Thursday, 17 August 2017

Satar Fasaha!

Salam. Fatan alheri da koshin lafiya ga customers namu da masoyan wannan shafi. Muna godiya ga Allah Madaukakin Sarki da nasarar da yake bamu da kuma hadin kanku da soyayyarku da kuke nuna mana.

Gargagadi: Hakika muna sane da cewa wasu mutane mararsa kishi na daukar bayanan mu a wannan shafi da muka wallafa kuma suna amfani da wallafe-wallafen a dandalinsu  tamkar sune suka rubuta bayanan  ba tare da nuna inda suka sami bayanan ba- wato suna satar fasaha. Wani lokacin ma sai suyi ma wani yankin rubutun  sauye-sauye ko qari a cikin bayanan da suka cirato kai tsaye daga gare mu.

Don haka , muna gargagadi ga masu wannan aiki, suji tsoron Allah. Bamu yarda ba wani ko wata ya canja wani abu ko yayi amfani da rubuce-rubucen mu ba tare da izinin mu ba face sai an ayyana ma6u66ugar bayanan, wato Madinah Islamic Medicine. Don haka muna kira ga masoyan mu dasu su taimaka mana da bamu rahotan duk inda suka ga anyi amfani da rubutun mu ba akan ka'ida ba domin mu aika da sakon korafi na COPYRIGHT a yanar gizo. Idan an lura dukkanin rubutun mu nada rana da kwanan wata. Don haka idan kaga rubutu ko wallafe-wallafen mu a wani blog  ko website da suka sata bayan mun wallafa kuma ba abisa ka'ida ko suna ikirarin nasu ne to sai ataimaka a kira mu ko a turo mana sakon email. Da fatan za'a taimaka.

Email: madinahislamicmed@gmail.com
Nambar waya: +234808 402 8794

Mun gode kwarai Allah Ya barmu tare.

Wednesday, 16 August 2017

Amfanin Shan Madarar Raƙumi ga Lafiyar Ɗan-adam


Madarar raƙumi ko nonon raƙumi (camel milk) sinadari ce mai matukar amfani ga lafiyar ɗan adam. Tsawon lokaci mai yawa Larabawa masu yawon kiwo da Buzaye a cikin sararin sahara sun kasance suna amfani da wannan madara wacce ake tatsowa daga hantsar dabbar taguwa a matsayin abinci abar sha da kuma magani a cikin tafiyarsu  mai nisa cikin sahara domin rayuwa.

Taguwa dabba ce mai asali da ban mamaki dake rayuwa musamman a yankunan sahara masu tsananin zafi a duniya. Tsawon lokaci mai yawa , tarihi ya nuna cewa mutanen sahara na amfani da madara ko fitsarin wannan dabba wajen magance matsalolin lafiya na daban-daban. Allah (S.W.A.) Yasa albarka da waraka a cikin madarar wannan dabba wacce bata da abinci daya wuce itacen ƙaya da ruwa a dajin sahara. Itacen ƙaya da wannan dabba ke ci  anyi imani cewa mafi yawansu na ɗauke da magunguna wanda za'a iya samun amfaninsu cikin madarar idan mutum ya sha ta. Bugu da ƙari, ana sarrafa madarar domin samar da wani abinci dake ake cema CUKU ko CUKWI (Camel cheese) .Shin ko ka taba ganin harshen raƙumi a mahauta bayan an yanka/soke shi? Da yawa zaka ga ƙaya mai tsawo cikin harshen duk ta soke/lume cikin tsokar harshen  saboda yawan cin ƙayarsa.

