Thursday 28 December 2017

ALAMOMIN BUƊAƊƊEN GABA


Yanayin halittar farji tamkar robar danƙo ce wacce zata iya buɗewa idan aka yi mata talala, haka kuma  zata iya komawa ta haɗe, wato ta  tsuke bayan buɗewa. Tsokokin bangon  farji masu motsi ne kuma zasu  iya tsukewa ko buɗewa idan mace tayi yunkurin tayi hakan, wato idan ta motsa su ko matse su ta ciki. Buɗaɗɗen farji (loose vagina) ko buɗewar farji (vaginal looseness) wani yanayi ne dake shafar mata da yawa musamman lokacin juna biyu da kuma bayan haihuwa inda farji ke canza yanayin halittarsa  ya ƙara girma, wato ya zama buɗaɗɗen wuri kasancewar naman dake zagaye da farji mai yiwa zakari zobe lokacin jima'i ya saki  , tsokokin sun saki basu iya damƙar zakari yanda ya kamata lokacin saduwa. Kamar dai yanayin halittar fatar jikin mutum, wasu mutanen fatarsu nada tauri  kamar roba marar sauƙin budewa idan aka jata,  wasu kuma fatarsu nada laushi da sauƙin yin talala idan aka jata, kusan haka itama halittar  gaban mace take. Wurin haihuwa jinjiri na fitowa ne ta farji inda wurin ke buɗewa sosai domin jinjiri ya fito. Bayan wani lokaci da haihuwa  farji na komawa ya tsuke . Duk da haka , farji ba zai taɓa komawa ba kamar yanda yake ada ko kamar na macen da bata taɓa haihuwa ba (ko budurwa) , koda kau anbi hanyoyin magani , farji zai zamanto ya ƙara  girma kaɗan ko da yawa.

Yawan haihuwar mace, budewar gaba saboda tiyatar likita/ƙarin kofa a lokacin haihuwa (tear) da yawan yin jima'i yau da gobe, na daga cikin dalilan dake haddasa budewar gaban mace. Idan buɗewar farji tayi yawa  yana zama kalubabale ga ma'aurata. Zaya iya zama matsala a rayuwarsu ta jima'i . Saboda wannan yanayi na sanya raguwar ɗanɗanon jima'i ga mace da mijinta koma ya hana macen jin ƙoluluwar daɗi  (orgasm) lokacin saduwa. Dalilin faruwar haka shine ,  farji baya matse/riƙe zakari da  kyau, ta yanda za'a samu ɗanɗanon gugar fata-da-fata tsakanin ma'aurata biyu wanda jin  wannan guga shine  zai kai ma'auratan biyu  ga gamsuwa mai ƙarfi a lokacin jima'i. Bugu da ƙari, wannan matsala  na iya saka mace cikin damuwa da jin cewa bata amsa sunanta na cikakkiyar mace ba saboda bata jin dadin saduwa kuma bata iya gamsar da mijinta da kyau. Hakan kuma zai iya sanya maigidan ya ƙara wani aure domin biyan buƙatarsa. Hakika gamsuwar aure itace saduwa mai daɗi tsakanin ma'aurata da zata samar da soyayya da zaman lafiya mai  ɗaurewa. Matsatstsen gaba (tight vagina) bakin gwargwado, yanayi ne mai kyau da zai iya ƙarawa mace gishirin  soyayya mai ƙarfi tsakaninta da mijinta.

YAYA ZA'AI KI GANE CEWA KO KINA DA  BUƊAƊƊEN GABA?

1. Mafi yawan mata masu fama da matsalar buɗaɗɗen gaba na fama da matsalar rashin riƙe fitsari , wato ɗigar fitsari.  Digar fitsarin zata iya faruwa a lokacinda kika ɗauki wani abu mai nauyi, ko lokacinda kika yi dariya, tari, ko atishawa. Wannan alamace cewa mace nada budadden gaba.Yawan shekaru, yawan haihuwa , yawan jima'i, tiyatar likita (ƙarin kofa) ko wani rauni a  gaban mace, ko   tsayawar al'ada (menopause) saboda karancin sinadarin "estrogen" na iya sanya raunin tsokokin farji wanda daga ƙarshe zai iya haddasa buɗewar tsokokin bangon  farji masu matse zakari .

