Monday, 16 February 2026

CIWON SANYI: Saƙon jiki kafin bayyanar matsala


Jiki yana magana,

amma bada murya ba.

Wasu lokuta yana magana ne da alama,

da sauyi,

da ƙananan canje-canje da mata kan raina.


Ƙaramar alama a yau,

na iya zama babban abu gobe.

Ba don tsoro ba,

amma don lura.


Domin jiki ba maƙiyi ba ne,

aboki ne da ke bada shawara.


Tambayar ita ce:

Kina kula da abin da jikin ke nuna miki?


MINENE CIWON SANYIN MARA?


KARIN HASKE AKAN KALMAR CIWON SANYI (INFECTIONS)


A cikin al'ummar Hausawa, ana amfani da kalmar "Ciwon Sanyi" don bayyana abubuwa da dama. To amma a likitance, ya kamata mu rarrabe su:


1. Infection na farji, Sanyin Mata (Vaginal Infections):

Kamar "Candidiasis" (Yeast) ko "Bacterial Vaginosis". Waɗannan galibi ba sa yaduwa ta jima'i, amma suna kawo ƙaiƙayi da fitar ruwa.


2. Ciwon Sanyin Mara na Fitsari (UTI):

Wannan yana shafar mafitsara ne, yana kawo zafi lokacin fitsari.


3. Cututtukan da ake samu ta Jima'i (STD/STIs), sanyin mata da maza , ciwon da mata ko maza zasu iya sawa juna ta jima'i:

Kamar Syphilis, Gonorrhea, ko Chlamydia. Waɗannan su ne suka fi haɗari ga mahaifa idan ba a yi magani ba.


TA HANYAR JIMA'I: Ciwon sanyin mara cuta ce da ake iya samu ta hanyar jima’i (STD/STIs).

Ana iya kamuwa da ita daga mutum zuwa wani mutum ta hanyar ruwan jiki, jini, ko mu’amalar al’aura.


Wasu nau’ikan cutar na bayyana da alamomi,

wasu kuma na iya kasancewa a jiki ba tare da wata alama ba. Saboda haka mutum na iya ɗauke da cuta, amma bai sani ba.


ALAMOMIN CIWON SANYIN MARA


Ga wasu daga cikin alamomin da ake iya gani:


1. Sauyin ruwa daga farji (launi, kauri, wari).


A dabi’a, farji yana fitar da ruwa na al’ada wanda ke taimakawa tsaftace jiki da kiyaye lafiyar gaba. Wannan ruwan yawanci ba ya wari, ba ya da launi mai kaifi, kuma ba ya da kauri sosai.


Bugu da kari, Ruwan farji yana iya zuwa da launuka daban-daban, kuma kowanne na da ma’anarsa: fari mai tsabta yawanci al’ada ne kuma ba ya nuna matsala; fari mai kauri sosai (kamar nono mai kauri) na iya nuna "yeast infection" musamman idan yana tare da ƙaiƙayi; kore yakan nuna kamuwa da cuta (kamar "Trichomoniasis") musamman idan yana wari ko kumfa; ruwan toka yawanci alamar bacterial "vaginosis" ne kuma yana zuwa da wari mai kama da ƙarnin kifi; rawaya na iya zama al’ada idan ba shi da wari ko zafi, amma idan ya kasance mai kauri da wari yana iya nuna cuta; ruwan madara mai duhu yawanci na nuna rikicewar kwayoyin halittar farji ko infection; ja ko ruwan jini na iya zama jinin al’ada ko sauyin "hormones", amma idan ya zo ba bisa lokaci ba yana bukatar dubawa; ruwan ruwan kasa yawanci tsohon jini ne daga mahaifa, amma idan yana yawan fitowa ko da wari yana bukatar bincike. 


A taƙaice, ba launi kaɗai ke nuna matsala ba, sai launi + wari + kauri + jin daɗi ko rashin daɗi tare.