Binciken kimiyya na  nuna cewa saboda muhimmancin madarar raƙumi  itace mafi kusa a cikin nau'in madarar dabbobi dake da yanayin amfani kusan irin na madarar ɗan adam, wato madarar da uwa ke bawa jinjirinta mai roman sinadarai masu yawa da inganta lafiyarsa. Saboda haka ne da yawa ake bawa jinjirin mutum madarar raƙumi wanda baya samun isasshen abinci mai lafiya a wasu al'adun. Abin nufi anan shine, madarar raƙumi ta banbanta da sauran nau'in madarar dabbobi kamar irinsu sanuwa, tumkiya da akuya kasancewar ta zarce su amfani a cikin jikin ɗan adam mai amfani da ita (mai shan madarar). Madarar rakumi na dauke da sinadari mai ƙara yawan jini da hana rashin  jinin (iron) mai yawa wanda   yafi yawan wanda ke akwai cikin madarar sanuwa har linki 10 da kuma sinadari mai ƙarfafa garkuwar jiki (vitamin c) wanda shima yafi yawan wanda madarar sanuwa ke ɗauke dashi sau 3. Madarar raƙumi na ƙunshe da sinadari mai gina-jiki (protein) mai yawa tare da wasu sinadarai masu bayarda da kariya daga cututtuka. Irin waɗannan sinadarai ana samun su kaɗan ne cikin madarar sanuwa idan aka kwatanta da ta raƙumi.
Amfanin madarar raƙumi a taƙaice - wasu daga cikin manya-manyan amfaninta, sune:

(Health benefits of camel milk)
1. Tana taimakawa masu ciwon-suga (diabetes). Madarar raƙumi na ƙunshe da sinadaran inganta lafiya da kuma sinadarin INSULIN mai yawa . Masu ciwon-suga zasu more amfaninta ta sosai.

2. Tana taimakawa  masu rashin lafiyar OSTIZAM (AUSTISM), wanda wata matsalar ƙwalwa ce dake bayyana tun farkon yarintar mutum wacce ke hana marar lafiyar yin tarayya mai kyau da mutane - wato haɗuwa da mutane da yin abokanai da kuma sanya sa wuyar magana, tunani ko sadarwa tsananin sa da sauran mutane. Madarar raƙumi nada wasu sinadarai masu sanya mararsa lafiyar su sami sauƙi sosai koma waraka daga wannan rashin lafiyar.

3.Tana taimakawa masu ALAJI (ALLERGY) , wato wani yanayi da garkuwar jikin mutum ke nuna bata son wani abu , musamman abinda bai cika cutar da lafiya ba  ko kuma baya cutar da mutane da dama amma sai ya cutar da mutum , yasa garkuwar jikinsa tayi tutsu bata son abin (allergic reaction). Misali, kamar wani nau'in abinci da baya cutar da lafiya amma idan mutum yaci sai yasa shi rashin lafiya, ko ruwan damuna kawai ya sanya ƙuraje su fito ma mutum ga jiki ko ƙaiƙayi, ko warin wata dabba yasa mutum atishawa ko mura, ko kuma taɓa wata dabba ko wani abu ya sanya rashin lafiya da sauransu. Shan madarar raƙumi na magance dangin waɗannan matsaloli abisa wasu bincike-bincike da aka gudanar.

4. ƙarfafa garkuwar jiki. Sinadarai masu ƙarfafa halittun garkuwar jiki dake cikin madarar raƙumi sun isa suyi yaƙi da cututtuka masu kai farmaki a cikin jikin ɗan-adam su halaka cututtukan.

5. Gina jiki da ƙoshin lafiya. Yawan sinadarai masu gina-jiki (proteins) dake cikin madarar na taimakawa wajen girman jiki da cigabansa.

6. Inganta lafiyar zuciya. Madarar nada sinadarai (FATTY ACIDS) wanda zasu iya daidaita sinadarin kolestarol ( CHOLESTEROL) dake cikin jini. Yawan kolestarol a jini nada haɗari, sinadari ne mai danƙo wanda zai iya toshe ƙofofin jinin zuciya (fayif) da take harba jini dasu zuwa sassan jiki (arteries). Idan hakan ya faru zai iya yin dameji ga zuciya. Madarar zata iya rage haɗarin faruwar damejin zuciya, mutuwar sashen jiki da kuma rage hawan jini , da sauran su.


