Thursday, 28 December 2017

ALAMOMIN BUƊAƊƊEN GABA


Yanayin halittar farji tamkar robar danƙo ce wacce zata iya buɗewa idan aka yi mata talala, haka kuma  zata iya komawa ta haɗe, wato ta  tsuke bayan buɗewa. Tsokokin bangon  farji masu motsi ne kuma zasu  iya tsukewa ko buɗewa idan mace tayi yunkurin tayi hakan, wato idan ta motsa su ko matse su ta ciki. Buɗaɗɗen farji (loose vagina) ko buɗewar farji (vaginal looseness) wani yanayi ne dake shafar mata da yawa musamman lokacin juna biyu da kuma bayan haihuwa inda farji ke canza yanayin halittarsa  ya ƙara girma, wato ya zama buɗaɗɗen wuri kasancewar naman dake zagaye da farji mai yiwa zakari zobe lokacin jima'i ya saki  , tsokokin sun saki basu iya damƙar zakari yanda ya kamata lokacin saduwa. Kamar dai yanayin halittar fatar jikin mutum, wasu mutanen fatarsu nada tauri  kamar roba marar sauƙin budewa idan aka jata,  wasu kuma fatarsu nada laushi da sauƙin yin talala idan aka jata, kusan haka itama halittar  gaban mace take. Wurin haihuwa jinjiri na fitowa ne ta farji inda wurin ke buɗewa sosai domin jinjiri ya fito. Bayan wani lokaci da haihuwa  farji na komawa ya tsuke . Duk da haka , farji ba zai taɓa komawa ba kamar yanda yake ada ko kamar na macen da bata taɓa haihuwa ba (ko budurwa) , koda kau anbi hanyoyin magani , farji zai zamanto ya ƙara  girma kaɗan ko da yawa.

Yawan haihuwar mace, budewar gaba saboda tiyatar likita/ƙarin kofa a lokacin haihuwa (tear) da yawan yin jima'i yau da gobe, na daga cikin dalilan dake haddasa budewar gaban mace. Idan buɗewar farji tayi yawa  yana zama kalubabale ga ma'aurata. Zaya iya zama matsala a rayuwarsu ta jima'i . Saboda wannan yanayi na sanya raguwar ɗanɗanon jima'i ga mace da mijinta koma ya hana macen jin ƙoluluwar daɗi  (orgasm) lokacin saduwa. Dalilin faruwar haka shine ,  farji baya matse/riƙe zakari da  kyau, ta yanda za'a samu ɗanɗanon gugar fata-da-fata tsakanin ma'aurata biyu wanda jin  wannan guga shine  zai kai ma'auratan biyu  ga gamsuwa mai ƙarfi a lokacin jima'i. Bugu da ƙari, wannan matsala  na iya saka mace cikin damuwa da jin cewa bata amsa sunanta na cikakkiyar mace ba saboda bata jin dadin saduwa kuma bata iya gamsar da mijinta da kyau. Hakan kuma zai iya sanya maigidan ya ƙara wani aure domin biyan buƙatarsa. Hakika gamsuwar aure itace saduwa mai daɗi tsakanin ma'aurata da zata samar da soyayya da zaman lafiya mai  ɗaurewa. Matsatstsen gaba (tight vagina) bakin gwargwado, yanayi ne mai kyau da zai iya ƙarawa mace gishirin  soyayya mai ƙarfi tsakaninta da mijinta.

YAYA ZA'AI KI GANE CEWA KO KINA DA  BUƊAƊƊEN GABA?

1. Mafi yawan mata masu fama da matsalar buɗaɗɗen gaba na fama da matsalar rashin riƙe fitsari , wato ɗigar fitsari.  Digar fitsarin zata iya faruwa a lokacinda kika ɗauki wani abu mai nauyi, ko lokacinda kika yi dariya, tari, ko atishawa. Wannan alamace cewa mace nada budadden gaba.Yawan shekaru, yawan haihuwa , yawan jima'i, tiyatar likita (ƙarin kofa) ko wani rauni a  gaban mace, ko   tsayawar al'ada (menopause) saboda karancin sinadarin "estrogen" na iya sanya raunin tsokokin farji wanda daga ƙarshe zai iya haddasa buɗewar tsokokin bangon  farji masu matse zakari .

2. Hanya ta biyu da zaki iya sanin ko kina da gaba mai faɗi itace: ki saka ɗan yatsanki guda (manuni) cikin gabanki sa'annan kiyi ƙoƙarin matse dan yatsan da tsokokin farjinki.  Idan har ki gwada yin hakan kuma ya zamanto baki iya jin kina matse dan yatsan da farji to zaya iya zama kina da babban wuri. Bugu da ƙari, idan kika saka yatsa 2 ko 3, misali manuninki da kuma yatsan tsakiyar hannnunki (mafi tsawo) , kuma baki ji wata alamar bangon farjinki yana matse yatsun ba to yiwuwar itace kina da buddden farji.

3. Idan ya zamanto yana da wuya kamin kiji ƙololuwar dadi (orgasm)/kawowa lokacin saduwa. Yana iya yiwuwa alamar budadden gaba ne. Haka kuma, raguwar jin dadi ba kamar daba shima na iya zama alamar.

4. Idan ya zamanto mace tana wasa da gabanta domin biyan buƙatarta kuma tafi sha'awar ta saka wani babban abu a gabanta akan ƙarami - wato bata jin dadin ƙaramin abu idan ta saka a farji sai babba. Shima alamace cewa mace nada girman farji.  A baya munyi bayani da tsoratarwa akan wasa da gaba. Yana da illa ga lafiya da rayuwar auren 'ya mace. Don haka sai a kiyaye.

5. Idan ya zamanto kina shan wahala kamin ki gamsar da mai gidanki wajen jima'i ba kamar daba.

6. Idan ya zamanto sai kin matse ko haɗe cinyoyin ki biyu  sosai sa'annan kike jin dadin jima'i da maigidanki. Wannan ma yana iya zama alamar budadden gaba. Duk da dai cewa wani lokacin yana iya zamantowa mijin ne keda ƙaramar al'aura. Amma idan kamin haihuwarki babu wannan matsalar sai daga baya to sai ki zargi budewar gaba.

7. Idan ya zamanto kina jin ƙarar fitar iska daga farjinki lokacin da maigidanki yake saduwa dake , iskan kamar fitar "tusa" amma ba tusa bace (fanny farting) kuma babu wari. Iskan yana shiga yana fitowa  lokacinda maigida yake kaikawo. Wannan alamace kina da budadden farji.

MINENE HANYOYIN TSUKE FARJI ?

Akwai hanyoyi da dama na matse gaba musamman bayan haihuwa wanda sun hada da hanyoyin magani, motsa jiki (exercise), tiyatar likita domin rage girman farji da sauransu. Wasu hanyoyin nada illa ga lafiya , wasu kuma hanyoyin basa da wata matsala ko hadari kamar dai yanda likitoci ke bayani. Wasu daga cikin hanyoyin:

1. Motsa jiki , hanyoyin motsa jiki na zamani domin matse gaban mace suna da yawa (such as kegel exercises) da sunaye. Motsa jikin ya shafi horo da mace zata iya bawa jikinta domin ya zamanto tsokokin gabanta masu motsi sun kara ƙarfi da tsukewa. Misali, wata kwararriyar likita a India Dr. Sangeeta Gomes ( Consultant Obstetrician and Gynaecologist) , ta nuna cewa mace zata iya inganta tsukewar gabanta idan tana yin motsa jikin dauke numfashi (breathing exercises). Zaki dauke numfashinki na tsawon 'yan daƙiƙoƙi (seconds) kadan sannan ki tsuke (tsokokin) farjinki matakam na tsawon wani lokaci a lokacinda kike mai dauke numfashin. Za kiyi hakan a kowace rana, sau 10 ko 15. Zaki iya yin hakan a kicin lokacinda kike aiki, a ofis, a tsaye ko a zaune , a ko ina  kuma  a ko wane wuri bata tare da ma wani yasan abinda kike yi ba. Sa'annan  zaki yawaita cin Ƴaƴan itatatuwa (kayan marmari) da abincin ganye (vegetables). Wannan ko shakka babu zai taimakawa  mace wajen matse gaba domin gyara aurenta. Wani nau'in motsa jikin kuma shine ake cema "Kegel exercise". Toh  yaya ake yinshi? Dr. Gomes ta nuna cewa idan kina yin fitsari sai ki tsaida fitar fitsarin, wato ki  riƙe fitarin, ki danne sa na tsawon daƙiƙoƙi 10 , wato ki ƙirga 1 zuwa 10 sa'annan ki saki fitsarin a hankali a hankali. Zaki iya yin hakan sau 2 ko 3 a rana idan za kiyi fitsari. Shima wannan nau'in motsa jikin na tsuke gaban mace.

2. Hanya ta biyu shine wanke gaba da ruwan sanyi mai ƙankara. Yana  taimakawa  wajen matse gaba amma sai an hada da motsa jikin da muka yi bayani. Wannan yana daga cikin hanyoyin da Dr. Gomes ta zayyana. Amma zaifi dacewa ace sai mace ta gama wankan jegonta na kwana 40 kwatakwata sa'annan tayi amfani da ruwan sanyin , wato bayan ta koma "normal". Saɓanin yanda al'adar Bahaushe tayi imani dashi cewa ruwan sanyi na lalata gaban mace ,wasu likitocin a wasu al'adun na ganin yana matse gaba.

3. Yin amfani da aluf (alum). Aluf yana matse gaba sosai sai dai likitoci na tsoratarwa akan yin hakan saboda da sinadarin kemikal ne.

4. Yin tiyatar likita domin rage budewar farji. Wannan ma hanya ce ta zamani amma ana tsoratarwa akan yin hakan saboda wasu dalilan lafiya.

5. Yunƙurin tsuke gaba a lokacin saduwa, wato ki matse farjinki ta ciki lokacinda mijinki yake kaikawo. Zaki yawaita yunƙuri domin tsuke gabanki domin mijinki yaji alamun ana riƙe masa al'aura tamkar zobe zagayen gabansa. Idan mace na yawaita yin da haka to zai zama ɗabi'arta kuma nan gaba ba zata san ma tanayin hakan ba saboda ta riga ta horar da jikinta, kuma hakan zai inganta jin daɗin mijinta sosai. Allah Ya taimaka.

6. Da sauransu.

Za'a iya neman taimako na musamman daga cibiyar mu domin magance wannan matsala wacce za'a haɗa da bayanan da mukayi anan domin samun sakamako mai kyau, da yardar Allah.

Sai a kira +2348084028794 (also WhatsApp number)

Email: madinahislamicmed@gmail.com
Blog: www.madinahislamicmed.blogspot.com

Ko azo shago ko office namu kamar haka:

Address: No. 5 Muhammad Dikko Road, daura da makarantar sikandire ta KCK (Katsina College Katsina) - hanyar babban asibitin Katsina, jihar Katsina.

Office Address: No.34 Sabuwar Unguwa , Dandagoro Area, Katsina, Jihar Katsina.

Yi LIKING shafin mu domin samun bayanan lafiya irin wadannan masu amfani.

https://m.facebook.com/MadinahIslamicMedicine/?ref=bookmarks

Tuesday, 12 December 2017

ALAMOMIN CIWON SANYIN MARA NA MAZA/ SANYIN GABA


Ciwon sanyi cuta ce da akafi yaɗawa ta hanyar jima'i (STDs/STIs) .ƙwayoyin halittun dake sanya cutar ana yaɗa sune daga wani mutum zuwa wani mutum, ta jini, maniyyi, ruwan farji ko ruwan jiki. Alamomin ciwon sanyi ga maza sun sha banban tsakanin mutane wanda ciwon ya harba. Hakan ya danganta ne da nau'in ƙwayar halittar cutar wacce ta haddasa ciwon  da kuma matakin da cutar ta takai a  jikin mutum - ma'ana, alamomi ko matakin farko da kamuwar cutar ko alamomi na gaba bayan ta soma jimawa a jikin marar lafiyar. Haka kuma, suma yanayin alamomin sunsha banban ta fuskar tsanani ko sauƙinsu,  koma rashin ganin alama ko ɗaya duk da  cewa kau akwai cutar a jikin marar lafiyar. Maza da yawa na zargin suna da ciwon sanyi ne kaɗai a lokacinda suka ga wasu alamomi da basu saba gani ba (baƙi) ga al'aurarsu, misali , kamar: feshin ƙananan ƙuraje ko ƙaikayi, ko fitar farin ruwa, jin raɗaɗin zafi daga maraina da sauransu. A taƙaice dai, alamomin ciwon sanyin maza zasu iya ɓuya amma gwaji a asibiti zai iya nuna akwai cutar idan akwaita.

Ciwon sanyi anfi yaɗasa ne ta hanyar jima'i kuma maza na iya harbin mata da ciwon ko kuma su matan masu ɗauke da ciwon su sakawa maza mararsa ciwon. Ciwon yafi yaɗuwa kuma anfi samunsa ga maza masu neman mata ko mata masu bin mazaje. Haka kuma mutum zaya iya kamuwa da ciwon ta wasu hanyoyin na daban daba  jima'i ba. Kuma lallai ciwon nada wuyar magani , musamman idan mutum bai samu  magani ingantacce ba. Zai iya yin wuyar magancewa saboda  rashin samun sahihin magani ko daɗewarsa cikin jiki ba'a magance ba.  Sau da yawa zaka ga cewa mutane sukan sha magunguna domin kaiwa ciwon hari da sukar alluran likita amma hakan bai  razana ciwon ba  sai kaga  yana ma mutane jeka-ka-dawo tsawon watanni koma shekaru ba'a samu waraka ba.

