Sunday 17 January 2016

Matsalolin Ciwon Sanyin-Mata /Sanyin Gaba [Vaginitis/vaginal infections/ toilet infections] da Rigakafi

SANYI kalma ce mai fadin ma'ana da Malam Bahaushe ke yin amfani da ita domin yin kokarin bayanan wasu matsalolin lafiya na daban-daban , misali , ciwon-sanyin jiki [rheumatism], ciwon sanyin mura [cold and flu] da ciwon sanyin-mara ko ciwon sanyin-mata [vaginitis] ko ciwon sanyin maza-da-mata da ake dauka ta hanyar jima'i [STDs/STIs like chlamydia, gonorrhea, syphilis, genital herpes, HPV etc] da sauransu. Saidai Malam Bahaushe baya kiran ciwon sida/kanjamau [HIV/AIDS] da ciwon sanyin-mara duk da cewa kau anfi yada cutar ta jima'i.

Za muyi bayani akan ciwon sanyin-mata ne kadai [Vaginitis]. Matsalolin ciwon sanyin-mata [vaginitis/vaginal infections or toilet infections] wasu cututuka ne ko matsaloli dake addabar gaban mace, wato cututtuka masu sanya kaikayin farji, ko radadin ciwo, kumburin gaba ko warin gaba , zubar farin ruwa, kurajen farji, zafi wajen yin fitsari ko wajen yin jima'i da sauransu. Ciwon sanyin-wata matsala ce dake faruwa ga mata da dama a cikin wasu lokutta na rayuwarsu. Ana samun wannan cututtuka ko matsaloli sabili da wani sauyin yanayin jiki da mata ke samu wasu lokutta da kuma sabili da wasu kwayoyin halittar 'bacteria' da 'fungus' dake zaune cikin al'aurar mace, haka kuma , mata na iya samun wannan ciwon a lokacin juna-biyu da kuma shayarwa [during pregnancy and breastfeeding] . Har ila yau, za'a iya samun ciwon ta hanyar jima'i [vaginal intercouse] da wasu dalilan ko hanyoyi na daban.

Nau'in ciwukan sanyin-mata suna da yawa, to amma bincike ya nuna cewa ciwon sanyin-mata nau'i uku ne (3) suka fi addabar mata da yawa. Za muyi bayani akansu kadai, a takaice insha Allahu, sune kamar haka: (sunayen su da yaren turanci) 1. 'Yeast infection' 2. 'Bacterial vaginosis' 3. 'Trichomonas'

1. ‘Yeast infection’ ('Candidiasis'). Akwai wasu kwayoyin halittun 'fungas' (masu suna 'candida') sune ke haddasa 'Yeat infection'. Su wadannan halittu wanda kwayar idon mutum baza ta iya ganin suba , saboda kankaantar su saida taimakon madubin likita ne za'a iya ganin su [microscope] . Halittun suna rayuwa a wasu wurare cikin jikin mutum kuma adadinsu baya da yawa . Ana samunsu cikin farji kuma, asali basu cika cutarwa ba.'Candida' suna san wuri mai gumi, lema da rashin iska domin girma da yaduwa. Idan suka samu wannan yanayi da suke so toh za suyi yawa su kuma haddasa ciwon sanyin 'Yeast infection'. Anfi yawan samun irin wannan ciwon sanyi ga mata da yawa , kusan kashi 75 cikin 100 na mata sun taba samun wannan ciwon a cikin wasu lokutta na rayuwarsu. Alamomin cutar sun hada da: zubar farin ruwa mai kauri daga farji, kuraje ko kaikayin farji da kuma labban farji suyi jawur ko cikin farji.

2. ‘Bacterial vaginosis’ , cuta ce dake shafar farji sabili da girman wasu kwayoyin halittun 'bacteria' masu cutarwa dake cikin farji suna rayuwa. Alamonin cutar sun hada da: zubar ruwa mai 'karnin kifi daga farji, warin sa musamman lokacin jima'i, ko radadin zafi lokacin fitsari, amma babu kaiyayi cikin alamomin. Alamomin cutar kuma na iya 'buya.