Sunday, 6 November 2016

Wasa-da-al'aura /Wasa-da-gaba da Illarsa

WASA DA-AL'AURA / WASA DA GABA DA ILLOLINSA GA LAFIYA

Wasa-da-al'aura ko wasa da gaba (Istimna'i [masturbation]) na nufin yin amfani da hannu, yatsa ko wani abu domin biyan bukatar jima'i ga mutum da kansa da tunanin saduwa da wata mace ko wani namiji , ga mace. Ana kiran wannan dabi'a "zinar hannu".Wasa-da-al'aura ko wasa da gaba dabi'a ce da take  faruwa da yaduwa cikin mutane da dama - yara matasa, da manya musamman cikin  matasa mararsa aure ko wanda aurensu ya mutu,  koma rashin gamsuwar aure. Wannan dabi'a ta zamo ruwan dare kuma abin 'kyama saboda wasu dalilai, wato dalilan  addini, na al'adu, da  kuma na lafiya. Dalilan lafiya da zamu yi magana akansu, suna magana ne game da yawan yin istimina'i da illarsa ga mai yawan yi wanda ya zama dabi'arsa koda yaushe (An addict person who overmasturbates ). Bincike-binciken wasu masana kimiyya da muka tattaro game da yawan wasa-da-al'aura (over-masturbation), na nuna cewa YAWAN WASA-DA -AL'AURA (excessive masturbation or over-masturbation) nada illololi ga lafiya. Duk da yake dai masana sunyi saɓani akan mas'alar istimna'i, inda wasu ke ganin yana da illa wasu kuma basa ganin haka saima kishiyar haka, to sai dai babu rikici akan cewa yawan yin istimna'i  nada illa ga lafiya. Yana  iya haddasa wadannan matsalolin idan ya zama halin mutum baya jin daɗi sai ya aikata (addiction):

Yawan mantuwa, rage hazaqar kwalwa, kankancewar zakari da maraina, saurin kawowa ko rashin karfin mazakuta. Sauran matsalolin dazai iya haddasawa , sun hada da:  ramar jiki ko 'karancin sha'awa, karancin maniyyi ko tsinkewar maniyyi da raguwar ingancinsa (wanda na iya haddasa rashin haifuwa) , raunin jiki, raunin garkuwar jiki, jin ciwon kai akai-akai, ciwon baya, fitar maniyyi daga zakari hakanan ba tare da mutum yayi niyya ba - ba tare da yayi istimna'i ba ko yayi jima'i, haka nan kawai. 
Wasu illololin da zasu iya faruwa saboda istimna'i: bushewar fatar kan zakari ko illa ga fatar saboda gugar fatar, karkacewar zakari (penis curvature) ko sauya masa sigarsa ta asali, bugawar zuciya da sauri, zubar gashi, kurajen fuska.

ILLAR ISTIMNA'I GA MACE

Mace zata iya samun wasu daga cikin matsalolin da mu kayi bayani a sama. Wasu matsalolin daka iya shafar mace sune: Rashin rike fitsari da kyau (ga mace) ko 
Yawan zuwa fitsari saboda saka wani abu cikin farji lokacin istimna'i,  wuyar kawowa ga mace wajen jima'i (dalilin  koyama jikinta  da sai an taɓa wani sashen farji don ta kawo, wanda mai yiwuwa ne zakari baya taɓa wurin lokacin  saduwa - a zahirin jima'i. Don haka istimna'i yana sa rashin gamsuwar jima'i ga mace - mijinta zai sha wahala wajen gamsar da ita. Jikinta ya riga ya koya, tayima kanta horo.  Dalilin haka, mace zata  ji dadin istimna'i fiye da jima'i , hakan kuma zai zamo mata matsala idan tayi aure.  Zata ringa tunanin mijinta baya iya gamsar da ita ko mazaje data aura, saboda sabon da tayi da koyama jikinta hanyar gamsar da kanta fiye da hanyar da ta dace, wato jima'i a cikin sunnar aure.  Ta canza dabi'ar ta. Da yawa zaka samu cewa  mata masu yawan istimna'i basu jin daɗin jima'i  sai istimna'i, koma basu gamsuwa sai sunyi istimna'i a bandaki bayan saduwa da mazajen aurensu. Wannan zai iya kawo babbar matsala a cikin aure. Bugu da kari, dadilan rashin gamsuwar mace wajen saduwa da mijinta suna da yawa. Don haka, bazamu iya cewa ba yin istimna'i kafin aure shine dalilin dake hana gamsuwa kadai ba.  Akwai wasu dalilan na daban, wasu matsalolin nada alaka da bangaren mazajen.

