🌿AMFANIN SHUKAR TAZARGADE 🌿
----------------------------------------------------
SUNAN SHUKA: الأرطماسيا أبسينثيوم Artemisia Absinthium/Wormwood/Tazargade
ASALINTA: Turai, Asiya, Afurka, Kasahen Larabawa, Amurka
------------------------------------------------
AMFANINTA:
1. Rage radadin ciwon jiki ko na gabobi
2. Kashe cutar zazzafin cizon sauro (Malaria). Da sinadarin wannan shuka ne, da kuma wasu na daban, ake yin maganin Malaria na bature ACT ( Artemisinin-based Combination Therapy).
3. 'Karfafa garkuwar jikin 'dan adam domin yaqi da cututuka da yaqi da cutar ciwon daji (cancer)
4. Maganin matsalar ciwon ciki wanda yake da alaqa da matsalar madaciyar hanta (gallbladder disorders)
5. Kashe 'kwari , kunama da korar macizai a gida, a zuba ta a wurin ko ayi hayaki
6. Cizon 'kwari, a shafa manta wurin cizon a fata
7. Korar iskan jinnu da harin maita/mayu, hayaki ko/da shayinta
8. Maganin rashin narkewar abinci a ciki (indigestion)
9. 'Karin sha'awa (increasing libido)
10. Maganin ciwon damuwa (depression)
11. Maganin yawan mantuwa
12. Maganin rashin cin abinci
13. Da sauransu/amfaninta nada yawa
------------------------------------------------
YANDA ZA'A IYA AMFANI DA ITA:
(a) Ayi shayi da tazargade, a tace shayin asha ruwan , za'a iya sanya zuma , da zuma ko babu zuma asha.
(b) Ayi hayakin tazargade da garwashin wuta domin korar iskan shedanu ko harin mayu/maitu, a lullu6e da zani , za'a iya kuma yin shayinta a sha.
(c) A zuba ta wurin da macizai ko kunamu ke zama a gida ko hanyarsu, zasu gudu
(d) A shafa manta ga jiki inda yake ciwo
------------------------------------------------
ABUBUWANDA ZATA IYA HADDASAWA MARAR DADI (SIDEEFFECTS):
Yawan amfani da ita na tsawon lokaci da adadi mai yawa yana iya sanya abubuwa masu illa ga lafiya maimakon neman lafiyar, , tazargade na iya sanya mutum ganin waibuwa (ta 'karya) saboda yawan shan ta, tana kuma iya sanya rashin bacci, mafarkin ban tsoro, juwa, kyarma, ciwon ciki da sauransu.
------------------------------------------------
GARGADI: Kada mace mai juna-biyu ko shayarwa tayi amfani da tazargade, zata iya zama abu mai hadari gare ta da yaronta. MEDICAL DISCLAIMER: Wannan jawabai basa nufin tazargade zata iya maye gurbin magungunan da aka bawa marar lafiya a asibiti. Bayanai ne kawai da mai bincike ya cirato daga wasu ma6u66ugar ilimi wanda suna bukatar karin hujjoji/bayanai da binciken kimiyya na masana akan amfaninta kafin cikakken amfani da ita ko izinin masani kwararre ga marar lafiya.
------------------------------------------------
Wallafar Madinah Islamic Medicine
www.madinahislamicmed.blogspot.com
WhatsApp: +2348084028794
Email: madinahislamicmed@gmail.com
Facebook: https://mobile.facebook.com/MadinahIslamicMedicine
YI DOWNLOADING MANHAJARMU A PLAYSTORE (APPLICATION):
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.andromo.dev679836.app866696
No comments:
Post a Comment