Friday 3 September 2021

SHARRIN ZINAR HANNU/ AUREN HANNU


 SHARRIN ZINAR HANNU


"Zinar hannu" ko "auren hannu", na nufin wasa da al'aura, wato ISTIMNA'I da larabci ko MASTURBATION a yaren turanci, wanda yana nufin wasa da gaba, wato yin amfani da hannu, yatsa ko wani abu domin mutum ya fitar da sha'awarsa da kansa ta jima'a, da tunanin yana saduwa da wata 'ya mace ko ita macen tana tunanin saduwa da wani 'da namiji, domin biyan bukatar jima'i.

WASU DAGA CIKIN ILLOLIN DA WASA DA GABA ZASU IYA SAMUN 'DA NAMIJI MAI YAWAN AIKATA AUREN HANNU:

*Saurin inzali
*Tsinkewar ruwan maniyyi/ zaya iya haddasa rashin haihuwa
*Rashin sha'awa
* Bugawar zuciya da karfi , zut-zut
*Kankancewar zakari/rashin karfin mazakuta
*Yawan mantuwa/matsalar riqe karatu
*Rikicewar tunani
*Ciwon damuwa
*Kasala/ciwon kai ko jiki
*Rama/zurmawar idanu
*Karkacewar zakari
*Raguwar karfin garkuwar jiki
*Gani buji-buji
*Hanaka aure
*Kallon batsa
(tarin zunubi) etc.

Shin kana jin 'daya, biyu ko fiye da haka daga illolin?

SIDE EFFECTS OF OVER-MASTURBATION:

*Quick ejaculation
*Low sperm count/watery sperm
* Low libido/desire
*Heart palpitations
*Penis shrinkage/ weak erection
*Loss of memory(forgetfulness)
*Confusion
*Depression
*Fatique, headache/body pains
*Weight loss/sunken eyes
*Penis curvature/bend
*Low immunity
*Poor vision/blurry vision
*Fear of marriage
*Addiction to porn (sinful) etc.

Karanta cikakken bayanin, latsa LINK:
https://www.facebook.com/621757857853133/posts/4439361146092766/?app=fbl

Maido da martabarka da lafiya ta 'da namiji , nemi magani:

CALL/WHATSAPP: +2348084028794

CIKAKKEN BAYANI AKAN ILLARSA:
AUREN HANNU / ZINAR HANNU DA ILLOLINTA GA MATASA MAZA DA MATA
Zinar hannu ko auren hannu na nufin wasa-da-al'aura , wato wasa da gaba (Istimna'i /masturbation) wanda yake nufin yin amfani da hannu, yatsa ko wani abu domin biyan bukatar jima'i ga mutum da kansa da tunanin saduwa da wata mace ko wani namiji , idan mace ce. Ana kiran wannan dabi'a "zinar hannu" , musamman ga masu kallon batsa ko jinta a waya ko computer a lokacinda suke fitar da sha'awarsu da hannunsu. Auren hannu shima na nuni da wannan dabiar dai, wato mutum ya fitar da sha'awa da hannu musamman ga masu yi suna cewa domin gudun yin zina saboda rashin aure, ba tare da kallon batsa ba ko jinta.
Dukkan wadannan dabia biyu wasa-da-al'aura ne , wato istimna'i da larabci. Istimna'i dabi'a ce da take ta faruwa da yaduwa cikin mutane da dama, cikin yara matasa dama manya, musamman mararsa aure ko wanda aurensu ya mutu, koma rashin gamsuwar aure. Wannan dabi'a ta zama ruwan dare kuma abin 'kyama sosai saboda wasu dalilai, wanda sun hada da dalilan addini, dalilan al'adu, da kuma wasu dalilan lafiya. Dalilan lafiya anan zamu yi bayaninsu kadai, wanda suna magana ne game da yawan yin istimina'i da illolinsa ga mai yawan aikatawa, wato wanda ya zama dabi'arsa koda yaushe kuma baya jin dadin rayuwarsa idan bai yiba (An addict person who overmasturbates ).
Bincike-binciken wasu masana kimiyya da muka tattaro game da yawan wasa-da-al'aura (over-masturbation), na nuna cewa YAWAN WASA-DA -AL'AURA (excessive masturbation or over-masturbation) nada illololi ga lafiya. Duk da yake dai masana sunyi saɓani akan mas'alar istimna'i, inda wasu ke ganin yana da illa wasu kuma basa ganin haka saima kishiyar haka, to sai dai babu rikici akan cewa yawan yin istimna'i nada illa ga lafiya. Yana iya haddasa wadannan matsalolin idan ya zama halin mutum baya jin daɗi sai ya aikata (addiction):
Yawan mantuwa, yawan damuwa, rage hazaqar kwalwa, kankancewar zakari da maraina, saurin kawowa ko rashin karfin mazakuta. Sauran matsalolin dazai iya haddasawa , sun hada da: ramar jiki ko 'karancin sha'awa, karancin maniyyi ko tsinkewar ruwan maniyyi da raguwar ingancinsa (wanda na iya haddasa rashin haifuwa) , raunin jiki, raunin garkuwar jiki, jin ciwon kai akai-akai, ciwon baya, fitar maniyyi daga zakari hakanan ba tare da mutum yayi niyya ba - ba tare da yayi istimna'i ba ko yayi jima'i, haka nan kawai.
Wasu illololin da zasu iya faruwa saboda istimna'i: bushewar fatar kan zakari ko illa ga fatar saboda gugar fatar, karkacewar zakari (penis curvature) ko sauya masa sigarsa ta asali, bugawar zuciya da sauri, zubar gashi, kurajen fuska.
ILLAR ISTIMNA'I GA MACE
Mace zata iya samun wasu daga cikin matsalolin da mu kayi bayani a sama. Wasu matsalolin daka iya shafar mace sune: Rashin rike fitsari da kyau (ga mace) ko
Yawan zuwa fitsari saboda saka wani abu cikin farji lokacin istimna'i, wuyar kawowa ga mace wajen jima'i (dalilin koyama jikinta da sai an taɓa wani sashen farji don ta kawo, wanda mai yiwuwa ne zakari baya taɓa wurin lokacin saduwa - a zahirin jima'i. Don haka istimna'i yana sa rashin gamsuwar jima'i ga mace - mijinta zai sha wahala wajen gamsar da ita. Jikinta ya riga ya koya, tayima kanta horo. Dalilin haka, mace zata ji dadin istimna'i fiye da jima'i , hakan kuma zai zamo mata matsala idan tayi aure. Zata ringa tunanin mijinta baya iya gamsar da ita ko mazaje data aura, saboda sabon da tayi da koyama jikinta hanyar gamsar da kanta fiye da hanyar da ta dace, wato jima'i a cikin sunnar aure. Ta canza dabi'ar ta. Da yawa zaka samu cewa mata masu yawan istimna'i basu jin daɗin jima'i sai istimna'i, koma basu gamsuwa sai sunyi istimna'i a bandaki bayan saduwa da mazajen aurensu. Wannan zai iya kawo babbar matsala a cikin aure. Bugu da kari, dadilan rashin gamsuwar mace wajen saduwa da mijinta suna da yawa. Don haka, bazamu iya cewa ba yin istimna'i kafin aure shine dalilin dake hana gamsuwa kadai ba. Akwai wasu dalilan na daban, wasu matsalolin nada alaka da bangaren mazajen.