Mutumin da matsalar yawan wasa-da-al'aura ta zama dabi'arsa koda yaushe (addict) zaya iya maganin matsalar. Idan har yazama dabi'ar mutum baya jin dadin rayuwarsa sai yayi istimna'i (sau 2, 3, 4 ko fiye da haka a kowace rana) [addiction] toh zai iya kawo sauye-sauye (canje-canje) ga jikin mutum wanda lafiya bata maraba dasu ( such as hormonal imbalance), saboda yawan zubda sinadaran jikin mutum wajen inzali fiye dabi'ar jima'i ta gaskiya da sauyin yanayin jiki sakamakon yawan hakan . Yana da hadari ga lafiya yanda wasu matasa suka maida wannan dabi'arsu ta koda yaushe, a bandaki, a daki, a waje, ko a wurinda dama ba'a tsammani suna istimna'i.
Mutumin da matsalar yawan wasa-da-al'aura ta zama dabi'arsa koda yaushe (addict) zaya iya maganin matsalar. Idan har yazama dabi'ar mutum baya jin dadin rayuwarsa sai yayi istimna'i (sau 2, 3, 4 ko fiye da haka a kowace rana) [addiction] toh zai iya kawo sauye-sauye (canje-canje) ga jikin mutum wanda lafiya bata maraba dasu ( such as hormonal imbalance), saboda yawan zubda sinadaran jikin mutum wajen inzali fiye dabi'ar jima'i ta gaskiya da sauyin yanayin jiki sakamakon yawan hakan . Yana da hadari ga lafiya yanda wasu matasa suka maida wannan dabi'arsu ta koda yaushe, a bandaki, a daki, a waje, ko a wurinda dama ba'a tsammani suna istimna'i. Yawan Istimna'i mummunar dabi'a ce. Yana da muhimmanci ga masu yawan sha'awa suyi aure , idan babu halin yin auren toh sai su lazimci  yin azumi kamar yanda addinin Musulunci ya koyar. Haka kuma, mutum zai iya dinga cin abinci wanda aka sarrafa da WAKEN- SUYA (soya bean) domin bincike ya nuna cewa  yana rage sha'awa. Za'a iya kuma yawaita amfani da NA'A-NA'A (pepper mint/mint) , na'a-na'a nada amfani ga lafiya sosai, toh amma sinadarin minti (menthol) da take dashi yana dakushe sha'awa idan yayi yawa. Don haka, a nemi bayanan Malaman Sunnah akan wannan mas'ala, don karin bayani.
~~~
Bugu da kari, mutum mai yawan sha'awa ya rage yawan zama cikin daki cikin kadaici yana tunane-tunane. Mutum ya maida kansa kullum BUSY da karatun Al-Qur'ani da kuma wani aiki, musamman idan yaji sha'awa na tsunkulin / muntsulin sa. Idan kuma mutum yasan yana kallace-kallacen haramun kamar fina-finan batsa, hotunan batsa (musamman a yanar gizo) ko kuma mata (masu kallon maza) akan hanya toh aji tsoron Allah a daina, domin kuwa wadannan na daga cikin manyan-manyan  masifun  dake jefa matasa cikin wannan hali.
~~~
Idan har daya ko fiye daya daga cikin wadancan alamomin illar  yawan wasa- da-gaba sun bayyana a gareka, toh ya zama dole idan kana  son lafiyarka  ko lafiyarki ki daina  kuma a nemi magani domin a tsiratar da  lafiya, ta dawo yanda take. Idan ba haka ba, zai iya shafar illahirin  lafiya, wani lokacin ma sai a dade ba'a gane abinda ke  damun mutum  ba. Wannan yana faruwa da yawa ga matasa, kuma muna ganin irin wadannan " cases" barkatai.  Haka kuma muna samun rahotanni da yawa sosai akan wannan matsala. Abin takaici shine, mutum baya neman taimako ko magani da wuri sai wai  anyi masa baiko ko kuma bikinsa saura wata 1 ko 2. Idan har kana da wannan matsala ba abin kunya bane neman magani, kada ka zauna a cikin matsala har sai  ta girma sa'annan ka nemi taimako a lokacinda  kunyar ta riga ta cutar dakai. .Muna bada da taimako (herbal remedy) da shawarwari,  musamman ga masu wannan matsala. Kuma babu kokwanto ana samun lafiya cikin yardar Allah. Haka kuma mutum zai iya zuwa asibiti yaga likita domin neman warwarar wannan matsala. Allah ya taimaka.