2. Hanya ta biyu da zaki iya sanin ko kina da gaba mai faɗi itace: ki saka ɗan yatsanki guda (manuni) cikin gabanki sa'annan kiyi ƙoƙarin matse dan yatsan da tsokokin farjinki.  Idan har ki gwada yin hakan kuma ya zamanto baki iya jin kina matse dan yatsan da farji to zaya iya zama kina da babban wuri. Bugu da ƙari, idan kika saka yatsa 2 ko 3, misali manuninki da kuma yatsan tsakiyar hannnunki (mafi tsawo) , kuma baki ji wata alamar bangon farjinki yana matse yatsun ba to yiwuwar itace kina da buddden farji.

3. Idan ya zamanto yana da wuya kamin kiji ƙololuwar dadi (orgasm)/kawowa lokacin saduwa. Yana iya yiwuwa alamar budadden gaba ne. Haka kuma, raguwar jin dadi ba kamar daba shima na iya zama alamar.

4. Idan ya zamanto mace tana wasa da gabanta domin biyan buƙatarta kuma tafi sha'awar ta saka wani babban abu a gabanta akan ƙarami - wato bata jin dadin ƙaramin abu idan ta saka a farji sai babba. Shima alamace cewa mace nada girman farji.  A baya munyi bayani da tsoratarwa akan wasa da gaba. Yana da illa ga lafiya da rayuwar auren 'ya mace. Don haka sai a kiyaye.

5. Idan ya zamanto kina shan wahala kamin ki gamsar da mai gidanki wajen jima'i ba kamar daba.

6. Idan ya zamanto sai kin matse ko haɗe cinyoyin ki biyu  sosai sa'annan kike jin dadin jima'i da maigidanki. Wannan ma yana iya zama alamar budadden gaba. Duk da dai cewa wani lokacin yana iya zamantowa mijin ne keda ƙaramar al'aura. Amma idan kamin haihuwarki babu wannan matsalar sai daga baya to sai ki zargi budewar gaba.

7. Idan ya zamanto kina jin ƙarar fitar iska daga farjinki lokacin da maigidanki yake saduwa dake , iskan kamar fitar "tusa" amma ba tusa bace (fanny farting) kuma babu wari. Iskan yana shiga yana fitowa  lokacinda maigida yake kaikawo. Wannan alamace kina da budadden farji.

MINENE HANYOYIN TSUKE FARJI ?

Akwai hanyoyi da dama na matse gaba musamman bayan haihuwa wanda sun hada da hanyoyin magani, motsa jiki (exercise), tiyatar likita domin rage girman farji da sauransu. Wasu hanyoyin nada illa ga lafiya , wasu kuma hanyoyin basa da wata matsala ko hadari kamar dai yanda likitoci ke bayani. Wasu daga cikin hanyoyin:

1. Motsa jiki , hanyoyin motsa jiki na zamani domin matse gaban mace suna da yawa (such as kegel exercises) da sunaye. Motsa jikin ya shafi horo da mace zata iya bawa jikinta domin ya zamanto tsokokin gabanta masu motsi sun kara ƙarfi da tsukewa. Misali, wata kwararriyar likita a India Dr. Sangeeta Gomes ( Consultant Obstetrician and Gynaecologist) , ta nuna cewa mace zata iya inganta tsukewar gabanta idan tana yin motsa jikin dauke numfashi (breathing exercises). Zaki dauke numfashinki na tsawon 'yan daƙiƙoƙi (seconds) kadan sannan ki tsuke (tsokokin) farjinki matakam na tsawon wani lokaci a lokacinda kike mai dauke numfashin. Za kiyi hakan a kowace rana, sau 10 ko 15. Zaki iya yin hakan a kicin lokacinda kike aiki, a ofis, a tsaye ko a zaune , a ko ina  kuma  a ko wane wuri bata tare da ma wani yasan abinda kike yi ba. Sa'annan  zaki yawaita cin Ƴaƴan itatatuwa (kayan marmari) da abincin ganye (vegetables). Wannan ko shakka babu zai taimakawa  mace wajen matse gaba domin gyara aurenta. Wani nau'in motsa jikin kuma shine ake cema "Kegel exercise". Toh  yaya ake yinshi? Dr. Gomes ta nuna cewa idan kina yin fitsari sai ki tsaida fitar fitsarin, wato ki  riƙe fitarin, ki danne sa na tsawon daƙiƙoƙi 10 , wato ki ƙirga 1 zuwa 10 sa'annan ki saki fitsarin a hankali a hankali. Zaki iya yin hakan sau 2 ko 3 a rana idan za kiyi fitsari. Shima wannan nau'in motsa jikin na tsuke gaban mace.