2. Ƙaiƙayi ko ɗan kaikayi a farji

3. Ƙananan kuraje

4. Raɗaɗi lokacin yin fitsari

5. Jin rashin daɗi yayin jima’i

6. Sauyin jinin al’ada

7. Ciwon mara

8. Zazzaɓi

9. Kasala

10. Bushewar farji

11. Raguwar sha’awa ko rashin ta

12. Ko ma rashin wata alama, amma cutar na iya kasancewa


Wasu cututtuka ba sa nuna alama kai-tsaye,

amma bincike zai iya gano su.


DALILIN DA YASA YA DACE A KULA SOSAI


Ciwon sanyi idan ba a kula da shi ba da wuri,

na iya jawo matsaloli a gaba, kamar:


a) matsalar jin daɗin jima’i

c) raguwar sha’awa

d) matsalar ɗaukar ciki

e) rashin daidaituwar lafiya


Kamar gini: idan ƙaramar tsagewa ta fara bayyana, mai hankali yana gyara ta, ba sai bangon ya fadi ba.


MUHIMMIN SAƘO


1. Jiki ba ya cutar da mutum da gangan,

yana faɗakarwa ne.


2. Gwaji ba alamar tsoro ba ne,

alamar kula da kai ne.


3.Neman magani ba rauni ba ne,

hankali ne.


SHAWARA


1. Ki kula da sauyin da jiki ke nuna

2. Kada ki raina alamomi

3. Ki nemi shawarar kwararre

4. Ki yi gwaji idan akwai buƙata

5. Ki bi magani daidai

6. Ki kula da tsabtar jiki da jima’i mai tsaro

7. Ki zaɓi ilimi kafin jin daɗi


KARSHEN SAƘO


Lafiya kamar amana ce: idan kin kula da ita,

zata kula da ke.


📞 KIRA / WHATSAPP DOMIN MAGANI. SHA KI WARKE, BAMU KOYA HADA MAGANI. MUNA SIYAR DA MAGANI NE KADAI

08084028794


Ki zaɓi kulawa.

Ki zaɓi hankali.

Ki zaɓi lafiya.

CIWON SANYI NA MAZA: Wutar da Ake Kashewa Tun Da Wuri Kafin Tayi Gobara



Ciwon Sanyi tamkar gobara ce; zata iya cinye lafiya.Tana yaduwa ta hanyar jima'i tamkar wutar daji ne: ta jini, maniyyi, ruwan farji ko wasu ruwan jiki, wanda shine makamashin dake dauke da kwayar cutar. Cuta ce mai shiru, zata iya bayyana, haka kuma, illar ta zata iya ɓuya ko bayyana.

Abin da jikinka ke nuna maka na alomomin cutar wadanda zamu lissafa, madubi ne. Abin da kowane namiji ya kamata ya sani anan shine:

Sanyin Gaba ko Sanyin Mara, cuta ce da ake ɗauka mafi yawa ta hanyar jima’i ba tare da kariya ba. Cutar na iya shafar zakari, maraina, fitsari, maniyyi, har ma da lafiyar aure gaba ɗaya idan ba a kula da ita da wuri ba.

Bugu da kari, cutar na iya kasancewa a jiki ba tare da wata alama ba, amma tana aiki a ɓoye, tamkar tururuwa a bango cikin duhun dare. Idan ka yi watsi da cutar ko alamomin da kake ji, za ta iya haifar da matsala mai tsanani daga baya.

MENENE CIWON SANYIN MARA?

Ciwon sanyi, kamar yanda muka bayyana a sama (STD/STI), cuta ce da ake yadawa ta hanyar saduwa, musamman ga mutane masu bin mata ; masu zinace-zinace. Mata zasu iya sakawa maza cutar , haka suma matan, zasu iya sakawa maza kwayar cutar:  ruwan farji, maniyyi , jini ko wasu ruwan jiki. Alamominsa suna bambanta dangane da:

a) Nau’in ƙwayar cutar

b) Matakin da cutar ta kai a jiki

c) Ƙarfin garkuwar jiki

Ka sani cewa: wasu cututtuka suna ɓoyewa, wasu suna bayyana da sauri. Gwaji shine madubin gaskiya. Sa'annan ita wuta ana kashe tane kafin ta zama gobara. Ka kula da lafiyar sai ta kula da kai.Domin lafiya jari ce.


