashi lokaci mai tsawo kafin yayi inzali.

g) Hanyoyin neman magani na musamman daga Likitan asibiti ko Malamin Islamic Chemist. Idan hanyoyin da muka zayyana basu yiwa mutum ba to sai yabi hanyar ganin ɗaya daga cikin wadannan mutanen domin neman taimako. Akwai wasu hanyoyi da dama na magance matsalar saurin inzali.

Wadannan bayanan cikin harshen Hausa da muka wallafa a sama, na cibiyar MADINAH ISLAMIC MEDICINE (CAC :KT2557) dake Jihar Katsina, Nigeria.

Office Address: No. 34. Sabuwar Unguwa Dandagoro, Katsina, Jihar Katsina.

Www.madinahislamicmed.blogspot.com

Email: madinahislamicmed@gmail.com

Phone no.: +2348084028794 (kuma WhatsApp no.)

Wednesday 7 March 2018

Amfanin Babunaj [بابونج/Chamomile] Ga Lafiya


Albabunaj/Babunaj  ganye ne da furen wata shuka mai albarka. Ana amfani dashi a matsayin maganin gargajiya. Furen Albabunaj magani ne daya shahara musamman wajen yin shayi dashi a kasashe da al'adu a duniya. A  America ya kasance shine fitattaccen abin yin shayi . Bincike da nszarin kimiyya ya nuna cewa yana da matukar amfani ga lafiya , kuma yin amfani dashi baya da wani cikas ga lafiya. Ana samun busasshen gari Albabunaj da kuma busasshen  fure nasa a Islamic Chemists a Nigeria. Ana kuma samun  mai nasa, amma a nemi mai kyau, musamman 'dan misra. Ga wasu daga cikin amfaninsa ga lafiya:

1. Yana inganta bacci da maganin rashin bacci . A dibi cikin cokalin shayi 1 [teaspoon] a tafasa ayi shayi dashi marar madara.  Ayi hakan safe da dare. Za'a iya kuma amfani da zuma, yana da kyau hakan.

2. Maganin mura (shima shayi za'ayi).

3. Yana maganin ciwon mara lokacin al'ada (shayi).

4. Maganin ciwon ciki (shayi).

5. Maganin huce wahala ko gajiyar kwalwa da damuwa (shayi dai,  malam ko malama). Za'a iya hadashi da kanimfari  ayi shayi.

6. Gyara fata da haske (shayi dai har yanzu).

7. Yana kashe kwayoyin cutar bakteriya da karfafa garkuwar jiki (shayi).

8. Yana maganin ciwon jiki - ciwon naman jiki (shayi).

9. Yana maganin kurajen fuska , da rage tabon kurajen (shayi).

10. Yana maganin amosanin kai [dandruff] - rabuwa dashi. A wanke kai da ruwansa  bayan an tafasa albabunaj an tace (wanke kai ba shayi ba).Sa'annan yana da kyau ayi amfani da man albabunaj ko man kwakwa bayan wanke kai - a shafa aka.

11. Yana rage saurin zufan jiki da fata (shayi).

12. Yana maganin bacin ciki ko rikicewar ciki.

13. Rage laulayin mai ciki da korar aljani daga jiki . Wannan bayani da amfanin an cirota sa ne daga likitancin Islamic Chemist.To saidai babu wani bayani a kimiyyance da ya nuna cewa Albabunaj baya da hadari ko cutarwa ga mai ciki. Don haka sai a nemi bayanan lafiya masu inganci kamin mai ciki tayi amfani dashi.  Masu ciki su guji shan wani magani idan bada izinin likita.

14.. Yana taimakawa masu ciwon suga - daidaita sukari cikin jini. (Shayi amma banda zuma fa, to kunji).

15.  Amfanin da yawa fa. To anan zamu sa aya dai.

Wannan bayanan cikin harshen Hausa da wallafa , na cibiyar MADINAH ISLAMIC MEDICINE (CAC :KT2557) dake Jazar Katsina, Nigeria.
Office Address: No. 34. Sabuwar Unguwa Dandagoro, Katsina, Jihar Katsina.
Www.madinahislamicmed.blogspot.com
Email: madinahislamicmed@gmail.com
Phone no.: +2348084028794 (Also WhatsApp no.)
Facebook: https://m.facebook.com/MadinahIslamicMedicine

Wednesday 17 January 2018

Amfanin Ƴaƴan Zogale ga Lafiya (A taƙaice)


  (A tauna a haɗiye da ruwa)

1.  Ƙarfafa garkuwar jiki
2.  Maganin basur maisa tsugunni a  
     bayi
3.  Maganin infection (cututtuka)
4.  Daidaita sukari cikin jini -
     maganin ciwon suga da
     hawan jini
5.  Inganta lafiyar zuciya
6.  Kashe kansa/ciwon daji (cancer)
     da kariya daga ciwon
7.  Gyaran fata tayi kyau da lafiya
8.  Ƙarin jini da kuzari
9.  Ƙarin ganin idanu
10.Inganta lafiyar ƙashi da haƙora ,
      da sauransu.

wwww.madinahislamicmed.blogspot.com

E-mail: madinahislamicmed@gmail.com

Phone no.: +2348084028794

Office Address: No.34 Sabuwar Unguwa  Dandagoro, Katsina, Katsina State.