2. Hanya ta biyu shine wanke gaba da ruwan sanyi mai ƙankara. Yana  taimakawa  wajen matse gaba amma sai an hada da motsa jikin da muka yi bayani. Wannan yana daga cikin hanyoyin da Dr. Gomes ta zayyana. Amma zaifi dacewa ace sai mace ta gama wankan jegonta na kwana 40 kwatakwata sa'annan tayi amfani da ruwan sanyin , wato bayan ta koma "normal". Saɓanin yanda al'adar Bahaushe tayi imani dashi cewa ruwan sanyi na lalata gaban mace ,wasu likitocin a wasu al'adun na ganin yana matse gaba.

3. Yin amfani da aluf (alum). Aluf yana matse gaba sosai sai dai likitoci na tsoratarwa akan yin hakan saboda da sinadarin kemikal ne.

4. Yin tiyatar likita domin rage budewar farji. Wannan ma hanya ce ta zamani amma ana tsoratarwa akan yin hakan saboda wasu dalilan lafiya.

5. Yunƙurin tsuke gaba a lokacin saduwa, wato ki matse farjinki ta ciki lokacinda mijinki yake kaikawo. Zaki yawaita yunƙuri domin tsuke gabanki domin mijinki yaji alamun ana riƙe masa al'aura tamkar zobe zagayen gabansa. Idan mace na yawaita yin da haka to zai zama ɗabi'arta kuma nan gaba ba zata san ma tanayin hakan ba saboda ta riga ta horar da jikinta, kuma hakan zai inganta jin daɗin mijinta sosai. Allah Ya taimaka.

6. Da sauransu.

Za'a iya neman taimako na musamman daga cibiyar mu domin magance wannan matsala wacce za'a haɗa da bayanan da mukayi anan domin samun sakamako mai kyau, da yardar Allah.

Sai a kira +2348084028794 (also WhatsApp number)

Email: madinahislamicmed@gmail.com
Blog: www.madinahislamicmed.blogspot.com

Ko azo shago ko office namu kamar haka:

Address: No. 5 Muhammad Dikko Road, daura da makarantar sikandire ta KCK (Katsina College Katsina) - hanyar babban asibitin Katsina, jihar Katsina.

Office Address: No.34 Sabuwar Unguwa , Dandagoro Area, Katsina, Jihar Katsina.

Yi LIKING shafin mu domin samun bayanan lafiya irin wadannan masu amfani.

https://m.facebook.com/MadinahIslamicMedicine/?ref=bookmarks

Tuesday 12 December 2017

ALAMOMIN CIWON SANYIN MARA NA MAZA/ SANYIN GABA


Ciwon sanyi cuta ce da akafi yaɗawa ta hanyar jima'i (STDs/STIs) .ƙwayoyin halittun dake sanya cutar ana yaɗa sune daga wani mutum zuwa wani mutum, ta jini, maniyyi, ruwan farji ko ruwan jiki. Alamomin ciwon sanyi ga maza sun sha banban tsakanin mutane wanda ciwon ya harba. Hakan ya danganta ne da nau'in ƙwayar halittar cutar wacce ta haddasa ciwon  da kuma matakin da cutar ta takai a  jikin mutum - ma'ana, alamomi ko matakin farko da kamuwar cutar ko alamomi na gaba bayan ta soma jimawa a jikin marar lafiyar. Haka kuma, suma yanayin alamomin sunsha banban ta fuskar tsanani ko sauƙinsu,  koma rashin ganin alama ko ɗaya duk da  cewa kau akwai cutar a jikin marar lafiyar. Maza da yawa na zargin suna da ciwon sanyi ne kaɗai a lokacinda suka ga wasu alamomi da basu saba gani ba (baƙi) ga al'aurarsu, misali , kamar: feshin ƙananan ƙuraje ko ƙaikayi, ko fitar farin ruwa, jin raɗaɗin zafi daga maraina da sauransu. A taƙaice dai, alamomin ciwon sanyin maza zasu iya ɓuya amma gwaji a asibiti zai iya nuna akwai cutar idan akwaita.

Ciwon sanyi anfi yaɗasa ne ta hanyar jima'i kuma maza na iya harbin mata da ciwon ko kuma su matan masu ɗauke da ciwon su sakawa maza mararsa ciwon. Ciwon yafi yaɗuwa kuma anfi samunsa ga maza masu neman mata ko mata masu bin mazaje. Haka kuma mutum zaya iya kamuwa da ciwon ta wasu hanyoyin na daban daba  jima'i ba. Kuma lallai ciwon nada wuyar magani , musamman idan mutum bai samu  magani ingantacce ba. Zai iya yin wuyar magancewa saboda  rashin samun sahihin magani ko daɗewarsa cikin jiki ba'a magance ba.  Sau da yawa zaka ga cewa mutane sukan sha magunguna domin kaiwa ciwon hari da sukar alluran likita amma hakan bai  razana ciwon ba  sai kaga  yana ma mutane jeka-ka-dawo tsawon watanni koma shekaru ba'a samu waraka ba.

