Wednesday 25 July 2018

ALAMOMIN CIWON SANYIN MARA NA MATA / SANYIN MATA WANDA AKE YAƊAWA TA JIMA'I


Waɗansu daga cikin alamomin ciwon sanyin mata da ake samu ta hanyar saduwa da namiji ko mace mai  ɗauke da ciwon : (STD/STI):

1. Fitar ruwa daga farji, ruwa mai kauri ko silili, kalar madara ko koren ruwa daga farji.
2. Kuraje masu ɗurar ruwa da fashewa a farji , musamman wurinda pant ya rufe.
3. Feshin ƙananan ƙuraje a farji ko cikin farji
4. Raɗaɗin zafi a lokacin yin fitsari
5. Jin zafi cikin farji lokacin jima'i
6. Zubar jinin al'ada mai yawa ko zuwan jinin al'ada mai wasa, wato akan lokacinda ya saba zuwa ba
7. Ciwon mara
8. Zazzaɓi
9 . Ciwon kai
10. Murar maƙoshi/maƙogwaro
11. Kasala/raunin jiki
12. Zubar jini lokacin saduwa
13. Dakushewar sha'awa, ko rashin sha'awa ko ɗaukewar  ni'ima
14. Bushewar farji
15. Ƙaiƙayin farji
16. Warin farji (ɗoyi) mai ƙarfi
17. Kumburin farji da yin jawur
18. Gudawa
18. Ko rashin ganin wata alama daga cikin wadannan alamomin da muka bayyana a sama.

A can baya munyi bayanin ciwon sanyin mata na "toilet infection" (vaginitiies: Yeast infection &  Bacterial vaginosis) wanda cutar sanyin mara ce  wacce ba'a yaɗata ta hanyar jima'i - wato sanyin mara wanda mace bazata iya harbin mijinta da cutar ba, wanda akafi samu daga "toilet" (bandaki/bayan gari). Duk da haka , munyi bayanin wata nau'in cutar sanyi guda 1 (Trichomoniasis) a cikin waɗancan  bayanan da suka gabata, wacce cuta ce da mace ka iya sakawa mijinta ciwon (STD). A wannan karon kuwa zamu yi bayani ne kaɗai  akan ciwon sanyin mata  wanda akafi samunsa  ko yaɗawa ta hanyar jima'i (STD/STI).

Ciwon sanyi cuta ce da akafi yaɗawa ta hanyar jima'i, wato ta hanyar saduwa da mai dauke da ciwon, shiyasa ake kiran dangin cututtukan da turanci da suna SEXUALLY TRANSMITTED DISEASES/ SEXUALLY  INFECTIONS (STDs/STIs), wato CUTUTTUKAN DA AKE YAƊAWA TA HANYAR JIMA'I. Ciwon sanyi anfi yaɗasa ne ta hanyar jima'i kuma maza na iya harbin mata da ciwon ko kuma su matan masu ɗauke da ciwon su sakawa maza mararsa ciwon. Ciwon yafi yaɗuwa kuma anfi samunsa ga maza masu neman mata ko mata masu bin mazaje.
Haka kuma za'a iya samun cututtukan sanyi ta wata hanyar daba jima'i ba, kamar ta hanyar bada jini ga marar lafiya - jinin mai ɗauke da cutar sanyi daga wani mutum, ko haɗuwar jikin wani da wani - fata-da-fata ; wato idan fata mai ɗauke da cutar ta fashe zata iya harbin fatar wani mutum mai lafiya da cutar, ta jini ko ruwan jiki dake a jikin fatar mai cutar zuwa fatar wanda baya da cutar - wato idan akwai kafa buɗaɗɗiya komin ƙaƙantarta zuwa cikin hanyoyin jinin wanda baya da ciwon a fata zai iya samun cutar,  misali ta hanyar sunbata (kissing) ko tsotsar al'aurar mai ciwon (oral sex),  ko ta hanyar saka kayan sawar wata (pant) mai ɗauke da kwayar cutar mai rai, ko ta hanyar amfani da reza (razor blade) wanda wani yayi amfani da ita, rezar mai ɗauke da kwayar cutar mai rai, da kuma wasu hanyoyin na daban. Ataƙaice, ƙwayoyin halittun dake sanya cutar ana yaɗa sune daga wani mutum zuwa wani mutum, ta jini, maniyyi, ruwan farji ko ruwan jiki.

Alamomin ciwon sanyi ga mata sun sha banban tsakanin mata wanda ciwon ya harba. Hakan ya danganta ne da nau'in ƙwayar halittar cutar wacce ta haddasa ciwon  da kuma matakin da cutar ta takai a  jikin mace - ma'ana, alamomi ko matakin farko da kamuwar cutar ko alamomi na gaba bayan ta soma jimawa a jikin marar lafiyar. Haka kuma, suma yanayin alamomin sunsha banban ta fuskar tsanani ko sauƙinsu,  koma rashin ganin alama ko ɗaya duk da  cewa kau akwai cutar a jikin mace. A taƙaice dai, alamomin ciwon sanyin  zasu iya ɓuya amma gwaji a asibiti zai iya nuna akwai cutar ko akasin haka.