Alamomin ciwon sanyin maza wanda akafi samu bainar mutane (game gari) :
1. ƙananan ƙuraje akan zakari, ko maraina ko ƙasansu.
2. ƙaikayi akan zakari (kan hular).
3. Fitar farin ruwa daga zakari, mai kalar madara ko ɗorawa, mai kauri ko wanda ya tsinke.
4. Jin zafi wajen yin fitsari.
5. Jin zafi yayin fitar maniyyi.
6. ƙuraje masu ɗurar ruwa da fashewa akan zakari.
Alamomi ciwon sanyin maza wanda ba game gari ba:
1. Rauni (gyambo) ga zakari ko maraina.
2. Zafi da kumburin maraina
3. Zafi da kumburi daga kwararo da  fitsari da maniyyi suke fitowa daga cikin zakari.
4. Zazzaɓi

Matsalolin jima'i da ciwon sanyi zai iya haddasa ma maza:

1. RASHIN KARFIN MAZAKUTA: Bincike ya nuna cewa cutar ciwon sanyi mai suna da turanci "Chlamydia" (kilamiidiya) zata iya sanya matsalar rashin ƙarfin mazakuta idan ciwon yayi ƙamari ba'a magance shi ba. Cutar maɓannaciya ce da take illa a ɓoye kuma mafi yawanci bata nuna wata alama a zahiri ga mai ɗauke da cutar. Ana samunta bainar mutane da yawa. Rashin ƙarfin mazakuta na nufin matsalar rashin cikakken ƙarfin al’aurar namiji ko raguwar ƙarfin al’aura yayinda aka fara saduwa ko kuma rashin miƙewar al’aura yayinda ake buƙatar fara jima’i. Bugu da ƙari,  matsalar na iya zuwa da saurin kawowa/inzali. Rashin  ƙarfin maza zai iya saka magidanci cikin damuwa da tawayar jinɗaɗin rayuwarsa ta jima'i, ko jin cewa bai cika mutum namiji ba, ko rashin haifuwa kasancewar bazai iya yima iyalinsa ciki ba saboda rashin miƙewar al'aura. Zuwa asibiti da wuri ko cibiyar lafiya zai iya tsiratar da mai wannan matsala,  inshaaAllah.

2 RASHIN HAIFUWA:. Cutar sanyi mai suna "Gonorrhea" (Gonoriya) , kamar dai ƙwayar cutar "Chlamydia", cutace daga halittar "bacteria" kuma zata iya laɓewa a cikin jiki ba tare da wasu alamomi ba. Duk da haka, tana zuwa da alamomi kamar fitar farin ruwa, mai kalar madara daga farkon cutar,  daga nan sai ya koma ɗorawa, mai kauri da yawa, wani lokacin harda ɗan jini-jini. Yin fitsari da zafi da yawan yin fitsari, ƙaikayin dubura, zubar jini,  murar maƙoshi/maƙogwaro, jan- ido ko ƙananan kuraje, ciwon gaɓoɓi da sauransu. Idan ba'a lura da cutar da wuri ba kuma aka magance ta, zata iya sanya rashin haifuwa ga namiji ko mace.

Nau'in ciwon sanyi (ire-irensu) suna da yawa kuma kowanne iri akwai ƙwayar halittar dake haddasa ciwon da alamominsa da kuma matakan cutar a jikin 'dan adam. Sunayen cututtukan da turanci suna da yawa kamar yawan cututtukan. Cutar sida/ƙanjamau (AIDS/HIV) tana daga cikin manyansu  saboda itama anfi yaɗata ta jima'i, kuma sau dayawa itace ke gayyatar sauran cututtuka a jikin 'dan adam.

3) KANKANCEWAR ZAKARI,  duk da dai cewa babu wani sahihin bayani a kimiyyance dake nuna cewa ciwon sanyi yana sa azzakarin namiji baligi ya koma ƙarami, akwai rahotanni da yawa daga mutane na ƙorafin cewa sanyi ya sace musu girman zakari. Wannan zance haka yake a zahiri, masu ciwon sanyi sune suka fi lura da damuwa akan ƙanƙancewar alƙalummansu.

Wasu daga cikin cututtukan sanyin da ake samu ta jima'i da ƙwayoyin halittu wanda ke haddasa su (a yaren turanci):

a) CHANCROID (bacteria) , cuta ce wacce ke zuwa da yanayin gyambo wani lokacin tare da ƙululu a hantsa.

b) CRABS (parasite), 'yan ƙananan halittu sosai , yanayin kwalkwata, masu cizo da tsotsar jini mai sanya mugun ƙaiƙayi. Ana samunsu daga gashin mara inda suka maida gidansu, ana kuma iya ɗaukarsu daga gashin gaban wani mutum zuwa na wani lokacin jima'i. Ana kuma iya samunsu ta kayan sawa, gado da sauransu.

c) GENITAL HERPES (virus) , cuta wacce take zuwa da ƙuraje masu ɗurar ruwa a baki ko kan zakari,  ƙurajen masu kama dana zazzaɓin dare (fever blisters). Idan ƙurajen suka fashe sai su zama gyambo. Haka kuma za'a iya samun ƙurajen a ɗuwawu, cinyoyi, ko a dubura. Ciwon kai ko baya, ko mura (flu) mai ɗauke da zazzaɓi,  ko kaluluwa da raunin jiki/kasala.

d) SYPHILIS (bacteria),  anfi samunta wajen 'yan luwaɗi. Tana da matakai bayan shigarta a jiki. Misali,  matakin farko (1): fitowar wani irin gyambo (chancre), wannan gyambon shine wajenda cutar ta shiga jikin mutum. Gyambon mai tauri, mai zagaye marar zafi. Wani lokacin abuɗe yake kuma da lema, ko zurfi musamman a hular zakari, wanda zaka ga wurin ya lotsa. Ana samunsa a zakari ko dubura ko leɓe (a baki). Ana kuma iya samun gyambon a ɓoye wani wajen cikin jiki. Mataki na biyu (2): ƙuraje a tafin hannu ko ƙarkashin tafin ƙafa ko wani sashen na jiki. 'Yar mura, zubar gashi, zazzabi marar tsanani, kasala,  murar maƙoshi, ciwon kai ko ciwon naman jiki da sauransu.  Mataki na gaba: mataki na gaba ko ƙarshe shine  wanda cutar zata iya ɓoyewa a jiki, 'buya idan ba'a magance taba,  kuma zata iya sanya ƙululun kansa/ciwon daji (tumour), makanta, mutuwar sashen jiki, matsalar ƙwalwa, kurumta, ciwon mantuwa mai tsanani (dimentia). Ana iya magance cutar cikin sauki da idan an lura da ita,  da wuri, da yardar Allah.

e) DA SAURANSU, suna da yawa kuma alamomin wani ciwon na kama da na wani ciwon wani lokacin. Don haka bincike a asibiti shine zai nuna nau'in ciwon.

Ciwon sanyi yana da haɗari sosai. Ya zama dole ga mutane su tsaya ga matan su na Sunnah idan har suna son lafiyarsu. Ciwon sanyi yana nan akan hanyar mai neman mata da zinace-zinace, zai cimmasa. Akwai ciwuka masu haɗari sosai kamar AIDS/HIV, wanda zasu iya wargaza iyali. Don haka maison zaman lafiyarsa da rayuwa mai kyau sai yaji tsoron Allah. Wanda kuma Allah Ya jarabta da ciwon bata hanyar zina ba to sai ya nemi magani,  haka shima wanda ya tuba ga Allah. Allah Ya bawa Musulmi lafiya.

Domin neman ƙarin bayani ko neman magani/waraka sai a

 kira +234808 402 8794
 domin neman taimako na musamman daga cibiyar mu ta kiwon lafiya ta Musulunci mai albarka da mutane.
Shafin mu na yanar gizo :
www.madinahislamicmed.blogspot.com
E-mail: madinahislamicmed@gmail.com

Adreshin mu: Sai a ziyarci cibiyar kai tsaye dake Katsina, Jihar Katsina, Najeriya-

Adreshin mu: Titin Muhammad Dikko, Katsina, daura da makarantar sikandire ta K.C.K. (Katsina College Katsina), Shago na 5 , cikin shagunan Majalissar Malamai ta Kasa , reshin Jihar Katsina, Najeriya.

Adreshin ofis: No. 34 Sabuwar Unguwa Dandagoro,  Katsina.

LIKE our Facebook page domin samun bayanan lafiya irin wadannan masu muhimmanci:
https://mobile.facebook.com/MadinahIslamicMedicine


Saturday, 18 November 2017

Abubuwa 10 Dake Hana Mata Jin Dadin Jima'i/Gamsuwa ko Sha'awa a Rayuwar Aure


Shin kona mamakin mi yasa iyalinka bata da sha'awa? Ko kema kina mamakin mi yasa baki jin dadin jima'i ko baki da sha'awa? Sai ku duba ku gani mai yiwuwa wannan bayanai zasu iya baku haske akan matsalar dake damunku domin neman mafita.

Duk da yake anfi ganin cewa mata sunfi maza yawan sha'awa da son jima'i a yanayin halittarsu akan maza, ba abin mamaki bane a sami akasin haka wani lokacin, cewa akwai mata da yawa wanda basa da sha'awa ko kwadayin jima'i saboda wasu  dalilai na lafiya . Hakan na faruwa inda zaka  sami mace na gudun kwanciyar aure ko bata damu da ayi kwanciyar ba ko kada ayi (duk daya ne a gurinta) saboda koda anyi ma  bata jin dadin jima'in sam , ko kuma bata jin dandanonsa irin yanda take tsammani ake ji , kamar yanda sauran mata  'yan uwanta ke jin dadin rayuwar aure da mazajen su. Tana yin kwanciyar aure ne kawai a matsayin wani aiki (duty) na biyan bukatar mijinta ba bukatar taba, kuma ba don tana jin dadi ba ko gamsuwa , saidai kawai don bautar aure ko gudun fushin sabawa al'ada, ko kuma domin kare mijinta daga fadawa tarkon zina.  Hakika akwai mata da yawa da suke cikin wannan yanayin rayuwar aure marar dadi,  wanda sun hakura da hakkinsu na jin dadin aure inda wasu matan kuma ke kokarin neman mafita daga wannan matsala ta neman hakkinsu daga mazajensu ko neman magani, koma kokarin fahimtar matsalar dake hana su jin dadin da nufin neman warwarar matsalarsu.  Wannan kalubale ne babba. 

Anan zamu ari wasu bayanan lafiya domin bada haske ko bayani  akan wasu daga cikin dalilan da yasa wasu mata basa da sha'awa, ko basa jin dadin jima'i (salaf suke ji), ko basa jin dadi sosai, ko kuma ma basu taba jin dadin ba a rayuwar aurensu. Wasu dalilai nada alaka da macen, wasu kuma namijin ne. Sune kamar haka:

1. CIWON SANYIN MARA KO MATSALOLIN  MARA DA MAHAIFA: Kama daga sanyin mara (vaginities/toilet infections, UTI & STDs), yoyon fitsari, 'kululun mahaifa (fibroid), da sauran cututtukan al'aura na daga cikin abubuwan da ka iya hana mace jin dadin jima'i.Misali, sanyin gaba mai zuwa da 'yan 'kananan kuraje cikin farji , na sanya mace taji zafi wajen jima'i yayinda zakari ke kai-kawo cikin farji, wanda sau da yawa masu kurajen basu ma san suna da kurajen ba cikin al'aura, saidai suce suna jin zafi lokacin saduwa. Kurajen suna fashewa saboda da gugar zakari, sai wurin ya zama rauni. Hakan nasa mata tsoron jima'i da ganinsa  abin azabtarwa gare su mai maimakon abin  jin dadi. Sau tari basu san abinda ya haddasa zafin ba, wanda kuma mai yiwuwa ciwon sanyi. Ciwon sanyi na iya dakushe sha'awar mace ko namiji. Ciwon sanyi na iya haddasa bushewar gaba (vaginal dryness) wanda alamunsa shine daukewar ni'ima da 'kaikayin gaba. Idan gaba ya bushe zaiyi wahala mace da miji suji dadin jima'i in banda zafi. Haka kuma shima 'kululun mahaifa (fibroid)  yakan ci karo da zakari cikin farji sai mace taji wani irin yanayi marar dadi (discomfort) lokacin nishadin aure. Kuma yana danne mahaifa ya hana haifuwa da kuma sanya yawan zubar jini. Don haka neman magani shine mafita. 

2. BUDADDEN GABA: Rashin tsukakken farji  yanda zai damki zakari da kyau domin samar da jin dandanon fata-da -fata a matse. Budadden gaba kalubale ne dake sanya raguwar jindadi tsakanin ma'aurata. Sau da yawa ma'auratan biyu ba zasu sami gamsuwa ba da kyau, sa'annan macen baza ta iya jin 'kololuwar dadi ba (orgasm). Akwai dabarun kwanciya da magani na zamani da zasu  iya magance wannan matsala. 