~~~
Domin neman karin bayani/Neman magani
Sai azo Office branch namu mai address kamar haka:
No. 34 Sabuwar Unguwa Dandagoro, Katsina, Jihar Katsina.
Kira: +2348084028794 (WhatsApp number)
E-mail: madinahislamicmed@gmail.com


MADINAH ISLAMIC MEDICINE
(based in Katsina,  Katsina State of Nigeria ) provides effective and affordable herbal products (alternative medical practice, trading/ merchandise and general contracts):

Arab-Islamic medicine, Ayuvedic medicine (Indian traditional medicines), Chinese traditional  medicines, traditional African herbal medicines, etc.

We have modern herbal products for effective treatment (very long-time control of hypertension and diabetes) of high blood pressure, diabetes, sickle cell anaemia. Fight high cholesterol level in your blood, fibroid, ovarian cysts, cancer, vaginal infections (vaginitis), arthritis, rheumatism, gout, ulcer with unique herbal products. You really need our sexual enhancement products: approdisiac,  male and female  enhancement product ,  herbs for increasing sperm count, increasing sexual vitality and fertility, fighting erectile dysfunction, increasing libido, fighting premature ejaculation, memory enhancement, anxiety, depression, skincare and haircare  products etc.
Our products work wonders with grace of God , and we are known for that, we have lots of testimonies. And that's what plucks us from obscurity.
Visit or contact us , let us know your problems , get our herbal products from anywhere in Nigeria , especially in the north  or visit us in Katsina, Katsina State of Nigeria.

For more info, call +2348084028794 or email us @ madinahislamicmed@gmail.com

Saturday, 5 November 2016

Amfanin Lemongrass ga Lafiya (Ciyawa-mai-kamshin-lemu)

Amfanin Lemongrass ga Lafiya (Ciyawa-mai-kamshin-lemu)

Lemongrass (Cymbopogon citratus) shuka ce mai dadin kamshi, wato wata irin ciyawace doguwa mai launin kore da kamshin lemun-zaki. Duk da yake dai bata da alaka da lemun-zaki, kamshin ciyawar mai karfi da dandano yayi kama dana lemun-zaki (amma bata da zaki). Ana samun ciyawar a kasashe masu yanayin zafi ko yanayin dumi. Anfi yawan amfani da ita a kasashen Asiya, Afurka da Australia . Haka kuma, anfi yawan amfani da wannan ciyawa a kasashen Asiya wajen girki. A kasar Indiya kuwa akanyi amfani da ita a matsayin maganin gargajiya (herb). Ana amfani da busassar ciyawar ko danyarta domin amfani na daban-daban. Kuma anfi amfani da ita wajen hada shayi , miya ko kori (curry) domin ta zamo hadin kayan kamshin girki. Ana samun manta (lemongrass oil) a kasuwa wanda shima ake amfani dashi na daban-daban.

Amfaninta:

Mai yiwuwa ne kana da wannan shuka a gida ko a lambunka , koma kana amfani da ita, to amma baka san ainahin amfaninta taba ga lafiya, kawai dai ka dauketa shuka ce domin k'awata gida, ko filebo maisa kamshi a kofin shayin ka a lokacinda kake kurɓawa. To ka bude idanunka, domin kuwa wannan ciyawa amfaninta ya wuce na adon gida kadai ko kamshin shayinka da kake jin dadin sha saboda dandano da kamshin da take baka a lokacin da kayi amfani da ita. Ciyawar Lemongrass nada ado da zata iya yima lafiyarka domin inganta ta. Wasu daga cikin amfanin wannan ciyawa mai albarka sun hada da:

1. Kariya daga ciwon-daji/kansa (Anti-cancer). Shukar lemongrass nada sinadari mai kamshi na "citral", wanda binciken kimiyya ya nuna cewa yana kashe kwayoyin halitta da ciwon kansa ya harba a jiki (cancer cells). Haka kuma yana inganta lafiyar kwayoyin halittar jiki gaba daya (improving cellular health).

2. Karin-jini da hana rashin-jini (Anaemia). Lemongrass nada sinadarin "iron" mai yawa, wato sinadari maisa karin-jini domin cikakkiyar lafiya da kuma hana wasu matsalolin rashin jini.

3. Rage hawan-jini (Reducing high blood pressure). Yawan sinadarin "potessium" a cikin lemongrass, sinadarin mai inganta lafiyar zuciya, koda da sauran sassan jiki, na taimakawa wajen hana hawan-jini, cututtukan zuciya, mutuwar sashen jiki, ciwo kansa, matsalolin rashin narkewar abinci da rashin haihuwa, cikin yardar Allah.

4. Kariya da hana girman kananan halittu masu haddasa cututtuka a jiki (Anti-septic) da kuma hana kumburi, wuri yayi ja, da radadin ciwo a jiki (Anti-imflammatory), musamman taimako ce ga masu ciwon gabobi da sassan jiki da sauransu (gout, arthritis, etc).

5.Yaki da cututtukan bakteriya dana fangas (Anti-bacterial and anti-fungal). Don haka, tana maganin zazzabin cizon-sauro da taifot (Malaria and typhoid) [yi shayi] , da sauransu. Haka kuma, tana maganin cin-ruwa na yatsun kafa da makero [yi amfani da manta] da sauransu ( athlete's foot, ringworm, etc).

6. Maganin mura, zubar hanci da hawaye, kaikayin ido, atishawa, toshewar hanci (Cold,flue and hay fever).

7. Tace duk wani abu mai guba ga jiki , musamman na abinci, ko wani abu mai cutarwa da fitar dasu daga jiki (Detoxifying). Tana tsaftace hanta, koda, mafitsara da sauransu.

8. Inganta bacci / yakar da rashin bacci (Fighting insomnia). lemongrass nada tasiri wajen kwantar da hankali da fada da rashin bacci domin samun cikakkiyar lafiya.

9. Taimako ga masu ciwon-suga (Diabetes). Tana rage yawan suga cikin jini, tsarkake saifa da inganta aikinta.

10. Inganta kwalwa (Improving nervous system). Lemongrass na taimakawa kwalwa wajen maida hankali don lakantar karatu, rike karatun da kuma taimakawa wajen sarrafa karatun/ilimi. Sinadarin "magnesium", "phosphorus" da "folate" da ake samu a cikin ciyawar nada tasirin kyautata lafiyar kwalwa.

11. Rage kiba (Weight loss). Shan lemongrass musamman a shayi na narkarda kitshe. Tana sanya yin fitsari akai-akai a lokacinda take fitar da duk wani abu mai yawa da jiki baya bukata wanda zai iya cutar da lafiya.

Da sauransu.

Medical Disclaimer: Wanda ya rubuta wannan bayanai ba likita bane, mai bincike ne kawai akan magungunan gargajiya, masani akan abinda ya rubuta sakamakon bincike daya gabata. Wannan bayanin amfanin ciyawar lemongrass da duk kanin bayanan magunguna daya wallafa a wannan shafin yanar gizo, baya nufin masu matsalolin lafiya zasu iya barin yin amfani da magungunan da aka basu a asibiti ba domin su lazimci yin amfani da maganin gargajiya, a maimakon magungunan. A nemi shawarwarin likita da masana ilimin maganin gargajiya akan yanda za'a iya amfani da magungunan da kuma sanin wanda zai iya amfani da ciyawar da wanda bazai iya amfani da ita ba wasu lokuttan.


