Ciwon Sanyi tamkar gobara ce; zata iya cinye lafiya.Tana yaduwa ta hanyar jima'i tamkar wutar daji ne: ta jini, maniyyi, ruwan farji ko wasu ruwan jiki, wanda shine makamashin dake dauke da kwayar cutar. Cuta ce mai shiru, zata iya bayyana, haka kuma, illar ta zata iya ɓuya ko bayyana.
Abin da jikinka ke nuna maka na alomomin cutar wadanda zamu lissafa, madubi ne. Abin da kowane namiji ya kamata ya sani anan shine:
Sanyin Gaba ko Sanyin Mara, cuta ce da ake ɗauka mafi yawa ta hanyar jima’i ba tare da kariya ba. Cutar na iya shafar zakari, maraina, fitsari, maniyyi, har ma da lafiyar aure gaba ɗaya idan ba a kula da ita da wuri ba.
Bugu da kari, cutar na iya kasancewa a jiki ba tare da wata alama ba, amma tana aiki a ɓoye, tamkar tururuwa a bango cikin duhun dare. Idan ka yi watsi da cutar ko alamomin da kake ji, za ta iya haifar da matsala mai tsanani daga baya.
MENENE CIWON SANYIN MARA?
Ciwon sanyi, kamar yanda muka bayyana a sama (STD/STI), cuta ce da ake yadawa ta hanyar saduwa, musamman ga mutane masu bin mata ; masu zinace-zinace. Mata zasu iya sakawa maza cutar , haka suma matan, zasu iya sakawa maza kwayar cutar: ruwan farji, maniyyi , jini ko wasu ruwan jiki. Alamominsa suna bambanta dangane da:
a) Nau’in ƙwayar cutar
b) Matakin da cutar ta kai a jiki
c) Ƙarfin garkuwar jiki
Ka sani cewa: wasu cututtuka suna ɓoyewa, wasu suna bayyana da sauri. Gwaji shine madubin gaskiya. Sa'annan ita wuta ana kashe tane kafin ta zama gobara. Ka kula da lafiyar sai ta kula da kai.Domin lafiya jari ce.
ME YA SA WASU BA SA WARKEWA DA WURI?
1.Shan maganin ba tare fahimta ko rashin fahimtar matsalar ko ma rashin sani abinda ke damun mutum
2.Karɓar magani daga wani wanda bashi bane ya dace matsalar ba. Wato cuta daban , magani na daban.
3.Daina shan magani kafin cikar lokacin warkewa
4. Rashin samun sahihin magani ko jinkiri
A nan ne cuta ke zama “jeke-ka-dawo”; tana bacewa na ɗan lokaci, sai ta dawo da ƙarfi.
ALAMOMIN SANYIN GABA
Alamomin da ake gani fili:
1. Ƙananan ƙuraje a zakari, maraina ko ƙasansu
2. Ƙaiƙayi a kan hular zakari
3. Fitar farin ruwa mai ɗorawa ko kauri, ko lokacin yunkurin ba haya ko fitsari
4. Zafi yayin fitsari
5. Zafi yayin fitar maniyyi
6. Ƙuraje masu ruwa da ke fashewa
Wasu Alamomin Nau'in Cutar:
1. Gyambo a zakari ko maraina
2. Kumburi da zafi a maraina
3. Zafi da kumburi yayin fitsari
4. Dan zazzaɓi ko kasala
Lura: Rashin alama ba hujjar rashin cuta ba ce.
ILLAR CIWON SANYI GA MAZA
1) RASHIN ƘARFIN MAZAKUTA
Wasu cututtuka kamar Chlamydia na iya rage ƙarfin mazakuta idan ba a magance su da wuri ba. Wannan yana haifar da: Rashin miƙewa yadda ya dace, raguwar sha’awa, saurin inzali
Kamar tushen wuta da aka bari yana ƙonewa a ciki, rashin kulawa zai iya jefa namiji cikin damuwa da rashin jin daɗin aure.
2) RASHIN HAIFUWA
Gonorrhea da Chlamydia na iya lalata hanyoyin haihuwa. Alamominsu sun haɗa da: Fitar ruwa mai kauri, wani lokaci da ɗan jini, zafi da yawan fitsari, kaiƙayi ko zubar jini a dubura,alamomin mura ko ciwon gaɓoɓi
Idan ba a kula da wuri ba, cutar na iya kawo rashin haihuwa ga namiji ko mace.
3) DAMUWAR KANKANCEWAR ZAKARI
Ko da babu cikakken tabbacin kimiyya, mutane da yawa na jin damuwar jima’i da rashin ƙarfin mazakuta. Wannan na iya haifar da ƙuncin rai da damuwa da zaya sanya zakari ya noke.
WASU IRE-IREN SANYIN DA AKE SAMU TA JIMA’I
1.Chancroid: gyambo mai raɗaɗi
2. Crabs: ƙwari masu tsotsar jini da haddasa ƙaiƙayi
3. Genital Herpes: ƙuraje masu durar ruwa da ke zama gyambo
4. Syphilis: cuta mai matakai da ke iya lalata ƙwalwa da ido
5. HIV/AIDS: cutar sida/kanjamau mai raunana garkuwar jiki, tana gayyatar sauran cututtuka
Alamomin wasu na kama da na wasu, bincike a asibiti shine mafita.
HANYOYIN KARIYA DA MAGANI
1. Tsayawa ga halal
2. Gujewa zina da matan banza
3. Yin gwaji lokaci zuwa lokaci
4. Tuntubar likita idan anji sauyin lafiyar jiki
5. Kula da lafiyar matar da zaka aura ko kuke alakar banza
Ka tuna: lafiya amana ce — idan ka kula da ita, za ta kula da kai.
DOMIN NEMAN MAGANI
📞 Kira ko WhatsApp: +234808 402 8794
S/Unguwa Dandagoro, Katsina.

No comments:
Post a Comment