3. KACIYAR MATA (WUCE GONA DA IRI WAJEN YINTA): kaciyar mata (female circumcision)  wacce Wanzan ya yanke beli da yawa fiye da yanda ya  dace. Yin hakan na kashe sha'awar mace idan ta girma. Da yawa mata an yanke musu sha'awa a duniya tun lokacinda suna jarirai. Wasu al'adun a duniya suna yanke beli ne kadan,  wasu kuma kamar rabi ne ake fillewa, wasu kuma cire shi suke duka,  wato yanke shi suke gaba daya. Yanke beli da yawa ko duka matsalace dake hana mace jin dadin jima'i,  domin kuwa beli (clitoris) shine matattarar jin dadin jima'in mace. Kamar yanda dai Malamai sukai bayani cewa yin kaciyar mata Mustahabbi ne a Musulunci,  Sharia kuma  tayi nuni da cewa kada a wuce gona da iri wurin yankan, ba kamar yanda wasu wanzamai ke aikatawa ba yanzu.  To sai a nemi bayanan Malaman Sunnah domin fahimtar mas'alar baki daya. Bugu da kari,  za'a iya neman magani domin inganta jin dadin aure. 

4. MAGUNGUNA : Ko shakka babu akwai nau'in magungunan turawa ko gargajiya da zasu iya dakushe sha'awar mace, misali magungunan da ake bayarwa domin rage ciwon damuwa ko tsananin 'bacin zuciyar mutum (antidepressants)  da sauransu. Kina mamakin cewa ada kina da sha'awa amma yanzu shiru ne toh mai yiwuwa wannan maganin da kike sha wata da watanni , ko cikin satin nan , shine ke sace miki sha'awa. Yana da kyau duk maganin da aka bawa marar lafiya a asibiti ko wani wuri yasan tutsun maganin ("side-effects" nashi) don kada wani abu ya dameshi bai san abinda ya jaza masa ba. 

5. RASHIN INGANTACCEN ABINCI MAI LAFIYA: Idan mace bata cin abinci mai kyau ta koshi wanda zai inganta lafiyarta da jikinta da sinadarai na ni'ima ,to sha'awarta tamkar shukace wacce bata samun ruwa wacce zata mutu. Kifi, naman kaza,  madara,  yogat, hanta, kwai, zuma, dabino, aya, gyada, kankana, aiba da sauran abincin mai gina jiki da kuzari tare da 'ya'yan itatuwa zasu iya cika mace da sha'awa da ni'ima bayan 'daukewar sha'awa. Wadannan abubuwa marmari da abinci tamkar taki ne da ruwa ga shuka, wato sha'awar 'ya mace. Don haka mazaje su siyama matansu kayan dadi domin moruwa daidai gwargwadon hali. 

6. SAURIN INZALIN MAIGIDA/ SAURIN KAWOWA/RASHIN KARFIN MAZAKUTA: Wannan matsalar nada alaka da mazajen aure kai tsaye. Wannan matsalar na cutawa mata sosai kuma wani lokacin tana da alaka kai tsaye da rashin karfin mazakuta. Idan akwai karfin mazakuta ga namiji koda ba babba bane zakarin zai iya gamsar da iyalinsa idan akwai karfi sosai, kuma zai dade yana saduwa da iyalinsa har ta biya bukatarta. Haka kuma idan muka kalli matsalar ta wata mahangar, hakan na faruwa ne saboda rashin sha'awar namiji - wato sinadaran jima'insa (sex hormones /low testosterone) sun ragu ko sunyi 'kasa , ko kuma hawan-jini ko ciwon-suga suke haddasa masa matsalar ko ma yawan sinadarin kolesterol ko wasu matsalolin zagayawar jini. . Don haka  cin abinci mai inganta lafiya da harkar  jima'i ko magani mai kyau da likita yayi izini dashi zai iya gyara matsalar. Mafi yawan lokutta mata na bukatar tsawon lokaci kamin su kawo (kololuwar dadi /"orgasm") sabanin lokacinda maza da dama ke iya jurewa su biya musu bukata. Don haka,  yin wasanni , yima iyali wasa tsawon lokaci (foreplay) na iya fansar lokacinda maigida baya iya kaiwa ta yanda mace zata iya fara biyan bukatarta ko kawowa kamin saduwa da ita ta.

7. RASHIN FAHIMTAR YANAYIN JIKIN MACE DA BUKATUNTA NA KWANCIYA : Ko wace mace da irin bukatunta na jima'i , akwai irin abinda take so ayi mata da na'uin kwanciyar da take jin dadinta amma da yawa kunya na hana mata bayyana abinda suke so, don haka sai subar mazajensu cikin duhu suna ta kokarin jarraba abubuwanda basa yi musu.  Don haka matan aure su fidda kunya domin tattaunawa da mazajensu akan  abinda suke so wajen jima'i da mazajen suma su bayyana irin bukatun nasu domin fahimtar juna da  jin dadin rayuwar aurensu. Haka kuma yana da kyau maigida ya rinka lura da nazari akan bukatun wasu sassan jikin matarsa idan mai yawan kunya ce. Yau da gobe zai iya gane abinda ke yimata wajen saduwa. Yau da gobe zaka  tara ilimi mai yawa akan bukatar matarka amma  idan har kana lura da kyau. 

8. WASA DA GABA: Idan mace na wasa da farjinta (istimna'i) da yatsa ko wani abu ta take sakawa,  zai iya sanyawa  taji bata jin dadin jima'i ko gamsuwa da maigidanta sai tayi istimna'i saboda tafi kowa sanin jikinta da mallakarsa, ta gano bukatunta na shaidan wanda aurenta bazai iya biya mata ba.   Musamman bainar  zawarawa da 'yan mata wannan abune game gari,  da yawa sun saba biyama kansu bukata kuma zai iya shafar tarayyarsu da mazajen da zasu aura nan gaba. Kamar dai yanda muka yi bayani a wata wallafar mu a can baya cewa,  istimna'i nasa wuyar kawowa ga mace wajen jima'i (dalilin koyama jikinta da sai an taɓa wani sashen farji don ta kawo, wanda mai yiwuwa ne zakari baya taɓa wurin lokacin saduwa - a zahirin jima'i. Don haka istimna'i yana sa rashin gamsuwar jima'i ga mace - mijinta zai sha wahala wajen gamsar da ita. Jikinta ya riga ya koya, tayima kanta horo. Zata ringa tunanin mijinta baya iya gamsar da ita ko mazaje data aura, saboda sabon da tayi da koyama jikinta hanyar gamsar da kanta fiye da hanyar da ta dace, wato jima'i a cikin sunnar aure. Ta canza dabi'ar ta. Da yawa zaka samu cewa mata masu yawan istimna'i basu jin daɗin jima'i sai istimna'i, koma basu gamsuwa sai sunyi istimna'i a bandaki bayan saduwa da mazajen aurensu. Wannan zai iya kawo babbar matsala a cikin aure. 

9. ALJANIN SOYAYYA(JINNUL AASHIQ): kamar dai yanda muka tattaro wasu bayanai daga Zauren Fiqh da wata mabubbugar. Aljani na iya shiga jikin mace da sunan soyayya ya dinga saduwa da ita koma ya aureta. Hakan zaisa aljanin ya hana ta aure, ko haifuwa, ko rashin zama lafiya da miji idan tayi auren, kuma zaisa mata daukewar sha'awa da ni'ima ga mijinta, ko zubar jini ko ruwa mai wari koma gaban mijin yaki mikewa lokacin saduwa.  Zata rinka mafarkin ana saduwa ta ita wanda shedanin zo mata da siffar mijinta ko wani mutum, ko siffar  mace na saduwa da ita. Ko ta dinga ganin mutum tsirara gabanta. Wadannan suna daga cikin alamomin, kuma dalilin take hana mace jin dadin jima'i ko sha'awa. 

10. RASHIN SHA'AWA SABODA KARANCIN SINADARAN JIMA'I A JINI KO CIWON DAMUWA : Karancin sinadarin jima'i da sauye-sauyen halittar mace( low estrogen) na iya haddasa sallacewar sha'awar mace. Alamomin karancin sinadarin sune: jin zafi wajen jima'i saboda rashin ruwan gaban mace, zuwan al'ada ba akan lokaci ba ko rashin yinta , karuwar cututtukan mafitsara (UTIs)  canjin yanayin rai - daga farin ciki zuwa damuwa, ciwon nono, ciwon kai,  ciwon damuwa , kasala,  wuyar lura ko nazari , rashin 'kwarin 'kashi, da sauransu. Idan ba'a magance matsalar  ba zai iya sanya mace rashin haifuwa. Abubuwanda ke haddasa karancin sinadarin sun hada da: ciwon kwada mai tsanani, tsananin motsa jiki, zufar dare,  gumin jiki, rashin bacci , rashin cin abinci saboda tsoron yin 'kiba; haka kuma, ga mata wanda suka haura shekara 40 na haifuwa karancin sinadarin na iya zama alama ne cewa sun kusa gama al'ada. Don haka sai aga likita domin magance matsakar ko a nemi magani. Allah Ya taimaka. 

Sai a kira +234808 402 8794 domin neman taimako/magani na musamman daga cibiyar mu ta kiwon lafiya ta Musulunci mai albarka da mutane.

Shafin mu na yanar gizo :
www.madinahislamicmed.blogspot.com
E-mail: madinahislamicmed@gmail.com
Adreshin mu: Sai a ziyarci cibiyar kai tsaye dake Katsina, Jihar Katsina, Najeriya. Adreshin mu: Titin Muhammad Dikko, Katsina, daura da makarantar sikandire ta K.C.K. (Katsina College Katsina), Shago na 5 , cikin shagunan Majalissar Malamai ta Kasa , reshin Jihar Katsina, Najeriya.

LIKE our Facebook page domin samun bayanan lafiya irin wadannan masu muhimmanci:

https://m.facebook.com/MadinahIslamicMedicine

Tuesday, 12 September 2017

WASA-DA-AL'AURA / WASA -DA-GABA DA ILLOLINSA GA LAFIYA

Wasa-da-al'aura ko wasa da gaba (Istimna'i [masturbation]) na nufin yin amfani da hannu, yatsa ko wani abu domin biyan bukatar jima'i ga mutum da kansa da tunanin saduwa da wata mace ko wani namiji , ga mace. Wasa-da-al'aura ko wasa da gaba dabi'a ce da take  faruwa da yaduwa cikin mutane da dama - yara matasa, da manya musamman cikin  matasa mararsa aure ko wanda aurensu ya mutu,  koma rashin gamsuwar aure. Wannan dabi'a ta zamo ruwan dare kuma abin 'kyama saboda wasu dalilai, wato dalilan  addini, na al'adu, da  kuma na lafiya. Dalilan lafiya da zamu yi magana akansu, suna magana ne game da yawan yin istimina'i da illarsa ga mai yawan yi wanda ya zama dabi'arsa koda yaushe (An addict person who overmasturbates ). Bincike-binciken wasu masana kimiyya da muka tattaro game da yawan wasa-da-al'aura (over-masturbation), na nuna cewa YAWAN WASA-DA -AL'AURA (excessive masturbation or over-masturbation) nada illololi ga lafiya. Duk da yake dai masana sunyi saɓani akan mas'alar istimna'i, inda wasu ke ganin yana da illa wasu kuma basa ganin haka saima kishiyar haka, to sai dai babu rikici akan cewa yawan yin istimna'i  nada illa ga lafiya. Yana  iya haddasa wadannan matsalolin idan ya zama halin mutum baya jin daɗi sai ya aikata (addiction):

Yawan mantuwa, rage hazaqar kwalwa, kankancewar zakari da maraina, saurin kawowa ko rashin karfin mazakuta. Sauran matsalolin dazai iya haddasawa , sun hada da:  ramar jiki ko 'karancin sha'awa, karancin maniyyi ko tsinkewar maniyyi da raguwar ingancinsa (wanda na iya haddasa rashin haifuwa) , raunin jiki, raunin garkuwar jiki, jin ciwon kai akai-akai, ciwon baya, fitar maniyyi daga zakari hakanan ba tare da mutum yayi niyya ba - ba tare da yayi istimna'i ba ko yayi jima'i, haka nan kawai. Wasu illololin da zasu iya faruwa saboda istimna'i: bushewar fatar kan zakari ko illa ga fatar saboda gugar fatar, karkacewar zakari (penis curvature) ko sauya masa sigarsa ta asali, bugawar zuciya da sauri, zubar gashi, kurajen fuska,

ILLAR ISTIMNA'I GA MACE

 Rashin rike fitsari da kyau (ga mace) ko yawan zuwa fitsari saboda saka wani abu cikin farji lokacin istimna'i,  wuyar kawowa ga mace wajen jima'i (dalilin  koyama jikinta  da sai an taɓa wani sashen farji don ta kawo, wanda mai yiwuwa ne zakari baya taɓa wurin lokacin  saduwa - a zahirin jima'i. Don haka istimna'i yana sa rashin gamsuwar jima'i ga mace - mijinta zai sha wahala wajen gamsar da ita. Jikinta ya riga ya koya, tayima kanta horo.  Dalilin haka, mace zata  ji dadin istimna'i fiye da jima'i , hakan kuma zai zamo mata matsala idan tayi aure.  Zata ringa tunanin mijinta baya iya gamsar da ita ko mazaje data aura, saboda sabon da tayi da koyama jikinta hanyar gamsar da kanta fiye da hanyar da ta dace, wato jima'i a cikin sunnar aure.  Ta canza dabi'ar ta. Da yawa zaka samu cewa  mata masu yawan istimna'i basu jin daɗin jima'i  sai istimna'i, koma basu gamsuwa sai sunyi istimna'i a bandaki bayan saduwa da mazajen aurensu. Wannan zai iya kawo babbar matsala a cikin aure. Bugu da kari, dadilan rashin gamsuwar mace wajen saduwa da mijinta suna da yawa. Don haka, bazamu iya cewa ba yin istimna'i kafin aure shine dalilin dake hana gamsuwa kadai ba.  Akwai wasu dalilan na daban, wasu matsalolin nada alaka da bangaren mazajen.