Alamomin ciwon sanyi na " toilet infection "  na iya kama da alamomin cutar sanyi da ake samu ta jima'i (STD/STI). Saidai banbancin shine hanyoyin samun cututtukan , kuma cutar sanyin "toilet infection" tafi saukin magancewa; ita kuwa cutar sanyin da ake yaɗawa ta jima'i (STD) nada wuyar magani da naci, musamman saboda wasu na'uin cutar daga kwayar cutar "virus" ne (kamar "syphillis" da "genital herpes"). Gwaji a asibiti shine zai iya nuna na'uin cutar da maganin da ya dace, imma "toilet infection" ko kuma cutar sanyin jima'i wacce tafi muni da wuyar magani.

MATSALOLIN DA CIWON SANYIN ZAI IYA HADDASAWA MACE:

a) RASHIN SAMUN JUNA-BIYU/ HAIHUWA: Cutar sanyi mai suna "Gonorrhea" (Gonoriya) , ƙwayar cuta ce daga halittar "bacteria" kuma zata iya laɓewa a cikin jiki ba tare da wasu alamomi ba. Itace mafi tsohuwar cutar sanyin da akafi sani. Gonoriya bata cika nuna alamun taba a jikin mace, musamman a matakin farko na shigarta cikin jiki, ba kamar ga maza ba wanda alamomin kan bayyana gare su . Mata da yawa basu san ma suna dauke da cutar ba a jikinsu. Duk da haka, tana iya zuwa da alamomi kamar fitar ruwa daga farji ko ɗan koren ruwa, mai kalar madara daga farkon cutar, yin fitsari da zafi da yawan yin fitsari,  yawan zubar jinin al'adah, murar maƙoshi/maƙogwaro, jin zafi a farji yayin jima'i, da sauransu. Idan ba'a lura da cutar da wuri ba kuma aka magance ta, zata iya sanya rashin haifuwa ga mace ko namji.  Tana shafar wani hangaren mahaifa da yi masa dameji, sai mace ta kasa samun juna-biyu.

Haka kuma itama cutar "Chlamydia" (kilamidiya), wacce kwayar halittar "bacteria" ke haddasata , na daga cikin game garin cutar sanyi wacce ke hana mace ɗaukar ciki. Hakan yafi faruwa idan mace nada cutar na tsawon lokaci  ko kuma ta samu cutar wasu lokutta na rayuwarta da dama. Idan an gano cutar kuma an magance ta da wuri zai rage illa ga mahaifar mace a gaba. Cutar "Chlamydia" maɓannaciya ce da take illa a ɓoye kuma mafi yawanci bata nuna wata alama a zahiri ga mai ɗauke da cutar. Ana samunta bainar mata da yawa fiye da maza. Mafi yawanci bata nuna wata alama sai haddasa rashin haihuwa.

b) RASHIN JIN DADIN JIMA'I , ƊAUKEWAR NI'IMA , KO DAKUSHEWAR SHA'AWA KOMA RASHINTA
Sanyin gaba mai zuwa da 'yan 'kananan kuraje cikin farji , na sanya mace taji zafi wajen jima'i yayinda zakari ke kai-kawo cikin farji, wanda sau da yawa masu kurajen basu ma san suna da kurajen ba cikin al'aura, saidai suce suna jin zafi lokacin saduwa. Kurajen suna fashewa saboda da gugar zakari, sai wurin ya zama rauni. Hakan nasa mata tsoron jima'i da ganinsa  abin azabtarwa gare su mai maimakon abin  jin dadi. Sau tari basu san abinda ya haddasa zafin ba, wanda kuma mai yiwuwa ciwon sanyi. Ciwon sanyi na iya dakushe sha'awar mace ko namiji. Ciwon sanyi na iya haddasa bushewar gaba (vaginal dryness) wanda alamunsa shine daukewar ni'ima da 'kaikayin gaba. Idan gaba ya bushe zaiyi wahala mace da miji suji dadin jima'i in banda zafi.

Wasu daga cikin cututtukan sanyin da ake samu ta jima'i da ƙwayoyin halittu wanda ke haddasa su (a yaren turanci):

a) CHANCROID (bacteria) , cuta ce wacce ke zuwa da yanayin gyambo wani lokacin tare da ƙululu a hantsa.

b) CRABS (parasite), 'yan ƙananan halittu sosai , yanayin kwalkwata, masu cizo da tsotsar jini mai sanya mugun ƙaiƙayi. Ana samunsu daga gashin mara inda suka maida gidansu, ana kuma iya ɗaukarsu daga gashin gaban wani mutum zuwa na wani lokacin jima'i. Ana kuma iya samunsu ta kayan sawa, gado da sauransu.

c) GENITAL HERPES (virus) , cuta wacce take zuwa da ƙuraje masu ɗurar ruwa a baki ko kan zakari,  ƙurajen masu kama dana zazzaɓin dare (fever blisters). Idan ƙurajen suka fashe sai su zama gyambo. Haka kuma za'a iya samun ƙurajen a ɗuwawu, cinyoyi, ko a dubura. Ciwon kai ko baya, ko mura (flu) mai ɗauke da zazzaɓi,  ko kaluluwa da raunin jiki/kasala.