3. ‘Trichomoniasis ’ : A cikin cututtukan sanyi da muka yi bayanin su a baya (wato cuta ta 1 da ta 2) , 'Trichomoniasis' ta 3, itace cutar sanyin-mata da ake yadawa ta hanyar jima'i ga maza (STD) fiye da sauran a zahiri, wato mace zata iya harbin mijinta da cutar ko mijin ga matar. Idan ya kasance miji nada wata mata ko yana neman matan waje masu cutar ko kuma macen ta taba saduwa da wani mutum mai cutar daya samo cutar daga wata mace, to akwai yiwuwar ma'aurata su samu cutar koma mafi hadari HIV da wasu cututtukan jima'i (STDs). Ana kiran 'yar kankanuwar halittar [parasitic organism] dake sanya wannan cuta da suna 'Trichomonas vaginalis'. Mazaje ba kaso suke sanin suna da cutar ba kasancewar alamomin cutar basu cika bayyana ga maza ba. Yawanci sai idan ciwon ya kama matan su suna cikin neman magani suke gano suna da cutar. Idan anyi sa'a alamomin ciwon sun bayyana ga maza, ana iya samun alamomi kamar haka: zubar farin-ruwa kadan, zafi kadan bayan fitsari ko bayan fitar maniyyi. Alamomin cutar ga mata suna iya kama da ciwon sanyi na 1 da na 2 da muka yi bayani a sama, ko kuma: zubar ruwa mai launin kore-da-dorawa - mai kumfa da wari, zafi wajen yin fitsari, rashin jin dadi wajen jima'i. Wannan cuta tana da hadari ga mace mai juna-biyu ga abunda ke cikinta, musamman idan ba'a nemi magani ba.

Matakin da Zaki Dauka Idan Har Kinga Alamomin Ciwon-Sanyi

Idan har kina da daya ko biyu daga cikin wadannan alamomin ciwon kai koma fiye da haka, mataki na farko da zaki dauka shine, ki garzaya zuwa asibiti ko wata cibiyar lafiya domin neman taimako. A asibiti ne idan anga kwararriyar likita, musamman 'gynaecologists' wanda suka shahara akan fagen matsalolin mata , za'a duba matsalar, sa'annan ayi bincike 'lab test' ko da 'microscope' asan abunda ke damun ki a kuma baki maganin daya dace da shawarwari. Haka kuma , idan anyi binciken kuma an tabbatar da irin ciwon sanyin dake damun marar lafiyar toh za'a iya zuwa wannan cibiya tamu mai albarka ta Madinah Islamic Medicine Katsina domin neman magani/waraka da yardar Allah.

Wasu Halayen Da Zasu Iya Taimakawa Wajen Samun Ciwon Sanyi da Rigakafin su:

> Wajen Tsaftace Gaba [ Vaginal Douching] A cikin farji akwai wasu kwayoyin halittar 'bacteria' marar sa cutarwa kuma masu amfani (wato 'Normal flora'). Su 'normal flora' suna taimakawa wajen bada kariya ga farji daga wasu nau'in 'bacteria' na daban masu cutarwa (masu suna 'Bacterial pathogens'). Garin neman kiba akan nemo rama, wasu mata kanyi amfani da wasu hanyoyi domin tsaftace farji, kamar ta hanyar yin amfani da sabullan magani, harba magani cikin gaba, ruwan dumi da gishiri ko dettol domin wanke farji don tsaftacewa ko rigakafi daga 'bacteria' da zata iya cutarwa. Wadannan abubuwa da ake amfani dasu don rigakafi na kashe 'bacteria' masu amfani [the normal flora] cikin farji, hakan zaisa 'bacteria' masu cutarwa su samu damar shigowa cikin farji su cutar da lafiya da ciwon-sanyi, sabili da babu 'bacteria' mai bada kariya dake hana su shiga ko 'barna. Don haka , idan har lafiyar ki lau kuma kina son tsaftace gabanki toh sai ayi amfani da ruwa , musamman lokacin wanka a tsaftace gaba. Ki guji fesa turare ko wanke gaba da sabili mai kamshi. Idan har lafiyar ki lau kada kiyi amfani da wani abu idan ba ruwa ba. Ki sani cewa farji yana tsaftace kanshi da kanshi a yanayin halittarshi, yana fitar da wani ruwa [secrets fluid] na musamman dake wanke illahirin gaban mace.