Mutumin da matsalar yawan wasa-da-al'aura ta zama dabi'arsa koda yaushe (addict) zaya iya maganin matsalar. Idan har yazama dabi'ar mutum baya jin dadin rayuwarsa sai yayi istimna'i (sau 2, 3, 4 ko fiye da haka a kowace rana) [addiction] toh zai iya kawo sauye-sauye (canje-canje) ga jikin mutum wanda lafiya bata maraba dasu ( such as hormonal imbalance), saboda yawan zubda sinadaran jikin mutum wajen inzali fiye dabi'ar jima'i ta gaskiya da sauyin yanayin jiki sakamakon yawan hakan . Yana da hadari ga lafiya yanda wasu matasa suka maida wannan dabi'arsu ta koda yaushe, a bandaki, a daki, a waje, ko a wurinda dama ba'a tsammani suna istimna'i...Idashe karanta sauran wannan bayanin (latsa LINK a kasa)

http://madinahislamicmed.blogspot.com.ng/2016/11/wasa-da-alaura-da-illarsa.html?m=1

Domin neman karin bayani ko taimako:
Kira: +2348084028794
E-mail: madinahislamicmed@gmail.com

DALILAN DAKE HADDASA MATSALAR RASHIN KARFIN MAZAKUTA

Rashin karfin mazakuta na nufin matsalar rashin cikakken karfin al’aurar namiji ko raguwar karfin al’aura yayinda aka fara saduwa ko kuma rashin mikewar al’aura yayinda ake bukatar fara jima’i. Bincike ya nuna cewa wannan matsala tafi yawa ga masu shekaru 40 zuwa 70, kuma tana karuwane a lokacinda mutum yake manyanta. Saidai duk da haka akwai matasa da dama masu irin wannan matsala. Wasu daga cikin dalilan wannnan matsalar sune kamar haka... Idashe karanta sauran wannan bayanin (latsa LINK)

http://madinahislamicmed.blogspot.com.ng/2013/07/kalubale-ga-maaurata-kashi-na-2_25.html?m=1

SAURIN INZALI/KAWOWA

Abincin tunani shine ilimi, abincin ruhi shine kwanciyar hankali, abincin zuciya farin ciki, abincin sha'awa biyan bukata. Biyan bukatar jima'i tsakanin ma'aura na fuskantar 'kalubale da barazana ga wasu ma'auratan da dama. Shin kokasan cewa rashin biyan bukatar iyalinka zai iya haddasa maku matsaloli munana?

Wasu masana a wata cibiyar bincike ta kimiyya dake Amurka sun gano  cewa: Biyan bukatar namiji da mace wajen jima'i yasha banban ta fuskar tsawon lokaci. Kashi 68 cikin 100 na mata suna bukatar minti 8  su biya bukatarsu da mazajensu, haka kuma, kashi 45 na wasu matan na bukatar minti 12 yayin saduwa. Abin mamaki shine, kashi 75 na wasu maza na kasa jurewa su tsawaita lokacin biyan bukatarsu zuwa minti 3 ko 6, sabanin lokacinda wasu matan ke bukata don biyan bukatarsu. (Qinghai Province Xining City Ailida Biotechnology Company's research information, 2012)

Haryanzu  dai babu wani sahihin bayani ko dalili dake bayyana dalilin wannan matsala, saidai wasu bayanai akan dalilan dake iya bada haske gameda matsalar saurin kawowa ga wasu mazan (premature ejaculation). Sune kamar haka ... Ida Karanta sauran wannan bayanin (latsa LINK a kasa)

http://madinahislamicmed.blogspot.com.ng/2013/07/kalubale-ga-maaurata.html?m=1

ƘANƘANCEWAR ZAKARI

Kankancewar zakari na nufin raguwar girman al'aura, wato wani yanayi ne da al'aurar namiji baligi ke zama ƙarama tamkar ta ƙaramin yaro - ta shige ciki ko ta rage tsawo ko kauri a lokacin da take kwance (flaccid state) ko a miƙe (erect state) saɓanin yanda take ada. Wannan yanayi na faruwa ga mutum ne a lokacin da yake manyanta cikin rayuwarsa, a dabi'ance. Hakan na faruwa ne ga mutane  da shekarunsu na haifuwa suka kai 30 zuwa 40. Amma duk da haka akan sami matasa da yawa wanda basu kai ga wadannan shekarun haifuwa ba masu fama da wannan matsalar...Idashe karanta sauran wannan bayanin (latsa LINK a kasa)

http://madinahislamicmed.blogspot.com.ng/2017/08/anancewar-alaurazakari-penile-shrinkage.html?m=1

AMFANIN JIMA'I GA LAFIYA

Karanta wannan bayanin...(latsa LINK a kasa):
http://madinahislamicmed.blogspot.com.ng/2013/11/kalubale-ga-maaurata-kashi-na-4.html?m=1

CIWON MARA/ SANYIN MATA/TOILET INFECTION

Karanta bayanin ciwon sanyin
(Latsa LINK a kasa domin karantawa)
http://madinahislamicmed.blogspot.com.ng/2016/01/matsalolin-ciwon-sanyin-mata-sanyin_17.html?m=1

TAIMAKO GA MA'AURATA

Hakika mutane sun sani cewa munyi fice wajen magance matsalolin jima'i tsakanin ma'aurata da kuma inganta jin dadin aure ta wannan fuska , cikin ikon Allah. Domin neman taimako na musamman ga MIJI da MATA , ANGO ko AMARYA , ZAWARA da BAZAWARI masu jiran rana, musamman masu wadannan matsalolin ko don inganta Lafiya:

~ Ciwon-sanyi
~ Zafi wajen jima'i
~ Rashin karfin mazakuta
~ Kankancewar zakari
~ Saurin inzali/kawowa
~ Karancin maniyyi ko rashin kaurinsa
~ Fitar maniyyi haka nan ba tare da mutum yayi wani abu ba ko jin dadi
~ Rashin sha'awa ko rashin son jima'i ga mace ko namiji
~ Budewar gaban mace,
~ Daukewar ni'ima ga mace/kumburin gaba
~ Neman girman mama
~ Rage kiba
~ Rashin jin dadin Jima'i ga mace ko namiji
~ Warin gaban mace
~ Rashin haifuwa
~ Tsanki
 ~ Matsalalolin al'ada da sauransu,

Sai a kira +234808 402 8794 domin neman taimako na musamman daga cibiyar mu ta kiwon lafiya ta Musulunci mai albarka da mutane.
Shafin mu na yanar gizo : www.madinahislamicmed.blogspot.com
E-mail: madinahislamicmed@gmail.com

Adreshin mu: Sai a ziyarci cibiyar kai tsaye dake Katsina, Jihar Katsina, Najeriya. Adreshin mu: Titin Muhammad Dikko, Katsina, daura da makarantar sikandire ta K.C.K. (Katsina College Katsina), Shago na 5  , cikin shagunan Majalissar Malamai ta Kasa , reshin Jihar Katsina, Najeriya.

LIKE our Facebook page domin samun bayanan lafiya irin wadannan masu muhimmanci:

https://m.facebook.com/MadinahIslamicMedicine/?ref=m_notif&notif_t=like

MADINAH ISLAMIC MEDICINE  (herbal centre based in Katsina, Katsina State of Nigeria)
(Alternative Medicine - Herbalism: Arab Traditional Medicine, Ayurvedic Medicine, Chinese Traditional Medicine, Traditional African Medicine [especially Hausa Traditional Medicine]).

Enjoy the healing and rejuvenating power of our unique natural / herbal preparations (herbal medicines/supplements, safe and highly effective) for:

FEMALE SEXUAL HEALTH/ENHANCEMENT
~ Breast Enlargement
~ Slimming
~ Boosting female libido/approdisiacs(sex appetizers) & vaginal rejuvenation herbs
~ Dry vaginal remedies/vaginal lubrication, health, tightening and other female enhancement herbs
~ Vaginities/vaginal infections
~  Sexually Transmitted Diseases (STDs)
~ Infertility & menstrual problems
~ Skincare/haircare
~ Exorcism herbs etc.

MALE SEXUAL HEALTH/ ENHANCEMENT
~ Erectile dysfunction (ED)
~ Premature ejaculation/erection enhancers/energizers
~ Low sperm count/volume/motility
~ Penis shrinkage
~ Male low libido / sex appetizers
~ Male Infertility
~ Spermatorrhea (involuntary release of semen without orgasm)
 Sexually Transmitted Diseases (STDs) etc.

Visit our herbal centre in Katsina, Katsina State:
ADDRESS: Muhammad Dikko Road, Opposite K.C.K. (Katsina College Katsina) - Council of Ulama shop no.5, Katsina, Katsina State of Nigeria.

MOBILE: +2348084028794 (call now to order)
EMAIL: madinahislamicmed@gmail.com
BLOG: www.madinahislamicmed.blogspot.com

LIKE our Facebook page LIKE our Facebook :

https://m.facebook.com/MadinahIslamicMedicine/?ref=m_notif&notif_t=like

Saturday, 26 August 2017

TAIMAKO GA MA'AURATA

TAIMAKO GA MA'AURATA

Hakika mutane sun sani cewa munyi fice wajen magance matsalolin jima'i tsakanin ma'aurata da kuma inganta jin dadin aure ta wannan fuska , cikin ikon Allah. Domin neman taimako na musamman ga MIJI da MATA , ANGO ko AMARYA , ZAWARA da BAZAWARI masu jiran rana, musamman masu wadannan matsalolin ko don inganta Lafiya:

~ Ciwon-sanyi
~ Zafi wajen jima'i
~ Rashin karfin mazakuta
~ Kankancewar zakari
~ Saurin inzali/kawowa
~ Karancin maniyyi ko rashin kaurinsa
~ Fitar maniyyi haka nan ba tare da mutum yayi wani abu ba ko jin dadi
~ Rashin sha'awa ko rashin son jima'i ga mace ko namiji
~ Budewar gaban mace,
~ Daukewar ni'ima ga mace/kumburin gaba
~ Neman girman mama
~ Rage kiba
~ Rashin jin dadin Jima'i ga mace ko namiji
~ Warin gaban mace
~ Rashin haifuwa
~ Tsanki
 ~ Matsalalolin al'ada da sauransu,

Sai a kira +234808 402 8794 domin neman taimako na musamman daga cibiyar mu ta kiwon lafiya ta Musulunci mai albarka da mutane.
E-mail: madinahislamicmed@gmail.com

Adreshin mu: Sai a ziyarci cibiyar kai tsaye dake Katsina, Jihar Katsina, Najeriya. Adreshin mu: Titin Muhammad Dikko, Katsina, daura da makarantar sikandire ta K.C.K. (Katsina College Katsina), Shago na 5  , cikin shagunan Majalissar Malamai ta Kasa , reshin Jihar Katsina, Najeriya.
MADINAH ISLAMIC MEDICINE  (A herbal point based in Katsina State)
CAC: KT2557  Alternative Medical Practice, General Merchandise/Trading , General Contracts

Herbalism/herbal consultation service: We specialized in Arab Traditional Medicine, Ayurvedic Medicine, Chinese Traditional Medicine, Traditional African Medicine [especially Hausa Traditional Medicine].

FEMALE SEXUAL HEALTH/ENHANCEMENT /HERBAL PRODUCTS
~ Breast/hips enlargement
~ Slimming
~ Boosting female libido/approdisiacs(sex appetizers) & vaginal rejuvenation herbs
~ Dry vaginal remedies/vaginal lubrication, health, tightening and other female enhancement herbs
~ Vaginities/vaginal infections (toilet infection)
~  Sexually Transmitted Diseases (STDs)
~ Infertility & menstrual problems
~ Skincare/haircare
~ Exorcism herbs etc.

MALE SEXUAL HEALTH/ ENHANCEMENT
~ Side effects/symptoms of overmasturbation (excessive masturbation): loss of memory(forgetfulness), low libido, penis shrinkage, weak erection, premature ejaculation, low sperm count, hormonal imbalance, weight loss, penis curvature, sunken eyes, low immunity, back pain, heart palpitation, poor vision, frequent headache etc. We treat these problems which are related to excessive masturbation with the healing power of unique herbs with grace of God- herbal therapy. Other problems we treat:
~ Erectile dysfunction (ED)
~ Premature ejaculation/erection enhancers/energizers
~ Low sperm count/volume/motility
~ Penis shrinkage
~ Male low libido / sex appetizers
~ Male Infertility
~ Spermatorrhea (involuntary release of semen without orgasm)
 Sexually Transmitted Diseases (STDs) etc.