ME YA SA WASU BA SA WARKEWA DA WURI?

1.Shan maganin ba tare fahimta ko rashin fahimtar matsalar ko ma rashin sani abinda ke damun mutum

2.Karɓar magani daga wani wanda bashi bane ya dace matsalar ba. Wato cuta daban , magani na daban. 

3.Daina shan magani kafin cikar lokacin warkewa

4. Rashin samun sahihin magani ko jinkiri

A nan ne cuta ke zama “jeke-ka-dawo”; tana bacewa na ɗan lokaci, sai ta dawo da ƙarfi.


ALAMOMIN SANYIN GABA


Alamomin da ake gani fili:

1. Ƙananan ƙuraje a zakari, maraina ko ƙasansu

2. Ƙaiƙayi a kan hular zakari

3. Fitar farin ruwa mai ɗorawa ko kauri, ko lokacin yunkurin ba haya ko fitsari 

4. Zafi yayin fitsari

5. Zafi yayin fitar maniyyi

6. Ƙuraje masu ruwa da ke fashewa


Wasu Alamomin Nau'in Cutar:

1. Gyambo a zakari ko maraina

2. Kumburi da zafi a maraina

3. Zafi da kumburi yayin fitsari

4. Dan zazzaɓi ko kasala

Lura: Rashin alama ba hujjar rashin cuta ba ce.

ILLAR CIWON SANYI GA MAZA


1) RASHIN ƘARFIN MAZAKUTA

Wasu cututtuka kamar Chlamydia na iya rage ƙarfin mazakuta idan ba a magance su da wuri ba. Wannan yana haifar da: Rashin miƙewa yadda ya dace, raguwar sha’awa, saurin inzali

Kamar tushen wuta da aka bari yana ƙonewa a ciki, rashin kulawa zai iya jefa namiji cikin damuwa da rashin jin daɗin aure.

2) RASHIN HAIFUWA

Gonorrhea da Chlamydia na iya lalata hanyoyin haihuwa. Alamominsu sun haɗa da: Fitar ruwa mai kauri, wani lokaci da ɗan jini, zafi da yawan fitsari, kaiƙayi ko zubar jini a dubura,alamomin mura ko ciwon gaɓoɓi

Idan ba a kula da wuri ba, cutar na iya kawo rashin haihuwa ga namiji ko mace.

3) DAMUWAR KANKANCEWAR ZAKARI

Ko da babu cikakken tabbacin kimiyya, mutane da yawa na jin damuwar jima’i da rashin ƙarfin mazakuta. Wannan na iya haifar da ƙuncin rai da damuwa da zaya sanya zakari ya noke.

WASU IRE-IREN SANYIN DA AKE SAMU TA JIMA’I

1.Chancroid: gyambo mai raɗaɗi

2. Crabs: ƙwari masu tsotsar jini da haddasa ƙaiƙayi

3. Genital Herpes: ƙuraje masu durar ruwa da ke zama gyambo

4. Syphilis: cuta mai matakai da ke iya lalata ƙwalwa da ido

5. HIV/AIDS: cutar sida/kanjamau mai raunana garkuwar jiki, tana gayyatar sauran cututtuka

Alamomin wasu na kama da na wasu, bincike a asibiti shine mafita.


HANYOYIN KARIYA DA MAGANI

1. Tsayawa ga halal

2. Gujewa zina da matan banza 

3. Yin gwaji lokaci zuwa lokaci

4.  Tuntubar likita idan anji sauyin lafiyar jiki

5. Kula da lafiyar matar da zaka aura ko kuke alakar banza

Ka tuna: lafiya amana ce — idan ka kula da ita, za ta kula da kai.

