Zogale
(Moringa oleifera) itaciya ce mai ban mamaki dangane
da amfaninta ga lafiyar 'dan adam. Allah
(S.W.T.) yasa albarka da waraka ga
wannan itaciya. Zogale abinci ne mai romon sinadaran lafiya a bayan kasa, baza'a iya kwatanta shiba da sauran ganyaye ta fuskar amfaninsa ga lafiyar 'dan adam. Wannan dalili yasa wasu ke kiransa da suna ITACIYAR RAYUWA ( The tree of life). Ganyen zogale na kunshe da romon
sinadari mai yawa na VITAMIN A (wanda ke
karama idanun 'dan adam lafiya da gani) fiye da
VITAMIN A dake cikin karas har sau 4. Ganyen
zogale haka kuma yana da sinadari mai yawa na
CALCIUM (mai sanya qashi da hakoran 'dan
adam kwari da lafiya) fiye da yawan na cikin madara linki 4. Yana da sinadarin
VITAMIN C (wanda ke karfafa garkuwar jikin 'dan adam domin fada da cututtuka masu kai farmaki ga lafiyar mutum),
yanada wannan sinadarin mai yawa fiye da irin
wannan sinadarin dake cikin lemu har linki 7.
Haka kuma yanada sinadarin PROTEIN (sinadari
mai gina jikin 'dan adam), fiye da na cikin madara sau 2. Bugu da qari, yana da VITAMIN E
(sinari mai gyara fata da lafiyar fata). Masana ilimin kimiyya da bincike akan wannan itaciyar lafiya sun bayyana cewa ZOGALE/ZOGALA nada wadannan magunguna:
-Yana daidaita sukari cikin jini.
-Yana rage hawan-jini
-Yana taimakama mace mai shayarwa da ruwan nono.
-Yana kashe kwayoyin cutar bakteriya (bacteria).
-Yana saukake narkewar abinci a ciki.
-Yana wanke ciki, musamman idan aka cishi kafin aci komai.
-Yana kare lafiyar hanta da koda.
-Yana taimakawa da kuzari ga jikin mutum.
-Yana rage kiba.
-Yana gyara kwalwa.
Da sauransu.
No comments:
Post a Comment