Visit our herbal centre / office in Katsina, or call to order our herbal medicines from anywhere in Nigeria and beyond. Contact us to enjoy the healing power of our unique natural / herbal preparations (herbal medicines/supplements, safe and highly effective).


ADDRESS1:. No. 5 Muhammad Dikko Road, Opposite K.C.K. (Katsina College Katsina), Katsina, Katsina State of Nigeria.

ADDRESS2: Branch Office - No. 34 Sabuwar Unguwa, Dandagoro Area , Katsina , Katsina State.
MOBILE: +2348084028794 (call now to order herbal products)

EMAIL:
madinahislamicmed@gmail.com
BLOG: www.madinahislamicmed.blogspot.com

LIKE our Facebook page:

https://m.facebook.com/MadinahIslamicMedicine/?ref=m_notif&notif_t=like

Wednesday, 23 August 2017

ƙanƙancewar Zakari (Penile shrinkage)

Kankancewar zakari na nufin raguwar girman al'aura, wato wani yanayi ne da al'aurar namiji baligi ke zama ƙarama tamkar ta ƙaramin yaro - ta shige ciki ko ta rage tsawo ko kauri a lokacin da take kwance (flaccid state) ko a miƙe (erect state) saɓanin yanda take ada. Wannan yanayi na faruwa ga mutum ne a lokacin da yake manyanta cikin rayuwarsa, a dabi'ance. Hakan na faruwa ne ga mutane  da shekarunsu na haifuwa suka kai 30 zuwa 40. Amma duk da haka akan sami matasa da yawa wanda basu kai ga wadannan shekarun haifuwa ba masu fama da wannan matsalar. Saidai wasu da yawa daga cikin masu bada maganin gargajiyar Hausa na ganin cewar matsalar ƙanƙancewar zakari matsala ce kai tsaye dake da alaƙa da ZAFI ko  SANYIN MARA, suke iƙrari.

Kankancewar zakari dai matsala ce dake cima mazaje tuwo a ƙwarya musamman irin yanda wasu da yawa ke jin kimarsu da alfaharinsu na kasancewarsu maza na fuskantar ƙalubale. Mutane a al'adun duniya da dama na ganin isasshen al'aurar namiji ita ce  abin tunƙaho da fahari ga kowani mutum dake amsa sunansa namiji , kuma itace kimarsa ga 'ya mace. To saidai ƙanƙancewar zakari idan ba yawa tayi ba  ba'a tunanin zata iya haddasa rashin gamsuwar jima'i tsakanin ma'aurata. Akwai dalilai na lafiya da dama da zasu iya bada haske gameda ƙanƙancewar gaba. Wasu dalilai na daban da ka iya haddasa kankancewar zakari ga matasa ko manya sun hada da:

1. Aiki ko tiyatar likita ga al'aura domin cire wani  ƙullutun ciwon daji ko kansa daga al'aura (Prostate tumour/cancer surgery removal). Yana iya haddasa kankancewar gaba bayan aikin.

2. Wata cuta (Peyronie's disease) mai sauya sigar zakari, wato karkacewar zakari sosai da wuya ko zafi wajen yin jima'i. Yin tiyatar likita /ofereshin (surgery) domin maganin matsalar na iya haddasa ƙanƙancewar zakari.

3. Yanayin sanyi (temperature) . Idan sanyi  ya  yawaita fiye da yanda ya dace ga jiki to zakari zai iya noƙewa/ɓoyewa saboda ɗari. Hakan na hana gudanar jini da kyau a cikin al'aura .Samun yanayi mai kyau da gumi  zai iya maganin matsalar.

4. Sanya wandon ciki (under pants) wanda ya tsuke hantsa ko al'aura. Yana sanya karancin gudanar jini cikin al'aura wanda sakamakon hakan zai iya sanya zakari ya takura dalilin jini baya shiga ciki da kyau ta yanda zakar zai cika da jini ya kumboro (ya mike) a lokacin sha'awa ko jima'i. Wato jijiyoyin jinin basa aiki da kyau saboda takura.

5. Yawan fitar maniyyi sakamakon yawan yin istimna'i/ wasa da al'aura amma ba jima'i ba. Da zaran maniyyi ya fita daga jikin mutum jakar marainansa data sauko ƙasa kafin fitar maniyyi zata nade ta koma sama ta tsuke marainan biyu bayan fitar maniyyin. A lokacin faruwar haka kuma zakari na shigewa shima ya koma gareji tare da marainan.

6. ƙiba: masu ƙiba da yawa na fama da ƙanƙancewar gaba domin kuwa tana sanya zakari ya shige ciki. Don haka, motsa jiki da rage ƙiba ta hanyar daya dace zaya iya maganin matsalar.
Barin shan taba ko giya, cin abinci mai kyau, motsa jiki, magani da shan wadataccen ruwa yanda  ya dace zai taimaka sosai wajen magance matsalar ƙanƙancewar gaba. Allah Ya taimaka.

Domin neman ƙarin bayani ko taimako sai a kira +2348084028794  ko email madinahislamicmed@gmail.com

Thursday, 17 August 2017

Copyrighted.com Registered & Protected  0YXI-CS2X-EBNW-MCG2

Satar Fasaha!

Salam. Fatan alheri da koshin lafiya ga customers namu da masoyan wannan shafi. Muna godiya ga Allah Madaukakin Sarki da nasarar da yake bamu da kuma hadin kanku da soyayyarku da kuke nuna mana.

Gargagadi: Hakika muna sane da cewa wasu mutane mararsa kishi na daukar bayanan mu a wannan shafi da muka wallafa kuma suna amfani da wallafe-wallafen a dandalinsu  tamkar sune suka rubuta bayanan  ba tare da nuna inda suka sami bayanan ba- wato suna satar fasaha. Wani lokacin ma sai suyi ma wani yankin rubutun  sauye-sauye ko qari a cikin bayanan da suka cirato kai tsaye daga gare mu.

Don haka , muna gargagadi ga masu wannan aiki, suji tsoron Allah. Bamu yarda ba wani ko wata ya canja wani abu ko yayi amfani da rubuce-rubucen mu ba tare da izinin mu ba face sai an ayyana ma6u66ugar bayanan, wato Madinah Islamic Medicine. Don haka muna kira ga masoyan mu dasu su taimaka mana da bamu rahotan duk inda suka ga anyi amfani da rubutun mu ba akan ka'ida ba domin mu aika da sakon korafi na COPYRIGHT a yanar gizo. Idan an lura dukkanin rubutun mu nada rana da kwanan wata. Don haka idan kaga rubutu ko wallafe-wallafen mu a wani blog  ko website da suka sata bayan mun wallafa kuma ba abisa ka'ida ko suna ikirarin nasu ne to sai ataimaka a kira mu ko a turo mana sakon email. Da fatan za'a taimaka.

Email: madinahislamicmed@gmail.com
Nambar waya: +234808 402 8794

Mun gode kwarai Allah Ya barmu tare.

Wednesday, 16 August 2017

Amfanin Shan Madarar Raƙumi ga Lafiyar Ɗan-adam


Madarar raƙumi ko nonon raƙumi (camel milk) sinadari ce mai matukar amfani ga lafiyar ɗan adam. Tsawon lokaci mai yawa Larabawa masu yawon kiwo da Buzaye a cikin sararin sahara sun kasance suna amfani da wannan madara wacce ake tatsowa daga hantsar dabbar taguwa a matsayin abinci abar sha da kuma magani a cikin tafiyarsu  mai nisa cikin sahara domin rayuwa.

Taguwa dabba ce mai asali da ban mamaki dake rayuwa musamman a yankunan sahara masu tsananin zafi a duniya. Tsawon lokaci mai yawa , tarihi ya nuna cewa mutanen sahara na amfani da madara ko fitsarin wannan dabba wajen magance matsalolin lafiya na daban-daban. Allah (S.W.A.) Yasa albarka da waraka a cikin madarar wannan dabba wacce bata da abinci daya wuce itacen ƙaya da ruwa a dajin sahara. Itacen ƙaya da wannan dabba ke ci  anyi imani cewa mafi yawansu na ɗauke da magunguna wanda za'a iya samun amfaninsu cikin madarar idan mutum ya sha ta. Bugu da ƙari, ana sarrafa madarar domin samar da wani abinci dake ake cema CUKU ko CUKWI (Camel cheese) .Shin ko ka taba ganin harshen raƙumi a mahauta bayan an yanka/soke shi? Da yawa zaka ga ƙaya mai tsawo cikin harshen duk ta soke/lume cikin tsokar harshen  saboda yawan cin ƙayarsa.

Binciken kimiyya na  nuna cewa saboda muhimmancin madarar raƙumi  itace mafi kusa a cikin nau'in madarar dabbobi dake da yanayin amfani kusan irin na madarar ɗan adam, wato madarar da uwa ke bawa jinjirinta mai roman sinadarai masu yawa da inganta lafiyarsa. Saboda haka ne da yawa ake bawa jinjirin mutum madarar raƙumi wanda baya samun isasshen abinci mai lafiya a wasu al'adun. Abin nufi anan shine, madarar raƙumi ta banbanta da sauran nau'in madarar dabbobi kamar irinsu sanuwa, tumkiya da akuya kasancewar ta zarce su amfani a cikin jikin ɗan adam mai amfani da ita (mai shan madarar). Madarar rakumi na dauke da sinadari mai ƙara yawan jini da hana rashin  jinin (iron) mai yawa wanda   yafi yawan wanda ke akwai cikin madarar sanuwa har linki 10 da kuma sinadari mai ƙarfafa garkuwar jiki (vitamin c) wanda shima yafi yawan wanda madarar sanuwa ke ɗauke dashi sau 3. Madarar raƙumi na ƙunshe da sinadari mai gina-jiki (protein) mai yawa tare da wasu sinadarai masu bayarda da kariya daga cututtuka. Irin waɗannan sinadarai ana samun su kaɗan ne cikin madarar sanuwa idan aka kwatanta da ta raƙumi.
Amfanin madarar raƙumi a taƙaice - wasu daga cikin manya-manyan amfaninta, sune:

(Health benefits of camel milk)
1. Tana taimakawa masu ciwon-suga (diabetes). Madarar raƙumi na ƙunshe da sinadaran inganta lafiya da kuma sinadarin INSULIN mai yawa . Masu ciwon-suga zasu more amfaninta ta sosai.

2. Tana taimakawa  masu rashin lafiyar OSTIZAM (AUSTISM), wanda wata matsalar ƙwalwa ce dake bayyana tun farkon yarintar mutum wacce ke hana marar lafiyar yin tarayya mai kyau da mutane - wato haɗuwa da mutane da yin abokanai da kuma sanya sa wuyar magana, tunani ko sadarwa tsananin sa da sauran mutane. Madarar raƙumi nada wasu sinadarai masu sanya mararsa lafiyar su sami sauƙi sosai koma waraka daga wannan rashin lafiyar.

3.Tana taimakawa masu ALAJI (ALLERGY) , wato wani yanayi da garkuwar jikin mutum ke nuna bata son wani abu , musamman abinda bai cika cutar da lafiya ba  ko kuma baya cutar da mutane da dama amma sai ya cutar da mutum , yasa garkuwar jikinsa tayi tutsu bata son abin (allergic reaction). Misali, kamar wani nau'in abinci da baya cutar da lafiya amma idan mutum yaci sai yasa shi rashin lafiya, ko ruwan damuna kawai ya sanya ƙuraje su fito ma mutum ga jiki ko ƙaiƙayi, ko warin wata dabba yasa mutum atishawa ko mura, ko kuma taɓa wata dabba ko wani abu ya sanya rashin lafiya da sauransu. Shan madarar raƙumi na magance dangin waɗannan matsaloli abisa wasu bincike-bincike da aka gudanar.

4. ƙarfafa garkuwar jiki. Sinadarai masu ƙarfafa halittun garkuwar jiki dake cikin madarar raƙumi sun isa suyi yaƙi da cututtuka masu kai farmaki a cikin jikin ɗan-adam su halaka cututtukan.

5. Gina jiki da ƙoshin lafiya. Yawan sinadarai masu gina-jiki (proteins) dake cikin madarar na taimakawa wajen girman jiki da cigabansa.

6. Inganta lafiyar zuciya. Madarar nada sinadarai (FATTY ACIDS) wanda zasu iya daidaita sinadarin kolestarol ( CHOLESTEROL) dake cikin jini. Yawan kolestarol a jini nada haɗari, sinadari ne mai danƙo wanda zai iya toshe ƙofofin jinin zuciya (fayif) da take harba jini dasu zuwa sassan jiki (arteries). Idan hakan ya faru zai iya yin dameji ga zuciya. Madarar zata iya rage haɗarin faruwar damejin zuciya, mutuwar sashen jiki da kuma rage hawan jini , da sauran su.