> Kayan-sawa na ciki/wandon pant [Under-wears/under-pants] Wasu matan kanyi amfani da wandon pant ko 'skin-tight' kwana da kwanaki ba tare da canzawa ba ko wankewa. Irin wannan halin kazanta na dauda da lema, na bawa cututtuka (Germs) dama su shiga cikin farji su kuma girma cikin 'dan kankanin lokaci har su haddasa ciwon sanyi. Don haka , yana da kyau a canza 'under-wears' wankakku masu tsafta a kowace rana. Idan lokacin zafi ne ko kinyi aiki kuma akwai zufa a jikin ki to sai ki canza wando akalla sau 2 a rana. Kuma yana da kyau ayi amfani da wandon da akayi da auduga [cotton under-wears] domin yana taimakawa wajen tsotse lema da bushewa, sabanin wando da akayi da 'nylon' [nylon under-wear].

> Wajen wanke bayan-gida [Way of cleaning the anus after faeces] Yana daga cikin halayen wasu mata idan sunyi bahaya suna fara wanke dubura sa'annan gabansu, wasu kuma suna hadawa ne duka , wato gabansu da dubura su wanke lokaci daya, wannan ba dabi'a bace ba mai kyau ga mace, domin kuwa idan kika wanke dubura farko sa'annan gabanki ko kika wanke su a lokaci daya toh zaki iya goga ma farjinki wasu cututtuka dake cikin kashi/bayan gida. Don haka , sai a fara wanke farji farko, bayan angama wanke shi da ruwa da kyau to sai a wanke dubura.'Toilet infection' kalma ce da mutane suka kirkira kuma ta samu asali ne daga mummunar dabi'ar wanke dubara tare da farji, wanda wasu ke tunanin shine ke kawo cutar sanyin-mata. Toh saidai dadilan dake kawo cutar sanyin mata suna da yawa kamar dai yanda mu kayi bayani a baya, kuma ita kalmar 'Toilet infection' ba tada muhalli a cikin 'Kamus din likitoci a matsayin sunan cuta. Mutane ne wanda ba ma'aikatan lafiya ba suke amfani da kalmar da nufin 'vaginal infections' ko 'vaginitis' (kalmar da ma'aikatan lafiya suka fi amfani da ita).

> Tsugunni a bandaki [Squatting in toilets] Yin tsugunni a bandakin da mutane da yawa ke amfani dashi nada hadari ga lafiya, musamman bandaki mai dauda da kazanta. Sau da yawa mace zata tsugunna tayi fitsari cikin bandaki sai fitsarinta ya doki kasa yayi tsalle ya fallatso mata ko ya dawo mata tare da wani ruwan dake kwance a kasa ko fitsarin wata macen.Digo daya na fitsarin mai ciwon sanyi zai iya harbar ki da ciwon idan ya fallatso maki ga ga gaba.Don haka, idan zaki yi fitsari kada kiyi inda kowa keyin fitsari a cikin bandaki, ki samu wuri na daban mai tsafta cikin bandakin kuma inda babu ruwa a kwance. Haka kuma kada ki bari gabanki ya taba kasa. Kiyi fitsari a hankali. A yawaita wanke bandaki kullum da dettol ko danginshi 'germicides' masu inganci domin kashe cututtuka.