Alamomin ciwon sanyin maza wanda akafi samu bainar mutane (game gari) :
1. ƙananan ƙuraje akan zakari, ko maraina ko ƙasansu.
2. ƙaikayi akan zakari (kan hular).
3. Fitar farin ruwa daga zakari, mai kalar madara ko ɗorawa, mai kauri ko wanda ya tsinke.
4. Jin zafi wajen yin fitsari.
5. Jin zafi yayin fitar maniyyi.
6. ƙuraje masu ɗurar ruwa da fashewa akan zakari.
Alamomi ciwon sanyin maza wanda ba game gari ba:
1. Rauni (gyambo) ga zakari ko maraina.
2. Zafi da kumburin maraina
3. Zafi da kumburi daga kwararo da  fitsari da maniyyi suke fitowa daga cikin zakari.
4. Zazzaɓi

Matsalolin jima'i da ciwon sanyi zai iya haddasa ma maza:

1. RASHIN KARFIN MAZAKUTA: Bincike ya nuna cewa cutar ciwon sanyi mai suna da turanci "Chlamydia" (kilamiidiya) zata iya sanya matsalar rashin ƙarfin mazakuta idan ciwon yayi ƙamari ba'a magance shi ba. Cutar maɓannaciya ce da take illa a ɓoye kuma mafi yawanci bata nuna wata alama a zahiri ga mai ɗauke da cutar. Ana samunta bainar mutane da yawa. Rashin ƙarfin mazakuta na nufin matsalar rashin cikakken ƙarfin al’aurar namiji ko raguwar ƙarfin al’aura yayinda aka fara saduwa ko kuma rashin miƙewar al’aura yayinda ake buƙatar fara jima’i. Bugu da ƙari,  matsalar na iya zuwa da saurin kawowa/inzali. Rashin  ƙarfin maza zai iya saka magidanci cikin damuwa da tawayar jinɗaɗin rayuwarsa ta jima'i, ko jin cewa bai cika mutum namiji ba, ko rashin haifuwa kasancewar bazai iya yima iyalinsa ciki ba saboda rashin miƙewar al'aura. Zuwa asibiti da wuri ko cibiyar lafiya zai iya tsiratar da mai wannan matsala,  inshaaAllah.

2 RASHIN HAIFUWA:. Cutar sanyi mai suna "Gonorrhea" (Gonoriya) , kamar dai ƙwayar cutar "Chlamydia", cutace daga halittar "bacteria" kuma zata iya laɓewa a cikin jiki ba tare da wasu alamomi ba. Duk da haka, tana zuwa da alamomi kamar fitar farin ruwa, mai kalar madara daga farkon cutar,  daga nan sai ya koma ɗorawa, mai kauri da yawa, wani lokacin harda ɗan jini-jini. Yin fitsari da zafi da yawan yin fitsari, ƙaikayin dubura, zubar jini,  murar maƙoshi/maƙogwaro, jan- ido ko ƙananan kuraje, ciwon gaɓoɓi da sauransu. Idan ba'a lura da cutar da wuri ba kuma aka magance ta, zata iya sanya rashin haifuwa ga namiji ko mace.

Nau'in ciwon sanyi (ire-irensu) suna da yawa kuma kowanne iri akwai ƙwayar halittar dake haddasa ciwon da alamominsa da kuma matakan cutar a jikin 'dan adam. Sunayen cututtukan da turanci suna da yawa kamar yawan cututtukan. Cutar sida/ƙanjamau (AIDS/HIV) tana daga cikin manyansu  saboda itama anfi yaɗata ta jima'i, kuma sau dayawa itace ke gayyatar sauran cututtuka a jikin 'dan adam.

3) KANKANCEWAR ZAKARI,  duk da dai cewa babu wani sahihin bayani a kimiyyance dake nuna cewa ciwon sanyi yana sa azzakarin namiji baligi ya koma ƙarami, akwai rahotanni da yawa daga mutane na ƙorafin cewa sanyi ya sace musu girman zakari. Wannan zance haka yake a zahiri, masu ciwon sanyi sune suka fi lura da damuwa akan ƙanƙancewar alƙalummansu.

