Tuesday 27 March 2018

ƘARIN GIRMAN MAMA (BREAST ENLARGEMENT)

Mata da yawa na ganin ƙirjin mace  kimar ɗiya mace ne  kuma abin tinƙaho ne ga mace da jan hankali ga maza da kuma birgewa. Don haka  mata da yawa sun ɗauki gyaran mama wani muhimmin  abu, musamman bayan shayarwa ko faɗuwar nonuwan budurwa  a gida ko rashin girman sa.

Girman mama an alaƙanta shi  daga cikin abubuwa  wanda ke sa mace a ganta mai kyakkyawar halitta da ban sha'awa da birgewa ga maza kasancewar maza mafi yawa na son mata masu wannan yanayi.  Wannan lamari nada tasiri sosai ga tunanin mata da yawa,  ta yanda wasu ke jin alfaharinsu da tinƙaho  zai faɗi idan maman su ya faɗi ko suka bari ya canza daga sigar da ake bege. Shi dai nono wani dandazo ko cincirundon tsokar nama ne mai zagaye da kitse daya taso sama a ƙirjin mace baliga. Tsokokin suna canzawa lokacin balaga, haila, juna-biyu da lokacin shayarwa, da kuma lokacin barin al'adar mace (menopause). Waɗannan tsokoki kuma zasu iya buɗewa su ƙara girma saboda wasu magunguna ko tsirran magani.

Mata da yawa ne ke neman magani a kasuwanni domin gyaran mama kuma hanyoyin gyaran maman da ake bi suna da yawa amma amma a zahiri ingancinsu kaɗan ne, wanda sun hada da: ƙwayoyin magani, man shafawa, famfon iska na ƙara girman mama (breast pump), gari , ofireshin/tiyata (surgery)domin ƙara girman nono da sauransu . Wasu hanyoyin nada hadari ga lafiya, kuma sakamakon amfani da magungunan ko hanyoyin ya sha banban tsakanin mata masu ta'ammuli da magungunan, inda wasu sun sami nasarar  ƙara girman mamansu wasu kuma babu wani canji.

Anyi gargadi akan amfani da kayan turawa na kemikal (chemicals) wanda zasu iya haddasa cutar sankarar mama (ciwon daji/cancer), musamman man shafawa na turawa. Domin rage haɗarin dake tattare da yin amfani da magunguna barkatai wanda da zasu iya haddasa illa ga lafiya, MADINAH ISLAMIC MEDICINE mun yanke shawarar bayyana sirrin wasu daga cikin hanyoyi masu inganci kuma marar haɗari da mace zata iya  ƙara GIRMAN NONO ko CIKOWAR NONO idan ya kwanta. Bugu da ƙari, hanyoyin na  bada kariya daga cutar sankaran nono (breast cancer) kasancewar abubuwanda da za'a yi amfani dasu daga tsirrai ne na ɗabia (nature/natural). Abubuwan da za'a nema a ISLAMIC CHEMIST domin ayi amfani dasu sune:

1. HULBA (Fenugreek) da man ta (oil).
2. SHAMMAR (Fennel seeds)

Mai yiwuwa kin taɓa amfani da HULBA, kuma da kika ga hulba cikin abubuwa 2 da muka bayyana kya ce "Hmm. Ai nasan hulba , na jarraba amma shiru ne." Idan kina daga cikin masu irin wannan tunanin to akwai yiwuwar cewa baki yi amfani da hulba ba na tsawon lokaci kullum ko kuma baki yi amfani da ita ba yanda ya dace. Domin kuwa bincike ya tabbatar da tasirin yin amfani da hulba a halittar nonan mace. Hulba na sanya fata da tsokar dake zagaye da nonon mace su buɗe kuma nono ya ciko ɓulɓul  , musamman nonuwa wanda suna da girma amma ba'a miƙe suke ba, sun baje ko sun kwanta. Cikar nonuwan zaisa su miƙe su domin cika ƙirji da siga mai kyau.

SHAMMAR (fennel seeds) kuwa , shima ƴaƴan wani tsiron shuka ne masu kamar ƴaƴan  alkama ko shinkafa wacce ba'a cire ɓawon ba.

YANDA ZA'AI AMFANI DASU
A sami ƴaƴan hulba da  ƴaƴan shammar a Islamic Chemist  sai a niƙe su , a dake su sosai amma kowanne  daban-daban. Haka kuma za'a iya samun garin nasu a Islamic Chemist ba sai an sha wahalar daka ba. Sai a ɗibi cikin ƙaramin cokalin shayi na garin hulbar guda (1 teaspoon) a zuba a kofi , sa'annan a ɗibi garin  shammar ɗin shima cikin ƙaramin cokali guda a haɗe su a kofi ɗaya ( hulba + shammar). Sai a tafasa ruwan zafi idan ya tafasa sai zuba cikin kofin maganin a motsa da cokali sosai a sa'annan a rufe bakin kofin. Idan yayi minti 10 arufe - ya jiƙa sai a tace da rariya a zuba zuma ga ruwan da aka tace asha. Sa'annan a shafa man hulba ga mama safe da dare. Ashafa man a linda/luliya (massage)  ya shiga fatar nono sosai.  Za'a yi hakan (yin shayi da shafa man hulba) sau biyu (2) a rana - safe da dare har na tsawon wata daya. Za'a ga cikakken sakamako bayan wannan lokaci da yardar Allah. Daga zuwa wannan lokaci ko kafin lokacin mace zata fara jin nonuwanta sun kara nauyi, wanda alamace na girma da suke karawa. Kara girman nono ba abu bane dake faruwa cikin dare daya kamar yanda wasu ke tunani. Don haka akwai bukatar hakuri kamin aga sakamakon da ake bukata.

Man hulba yana da amfani idan aka jure ana amfani dashi.  Yana da amfani 2: Na farko, yana sanya gudanar jini da kyau wajen nono wanda zai taimaka wajen inganta lafiyar nono da kyawon fatar nono. Na biyu, yana buɗe tsokokin nono yanda zasu ƙara girma da ƙarfin fata (firming)  mai riƙe nono tsaye ba mai yawan taushi ba  wanda kesa mai sanya mama ya sunkuya saboda yawan taushi. A nemi man hulba ɗan Misra ko Hemani (Pakistani). Allah Ya taimaka.

Wadannan bayanan cikin harshen Hausa da muka wallafa a sama, na cibiyar MADINAH ISLAMIC MEDICINE (CAC :KT2557) dake Jihar Katsina, Nigeria.
Office Address: No. 34. Sabuwar Unguwa Dandagoro, Katsina, Jihar Katsina.

Www.madinahislamicmed.blogspot.com
Email: madinahislamicmed@gmail.com
Phone no.: +2348084028794 (kuma WhatsApp no.)



6 comments:

  1. 1. Hawan Jini; Wannan jinya ce dake haifar da illoli ga lafiyar mutum daga ciki har da raunata da namiji.

    2. Ciwon Siga; Hakanan shi ma wannan ciwo idan ba ai da gaske ba yana iya kashe mazakuta gaba daya.
    https://mynovels.com.ng/abubuwan-da-ke-haifar-da-raunin-mazakuta/

    ReplyDelete