Saturday 28 December 2013

BASIR-MAI-TSIRO

A cikin duburar 'dan adam akwai jijiyoyin jini
wadanda wani lokacin suna samun matsatsi
da talala mai takurasu. A lokacinda suka
samu takurawa da yawa, sai su kumbura.
Kumburin wadannan jijiyoyin jini na kara matsi
da takura a garesu cikin dubura. Dalilin
wannan yanayi marar-dadi ga jijiyoyin, sai
kaga wani tsiro ya fito maka a bakin dubura
wanda jijiyar jinince. Zakaji ciwo, ko kai-kayi
koma zubar jini. Wannan lamari shine Malam
Bahaushe ke kira da BASIR-MAI-TSIRO
(Hemorrhoid/ Pile).
Wasu daga dalilanda ke haddasa shi sune
kamar haka:
1. Gaggawa wajen yin yun'kurin kasaye
abunda dake cikin mutum (kashi). Hakan na
takurama jijiyoyin dubura.

2. Yawan zawo(gudawa) ko 'kin fitowar kashi
maisa yawan tsugunni a ban-daki.
3. Yawan kiba, musamman wajen mara ko
duwawu.

4. Juna-biyu da nakuda (musamman wajen
yunkurin fito da jinjiri daga farji). Yana yima
dubura talala da matsi.

5. Jima'i ta dubura (haramun!). Masu jima'i da
iyalansu ta dubura da mafi yawan 'yan luwadi
na fama da basir mai tsiro.

6.Zama mai tsawo kamar na cikin mota ko na
tela, da sauransu.

7. Matsalolin zuciya kona anta na tsawon
lokaci wanda ka iya jaza talalar jijiyoyin jini.
8. Da sauransu.

Zaka iya maganin rashin fitowar kashi maisa
yawan tsugunni ta hanyar cin 'ya'yan itace da
ganye (fibre foods). Yana da kyau sosai ga
marar-lafiya ya rinka tafasa ruwan zafi ya bari
yayi 'dumi ya gasa basir nashi da auduga ko
kuma ya zauna cikin robar ruwan mai dumi
minti 30 sau 2 a rana, domin samun saukin
ciwo da kumburi. Bayan angama gasawa toh
sai asamu DETTOL a wanke wajen domin
gudun kamuwa da wata bakuwar cuta. Aje
asibiti neman magani. Haka kuma zaka iya
neman taimakon magani daga gare mu. Allah
ya taimaka, Ameen.
Akwai wani irin nau'in basir na cikin ciki maisa
zawo da jini wanda wata cuta ke jazawa ta
daban, wato DYSENTERY a turance. Haka kuma akwai "Fitar-baya" wato RECTAL PROLAPSE za muyi
bayanai akansu insha Allahu anan gaba.

5 comments:

  1. Assalamu alaikum. Sunana Abdallah Ahmad.ni Dan katsina ne Amma ina zama a garin funtua. Ni na kasance Dalilbi ne kuma ina fama da ciwon basir. Na dade ina yi mashi magani amma haryanzun bandace Da magani wanda zaisa naji saukin wannan ciwon ba wato basir. Don Allah fa yaya zansamu na tuntunbeku Don nayi maku karin bayani. GA number waya na nan 08033331172 or 08033331003. Na gode kwarai dagaske

    ReplyDelete
  2. This comment has been removed by the author.

    ReplyDelete
  3. Jazakallahu Bi Kairan, Assalam Alashi Gafarta Malam Dan Allah Wasu Irin Magunguna Zamu Iya Amfani Dasu Wajen Warware Wannan Matsala Ta Basir Din?

    ReplyDelete
  4. Dan Allah Ina fama da Basir har ya tsiro babba Yazanyi 08068786102

    ReplyDelete
  5. Assalamu aleykoum Malam dan allah ataymakamun da maganin wannan ciwon,me da me zamu hada don magance chi,kanwatace take fama dachi nagode

    ReplyDelete