DOMIN NEMAN MAGANI

📞 Kira ko WhatsApp: +234808 402 8794

S/Unguwa Dandagoro, Katsina.

CIWON OLSA: Cikinka na magana a ɓoye; saurara kafin ya fusata!

 




Olsa (القرحة الهضمية / alqurḥah al-hadmiyyah) wani irin gyambo ne da ke fitowa a cikin tumbi ko farkon ƙaramin hanji (duodenum). Idan ya tsananta, yana iya jawo zubar jini a ciki, wanda ke da haɗari sosai.

Gastric ulcer: gyambo a cikin tumbi

Duodenal ulcer: gyambo a farkon ƙaramin hanji

Shin ciwon olsa yana tauye maka jin daɗin rayuwa ?

ALAMOMIN CIWON OLSA

Mai olsa na iya fuskantar:

•Ciwon ciki, musamman saman mara

•Jin ƙuna a kirji ko zuciya (kamar wuta)

•Rashin son cin abinci

•Rashin narkewar abinci

•Yawan gyatsa ko tashin gas

•Amai

•Kasala da rashin jin daɗi

•Ramewa

•Jin ciwo bayan cin abinci ko idan yunwa ta kama

•Yin kashi mai jini ko baƙin launi

•Zawo mai ruwa a wasu lokuta


ABIN DA KE KAWO OLSA

Mafi yawan sanadi:

✔️ Kwayar cuta ta H. pylori

✔️ Amfani da magungunan rage zafi na tsawon lokaci

✔️ Yunwa mai yawa

✔️ Damuwar zuciya (stress)

✔️ Shan taba ko barasa


Magungunan da suka fi haddasa olsa idan ana sha da yawa:

•Ibuprofen

•Diclofenac

•Aspirin

•Sauran magungunan kumburi

Olsa na faruwa ne idan acid na ciki ya wuce kima, ya fara cin jikin tumbi ko hanji har sai gyambo ya fito.

ABUBUWAN DA YA KAMATA KA GUJE SU

Don hana ciwon olsa tsananta:

❌ Abinci mai yaji sosai

❌ Lemukan kwalba masu gas

❌ Abinci mai tsami ko mai zafi/sanyi sosai

❌ Soyayyen abinci da mai , mai da yawa

❌ Gishiri mai yawa

❌ Shayi mai caffeine, coffee, goro

❌ Shan taba da barasa

❌ Kwanciya nan take bayan cin abinci


Lura:  Madara na iya rage zafi na ɗan lokaci, amma tana iya ƙara acid daga baya ga wasu mutanen. Wani kuma ya iya samun sauki saboda shan madara; akwai banbanci tsakanin mutane.


ABUBUWANDA ZASU TAIMAKA MAI OLSA

✔️ Cin abinci kaɗan-kaɗan amma sau da yawa (sau 5–6 a rana)

✔️ Cin ‘ya’yan itatuwa masu sauƙin narkewa

✔️ Ganyayyaki masu amfani kamar zogale da alayyahu

✔️ Shan zuma 

✔️ Samun hutu bayan cin abinci

✔️ Tauna abinci sosai kafin hadiyewa

✔️ Rage damuwa


LOKUTAN DA YA KAMATA A GA LIKITA DA GAGGAWA

Idan aka samu:

•Amai da jini

•Kashi baƙi 

•Tsananin ciwon ciki mai ci gaba

•Ramewa ba tare da dalili ba

•Kasala mai tsanani


SAƘO MAI MUHIMMANCI

Olsa ba kawai “ciwon ciki” ba ne; gyambo ne da zai iya zama barazana ga rayuwa idan aka yi sakaci.


Ka fara shiri yau, domin ka more Ramadan lafiya da farin ciki! Albishir: masu ciwon olsa na samun sauki sosai a watan Ramadana mai albarka.