Wasu daga cikin cututtukan sanyin da ake samu ta jima'i da ƙwayoyin halittu wanda ke haddasa su (a yaren turanci):

a) CHANCROID (bacteria) , cuta ce wacce ke zuwa da yanayin gyambo wani lokacin tare da ƙululu a hantsa.

b) CRABS (parasite), 'yan ƙananan halittu sosai , yanayin kwalkwata, masu cizo da tsotsar jini mai sanya mugun ƙaiƙayi. Ana samunsu daga gashin mara inda suka maida gidansu, ana kuma iya ɗaukarsu daga gashin gaban wani mutum zuwa na wani lokacin jima'i. Ana kuma iya samunsu ta kayan sawa, gado da sauransu.

c) GENITAL HERPES (virus) , cuta wacce take zuwa da ƙuraje masu ɗurar ruwa a baki ko kan zakari,  ƙurajen masu kama dana zazzaɓin dare (fever blisters). Idan ƙurajen suka fashe sai su zama gyambo. Haka kuma za'a iya samun ƙurajen a ɗuwawu, cinyoyi, ko a dubura. Ciwon kai ko baya, ko mura (flu) mai ɗauke da zazzaɓi,  ko kaluluwa da raunin jiki/kasala.

d) SYPHILIS (bacteria),  anfi samunta wajen 'yan luwaɗi. Tana da matakai bayan shigarta a jiki. Misali,  matakin farko (1): fitowar wani irin gyambo (chancre), wannan gyambon shine wajenda cutar ta shiga jikin mutum. Gyambon mai tauri, mai zagaye marar zafi. Wani lokacin abuɗe yake kuma da lema, ko zurfi musamman a hular zakari, wanda zaka ga wurin ya lotsa. Ana samunsa a zakari ko dubura ko leɓe (a baki). Ana kuma iya samun gyambon a ɓoye wani wajen cikin jiki. Mataki na biyu (2): ƙuraje a tafin hannu ko ƙarkashin tafin ƙafa ko wani sashen na jiki. 'Yar mura, zubar gashi, zazzabi marar tsanani, kasala,  murar maƙoshi, ciwon kai ko ciwon naman jiki da sauransu.  Mataki na gaba: mataki na gaba ko ƙarshe shine  wanda cutar zata iya ɓoyewa a jiki, 'buya idan ba'a magance taba,  kuma zata iya sanya ƙululun kansa/ciwon daji (tumour), makanta, mutuwar sashen jiki, matsalar ƙwalwa, kurumta, ciwon mantuwa mai tsanani (dimentia). Ana iya magance cutar cikin sauki da idan an lura da ita,  da wuri, da yardar Allah.

e) DA SAURANSU, suna da yawa kuma alamomin wani ciwon na kama da na wani ciwon wani lokacin. Don haka bincike a asibiti shine zai nuna nau'in ciwon.

Ciwon sanyi yana da haɗari sosai. Ya zama dole ga mutane su tsaya ga matan su na Sunnah idan har suna son lafiyarsu. Ciwon sanyi yana nan akan hanyar mai neman mata da zinace-zinace, zai cimmasa. Akwai ciwuka masu haɗari sosai kamar AIDS/HIV, wanda zasu iya wargaza iyali. Don haka maison zaman lafiyarsa da rayuwa mai kyau sai yaji tsoron Allah. Wanda kuma Allah Ya jarabta da ciwon bata hanyar zina ba to sai ya nemi magani,  haka shima wanda ya tuba ga Allah. Allah Ya bawa Musulmi lafiya.

Domin neman ƙarin bayani ko neman magani/waraka sai a

 kira +234808 402 8794
 domin neman taimako na musamman daga cibiyar mu ta kiwon lafiya ta Musulunci mai albarka da mutane.
Shafin mu na yanar gizo :
www.madinahislamicmed.blogspot.com
E-mail: madinahislamicmed@gmail.com

Adreshin mu: Sai a ziyarci cibiyar kai tsaye dake Katsina, Jihar Katsina, Najeriya-

Adreshin mu: Titin Muhammad Dikko, Katsina, daura da makarantar sikandire ta K.C.K. (Katsina College Katsina), Shago na 5 , cikin shagunan Majalissar Malamai ta Kasa , reshin Jihar Katsina, Najeriya.

Adreshin ofis: No. 34 Sabuwar Unguwa Dandagoro,  Katsina.

LIKE our Facebook page domin samun bayanan lafiya irin wadannan masu muhimmanci:
https://mobile.facebook.com/MadinahIslamicMedicine