Friday 23 March 2018

YAWAN WASA-DA -AL'AURA DA ILLARSA GA ƘWALWAR MATASA : YAWAN MANTUWA



A ɗabi'ance  , a lokacinda mutum yakai shekara 30 da haihuwa kwalwarsa zata fara samun ja baya , ci bayan zai fara gudu a lokacinda mutum ya kai shekara 50. To amma a wannan zamanin ga alama cibayan zai iya zuwa da wuri kafin shekarun tsufan  samari yazo. Ko minene yasa haka? Amsar itace, "Zinar hannu" , wato wasa-da-al'aura (istimna'i) da ya zama ruwan dare bainar matasa, musamman saboda wayar salula da ake ƴada hotunan batsa da video wanda ke jefa matasa cikin matsananciyar sha'awa da aikata wasa da al'aura koma abu mafi muni zinace-zinace.

KO MINENE ALAƘAR ISTIMNA'I DA YAWAN MANTUWAR MATASA?

Kafin mu amsa wannan tambayar yana da kyau mu yi bayanin abinda ake cewa "Istimna'i" ko "wasa-da-al'aura".Wasa-da-al'aura dai ko wasa da gaba (Istimna'i [masturbation]) na nufin yin amfani da hannu, yatsa ko wani abu domin biyan bukatar jima'i ga mutum da kansa da tunanin saduwa da wata mace ko wani namiji , ga mace. Ana kiran wannan ɗabi'a "zinar hannu". Istimna'i dabi'a ce da take faruwa da yaduwa cikin mutane da dama - yara matasa, da manya mutane, musamman cikin matasa mararsa aure ko wanda aurensu ya mutu, koma rashin gamsuwar aure. Yawan aikata istimna'i (excessive masturbation/over-masturbation) na da illa ga lafiya sosai. Kuma idan ya zama ɗabi'ar mutum koda yaushe to yafi zama matsala ga lafiya da wuyar bari (addiction) wanda hakan zai jefa mutum cikin wani ƙalubalen lafiya mai muni.

To tunda mun fahimci ko minene istimna'i , bari mu koma ga tambayar mu ta farko,  minene alaƙar istimna'i da yawan mantuwa wacce kesa dusashewar ƙwalwar matasa,  rashin riƙe karatu tun kafin tsufa yazo musu? Domin amsa wannan tambaya,  bari mu shiga jikin mutum mu ga abinda ke faruwa  kimiyyance kamar yanda masana suka yi bayani : A duk lokacinda jikin mutum ya fitar da maniyyi da yawa jikin na rasa wasu muhimman sinadarai (neurochemicals/acetylcholine) wanda ke kai saƙo ga kwalwa mutum , kuma su waɗannan sinadaran lafiya suna taimakawa wajen nazari, maida hankali da riƙe wani abu ko karatu a ƙwalwa. Mutumin da yake yawan yin istimna'i jikinsa na samun ƙarancin sinadaran. Sinadarin " acetylcholine" da wasu sinadaran gina jiki (proteins) suna raguwa. Ƙarancin sinadarin (acetylcholine) na sanya ƙwalwa rauni da mantuwa (memory loss/forgetfulness). Bugu da ƙari, ƙarancin na sanya yawan kasalar jiki, da rashin gani da kyau , wato gani buji-buji (blurry vision),  ko ciwon baya (back pain) da zubar gashi (hair loss). Matsalolin lafiya da yawan istimna'i yake haddasawa suna da yawa.

