Wednesday 23 August 2017

ƙanƙancewar Zakari (Penile shrinkage)

Kankancewar zakari na nufin raguwar girman al'aura, wato wani yanayi ne da al'aurar namiji baligi ke zama ƙarama tamkar ta ƙaramin yaro - ta shige ciki ko ta rage tsawo ko kauri a lokacin da take kwance (flaccid state) ko a miƙe (erect state) saɓanin yanda take ada. Wannan yanayi na faruwa ga mutum ne a lokacin da yake manyanta cikin rayuwarsa, a dabi'ance. Hakan na faruwa ne ga mutane  da shekarunsu na haifuwa suka kai 30 zuwa 40. Amma duk da haka akan sami matasa da yawa wanda basu kai ga wadannan shekarun haifuwa ba masu fama da wannan matsalar. Saidai wasu da yawa daga cikin masu bada maganin gargajiyar Hausa na ganin cewar matsalar ƙanƙancewar zakari matsala ce kai tsaye dake da alaƙa da ZAFI ko  SANYIN MARA, suke iƙrari.

Kankancewar zakari dai matsala ce dake cima mazaje tuwo a ƙwarya musamman irin yanda wasu da yawa ke jin kimarsu da alfaharinsu na kasancewarsu maza na fuskantar ƙalubale. Mutane a al'adun duniya da dama na ganin isasshen al'aurar namiji ita ce  abin tunƙaho da fahari ga kowani mutum dake amsa sunansa namiji , kuma itace kimarsa ga 'ya mace. To saidai ƙanƙancewar zakari idan ba yawa tayi ba  ba'a tunanin zata iya haddasa rashin gamsuwar jima'i tsakanin ma'aurata. Akwai dalilai na lafiya da dama da zasu iya bada haske gameda ƙanƙancewar gaba. Wasu dalilai na daban da ka iya haddasa kankancewar zakari ga matasa ko manya sun hada da:

1. Aiki ko tiyatar likita ga al'aura domin cire wani  ƙullutun ciwon daji ko kansa daga al'aura (Prostate tumour/cancer surgery removal). Yana iya haddasa kankancewar gaba bayan aikin.

2. Wata cuta (Peyronie's disease) mai sauya sigar zakari, wato karkacewar zakari sosai da wuya ko zafi wajen yin jima'i. Yin tiyatar likita /ofereshin (surgery) domin maganin matsalar na iya haddasa ƙanƙancewar zakari.

3. Yanayin sanyi (temperature) . Idan sanyi  ya  yawaita fiye da yanda ya dace ga jiki to zakari zai iya noƙewa/ɓoyewa saboda ɗari. Hakan na hana gudanar jini da kyau a cikin al'aura .Samun yanayi mai kyau da gumi  zai iya maganin matsalar.

4. Sanya wandon ciki (under pants) wanda ya tsuke hantsa ko al'aura. Yana sanya karancin gudanar jini cikin al'aura wanda sakamakon hakan zai iya sanya zakari ya takura dalilin jini baya shiga ciki da kyau ta yanda zakar zai cika da jini ya kumboro (ya mike) a lokacin sha'awa ko jima'i. Wato jijiyoyin jinin basa aiki da kyau saboda takura.

5. Yawan fitar maniyyi sakamakon yawan yin istimna'i/ wasa da al'aura amma ba jima'i ba. Da zaran maniyyi ya fita daga jikin mutum jakar marainansa data sauko ƙasa kafin fitar maniyyi zata nade ta koma sama ta tsuke marainan biyu bayan fitar maniyyin. A lokacin faruwar haka kuma zakari na shigewa shima ya koma gareji tare da marainan.

6. ƙiba: masu ƙiba da yawa na fama da ƙanƙancewar gaba domin kuwa tana sanya zakari ya shige ciki. Don haka, motsa jiki da rage ƙiba ta hanyar daya dace zaya iya maganin matsalar.
Barin shan taba ko giya, cin abinci mai kyau, motsa jiki, magani da shan wadataccen ruwa yanda  ya dace zai taimaka sosai wajen magance matsalar ƙanƙancewar gaba. Allah Ya taimaka.

Domin neman ƙarin bayani ko taimako sai a kira +2348084028794  ko email madinahislamicmed@gmail.com

23 comments:

  1. Allah gafarta malam, toh shin wani irin taimako za'aiya samu game da warakar wanannan matsala?

    ReplyDelete
    Replies
    1. Mlm Dan Allah aina kuke anajeria please

      Delete
    2. gafarta malam, toh shin wani irin taimako za'aiya samu game da warakar wanannan matsala?

      Delete
  2. Shin akwai maganin da yake Kara girman alzakarin namijine

    ReplyDelete
  3. To yaza, ai amagance matsalar malam

    ReplyDelete
  4. Allah ya saka da alhairin sa ameen thusma Ameen

    ReplyDelete
  5. Allah ya saka da alhairin sa ameen thusma Ameen

    ReplyDelete
  6. Allah ya saka da alhairin sa ameen thusma Ameen

    ReplyDelete
  7. I need more about this issue imI having this very problem

    ReplyDelete
  8. Mlm a taimaka da maganin wannan matsala

    ReplyDelete
  9. Ina da irin wannan Matsalar, Amman inaga sakamakon tiyata ne sanadiyar hakan,ina mafita..?

    ReplyDelete
  10. Slm mlm inada irin wannan matsalar Dan Allah taya zan iya maganceta

    ReplyDelete
  11. allah yabiyaka, malam nikuma ta dalilin istima,ine nake tinanin samuwar wannan matsalar ataimaka taya zan maganceta

    ReplyDelete
  12. Herbal treatment is 100% guaranteed to cure Herpes Virus, i have tried and it worked perfectly, contact {{Robinsonbuckler11}} @gmail. com,....

    Acne
    Addison’s
    Allergy
    Alopecia Areata
    Alzheimer’s
    Ankylosing Spondylitis
    Anxiety disorders
    Aplastic Anemia
    Asthma
    Atopic dermatitis
    Autism
    Back Pain
    Bell’s Palsy
    Bronchitis
    Callosities
    Cancer
    Candidiasis
    Cardiac
    Cellulitis
    Cervical Spondylitis
    Chalazion
    Actinic Keratosis
    Athlete’s Foot
    Cosmetic Consultations
    Cold Sores
    Dandruff
    Dermatitis
    Eczema
    Genital Herpes
    Genital Warts
    Hair Loss
    Hives
    Impetigo
    Jock Itch
    Moles
    Nail Fungus
    Poison Ivy
    Post Treatment Concerns
    Psoriasis
    Ringworm
    Scabies
    Dermatitis
    Shingles (Herpes Zoster)
    Warts

    ReplyDelete