> Yin amfani da wandon pant na 'kawar ki, yar'uwar ki ko wata mace [Sharing under-wears] Kawar ki, kanwar ki ko wata yar'uwarki mutane ne masu iya kamuwa da cuta. Zai iya kasancewa suna da ciwon-sanyi , don haka idan kina jin cewa kinyarda da ita ko kuma kun zama jini da tsoka toh ki shirya fama da ciwon sanyi da zasu iya harbarki dashi idan kina amfani da wandon su. Koda basu da ciwon , bai kamata ku rinka amfani da pant din junanku ba. Riga kafi yafi magani.

> Rashin kula wajen yin jima'i [Sexual intercourse without care] Yanada matukar muhimmanci ki kiyaye da jin rauni a farji a lokacin saduwa da maigida. Barin gashin gaba ba'a rage shiba da kuma yin jima'i tsawon lokaci ko da karfin tsiya na daga cikin dalilan dake sa mace ta samu rauni a gabanta. Samun rauni ko fashewar fata cikin al'aura na bawa cututtuka kofar shiga jiki su cutar da lafiya da 'infections'.

>Mataki na biyu da zaki iya dauka shine: bayan kin san abunda ke damun ki domin a asibiti an bayyana maki, idan har ya tabbata sanyi ne kuma kin sha magani amma baki samu sauki ba, ko kuma kin samu sauki amma baki warke duka ba yana dawowa, toh zaki iya amfani da wannan taimakon da zamu baki :

Ki samu 'Khal tufah' [Apple cider vinegar] a Islamic Chemist. Ki tafasa ruwa mai yawa yayi zafi, idan yayi 'dumi sai ki samu robar wanka ki juye ruwan ya cika robar, sa'anna ki zuba khal tufah cikin ruwan kimanin adadin kofin shayi [small tea cup] 1 ko 2 cikin robar wankan, sai ki zauna ciki minti 15. Bayan kin tashi daga robar sai ki tsane lemar ruwan dake gabanki da tawul mai kyau ya bushe. Sai ki samu man-kwakwa [coconut oil] da auduga ki goge gabanki, man-kwakwa nada sinadarai masu kashe kwayoyin cuta [ antiviral, antibacterial and antifungal properties] Kiyi amfani da man-kwakwa sau 3 a rana. Za kiyi amfani da Khal tufah kamar yanda mu kayi bayani kullum sau 1 a rana har sai kin samu sauki.
Haka kuma, zaki iya amfani da Tafarnuwa [Garlic]. Ki samu salar tafarnuwa 2 ko 1 ki karkare bawon da ledar ta, kiyi matsi dasu da dare idan zaki kwanta bacci sai da safe ki cire ki yar. Tafarnuwa magani ce mai karfi (kuma 'antibiotic') , itama tana da sinadarai masu kashe cututtuka [antiviral, antibacterial and antifungal properties]. Kuma zaki iya cin tafarnuwa ko amfani da 'capsules' nata, idan zaki iya.
Bugu da kari, zaki iya neman garin Hulba [Fenugreek powder] a Islamic Chemist da zuma (honey) kiyi shayi, ki tasa ruwa ki zuba hulba karamin cokali 1 cikin kofin shayi ki motsa, sai ki sha. Kiyi haka safe da dare, har sai kin samu sauki. Idan mace tana da juna-biyu kada tayi haka sai ta nemi shawarar likitan Islamic Chemist/ likitan asibiti da yasan 'Hulba' ko masani amma babu laifi ga mai shayarwa tayi amfani da hulba, hakan zai kara samar mata da ruwan nono. Masu juna-biyu su guji sha-shayen magunguna ba tare da izinin likita ba. Allah ya taimaka.

Madinah Islamic Medicine: Wannan bayanai Da suka gabata kokarin bincike ne da wallafar Hausa na Madinah Islamic, Katsina. Za'a iya yima bayanan gyara a duk lokacin da bukatar hakan ta taso. Domin neman karin bayani ko gyara, ko kuma neman magungunan Musulunci akan matsalar da wasu:

Kira +2348084028794 

ko email: madinahislamicmed@gmail.com