Mutumin da matsalar yawan wasa-da-al'aura ta zama dabi'arsa koda yaushe (addict) zaya iya maganin matsalar. Idan har yazama dabi'ar mutum baya jin dadin rayuwarsa sai yayi istimna'i (sau 2, 3, 4 ko fiye da haka a kowace rana) [addiction] toh zai iya kawo sauye-sauye (canje-canje) ga jikin mutum wanda lafiya bata maraba dasu ( such as hormonal imbalance), saboda yawan zubda sinadaran jikin mutum wajen inzali fiye dabi'ar jima'i ta gaskiya da sauyin yanayin jiki sakamakon yawan hakan . Yana da hadari ga lafiya yanda wasu matasa suka maida wannan dabi'arsu ta koda yaushe, a bandaki, a daki, a waje, ko a wurinda dama ba'a tsammani suna istimna'i. Yawan Istimna'i mummunar dabi'a ce. Yana da muhimmanci ga masu yawan sha'awa suyi aure , idan babu halin yin auren toh sai su lazimci yin azumi kamar yanda addinin Musulunci ya koyar. Haka kuma, mutum zai iya dinga cin abinci wanda aka sarrafa da WAKEN- SUYA (soya bean) domin bincike ya nuna cewa yana rage sha'awa. Za'a iya kuma yawaita amfani da NA'A-NA'A (pepper mint/mint) , na'a-na'a nada amfani ga lafiya sosai, toh amma sinadarin minti (menthol) da take dashi yana dakushe sha'awa idan yayi yawa. Don haka, a nemi bayanan Malaman Sunnah akan wannan mas'ala, don karin bayani.
~~~
Bugu da kari, mutum mai yawan sha'awa ya rage yawan zama cikin daki cikin kadaici yana tunane-tunane. Mutum ya maida kansa kullum BUSY da karatun Al-Qur'ani da kuma wani aiki, musamman idan yaji sha'awa na tsunkulin / muntsulin sa. Idan kuma mutum yasan yana kallace-kallacen haramun kamar fina-finan batsa, hotunan batsa (musamman a yanar gizo) ko kuma mata (masu kallon maza) akan hanya toh aji tsoron Allah a daina, domin kuwa wadannan na daga cikin manyan-manyan masifun dake jefa matasa cikin wannan hali.
~~~
Idan har daya ko fiye daya daga cikin wadancan alamomin illar yawan wasa- da-gaba sun bayyana a gareka, toh ya zama dole idan kana son lafiyarka ko lafiyarki ki daina kuma a nemi magani domin a tsiratar da lafiya, ta dawo yanda take. Idan ba haka ba, zai iya shafar illahirin lafiya, wani lokacin ma sai a dade ba'a gane abinda ke damun mutum ba. Wannan yana faruwa da yawa ga matasa, kuma muna ganin irin wadannan " cases" barkatai. Haka kuma muna samun rahotanni da yawa sosai akan wannan matsala. Wallahi akwai wanda zakarinsa ya samu matsala baya tashi sam, saboda yawan istimana'i koda yaushe , sai ya samu matsalar "hormonal imbalance", akayi ta yi masa allurai a asibiti a wata jiha, amma ba'a samu nasara ba. Akwai kuma wanda ya samu matsalar tsinkewar maniyyi saboda yawan yin masturbation kuma ba infection bane, yayi aure amma har yanzu babu haihuwa, akwai wacce bata jin dadin jima'i mazajen auren da tayi saboda yawan istimna'i , gashi tayi aure ba gamsuwa, saidai tayi istimana'i da take jin dadinsa a bandaki. Abin takaici shine, mutum baya neman taimako ko magani da wuri sai wai anyi masa baiko ko kuma bikinsa saura wata 1 ko 2. Idan har kana da wannan matsala ba abin kunya bane neman magani, kada ka zauna a cikin matsala har sai ta girma sa'annan ka nemi taimako a lokacinda kunyar ta riga ta cutar dakai. .Muna bada da taimako (herbal remedy) da shawarwari, musamman ga masu wannan matsala. Kuma babu kokwanto ana samun lafiya cikin yardar Allah. Haka kuma mutum zai iya zuwa asibiti yaga likita domin neman warwarar wannan matsala. Allah ya taimaka.
~~~
Domin neman karin bayani/Neman magani
Sai azo Office branch namu mai address kamar haka:
No. 34 Sabuwar Unguwar Dandagoro, Dandagoro, Katsina, Jihar Katsina.
Kira: +2348084028794 ko WhatsApp
E-mail: madinahislamicmed@gmail.com


1 comment: