Saturday 3 October 2020

TAQAITTUN SHAWARWARI 5 GA MAIGIDA DOMIN INGANTA JIMA'I



idTAQAITTUN SHAWARWARI 5 GA MAIGIDA DOMIN  INGANTA JIMA'I 


Mai yiwuwa ne daga fara karanta wannan bayani har ka fara hararo matsalarka ko matsalolinka masu ci maka tuwo a 'kwarya na jima'i tsakaninka da iyalinka, tabbas wannan damuwa ce da take cikin zukatan mazaje da yawa wanda ba zasu iya bayyanawa kowa ba sai  mai-magani ko wani amini nasu wanda suke ganin zaya iya taimakonsu da shawara. Don haka bakai kadai bane mai irin wannan damuwar ba a duniya, kuna da yawa. Irin wannan damuwa dai a koda yaushe bata wuce saurin kawowa, ko rashin karfin mazakuta, kankancewar zakari ko rashin ingantaccen maniyyi, ciwon sanyi mai hana lafiyar jima'i ko wata damuwa makamanciyar haka. 


Rashin karfin mazakuta na nufin matsalar rashin cikakken karfin al’aurar namiji baligi ko raguwar karfin azzakari yayinda aka fara saduwa ko kuma rashin miqewar al’aurar yayinda ake bukatar fara jima’i...

----------------------------------

Ga wasu taqaitattun shawarwari  domin inganta jima'i tsakaninka da iyalinka:


(1) MOTSA-JIKI (EXERCISE):Idan kana son qarin sha'awa da qarfin gaba da inganta illahirin lafiyar jikinka to ka dinga motsa jikinka 'dan uwa, aqalla na minti 30 a kowace rana, yi gudu, hau keke , tsalle , press-up ko wani nau'in  motsa jiki. Motsa jiki na inganta lafiyar zuciya da harba jini a sassan jiki da kyau , wanda hakan zaya inganta gudanar jini ga al'aura domin samun karfin gaba da lafiya. 


(2) CIN ABINCIN KIRKI: Cin abinci nau'in kayan marmari kamar su aiba, kankana, dabino, kwakwa, sai kuma albasa da tafarnu, yaji ga abinci, suna da tasiri wajen samar da qarfin gaba. Yaji nada sinadarin "capsaicin" mai inganta gudanar jini ga al'aura domin samun karfin mazakuta, shiyasa Hausawa ke hada YAJIN MAZA wanda ake yi da garin wani magani da kuma yajin. Sai aci kifi da yaji ko kwadon zogale. Sai nama da sauran abinci masu lafiya kamar kifi, kwai, gyada da sauran su. Asha shayin citta da zuma, safe da yamma - danyar citta ko busassa.


(3) KA LURA DA BUQATUN MATARKA: Ka biyawa matarka bukatar ta farko  da kyau , kayi jima'i da burin ka biya matarka bukata kafin biyan taka bukatar. Ka lura da me take so lokacin kwanciya , kuyi magana ku fahimci junanku , idan mai kunya ce sai ka lura da abinda yake sanyata kamuwa, yau da gobe zaka iya ganewa. Kuyi wasanni na tsawon lokaci kafin ku sadu gaba-da-gaba. Ka kuma koyi dabaru na kwanciya da salo iri-iri har ka gane wanda take so. Hikimar shine, idan kana biya mata bukata zata saki jiki dakai, itama zata yi bakin qokarinta ta biya maka taka bukatar, ko don ma tana jin dadin kwanciyar aure da kai kuma zaka ga tana qara samun sha'awarka,  wanda hakan na burge duk wani magidanci da bashi kwarin gwiwa. Ka fahimtar da ita abinda kake so na kwanciya naka.


Idan kaga mace na gudunka to mafi yawanci baka biyama mata bukata ne , wato kana barinta bata biya tata da bukatarba , ko kuma bata da lafiya, wannan kuma sai ku nemi magani.


(4) KA RAGE YAWAN QOSAWA: Tun baka tafasa ba ka qone. Saurin qosawar mutum yayi jima'i shine ke haddasa matsala biyu, wato matsalar saurin kawowa/inzali ga maigida da kuma rashin yin wasanni daga maigidan domin iyalinsa ta kamu da sha'awa wacce zata taimaka wajen biyan bukatarta. Idan maqeri bai zuga wuta ba , babu yanda za'a yi ya sanya qarfe yayi zafi/laushi har ya qera abinda yake so ya qera, haka shima maigida ga biyan bukatar matarsa. Maqeri na hakuri ya zuga wuta domin qarfensa yayi laushi, kaima maigida kayi hakurin zuga matarka tayi zafi, wato sha'awarta ta kumburo. Ga mai saurin kawowa, ya yawaita amfani da ku6ewa 'danya (okro)  , a yanyanka biyu manya a tafasa a tace ruwan mai yauqi asha, ayi haka safe da dare. Ko a nemi man na'a-na'a ('dan Misra) a dinga shafawa ga hular zakari minti 15 kafin  saduwa. 


(5) NEMI TAIMAKO A WAJEN KWARARREN LIKITA KO ASIBITI: Hawan jini ko ciwon suga, ko ciwon sanyin mara/sanyin gaba (STDs) na iya zama dalilin da ya haddasa maka wata matsalar ko matsaloli da masu da alaqa da jima'i wanda kake ji. Alamomin ciwon sanyin suna iya 6uya ko bayyana a jikinka. Wasu alamomin sun hada da: fitar farin ruwa daga zakari, jin zafi lokacin fitar maniyyi ko fitsari, kuraje ga zakari, kumburin maraina, ciwon mara da sauran su. Idan kana jin wata alama irin wannan ko makamanciyar haka sai ka garzaya asibiti ko wata 'kwararriyar cibiyar lafiya domin neman magani. Haka kuma, wani baya da wasu sinadarai ne a jikinsa wanda yana bukatar taimakon magani domin inganta jima'i.

-----------------------------------

NEMI MAGANI DAGA CIBIYAR MU ta Madinah Islamic Medicine, a garin Katsina, Nigeria.


Addireshi: No. 34, Sabuwar Unguwar Dandagoro, Katsina.


Kira  +2348084028794


Bugu da qari, za'a iya tura maka magani zuwa jihar da kake bayan tattaunawa damu.

 

WhatsApp/Call +2348084028794


Wannan bayanai a sama wallafar Madinah Islamic Medicine ne.


www.madinahislamicmed.blogspot.com

WhatsApp: +2348084028794

Email: madinahislamicmed@gmail.com

Facebook: https://mobile.facebook.com/MadinahIslamicMedicine


YI DOWNLOADING MANHAJARMU A PLAYSTORE (APPLICATION): 


https://play.google.com/store/apps/details?id=com.andromo.dev679836.app866696

No comments:

Post a Comment