Mutane sunfi yawan alaƙanta yawan mantuwa da tsufa , wato ana ganin tsofaffi keda yawan mantuwa ba yara ba , to amma abin mamaki shine " Ana zaton wuta a maƙera amma sai gata a masaƙa". Yanzu ana samun matasa da yawan mantuwa , rashin hazaƙar ƙwalwa ko maida hankali wanda ke sanyasu wuyar karatun Islamiyya da na Boko. Don haka, yawan istimna'i na na shafar bangaren kwalwa mai kula da ajiye bayanai (hippocampus) daga ma'ajiya ta kusa zuwa ta nesa, da kula da karatu ko maida hankali. Akwai dalilan lafiya na daban da dama wanda zasu iya sanya yawan mantuwa ko ciwon mantuwa (dimentia), kamar haɗari da ya shafi ƙwalwa, gado ko wata cuta. To saidai mantuwar da istimna'i ke haddasawa matasa na daga cikin ɓoyayyun dalilan matsalar mantuwar matasa a wannan zamani.
Wasu illolin da istimna'i zai iya haddasawa  na daban wadanda basu shafi mantuwa ba sun hada:
kankancewar zakari da maraina, saurin kawowa ko rashin karfin mazakuta. Sauran matsalolin dazai iya haddasawa , sun hada da: ramar jiki ko 'karancin sha'awa, karancin maniyyi ko tsinkewar maniyyi da raguwar ingancinsa (wanda na iya haddasa rashin haifuwa) , raunin jiki, raunin garkuwar jiki, jin ciwon kai akai-akai, ciwon baya, fitar maniyyi daga zakari hakanan ba tare da mutum yayi niyya ba - ba tare da yayi istimna'i ba ko yayi jima'i, haka nan kawai.
Wasu illololin da zasu iya faruwa saboda istimna'i: bushewar fatar kan zakari ko illa ga fatar saboda gugar fatar da hannu, karkacewar zakari (penis curvature) ko sauya masa sigarsa ta asali, bugawar zuciya da sauri kurajen fuska.da sauransu.

ILLAR ISTIMNA'I GA MACE

Mace zata iya samun wasu daga cikin matsalolin da mu kayi bayani a sama. Wasu matsalolin daka iya shafar mace sune: Rashin rike fitsari da kyau (ga mace) koYawan zuwa fitsari saboda saka wani abu cikin farji lokacin istimna'i, wuyar kawowa ga mace wajen jima'i (dalilin koyama jikinta da sai an taɓa wani sashen farji don ta kawo, wanda mai yiwuwa ne zakari baya taɓa wurin lokacin saduwa - a zahirin jima'i. Don haka istimna'i yana sa rashin gamsuwar jima'i ga mace - mijinta zai sha wahala wajen gamsar da ita. Jikinta ya riga ya koya, tayima kanta horo. Dalilin haka, mace zata ji dadin istimna'i fiye da jima'i , hakan kuma zai zamo mata matsala idan tayi aure. Zata ringa tunanin mijinta baya iya gamsar da ita ko mazaje data aura, saboda sabon da tayi da koyama jikinta hanyar gamsar da kanta fiye da hanyar da ta dace, wato jima'i a cikin sunnar aure. Ta canza dabi'ar ta. Da yawa zaka samu cewa mata masu yawan istimna'i basu jin daɗin jima'i sai istimna'i, koma basu gamsuwa sai sunyi istimna'i a bandaki bayan saduwa da mazajen aurensu. Wannan zai iya kawo babbar matsala a cikin aure. Bugu da kari, dadilan rashin gamsuwar mace wajen saduwa da mijinta suna da yawa. Don haka, bazamu iya cewa ba yin istimna'i kafin aure shine dalilin dake hana gamsuwa kadai ba. Akwai wasu dalilan na daban, wasu matsalolin nada alaka da bangaren mazajen.

Domin neman karin bayani cikakke akan illolin  yawan istimna'i ga lafiya da hanyoyin barinsa da kariya  sai a shiga wannan link kai tsaye (latsa) ko a kofa a liƙa a Google domin ayi searching:

http://madinahislamicmed.blogspot.com.ng/2016/11/wasa-da-alaura-da-illarsa.html?m=1

Ko a shiga Facebook (latsa LINK karanta) :

https://m.facebook.com/MadinahIslamicMedicine/photos/a.623324837696435.1073741826.621757857853133/1806983335997240/?type=3

Ko azo neman magani a Office Branch namu mai address kamar haka:
No. 34 Sabuwar Unguwa Dandagoro, Katsina, Jihar Katsina.
Kira: +2348084028794 (WhatsApp number)
E-mail: madinahislamicmed@gmail.com

1 comment:

  1. Assalamu alaikum. Dan allah tambaya ta ita ce mene ne maganin aiwata istimna'i ko kuma hanyar da za'a bi don gujewa aikata hakan

    ReplyDelete