Thursday, 2 August 2018
ALAMOMIN MATSALAR FAIBIROD [ الورم الليفي / FIBROID]
Kafin bayanin alamomin, mu fara da minene "fibroid"? Fibroid (الورم الليفي) wata matsalace a mahaifar mace, wato wani yanayi ne da wani curin nama yake fitowa kuma yana girma a mahaifar mace. Ƙululun naman mai cutar da lafiya yana ɗanfare da wani sashen mahaifar (uterus) da wasu igiyoyinsa matakam. " Fibroid" kalmar turanci ce, domin sauƙin furuci da Hausa, zamu cigaba da amfani da lafazin FAIBIROD a cikin bayanin mu anan . Anyi ƙiyasi cewa cikin mata 100, kashi 20 zuwa 50 na matan suna da fibroid, musamman a shekarunsu na samun haihuwa - wato daga shekara 16 zuwa 50. Wani ƙiyasin kuma ya nuna cewa mata 30 zuwa 77 suna samun matsalar fibroid a lokacin shekarunsu na samun haihuwa, wato lokacin ƙuruciyar balaga zuwa lokacin tsayawar al'adar mace saboda manyanta ko tsufanta (menopause). Mafi yawan nau'in faibirod da ake samu bayada alaƙa da ciwon-daji / kansa (not cancer). Ƙululun ko ƙwallon irin wanda baya da nasaba da ciwon-daji ne (benign/non-cancerous). Yana iya fitiwo fiye da ɗaya a mahaifa, kamar guda uku, huɗu koma fiye da haka a wurare daban-daban cikin mahifa.
TO MINENE ALAMOMIN MATSALAR FAIBIROD ƊIN?
Wasu daga cikin alamomin sun haɗa da:
1. Zubar jinin al'adah mai yawa, ko na tsawon lokaci
2. Zubar jini a baaƙin lokutta ko tsakanin lokuttan haila
3. Ciwon ƙugu, saboda ƙululun yana danne wani sashen jiki cikin mahaifa
4. Yawan fitsari
5. Ciwon baya daga ƙasan baya
6. Jin zafi /ciwo lokacin yin jima'i
7. Rashin jini saboda yawan zubar jini
8. Rashin jin dadi a mara, musamman saboda girman ƙululun a ciki
9. Basur maisa tsugunni a bayi saboda rashin fitar bahaya
10. Ciwon ƙafa
11. Girman ciki kamar mace tana da juna biyu amma ba juna biyu bane, musamman idan faibirod din ya girma
12. Koma rashin ganin wasu ko daya daga cikin alamamomin da muka yi bayani
WASU MATSALOLIN DA FAIBIROD ZAI IYA HADDASAWA:
- Matsala wajen haihuwa/lokacin naƙuda
- Matsala yayin fama da juna biyu
- Matsalar rashin samun juna biyu / rashin ɗaukar ciki ga mace saboda ƙululun ya toshe/taushe ko danne wani bangaren mahaifa
- Yawan bari/zubewar ciki
Yana da matuƙar muhimmanci mai jin daya ko fiye daga cikin wadannan matsalolin yaje asibiti domin binciki ko tana da matsalar faibirod ko akasin haka. Idan kuma kin riga kin sani to sai a nemi magani.
MINENE KE KAWO MATSALAR FAIBIROD?
Har yanzu dai masana ilimi a fannin lafiya na ƙoƙarin fahimtar cikakken dalilin daya sa ake samun fibroid. Saidai an gano cewa yawan sinadarin ESTROGEN (estarojin) a lokacin shekarun da mace ke iya samun haihuwa yana da nasaba da lokacin da mata ke samun matsalar faibirod. Daga shekara 16 zuwa 50 shine lokacin da sinadarin yafi yawa a cikin jinin mace. ESTROGEN daya ne daga cikin manyan sinadaran jikin mace, wato ESTROGEN sinadari ne na jinsin mace dake tafiyar da girman jikin mace, rayuwar mahaifarta da yanayin halittarta daya shafi jima'i . A lokacin balaga sinadarin na taimakawa yasa nonuwa da gashin mara da hammata su fito, kuma shine ke saka sha'awa ko yawan sha'awa ga mace idan yayi yawa. A lokacin balaga ƙwayayan mahaifa (ovaries) zasu fara samar da sinadarin. Za'a iya kiran ESTROGEN da suna MAƘERIN ƳAN MATA , domin kuwa shine ke taimakawa wajen sauye-sauyen halittar jikin mace yayinda take girma. A taƙaice, ESTROGEN shine sinadarin da faibirod suka dogara dashi domin samun daɗa girma a mahaifa, wato makamasin faibirod. Faibirod zai cigaba da girma har sai lokacinda mace ta bar yin al'ada saboda girma (menopause), daga nan sai ya fara ƙanƙancewa.
WASU DALILAI DA KA IYA SA YIWUWAR MACE TA SAMU FAIBIROD:
- Gaado : Idan mahaifiyarki ko ƴar uwarki ta taba samun fibroid zai iya yiwuwa ki samu saboda gadon jini.