NEMI MAGANIN MU A YAU, YANZU MA - SHA KA WARKE +2348084028794 (Kira ko WhatsApp)

Sunday, 15 February 2026

ZINAR HANNU: Jin Dadin Yanzu , Biyan Bashin Gobe, da Jiki da Martaba

 


Madubin Hannunka Zaya Nuna Maka Gobe...

Abin da mutane da yawa ke yi a boye suna kira “sauki”, shi ne abin da ke rikidewa ya zama sarka a wuyansu daga baya.

Wannan ba wasa ba ne; jin dadi yanzu, biyan bashin gobe da jiki, hankali, da martaba.

 Domin abin da kake wasa da shi yau, na iya zama abin da zaya karya ka gobe.

Idan hannunka ya zama yana biya ka abin da aure kadai ya kamata ya baka,  tambayar ita ce: Waye ke mallakarka ? kai ne ko sha’awarka ce ta mallake ka?

Idan wannan tambaya ta taba zuciyarka ko ta sa ka yi shiru na daƙiƙa biyu , to ka cigaba da karantawa domin amfanar kanka.

MINENE ZINAR HANNU?

“Zinar hannu” ko “auren hannu”, na nufin wasa da al’aura, wato ISTIMNA’I da Larabci ko Masturbation a yaren Turanci, wanda yana nufin yin amfani da hannu, yatsa ko wani abu domin mutum ya fitar da sha’awarsa da kansa ta jima’a, da tunanin yana saduwa da wata ’ya mace ko ita macen tana tunanin saduwa da wani ɗa namiji. Wannan batu ba na almara ba ne, gaskiya ce da mutane da yawa ke rayuwa da ita a boye.

TAMBAYA MAI NAUYI

 Shin kana sane da abin da yawan wasa da gaba ke iya jawo maka a rayuwa, lafiya, aure, da tunani?

WASU DAGA CIKIN ILLOLIN DA WASA DA GABA ZASU IYA SAMUN ƊA NAMIJI MAI YAWAN AIKATA AUREN HANNU:

Wannan yau-da-kullum da binciken lafiya ne ya tabbatar da haka:

a)Saurin inzali

b)Tsinkewar ruwan

 maniyyi / zaya iya haddasa rashin haihuwa

c)Rashin sha’awa ko daukewarta saboda yawan yi

d) Bugawar zuciya da karfi, zut-zut (palpitations)

e) Kankancewar zakari (penile shrinkage)/ rashin karfin mazakuta (ED)

f) Yawan mantuwa / matsalar rike karatu

g) Rikicewar tunani

h) Ciwon damuwa (depression)

i) Kasala / ciwon kai ko jiki

j) Rama / zurmawar idanu

k)Karkacewar zakari

l)Raguwar karfin garkuwar jiki

m) Gani buji-buji (blurred vision)

n) Hanaka aure/tsoron yin aure saboda raguwar martabar namiji wajen jima'i

o)Kallon batsa (tarin zunubi) da sauransu.

Shin kana jin daya, biyu ko fiye da haka daga cikin illolin?

Idan amsarka “eh” ce, to wannan sakon naka ne kai tsaye:


SHAWARA

Ka yi aure idan kana da halin yin, idan kuma baka da hali to lazimci yin azumi, musamman na Litinin da Alhamis, domin azumi yana dakushe sha’awa. Idan sha’awarka mai karfi ce sai ka yawaita azumin don cin galabarta. Ka nisanci kallon batsa, hoto ko video, kallon batsa a waya ya jefa mutane da yawa halakar zinar hannu. Idan zinar hannu ta riga ta maka illa ko illoli to nemi MAGANIN MU sahihi domin maido da martabarka da kima. Sha Ka Warke!

📞 KIRA KO WHATSAPP: 08084028794 


Yi hankali da mayaudara, ba kowa bane ke da magani ba. Bamu da agent a wani gari in ba a cibiyar mu ba nan Katsina.

👉 Maido da martabarka da lafiya ta ɗa namiji, nemi maganin mu.