Sunday, 6 November 2016

Wasa-da-al'aura /Wasa-da-gaba da Illarsa

WASA DA-AL'AURA / WASA DA GABA DA ILLOLINSA GA LAFIYA

Wasa-da-al'aura ko wasa da gaba (Istimna'i [masturbation]) na nufin yin amfani da hannu, yatsa ko wani abu domin biyan bukatar jima'i ga mutum da kansa da tunanin saduwa da wata mace ko wani namiji , ga mace. Ana kiran wannan dabi'a "zinar hannu".Wasa-da-al'aura ko wasa da gaba dabi'a ce da take  faruwa da yaduwa cikin mutane da dama - yara matasa, da manya musamman cikin  matasa mararsa aure ko wanda aurensu ya mutu,  koma rashin gamsuwar aure. Wannan dabi'a ta zamo ruwan dare kuma abin 'kyama saboda wasu dalilai, wato dalilan  addini, na al'adu, da  kuma na lafiya. Dalilan lafiya da zamu yi magana akansu, suna magana ne game da yawan yin istimina'i da illarsa ga mai yawan yi wanda ya zama dabi'arsa koda yaushe (An addict person who overmasturbates ). Bincike-binciken wasu masana kimiyya da muka tattaro game da yawan wasa-da-al'aura (over-masturbation), na nuna cewa YAWAN WASA-DA -AL'AURA (excessive masturbation or over-masturbation) nada illololi ga lafiya. Duk da yake dai masana sunyi saɓani akan mas'alar istimna'i, inda wasu ke ganin yana da illa wasu kuma basa ganin haka saima kishiyar haka, to sai dai babu rikici akan cewa yawan yin istimna'i  nada illa ga lafiya. Yana  iya haddasa wadannan matsalolin idan ya zama halin mutum baya jin daɗi sai ya aikata (addiction):

Yawan mantuwa, rage hazaqar kwalwa, kankancewar zakari da maraina, saurin kawowa ko rashin karfin mazakuta. Sauran matsalolin dazai iya haddasawa , sun hada da:  ramar jiki ko 'karancin sha'awa, karancin maniyyi ko tsinkewar maniyyi da raguwar ingancinsa (wanda na iya haddasa rashin haifuwa) , raunin jiki, raunin garkuwar jiki, jin ciwon kai akai-akai, ciwon baya, fitar maniyyi daga zakari hakanan ba tare da mutum yayi niyya ba - ba tare da yayi istimna'i ba ko yayi jima'i, haka nan kawai. 
Wasu illololin da zasu iya faruwa saboda istimna'i: bushewar fatar kan zakari ko illa ga fatar saboda gugar fatar, karkacewar zakari (penis curvature) ko sauya masa sigarsa ta asali, bugawar zuciya da sauri, zubar gashi, kurajen fuska.

ILLAR ISTIMNA'I GA MACE

Mace zata iya samun wasu daga cikin matsalolin da mu kayi bayani a sama. Wasu matsalolin daka iya shafar mace sune: Rashin rike fitsari da kyau (ga mace) ko 
Yawan zuwa fitsari saboda saka wani abu cikin farji lokacin istimna'i,  wuyar kawowa ga mace wajen jima'i (dalilin  koyama jikinta  da sai an taɓa wani sashen farji don ta kawo, wanda mai yiwuwa ne zakari baya taɓa wurin lokacin  saduwa - a zahirin jima'i. Don haka istimna'i yana sa rashin gamsuwar jima'i ga mace - mijinta zai sha wahala wajen gamsar da ita. Jikinta ya riga ya koya, tayima kanta horo.  Dalilin haka, mace zata  ji dadin istimna'i fiye da jima'i , hakan kuma zai zamo mata matsala idan tayi aure.  Zata ringa tunanin mijinta baya iya gamsar da ita ko mazaje data aura, saboda sabon da tayi da koyama jikinta hanyar gamsar da kanta fiye da hanyar da ta dace, wato jima'i a cikin sunnar aure.  Ta canza dabi'ar ta. Da yawa zaka samu cewa  mata masu yawan istimna'i basu jin daɗin jima'i  sai istimna'i, koma basu gamsuwa sai sunyi istimna'i a bandaki bayan saduwa da mazajen aurensu. Wannan zai iya kawo babbar matsala a cikin aure. Bugu da kari, dadilan rashin gamsuwar mace wajen saduwa da mijinta suna da yawa. Don haka, bazamu iya cewa ba yin istimna'i kafin aure shine dalilin dake hana gamsuwa kadai ba.  Akwai wasu dalilan na daban, wasu matsalolin nada alaka da bangaren mazajen.