- Jinsin baƙar fata: Mutanen Africa ko ƙasashen bakar fata, wato jinsin baƙar fata su suka fi kowanne jinsin mata a duniya samun matsalar faibirod. Kuma matasa mata baƙar fata sune suka fi samun matsalar a shekarunsu na matasa. A ƙasashen turawa, Indiya da Chana da sauran wasu ƙasashen, ba kaso ake samun matansu da matsalar ba.
- Amfani da hanyoyin tsaida haihuwa (ƙwayoyin tsaida haihuwa wani lokacin zasu iya sa faibirod ya girma), ƙiba, ƙarancin sindarin vitamin D, yawan cin jan-nama, rashin cin abincin ganye da yayan itatuwa, shangiya da sauransu.
Hanyoyin asibiti na magance matsalar asibiti ya ƙunshi: aikin tiyata (surgery) domin cire ƙululun tare da cire wani bangaren mahaifa "uterus" [Hysterectomy] wanda zai hana samun haihuwa, sa'annan wani nau'in aiki tiyatar [Myomectomy]wanda baya hana haihuwa a gaba, ƙwayoyin magani da wasu hanyoyin. Musamman idan ya girma aikin tiyata ne akafi yi domin rabuwa da matsalar.Girman faibirod na iya zama kwatankwacin girman dutse karami ko ƙasa da haka , ko girman lemun tsami ko na zaƙi, ko girman ƙwallo, girman jariri koma fiye da girman jariri, musamman idan ba'a cire shiba ko magance saba. Wasu likitocin naganin idan faibirod yakai girman inci 4 (4 inches/9-10 cm) to akwai buƙatar ayi aikin tiyata domin a cire shi.
Domin neman maganin gargajiya (herbal medicine) mai inganci akan wannan matsalar sai a kira +2348084028794 (kuma WhatsApp no. ce) ko email madinahislamicmed@gmail.com. Maganin musamman yana sanya FIBROID yayi ta ƙanƙancewa yana rage girma , ya maƙe har ya mutu.
Za'a iya neman maganin mu a ko ina kuke a Nigeria. Za'a iya biyan kudin magani kai tsaye ta account namu mai rigistar kamfani (corporate account) da suna MADINAH ISLAMIC MEDICINE (account name) a banki, mu kuma mu tura maka magani a duk inda kuke a Nigeria da cajin kudin mota ko Post Office mai sauki, kudin tura magani ta mota mafi sauki (amma banda kudin magani), kudin mota yana kamawa daga N2000, N1500, N1000 har zuwa N500 - a motar haya ko a Post Office idan garin da kuke ba'a Arewa bane. Ko azo office namu da yake a Katsina , Jihar Katsina.
Adreshin ofis: No. 34 Sabuwar Unguwa Dandagoro - kusa da solar Walu, Katsina, Jihar Katsina.
Adreshin mu: Titin Muhammad Dikko, Katsina, daura da makarantar sikandire ta K.C.K. (Katsina College Katsina), Shago na 5 , cikin shagunan Majalissar Malamai ta Kasa , reshin Jihar Katsina, Najeriya.
Kira +2348084028794
Go to:
www.madinahislamicmed.blogspot.com
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
ReplyDeleteHELLO EVERYONE
, I AM HERE TO TESTIFY OF WHAT DR EJEMAI DID FOR MY WIFE AND HOW SHE FINALLY GOT FREED FROM FIBROID
DISEASE THAT HAS BEEN INSIDE HER FOR THIRTEEN YEARS AND SHE WAS NOT ABLE TO GET PREGNANT . WELL IT IS A MIRACLE THAT DR
EJEMAI SAVED MY MARRIAGE AND MADE ME LOVE MY WIFE MORE, WE CONTACTED DR EJEMAI BECAUSE A FRIEND OF MINE TOLD ME ABOUT HIM
AND I WAS HAVING DOUBTS BUT HE ASSURED ME OF GOOD RESULTS. WELL I CONTACTED DR EJEMAI AND HE SENT US SOME MEDICINE WHICH MY
WIFE TOOK FOR 2 WEEEKS AND SHE WAS HEALED
CONTACT DR EJEMAI ON HIS (DREJEMAI@YANDEX.COM) OR ADD HIM ON WHATSAPP ON +1(202)930-5842
I ASSURE YOU OF GOOD RESULTS|
THANKS................
Hello everyone, am very happy to share this little awesome testimony about Dr olu a great herbal doctor who help me enlarge my penis size.3.2 cm to 8.3 cm longer with his herbal cream mixture, my girlfriend is now so amazed with the autonomous size of my penis , if you you are also in need of help on how to enlarge your penis to become bigger and stronger I adverse you to contact Dr on his email (drolusolutionhome@gmail.com) ) you or contact on whatsapp number +2348140654426 because he is one of the best herbal doctor that i can only show you up to, if your penis is 4.2 cm and want to get it reach 9.2 cm within three weeks i Dr olu is also specialized on obey m breast and boobs enlargement i advise you to contact him for help
ReplyDelete