Domin neman taimako ko siyan magungunan mu masu inganci sosai da karin bayani , sai a kira : +2347011591392 ko email : madinahislamicmed@gmail.com

Sunday, 17 January 2016

Matsalolin Ciwon Sanyin-Mata /Sanyin Gaba [Vaginitis/vaginal infections/ toilet infections] da Rigakafi

SANYI kalma ce mai fadin ma'ana da Malam Bahaushe ke yin amfani da ita domin yin kokarin bayanan wasu matsalolin lafiya na daban-daban , misali , ciwon-sanyin jiki [rheumatism], ciwon sanyin mura [cold and flu] da ciwon sanyin-mara ko ciwon sanyin-mata [vaginitis] ko ciwon sanyin maza-da-mata da ake dauka ta hanyar jima'i [STDs/STIs like chlamydia, gonorrhea, syphilis, genital herpes, HPV etc] da sauransu. Saidai Malam Bahaushe baya kiran ciwon sida/kanjamau [HIV/AIDS] da ciwon sanyin-mara duk da cewa kau anfi yada cutar ta jima'i.

Za muyi bayani akan ciwon sanyin-mata ne kadai [Vaginitis]. Matsalolin ciwon sanyin-mata [vaginitis/vaginal infections or toilet infections] wasu cututuka ne ko matsaloli dake addabar gaban mace, wato cututtuka masu sanya kaikayin farji, ko radadin ciwo, kumburin gaba ko warin gaba , zubar farin ruwa, kurajen farji, zafi wajen yin fitsari ko wajen yin jima'i da sauransu. Ciwon sanyin-wata matsala ce dake faruwa ga mata da dama a cikin wasu lokutta na rayuwarsu. Ana samun wannan cututtuka ko matsaloli sabili da wani sauyin yanayin jiki da mata ke samu wasu lokutta da kuma sabili da wasu kwayoyin halittar 'bacteria' da 'fungus' dake zaune cikin al'aurar mace, haka kuma , mata na iya samun wannan ciwon a lokacin juna-biyu da kuma shayarwa [during pregnancy and breastfeeding] . Har ila yau, za'a iya samun ciwon ta hanyar jima'i [vaginal intercouse] da wasu dalilan ko hanyoyi na daban.

Nau'in ciwukan sanyin-mata suna da yawa, to amma bincike ya nuna cewa ciwon sanyin-mata nau'i uku ne (3) suka fi addabar mata da yawa. Za muyi bayani akansu kadai, a takaice insha Allahu, sune kamar haka: (sunayen su da yaren turanci) 1. 'Yeast infection' 2. 'Bacterial vaginosis' 3. 'Trichomonas'

1. ‘Yeast infection’ ('Candidiasis'). Akwai wasu kwayoyin halittun 'fungas' (masu suna 'candida') sune ke haddasa 'Yeat infection'. Su wadannan halittu wanda kwayar idon mutum baza ta iya ganin suba , saboda kankaantar su saida taimakon madubin likita ne za'a iya ganin su [microscope] . Halittun suna rayuwa a wasu wurare cikin jikin mutum kuma adadinsu baya da yawa . Ana samunsu cikin farji kuma, asali basu cika cutarwa ba.'Candida' suna san wuri mai gumi, lema da rashin iska domin girma da yaduwa. Idan suka samu wannan yanayi da suke so toh za suyi yawa su kuma haddasa ciwon sanyin 'Yeast infection'. Anfi yawan samun irin wannan ciwon sanyi ga mata da yawa , kusan kashi 75 cikin 100 na mata sun taba samun wannan ciwon a cikin wasu lokutta na rayuwarsu. Alamomin cutar sun hada da: zubar farin ruwa mai kauri daga farji, kuraje ko kaikayin farji da kuma labban farji suyi jawur ko cikin farji.

