Monday, 16 February 2026

CIWON SANYI: Saƙon jiki kafin bayyanar matsala


Jiki yana magana,

amma bada murya ba.

Wasu lokuta yana magana ne da alama,

da sauyi,

da ƙananan canje-canje da mata kan raina.


Ƙaramar alama a yau,

na iya zama babban abu gobe.

Ba don tsoro ba,

amma don lura.


Domin jiki ba maƙiyi ba ne,

aboki ne da ke bada shawara.


Tambayar ita ce:

Kina kula da abin da jikin ke nuna miki?


MINENE CIWON SANYIN MARA?


KARIN HASKE AKAN KALMAR CIWON SANYI (INFECTIONS)


A cikin al'ummar Hausawa, ana amfani da kalmar "Ciwon Sanyi" don bayyana abubuwa da dama. To amma a likitance, ya kamata mu rarrabe su:


1. Infection na farji, Sanyin Mata (Vaginal Infections):

Kamar "Candidiasis" (Yeast) ko "Bacterial Vaginosis". Waɗannan galibi ba sa yaduwa ta jima'i, amma suna kawo ƙaiƙayi da fitar ruwa.


2. Ciwon Sanyin Mara na Fitsari (UTI):

Wannan yana shafar mafitsara ne, yana kawo zafi lokacin fitsari.


3. Cututtukan da ake samu ta Jima'i (STD/STIs), sanyin mata da maza , ciwon da mata ko maza zasu iya sawa juna ta jima'i:

Kamar Syphilis, Gonorrhea, ko Chlamydia. Waɗannan su ne suka fi haɗari ga mahaifa idan ba a yi magani ba.


TA HANYAR JIMA'I: Ciwon sanyin mara cuta ce da ake iya samu ta hanyar jima’i (STD/STIs).

Ana iya kamuwa da ita daga mutum zuwa wani mutum ta hanyar ruwan jiki, jini, ko mu’amalar al’aura.


Wasu nau’ikan cutar na bayyana da alamomi,

wasu kuma na iya kasancewa a jiki ba tare da wata alama ba. Saboda haka mutum na iya ɗauke da cuta, amma bai sani ba.


ALAMOMIN CIWON SANYIN MARA


Ga wasu daga cikin alamomin da ake iya gani:


1. Sauyin ruwa daga farji (launi, kauri, wari).


A dabi’a, farji yana fitar da ruwa na al’ada wanda ke taimakawa tsaftace jiki da kiyaye lafiyar gaba. Wannan ruwan yawanci ba ya wari, ba ya da launi mai kaifi, kuma ba ya da kauri sosai.


Bugu da kari, Ruwan farji yana iya zuwa da launuka daban-daban, kuma kowanne na da ma’anarsa: fari mai tsabta yawanci al’ada ne kuma ba ya nuna matsala; fari mai kauri sosai (kamar nono mai kauri) na iya nuna "yeast infection" musamman idan yana tare da ƙaiƙayi; kore yakan nuna kamuwa da cuta (kamar "Trichomoniasis") musamman idan yana wari ko kumfa; ruwan toka yawanci alamar bacterial "vaginosis" ne kuma yana zuwa da wari mai kama da ƙarnin kifi; rawaya na iya zama al’ada idan ba shi da wari ko zafi, amma idan ya kasance mai kauri da wari yana iya nuna cuta; ruwan madara mai duhu yawanci na nuna rikicewar kwayoyin halittar farji ko infection; ja ko ruwan jini na iya zama jinin al’ada ko sauyin "hormones", amma idan ya zo ba bisa lokaci ba yana bukatar dubawa; ruwan ruwan kasa yawanci tsohon jini ne daga mahaifa, amma idan yana yawan fitowa ko da wari yana bukatar bincike. 


A taƙaice, ba launi kaɗai ke nuna matsala ba, sai launi + wari + kauri + jin daɗi ko rashin daɗi tare.


2. Ƙaiƙayi ko ɗan kaikayi a farji

3. Ƙananan kuraje

4. Raɗaɗi lokacin yin fitsari

5. Jin rashin daɗi yayin jima’i

6. Sauyin jinin al’ada

7. Ciwon mara

8. Zazzaɓi

9. Kasala

10. Bushewar farji

11. Raguwar sha’awa ko rashin ta

12. Ko ma rashin wata alama, amma cutar na iya kasancewa


Wasu cututtuka ba sa nuna alama kai-tsaye,

amma bincike zai iya gano su.


DALILIN DA YASA YA DACE A KULA SOSAI


Ciwon sanyi idan ba a kula da shi ba da wuri,

na iya jawo matsaloli a gaba, kamar:


a) matsalar jin daɗin jima’i

c) raguwar sha’awa

d) matsalar ɗaukar ciki

e) rashin daidaituwar lafiya


Kamar gini: idan ƙaramar tsagewa ta fara bayyana, mai hankali yana gyara ta, ba sai bangon ya fadi ba.


MUHIMMIN SAƘO


1. Jiki ba ya cutar da mutum da gangan,

yana faɗakarwa ne.


2. Gwaji ba alamar tsoro ba ne,

alamar kula da kai ne.


3.Neman magani ba rauni ba ne,

hankali ne.


SHAWARA


1. Ki kula da sauyin da jiki ke nuna

2. Kada ki raina alamomi

3. Ki nemi shawarar kwararre

4. Ki yi gwaji idan akwai buƙata

5. Ki bi magani daidai

6. Ki kula da tsabtar jiki da jima’i mai tsaro

7. Ki zaɓi ilimi kafin jin daɗi


KARSHEN SAƘO


Lafiya kamar amana ce: idan kin kula da ita,

zata kula da ke.


📞 KIRA / WHATSAPP DOMIN MAGANI. SHA KI WARKE, BAMU KOYA HADA MAGANI. MUNA SIYAR DA MAGANI NE KADAI

08084028794


Ki zaɓi kulawa.

Ki zaɓi hankali.

Ki zaɓi lafiya.

No comments:

Post a Comment