Mutumin da matsalar yawan wasa-da-al'aura ta zama dabi'arsa koda yaushe (addict) zaya iya maganin matsalar. Idan har yazama dabi'ar mutum baya jin dadin rayuwarsa sai yayi istimna'i (sau 2, 3, 4 ko fiye da haka a kowace rana) [addiction] toh zai iya kawo sauye-sauye (canje-canje) ga jikin mutum wanda lafiya bata maraba dasu ( such as hormonal imbalance), saboda yawan zubda sinadaran jikin mutum wajen inzali fiye dabi'ar jima'i ta gaskiya da sauyin yanayin jiki sakamakon yawan hakan . Yana da hadari ga lafiya yanda wasu matasa suka maida wannan dabi'arsu ta koda yaushe, a bandaki, a daki, a waje, ko a wurinda dama ba'a tsammani suna istimna'i.
Mutumin da matsalar yawan wasa-da-al'aura ta zama dabi'arsa koda yaushe (addict) zaya iya maganin matsalar. Idan har yazama dabi'ar mutum baya jin dadin rayuwarsa sai yayi istimna'i (sau 2, 3, 4 ko fiye da haka a kowace rana) [addiction] toh zai iya kawo sauye-sauye (canje-canje) ga jikin mutum wanda lafiya bata maraba dasu ( such as hormonal imbalance), saboda yawan zubda sinadaran jikin mutum wajen inzali fiye dabi'ar jima'i ta gaskiya da sauyin yanayin jiki sakamakon yawan hakan . Yana da hadari ga lafiya yanda wasu matasa suka maida wannan dabi'arsu ta koda yaushe, a bandaki, a daki, a waje, ko a wurinda dama ba'a tsammani suna istimna'i. Yawan Istimna'i mummunar dabi'a ce. Yana da muhimmanci ga masu yawan sha'awa suyi aure , idan babu halin yin auren toh sai su lazimci  yin azumi kamar yanda addinin Musulunci ya koyar. Haka kuma, mutum zai iya dinga cin abinci wanda aka sarrafa da WAKEN- SUYA (soya bean) domin bincike ya nuna cewa  yana rage sha'awa. Za'a iya kuma yawaita amfani da NA'A-NA'A (pepper mint/mint) , na'a-na'a nada amfani ga lafiya sosai, toh amma sinadarin minti (menthol) da take dashi yana dakushe sha'awa idan yayi yawa. Don haka, a nemi bayanan Malaman Sunnah akan wannan mas'ala, don karin bayani.
~~~
Bugu da kari, mutum mai yawan sha'awa ya rage yawan zama cikin daki cikin kadaici yana tunane-tunane. Mutum ya maida kansa kullum BUSY da karatun Al-Qur'ani da kuma wani aiki, musamman idan yaji sha'awa na tsunkulin / muntsulin sa. Idan kuma mutum yasan yana kallace-kallacen haramun kamar fina-finan batsa, hotunan batsa (musamman a yanar gizo) ko kuma mata (masu kallon maza) akan hanya toh aji tsoron Allah a daina, domin kuwa wadannan na daga cikin manyan-manyan  masifun  dake jefa matasa cikin wannan hali.
~~~
Idan har daya ko fiye daya daga cikin wadancan alamomin illar  yawan wasa- da-gaba sun bayyana a gareka, toh ya zama dole idan kana  son lafiyarka  ko lafiyarki ki daina  kuma a nemi magani domin a tsiratar da  lafiya, ta dawo yanda take. Idan ba haka ba, zai iya shafar illahirin  lafiya, wani lokacin ma sai a dade ba'a gane abinda ke  damun mutum  ba. Wannan yana faruwa da yawa ga matasa, kuma muna ganin irin wadannan " cases" barkatai.  Haka kuma muna samun rahotanni da yawa sosai akan wannan matsala. Abin takaici shine, mutum baya neman taimako ko magani da wuri sai wai  anyi masa baiko ko kuma bikinsa saura wata 1 ko 2. Idan har kana da wannan matsala ba abin kunya bane neman magani, kada ka zauna a cikin matsala har sai  ta girma sa'annan ka nemi taimako a lokacinda  kunyar ta riga ta cutar dakai. .Muna bada da taimako (herbal remedy) da shawarwari,  musamman ga masu wannan matsala. Kuma babu kokwanto ana samun lafiya cikin yardar Allah. Haka kuma mutum zai iya zuwa asibiti yaga likita domin neman warwarar wannan matsala. Allah ya taimaka.
~~~
Domin neman karin bayani/Neman magani
Sai azo Office branch namu mai address kamar haka:
No. 34 Sabuwar Unguwa Dandagoro, Katsina, Jihar Katsina.
Kira: +2348084028794 (WhatsApp number)
E-mail: madinahislamicmed@gmail.com


MADINAH ISLAMIC MEDICINE
(based in Katsina,  Katsina State of Nigeria ) provides effective and affordable herbal products (alternative medical practice, trading/ merchandise and general contracts):

Arab-Islamic medicine, Ayuvedic medicine (Indian traditional medicines), Chinese traditional  medicines, traditional African herbal medicines, etc.

We have modern herbal products for effective treatment (very long-time control of hypertension and diabetes) of high blood pressure, diabetes, sickle cell anaemia. Fight high cholesterol level in your blood, fibroid, ovarian cysts, cancer, vaginal infections (vaginitis), arthritis, rheumatism, gout, ulcer with unique herbal products. You really need our sexual enhancement products: approdisiac,  male and female  enhancement product ,  herbs for increasing sperm count, increasing sexual vitality and fertility, fighting erectile dysfunction, increasing libido, fighting premature ejaculation, memory enhancement, anxiety, depression, skincare and haircare  products etc.
Our products work wonders with grace of God , and we are known for that, we have lots of testimonies. And that's what plucks us from obscurity.
Visit or contact us , let us know your problems , get our herbal products from anywhere in Nigeria , especially in the north  or visit us in Katsina, Katsina State of Nigeria.

For more info, call +2348084028794 or email us @ madinahislamicmed@gmail.com

Saturday, 5 November 2016

Amfanin Lemongrass ga Lafiya (Ciyawa-mai-kamshin-lemu)

Amfanin Lemongrass ga Lafiya (Ciyawa-mai-kamshin-lemu)

Lemongrass (Cymbopogon citratus) shuka ce mai dadin kamshi, wato wata irin ciyawace doguwa mai launin kore da kamshin lemun-zaki. Duk da yake dai bata da alaka da lemun-zaki, kamshin ciyawar mai karfi da dandano yayi kama dana lemun-zaki (amma bata da zaki). Ana samun ciyawar a kasashe masu yanayin zafi ko yanayin dumi. Anfi yawan amfani da ita a kasashen Asiya, Afurka da Australia . Haka kuma, anfi yawan amfani da wannan ciyawa a kasashen Asiya wajen girki. A kasar Indiya kuwa akanyi amfani da ita a matsayin maganin gargajiya (herb). Ana amfani da busassar ciyawar ko danyarta domin amfani na daban-daban. Kuma anfi amfani da ita wajen hada shayi , miya ko kori (curry) domin ta zamo hadin kayan kamshin girki. Ana samun manta (lemongrass oil) a kasuwa wanda shima ake amfani dashi na daban-daban.

Amfaninta:

Mai yiwuwa ne kana da wannan shuka a gida ko a lambunka , koma kana amfani da ita, to amma baka san ainahin amfaninta taba ga lafiya, kawai dai ka dauketa shuka ce domin k'awata gida, ko filebo maisa kamshi a kofin shayin ka a lokacinda kake kurɓawa. To ka bude idanunka, domin kuwa wannan ciyawa amfaninta ya wuce na adon gida kadai ko kamshin shayinka da kake jin dadin sha saboda dandano da kamshin da take baka a lokacin da kayi amfani da ita. Ciyawar Lemongrass nada ado da zata iya yima lafiyarka domin inganta ta. Wasu daga cikin amfanin wannan ciyawa mai albarka sun hada da:

1. Kariya daga ciwon-daji/kansa (Anti-cancer). Shukar lemongrass nada sinadari mai kamshi na "citral", wanda binciken kimiyya ya nuna cewa yana kashe kwayoyin halitta da ciwon kansa ya harba a jiki (cancer cells). Haka kuma yana inganta lafiyar kwayoyin halittar jiki gaba daya (improving cellular health).

2. Karin-jini da hana rashin-jini (Anaemia). Lemongrass nada sinadarin "iron" mai yawa, wato sinadari maisa karin-jini domin cikakkiyar lafiya da kuma hana wasu matsalolin rashin jini.

3. Rage hawan-jini (Reducing high blood pressure). Yawan sinadarin "potessium" a cikin lemongrass, sinadarin mai inganta lafiyar zuciya, koda da sauran sassan jiki, na taimakawa wajen hana hawan-jini, cututtukan zuciya, mutuwar sashen jiki, ciwo kansa, matsalolin rashin narkewar abinci da rashin haihuwa, cikin yardar Allah.

4. Kariya da hana girman kananan halittu masu haddasa cututtuka a jiki (Anti-septic) da kuma hana kumburi, wuri yayi ja, da radadin ciwo a jiki (Anti-imflammatory), musamman taimako ce ga masu ciwon gabobi da sassan jiki da sauransu (gout, arthritis, etc).

5.Yaki da cututtukan bakteriya dana fangas (Anti-bacterial and anti-fungal). Don haka, tana maganin zazzabin cizon-sauro da taifot (Malaria and typhoid) [yi shayi] , da sauransu. Haka kuma, tana maganin cin-ruwa na yatsun kafa da makero [yi amfani da manta] da sauransu ( athlete's foot, ringworm, etc).

6. Maganin mura, zubar hanci da hawaye, kaikayin ido, atishawa, toshewar hanci (Cold,flue and hay fever).

7. Tace duk wani abu mai guba ga jiki , musamman na abinci, ko wani abu mai cutarwa da fitar dasu daga jiki (Detoxifying). Tana tsaftace hanta, koda, mafitsara da sauransu.

8. Inganta bacci / yakar da rashin bacci (Fighting insomnia). lemongrass nada tasiri wajen kwantar da hankali da fada da rashin bacci domin samun cikakkiyar lafiya.

9. Taimako ga masu ciwon-suga (Diabetes). Tana rage yawan suga cikin jini, tsarkake saifa da inganta aikinta.

10. Inganta kwalwa (Improving nervous system). Lemongrass na taimakawa kwalwa wajen maida hankali don lakantar karatu, rike karatun da kuma taimakawa wajen sarrafa karatun/ilimi. Sinadarin "magnesium", "phosphorus" da "folate" da ake samu a cikin ciyawar nada tasirin kyautata lafiyar kwalwa.

11. Rage kiba (Weight loss). Shan lemongrass musamman a shayi na narkarda kitshe. Tana sanya yin fitsari akai-akai a lokacinda take fitar da duk wani abu mai yawa da jiki baya bukata wanda zai iya cutar da lafiya.

Da sauransu.

Medical Disclaimer: Wanda ya rubuta wannan bayanai ba likita bane, mai bincike ne kawai akan magungunan gargajiya, masani akan abinda ya rubuta sakamakon bincike daya gabata. Wannan bayanin amfanin ciyawar lemongrass da duk kanin bayanan magunguna daya wallafa a wannan shafin yanar gizo, baya nufin masu matsalolin lafiya zasu iya barin yin amfani da magungunan da aka basu a asibiti ba domin su lazimci yin amfani da maganin gargajiya, a maimakon magungunan. A nemi shawarwarin likita da masana ilimin maganin gargajiya akan yanda za'a iya amfani da magungunan da kuma sanin wanda zai iya amfani da ciyawar da wanda bazai iya amfani da ita ba wasu lokuttan.


Domin neman taimako ko siyan magungunan mu masu inganci sosai da karin bayani , sai a kira : +2347011591392 ko email : madinahislamicmed@gmail.com

Sunday, 17 January 2016

Matsalolin Ciwon Sanyin-Mata /Sanyin Gaba [Vaginitis/vaginal infections/ toilet infections] da Rigakafi

SANYI kalma ce mai fadin ma'ana da Malam Bahaushe ke yin amfani da ita domin yin kokarin bayanan wasu matsalolin lafiya na daban-daban , misali , ciwon-sanyin jiki [rheumatism], ciwon sanyin mura [cold and flu] da ciwon sanyin-mara ko ciwon sanyin-mata [vaginitis] ko ciwon sanyin maza-da-mata da ake dauka ta hanyar jima'i [STDs/STIs like chlamydia, gonorrhea, syphilis, genital herpes, HPV etc] da sauransu. Saidai Malam Bahaushe baya kiran ciwon sida/kanjamau [HIV/AIDS] da ciwon sanyin-mara duk da cewa kau anfi yada cutar ta jima'i.

Za muyi bayani akan ciwon sanyin-mata ne kadai [Vaginitis]. Matsalolin ciwon sanyin-mata [vaginitis/vaginal infections or toilet infections] wasu cututuka ne ko matsaloli dake addabar gaban mace, wato cututtuka masu sanya kaikayin farji, ko radadin ciwo, kumburin gaba ko warin gaba , zubar farin ruwa, kurajen farji, zafi wajen yin fitsari ko wajen yin jima'i da sauransu. Ciwon sanyin-wata matsala ce dake faruwa ga mata da dama a cikin wasu lokutta na rayuwarsu. Ana samun wannan cututtuka ko matsaloli sabili da wani sauyin yanayin jiki da mata ke samu wasu lokutta da kuma sabili da wasu kwayoyin halittar 'bacteria' da 'fungus' dake zaune cikin al'aurar mace, haka kuma , mata na iya samun wannan ciwon a lokacin juna-biyu da kuma shayarwa [during pregnancy and breastfeeding] . Har ila yau, za'a iya samun ciwon ta hanyar jima'i [vaginal intercouse] da wasu dalilan ko hanyoyi na daban.

Nau'in ciwukan sanyin-mata suna da yawa, to amma bincike ya nuna cewa ciwon sanyin-mata nau'i uku ne (3) suka fi addabar mata da yawa. Za muyi bayani akansu kadai, a takaice insha Allahu, sune kamar haka: (sunayen su da yaren turanci) 1. 'Yeast infection' 2. 'Bacterial vaginosis' 3. 'Trichomonas'

1. ‘Yeast infection’ ('Candidiasis'). Akwai wasu kwayoyin halittun 'fungas' (masu suna 'candida') sune ke haddasa 'Yeat infection'. Su wadannan halittu wanda kwayar idon mutum baza ta iya ganin suba , saboda kankaantar su saida taimakon madubin likita ne za'a iya ganin su [microscope] . Halittun suna rayuwa a wasu wurare cikin jikin mutum kuma adadinsu baya da yawa . Ana samunsu cikin farji kuma, asali basu cika cutarwa ba.'Candida' suna san wuri mai gumi, lema da rashin iska domin girma da yaduwa. Idan suka samu wannan yanayi da suke so toh za suyi yawa su kuma haddasa ciwon sanyin 'Yeast infection'. Anfi yawan samun irin wannan ciwon sanyi ga mata da yawa , kusan kashi 75 cikin 100 na mata sun taba samun wannan ciwon a cikin wasu lokutta na rayuwarsu. Alamomin cutar sun hada da: zubar farin ruwa mai kauri daga farji, kuraje ko kaikayin farji da kuma labban farji suyi jawur ko cikin farji.

2. ‘Bacterial vaginosis’ , cuta ce dake shafar farji sabili da girman wasu kwayoyin halittun 'bacteria' masu cutarwa dake cikin farji suna rayuwa. Alamonin cutar sun hada da: zubar ruwa mai 'karnin kifi daga farji, warin sa musamman lokacin jima'i, ko radadin zafi lokacin fitsari, amma babu kaiyayi cikin alamomin. Alamomin cutar kuma na iya 'buya.

3. ‘Trichomoniasis ’ : A cikin cututtukan sanyi da muka yi bayanin su a baya (wato cuta ta 1 da ta 2) , 'Trichomoniasis' ta 3, itace cutar sanyin-mata da ake yadawa ta hanyar jima'i ga maza (STD) fiye da sauran a zahiri, wato mace zata iya harbin mijinta da cutar ko mijin ga matar. Idan ya kasance miji nada wata mata ko yana neman matan waje masu cutar ko kuma macen ta taba saduwa da wani mutum mai cutar daya samo cutar daga wata mace, to akwai yiwuwar ma'aurata su samu cutar koma mafi hadari HIV da wasu cututtukan jima'i (STDs). Ana kiran 'yar kankanuwar halittar [parasitic organism] dake sanya wannan cuta da suna 'Trichomonas vaginalis'. Mazaje ba kaso suke sanin suna da cutar ba kasancewar alamomin cutar basu cika bayyana ga maza ba. Yawanci sai idan ciwon ya kama matan su suna cikin neman magani suke gano suna da cutar. Idan anyi sa'a alamomin ciwon sun bayyana ga maza, ana iya samun alamomi kamar haka: zubar farin-ruwa kadan, zafi kadan bayan fitsari ko bayan fitar maniyyi. Alamomin cutar ga mata suna iya kama da ciwon sanyi na 1 da na 2 da muka yi bayani a sama, ko kuma: zubar ruwa mai launin kore-da-dorawa - mai kumfa da wari, zafi wajen yin fitsari, rashin jin dadi wajen jima'i. Wannan cuta tana da hadari ga mace mai juna-biyu ga abunda ke cikinta, musamman idan ba'a nemi magani ba.

Matakin da Zaki Dauka Idan Har Kinga Alamomin Ciwon-Sanyi