d) SYPHILIS (bacteria),  anfi samunta wajen 'yan luwaɗi. Tana da matakai bayan shigarta a jiki. Misali,  matakin farko (1): fitowar wani irin gyambo (chancre), wannan gyambon shine wajenda cutar ta shiga jikin mutum. Gyambon mai tauri, mai zagaye marar zafi. Wani lokacin abuɗe yake kuma da lema, ko zurfi musamman a hular zakari, wanda zaka ga wurin ya lotsa. Ana samunsa a zakari ko dubura ko leɓe (a baki). Ana kuma iya samun gyambon a ɓoye wani wajen cikin jiki. Mataki na biyu (2): ƙuraje a tafin hannu ko ƙarkashin tafin ƙafa ko wani sashen na jiki. 'Yar mura, zubar gashi, zazzabi marar tsanani, kasala,  murar maƙoshi, ciwon kai ko ciwon naman jiki da sauransu.  Mataki na gaba: mataki na gaba ko ƙarshe shine  wanda cutar zata iya ɓoyewa a jiki, 'buya idan ba'a magance taba,  kuma zata iya sanya ƙululun kansa/ciwon daji (tumour), makanta, mutuwar sashen jiki, matsalar ƙwalwa, kurumta, ciwon mantuwa mai tsanani (dimentia). Ana iya magance cutar cikin sauki da idan an lura da ita,  da wuri, da yardar Allah.

e)  TRICHOMONIASIS (parasitic organism) , cutar sanyi maisa warin farji,  mace zata iya harbin mijinta da  cutar ko mijin ga matar. Idan ya kasance miji nada wata mata ko yana neman matan waje masu cutar ko kuma macen ta taba saduwa da wani mutum mai cutar daya samo cutar daga wata mace, to akwai yiwuwar ma'aurata su samu cutar. Mazaje ba kaso suke sanin suna da cutar ba kasancewar alamomin cutar basu cika bayyana ga maza ba. Yawanci sai idan ciwon ya kama matan su suna cikin neman magani a asibiti suke gano suna da cutar. Wasu daga cikin  alamomin cutar ga mata: zubar ruwa mai launin kore-da-dorawa - mai kumfa da wari, zafi wajen yin fitsari, rashin jin dadi wajen jima'i. Wannan cuta tana da hadari ga mace mai juna-biyu da abinda ke cikinta
f) DA SAURANSU, suna da yawa kuma alamomin wani ciwon na kama da na wani ciwon wani lokacin. Don haka bincike a asibiti shine zai nuna nau'in ciwon.

Ciwon sanyi anfi yaɗasa ne ta hanyar jima'i kuma maza na iya harbin mata da ciwon ko kuma su matan masu ɗauke da ciwon su sakawa maza mararsa ciwon. Ciwon yafi yaɗuwa kuma anfi samunsa ga maza masu neman mata ko mata masu bin mazaje. Haka kuma mutum zaya iya kamuwa da ciwon ta wasu hanyoyin na daban daba  jima'i ba. Kuma lallai ciwon nada wuyar magani , musamman idan mutum bai samu  magani ingantacce ba. Zai iya yin wuyar magancewa saboda  rashin samun sahihin magani ko daɗewarsa cikin jiki ba'a magance ba.  Sau da yawa zaka ga cewa mutane sukan sha magunguna domin kaiwa ciwon hari da sukar alluran likita amma hakan bai  razana ciwon ba  sai kaga  yana wa mutane jeka-ka-dawo tsawon watanni koma shekaru da dama ba'a samu waraka ba.

Domin neman magani mai inganci / waraka akan waɗannan cututtuka sai a kira +2348084028794 (kuma WhatsApp no. ce) ko email madinahislamicmed@gmail.com.

Za'a iya neman maganin mu a ko ina kuke a Nigeria. Za'a  iya biyan kudin magani kai tsaye ta account namu mai rigistar kamfani (corporate account) da suna MADINAH ISLAMIC MEDICINE (account name) a banki, mu kuma mu tura maka magani a duk inda kuke a Nigeria da cajin kudin mota ko Post Office mai sauki, kudin tura magani ta mota mafi sauki (amma banda kudin magani), kudin mota yana kamawa daga N2000, N1500, N1000  har zuwa N500 - a motar haya ko a Post Office idan garin da kuke  ba'a Arewa bane. Ko azo office namu da yake a Katsina , Jihar Katsina.

Adreshin ofis: No. 34 Sabuwar Unguwa Dandagoro - kusa da solar Walu, Katsina, Jihar Katsina.

Adreshin mu: Titin Muhammad Dikko, Katsina, daura da makarantar sikandire ta K.C.K. (Katsina College Katsina), Shago na 5 , cikin shagunan Majalissar Malamai ta Kasa , reshin Jihar Katsina, Najeriya.

Kira +2348084028794

Go to:
www.madinahislamicmed.blogspot.com