Monday 24 March 2014

AMFANIN ZUMA GA LAFIYA (A TAKAICE)

Zuma wani irin abinci ne mai zaki kamar shigen suga wanda kudan-zuma ke samarwa daga furen itace ko shuka -wato wani romon sinadari dake cikin furen itace ko shuka da kudan-zuma ke tsotsowa (nectar) domin sarrafa ruwan zuma. Mutane na amfani da zuma a matsayin abinci ko magani. Sabili da muhimmancin zuma, a cikin surorin Alqur'ani maigirma - akwai surah mai sunan kudan zuma - wato Surat An- Nahl. Allah (S.W.A.) ya bayyana mana muhimmancin zuma ga rayuwar 'dan adam a cikin wannan surah " ...waraka ce ga mutane." (An Nahl: 69). Hakika kuma Manzon Allah (S.A.W.) ya bayyana mana muhimmancin ta a wasu hadisai.
Don haka, zuma nada amfani ga lafiya kamar haka:
1. Tana kashe cutar bakteriya da fangas (bacteria & fungus) da kuma bada kariya daga kamuwa da ciwon-daji. Bincike ya nuna cewa zuma mai duhu-duhu tafi wannan amfanin.
2. Tana warkar da ciwo ko gyambo idan ana shafawa ko sha.
3. Tana taimaka ma mai-mura, tari , atishawa da sauran matsalolin sanyi.
4. Maganin gudawa ce.
5. Maganin gyambon ciki - Ulcer.
6. Tana karfafa garkuwar jiki.
7. Tana rage hadarin kamuwa daga cututtukan zuciya, musamman idan aka hadata da Kirfat (cinnamon).
8. Tana sanya kuzari a jiki.
9. Tana rage nauyin kiba. Shan ruwa mai-`dumi da lemun tsami tare da zuma kafin aci komi da safe zai taimaka wajen rage `kiba.
10. Tana saukaka narkewar abinci ga masu fama da rashin narkewar abinci.
11. Tana rage kumburi mai sanya waje yayi kalar ja da radadin ciwo.
12. Tana kyautata lafiyar kwalwa.
13. Tana gyara fata da rage kurajen fuska (pimples) idan ana shafa ta.
14. Da sauransu.












No comments:

Post a Comment