Idan har kina da daya ko biyu daga cikin wadannan alamomin ciwon kai koma fiye da haka, mataki na farko da zaki dauka shine, ki garzaya zuwa asibiti ko wata cibiyar lafiya domin neman taimako. A asibiti ne idan anga kwararriyar likita, musamman 'gynaecologists' wanda suka shahara akan fagen matsalolin mata , za'a duba matsalar, sa'annan ayi bincike 'lab test' ko da 'microscope' asan abunda ke damun ki a kuma baki maganin daya dace da shawarwari. Haka kuma , idan anyi binciken kuma an tabbatar da irin ciwon sanyin dake damun marar lafiyar toh za'a iya zuwa wannan cibiya tamu mai albarka ta Madinah Islamic Medicine Katsina domin neman magani/waraka da yardar Allah.

Wasu Halayen Da Zasu Iya Taimakawa Wajen Samun Ciwon Sanyi da Rigakafin su:

> Wajen Tsaftace Gaba [ Vaginal Douching] A cikin farji akwai wasu kwayoyin halittar 'bacteria' marar sa cutarwa kuma masu amfani (wato 'Normal flora'). Su 'normal flora' suna taimakawa wajen bada kariya ga farji daga wasu nau'in 'bacteria' na daban masu cutarwa (masu suna 'Bacterial pathogens'). Garin neman kiba akan nemo rama, wasu mata kanyi amfani da wasu hanyoyi domin tsaftace farji, kamar ta hanyar yin amfani da sabullan magani, harba magani cikin gaba, ruwan dumi da gishiri ko dettol domin wanke farji don tsaftacewa ko rigakafi daga 'bacteria' da zata iya cutarwa. Wadannan abubuwa da ake amfani dasu don rigakafi na kashe 'bacteria' masu amfani [the normal flora] cikin farji, hakan zaisa 'bacteria' masu cutarwa su samu damar shigowa cikin farji su cutar da lafiya da ciwon-sanyi, sabili da babu 'bacteria' mai bada kariya dake hana su shiga ko 'barna. Don haka , idan har lafiyar ki lau kuma kina son tsaftace gabanki toh sai ayi amfani da ruwa , musamman lokacin wanka a tsaftace gaba. Ki guji fesa turare ko wanke gaba da sabili mai kamshi. Idan har lafiyar ki lau kada kiyi amfani da wani abu idan ba ruwa ba. Ki sani cewa farji yana tsaftace kanshi da kanshi a yanayin halittarshi, yana fitar da wani ruwa [secrets fluid] na musamman dake wanke illahirin gaban mace.

> Kayan-sawa na ciki/wandon pant [Under-wears/under-pants] Wasu matan kanyi amfani da wandon pant ko 'skin-tight' kwana da kwanaki ba tare da canzawa ba ko wankewa. Irin wannan halin kazanta na dauda da lema, na bawa cututtuka (Germs) dama su shiga cikin farji su kuma girma cikin 'dan kankanin lokaci har su haddasa ciwon sanyi. Don haka , yana da kyau a canza 'under-wears' wankakku masu tsafta a kowace rana. Idan lokacin zafi ne ko kinyi aiki kuma akwai zufa a jikin ki to sai ki canza wando akalla sau 2 a rana. Kuma yana da kyau ayi amfani da wandon da akayi da auduga [cotton under-wears] domin yana taimakawa wajen tsotse lema da bushewa, sabanin wando da akayi da 'nylon' [nylon under-wear].

> Wajen wanke bayan-gida [Way of cleaning the anus after faeces] Yana daga cikin halayen wasu mata idan sunyi bahaya suna fara wanke dubura sa'annan gabansu, wasu kuma suna hadawa ne duka , wato gabansu da dubura su wanke lokaci daya, wannan ba dabi'a bace ba mai kyau ga mace, domin kuwa idan kika wanke dubura farko sa'annan gabanki ko kika wanke su a lokaci daya toh zaki iya goga ma farjinki wasu cututtuka dake cikin kashi/bayan gida. Don haka , sai a fara wanke farji farko, bayan angama wanke shi da ruwa da kyau to sai a wanke dubura.'Toilet infection' kalma ce da mutane suka kirkira kuma ta samu asali ne daga mummunar dabi'ar wanke dubara tare da farji, wanda wasu ke tunanin shine ke kawo cutar sanyin-mata. Toh saidai dadilan dake kawo cutar sanyin mata suna da yawa kamar dai yanda mu kayi bayani a baya, kuma ita kalmar 'Toilet infection' ba tada muhalli a cikin 'Kamus din likitoci a matsayin sunan cuta. Mutane ne wanda ba ma'aikatan lafiya ba suke amfani da kalmar da nufin 'vaginal infections' ko 'vaginitis' (kalmar da ma'aikatan lafiya suka fi amfani da ita).

> Tsugunni a bandaki [Squatting in toilets] Yin tsugunni a bandakin da mutane da yawa ke amfani dashi nada hadari ga lafiya, musamman bandaki mai dauda da kazanta. Sau da yawa mace zata tsugunna tayi fitsari cikin bandaki sai fitsarinta ya doki kasa yayi tsalle ya fallatso mata ko ya dawo mata tare da wani ruwan dake kwance a kasa ko fitsarin wata macen.Digo daya na fitsarin mai ciwon sanyi zai iya harbar ki da ciwon idan ya fallatso maki ga ga gaba.Don haka, idan zaki yi fitsari kada kiyi inda kowa keyin fitsari a cikin bandaki, ki samu wuri na daban mai tsafta cikin bandakin kuma inda babu ruwa a kwance. Haka kuma kada ki bari gabanki ya taba kasa. Kiyi fitsari a hankali. A yawaita wanke bandaki kullum da dettol ko danginshi 'germicides' masu inganci domin kashe cututtuka.

> Yin amfani da wandon pant na 'kawar ki, yar'uwar ki ko wata mace [Sharing under-wears] Kawar ki, kanwar ki ko wata yar'uwarki mutane ne masu iya kamuwa da cuta. Zai iya kasancewa suna da ciwon-sanyi , don haka idan kina jin cewa kinyarda da ita ko kuma kun zama jini da tsoka toh ki shirya fama da ciwon sanyi da zasu iya harbarki dashi idan kina amfani da wandon su. Koda basu da ciwon , bai kamata ku rinka amfani da pant din junanku ba. Riga kafi yafi magani.

> Rashin kula wajen yin jima'i [Sexual intercourse without care] Yanada matukar muhimmanci ki kiyaye da jin rauni a farji a lokacin saduwa da maigida. Barin gashin gaba ba'a rage shiba da kuma yin jima'i tsawon lokaci ko da karfin tsiya na daga cikin dalilan dake sa mace ta samu rauni a gabanta. Samun rauni ko fashewar fata cikin al'aura na bawa cututtuka kofar shiga jiki su cutar da lafiya da 'infections'.

>Mataki na biyu da zaki iya dauka shine: bayan kin san abunda ke damun ki domin a asibiti an bayyana maki, idan har ya tabbata sanyi ne kuma kin sha magani amma baki samu sauki ba, ko kuma kin samu sauki amma baki warke duka ba yana dawowa, toh zaki iya amfani da wannan taimakon da zamu baki :

Ki samu 'Khal tufah' [Apple cider vinegar] a Islamic Chemist. Ki tafasa ruwa mai yawa yayi zafi, idan yayi 'dumi sai ki samu robar wanka ki juye ruwan ya cika robar, sa'anna ki zuba khal tufah cikin ruwan kimanin adadin kofin shayi [small tea cup] 1 ko 2 cikin robar wankan, sai ki zauna ciki minti 15. Bayan kin tashi daga robar sai ki tsane lemar ruwan dake gabanki da tawul mai kyau ya bushe. Sai ki samu man-kwakwa [coconut oil] da auduga ki goge gabanki, man-kwakwa nada sinadarai masu kashe kwayoyin cuta [ antiviral, antibacterial and antifungal properties] Kiyi amfani da man-kwakwa sau 3 a rana. Za kiyi amfani da Khal tufah kamar yanda mu kayi bayani kullum sau 1 a rana har sai kin samu sauki.
Haka kuma, zaki iya amfani da Tafarnuwa [Garlic]. Ki samu salar tafarnuwa 2 ko 1 ki karkare bawon da ledar ta, kiyi matsi dasu da dare idan zaki kwanta bacci sai da safe ki cire ki yar. Tafarnuwa magani ce mai karfi (kuma 'antibiotic') , itama tana da sinadarai masu kashe cututtuka [antiviral, antibacterial and antifungal properties]. Kuma zaki iya cin tafarnuwa ko amfani da 'capsules' nata, idan zaki iya.
Bugu da kari, zaki iya neman garin Hulba [Fenugreek powder] a Islamic Chemist da zuma (honey) kiyi shayi, ki tasa ruwa ki zuba hulba karamin cokali 1 cikin kofin shayi ki motsa, sai ki sha. Kiyi haka safe da dare, har sai kin samu sauki. Idan mace tana da juna-biyu kada tayi haka sai ta nemi shawarar likitan Islamic Chemist/ likitan asibiti da yasan 'Hulba' ko masani amma babu laifi ga mai shayarwa tayi amfani da hulba, hakan zai kara samar mata da ruwan nono. Masu juna-biyu su guji sha-shayen magunguna ba tare da izinin likita ba. Allah ya taimaka.

Madinah Islamic Medicine: Wannan bayanai Da suka gabata kokarin bincike ne da wallafar Hausa na Madinah Islamic, Katsina. Za'a iya yima bayanan gyara a duk lokacin da bukatar hakan ta taso. Domin neman karin bayani ko gyara, ko kuma neman magungunan Musulunci akan matsalar da wasu:

Kira +2348084028794 

ko email: madinahislamicmed@gmail.com






Thursday, 1 January 2015

Ciwon-Suga ( Diabetes/Diabetes mellitus [DM])- A Takaice

Gabatarwa: Jikin 'dan adam na bukatar wani irin nau'in sinadarin suga (glucose) dake cikin jini domin aiwatar da wasu daga cikin manya-manyan ayyukan da suka shafi lafiyar jikin. Suga (glucose) na bayarda kuzari (energy) ga jikin 'dan adam wanda ake bukata wajen narkarda abinci da kuma rayuwar 'kananan halittun da suka tattaru yawa sukayi ginin jikin 'dan adam ko halittarsa tamkar bululluka [tubali] (cells). Wannan sugan 'glucose' shine makamashin dake bawa jikin 'dan adam kuzari domin rayuwa. Kuma ana samun sa ne daga abincin da muke ci - wato nau'in abinci mai samarda kuzari (carbohydrate), kamar irinsu gero, dawa, masara ,shinkafa da sauransu. Kwalwa (brain), wayoyi ko hanyoyin sadarwar kwalwa a jiki (nerves) da kuma wasu jajayen halittun jini ( developing red blood cells) , duk kaninsu suna amfani da wannan makamashi (glucose) domin samun rayuwa.

Ciwon-suga (diabetes) cutace wadda suga (glucose) dake cikin jini yake haurawa sama - wato suga yayi yawa a cikin jini. Yawansa nada illa ga lafiya. Dalilin yawansa na faruwa ne sabili da jikin mutum baya samarda da wani sinadarin kemical mai suna 'insulin' ( = type 1 diabetes) , ko jikin ne baya amfani da 'insulin' yadda ake so, ko kuma ma jikin baya samar da 'insulin' da kyau [wato isasshe] ( = type 2 diabetes). Idan har babu 'insulin' tofa sugan 'glucose' zai cigaba da taruwa da yawa cikin jini har yayi illa ga lafiya. Sinadarin 'insulin' (a hormone), saifar 'dan adam ce ke samar dashi (pancreas). Amfanin sinadarin 'insulin' shine daukar sugan 'glucose' dake cikin jinin zuwa cikin 'kananan halittun da sukayi ginin jikin 'dan adam (cells) domin samun kuzari gare su da cigaban rayuwa. Idan babu 'insulin' ko baya aiki yanda ake bukata to suga fa zai cigaba da taruwa cikin jini yayi yawa har ya haddasa munanan matsaloli ga lafiya. Sugan zai iya yin illa ga idanu, koda, wasu jijiyoyin jini da kuma wayoyi/hanyoyin sadarwar kwalwa a jiki. Ciwon-suga zai iya haddasa cutar zuciya, mutuwar sashen jiki koma ya jaza yanke kafar marar-lafiyar. Idan ciwon yayi 'karami zai iya haddasa matsalar 'kashi da gabobi, matsalar fata, matsalar narkewar abinci, rashin karfin mazakuta, matsalar hakora da dasashi.  'Type 2 diabetes' ,wato nau'in ciwon-suga na 2 da mukayi bayani (wanda jiki baya amfani da 'insulin' yadda ya dace) shine nau'in ciwon-suga da yafi yawa ga mutane da dama fiye da nau'in ciwon-suga na 1: 'type 1 diabetes' (wanda mu kace jiki baya samarda da sinadarin 'insulin').Alamomin Ciwon Alamomin Ciwon-suga Nau'i na 1 (type 1 diabetes symptoms):
• Yawan jin kishirwa sosai
• Yawan yin fitsari
• Yawan jin yunwa ko gajiya
• Raguwar nauyin mutum ba tare da mutum yayi kokarin ragewar nauyin ba
• Dadewar ciwo/gwambo bai warke ba/warkewa a hankali
• Rashin gani da kyauAwon jini zai iya nuna idan akwai ciwon ko sabanin haka. Idan akwai irin nau'in ciwon , toh mutum zai cigaba da amfani da sinadarin 'insulin' da aka samar a asibiti, za'a bashi sinadarin a asibiti akan 'ka'ida da umarnin 'kwararren likita. Anfi yawan samun 'kananan yara da matasa da irin wannan nau'in ciwon-suga (Juvenile diabetes/Insulin-dependent diabetes)duk dadai cewa zai iya shafar mutane a kowani shekarun su na rayuwa. Alamomin Ciwon-suga Nau'i na 2 (type 2 diabetes symptoms):
• Yawan jin kishirwa sosai
• Yawan yin fitsari
• Yawan jin yunwa ko gajiya
• Raguwar nauyin mutum ba tare da mutum yayi kokarin rage nauyin ba
• Bushewar fata, kaikayin fata
• Mutum yaji kamar ba kafarsa ba ko jin tsira a kafafu
Yin awon jini a asibiti ko wata ingantacciyar cibiyar lafiya zai iya nuna maka ko kana da ciwon suga ko kuma akasin haka. Motsa-jiki (exercise), rage nauyin jiki yanda ya dace dace da koyarwar cikon lafiya, da kuma kula da tsarin cin abinci daya dace da ciwon lafiya, ko shakka babu , zasu taimaka sosai wajen shawo matsalolin lafiya na ciwon-suga. Cututtukan saifa, magunguna, kemikals, kamuwa da wasu cututtukan da gado daga mahaifan mutum na daga cikin dalilin da ake alakantawa da suke haddasa ciwon-suga. Allah ya bamu lafiya. AMEEN.






Sunday, 13 April 2014

Amfanin Man-Zaitun ga Lafiya ( a takaice)

Man-zaitun ( Olive oil/ Olea europea ) wani irin nau'in mai ne da ake samarwa daga 'ya'yan itaciyar zaitun (Olive tree). Ana amfani dashi wajen girki, gyaran fata, magani, hada sabullai da kuma man-fitila ( a gargajiyance). Man-zaitun ana amfani dashi a 'kasashen duniya da dama, musamman kasar Spain, France (Faransa), Italy, Greece (kasar Girka), Syria, Lebanon, Egypt, Libya,Tunisia, Algeria, Morocco da sauransu. Toh amma kasashen da suka fi yawan amfani dashi sune Portugal, Spain, Italy da Greece. Daga shekara ta 2000 zuwa ta 2009, kasashe 3 da suka fi yawan samar dashi sune: 1. Spain 2. Italy 3. Greece. Kasar Syria itace ta 4 , sai mai-bimata kasar Tunisia, a matsayin ta 5.
Sabili da muhimmancin itaciyar zaitun, Allah Madaukakin sarki, Mai -halittu ya ambace ta a cikin Al-Qur'ani Maigirma - Surat At- Tin da Surat An- Nur.
Man-zaitun nada amfanin sosai ga lafiyar 'dan adam. Binciken ilimin kimiyya ya nuna cewa yana da amfani kamar haka:
1. Yana 'karfafa garkuwar jiki ( domin yaki da kwayar cutar biras, bacteriya, fangas (fighting virus, bacteria, fungus etc.) da sauransu. Wadannan cututtuka suke haddasa matsalolin lafiya da dama, kamar irinsu ciwon-anta, tetanus da cin-ruwa.
2. Yana da sinadarai masu bada kariya daga kamuwa da ciwon daji (rich in antioxidant subtances).
3. Kariya daga cututtukan zuciya - yana rage yawan sinadarin kolestirol (reducing high cholesterol) wanda idan yayi yawa a cikin jini yake da illa ga zuciya.
4. Rage hawan jini (reducing high blood pressure).
5. Taimako ga masu ciwon-suga (helping diabetic patients).
6. Kariya daga ciwon jiki (sanyin jiki) dana gabobi (anti-rheumatism & arthritis).
7. Inganta lafiyar zuciya (improving heart's function esp. to older people whose hearts are weak due to aging) musamman ga tsofaffi wanda zuciyar su ta fara rauni wajen aiki saboda tsufa. Yana gyara zuciya da quruciya.
8. Kariya daga ciwon daji dake shagar fata ( protection from skin cancer).
9. Inganta lafiyar qashi. (improving bone health).
10. Inganta lafiyar kwalwa wajen koyon wani abu kamar karatu ko rike karatun, musamman ga manya (improving cognitive function) da sauransu.
Ana iya amfani da man-zaitun kamar haka:
~ Asha cikin babban cokali sau 2 a rana - safe da rana, cokali daya a kowane lokacin.
~ Ayi girki dashi a matsayin man girki ko a zuba cikin abinci bayan girki.
~ Manshafawa kamar sauran man amfani na jiki.
~ Giris ga ma'aurata (sex lubricant). Bugu da kari, zai kuma bada kariya daga cututtuka.
~ Ciwon-kunne, digo 2 ko 3 na man a cikin kunne.
~ Da sauran wasu hanyoyin na inganta lafiya.
Allah Ya bada sa'a.