2. ‘Bacterial vaginosis’ , cuta ce dake shafar farji sabili da girman wasu kwayoyin halittun 'bacteria' masu cutarwa dake cikin farji suna rayuwa. Alamonin cutar sun hada da: zubar ruwa mai 'karnin kifi daga farji, warin sa musamman lokacin jima'i, ko radadin zafi lokacin fitsari, amma babu kaiyayi cikin alamomin. Alamomin cutar kuma na iya 'buya.

3. ‘Trichomoniasis ’ : A cikin cututtukan sanyi da muka yi bayanin su a baya (wato cuta ta 1 da ta 2) , 'Trichomoniasis' ta 3, itace cutar sanyin-mata da ake yadawa ta hanyar jima'i ga maza (STD) fiye da sauran a zahiri, wato mace zata iya harbin mijinta da cutar ko mijin ga matar. Idan ya kasance miji nada wata mata ko yana neman matan waje masu cutar ko kuma macen ta taba saduwa da wani mutum mai cutar daya samo cutar daga wata mace, to akwai yiwuwar ma'aurata su samu cutar koma mafi hadari HIV da wasu cututtukan jima'i (STDs). Ana kiran 'yar kankanuwar halittar [parasitic organism] dake sanya wannan cuta da suna 'Trichomonas vaginalis'. Mazaje ba kaso suke sanin suna da cutar ba kasancewar alamomin cutar basu cika bayyana ga maza ba. Yawanci sai idan ciwon ya kama matan su suna cikin neman magani suke gano suna da cutar. Idan anyi sa'a alamomin ciwon sun bayyana ga maza, ana iya samun alamomi kamar haka: zubar farin-ruwa kadan, zafi kadan bayan fitsari ko bayan fitar maniyyi. Alamomin cutar ga mata suna iya kama da ciwon sanyi na 1 da na 2 da muka yi bayani a sama, ko kuma: zubar ruwa mai launin kore-da-dorawa - mai kumfa da wari, zafi wajen yin fitsari, rashin jin dadi wajen jima'i. Wannan cuta tana da hadari ga mace mai juna-biyu ga abunda ke cikinta, musamman idan ba'a nemi magani ba.

Matakin da Zaki Dauka Idan Har Kinga Alamomin Ciwon-Sanyi

Idan har kina da daya ko biyu daga cikin wadannan alamomin ciwon kai koma fiye da haka, mataki na farko da zaki dauka shine, ki garzaya zuwa asibiti ko wata cibiyar lafiya domin neman taimako. A asibiti ne idan anga kwararriyar likita, musamman 'gynaecologists' wanda suka shahara akan fagen matsalolin mata , za'a duba matsalar, sa'annan ayi bincike 'lab test' ko da 'microscope' asan abunda ke damun ki a kuma baki maganin daya dace da shawarwari. Haka kuma , idan anyi binciken kuma an tabbatar da irin ciwon sanyin dake damun marar lafiyar toh za'a iya zuwa wannan cibiya tamu mai albarka ta Madinah Islamic Medicine Katsina domin neman magani/waraka da yardar Allah.

Wasu Halayen Da Zasu Iya Taimakawa Wajen Samun Ciwon Sanyi da Rigakafin su:

> Wajen Tsaftace Gaba [ Vaginal Douching] A cikin farji akwai wasu kwayoyin halittar 'bacteria' marar sa cutarwa kuma masu amfani (wato 'Normal flora'). Su 'normal flora' suna taimakawa wajen bada kariya ga farji daga wasu nau'in 'bacteria' na daban masu cutarwa (masu suna 'Bacterial pathogens'). Garin neman kiba akan nemo rama, wasu mata kanyi amfani da wasu hanyoyi domin tsaftace farji, kamar ta hanyar yin amfani da sabullan magani, harba magani cikin gaba, ruwan dumi da gishiri ko dettol domin wanke farji don tsaftacewa ko rigakafi daga 'bacteria' da zata iya cutarwa. Wadannan abubuwa da ake amfani dasu don rigakafi na kashe 'bacteria' masu amfani [the normal flora] cikin farji, hakan zaisa 'bacteria' masu cutarwa su samu damar shigowa cikin farji su cutar da lafiya da ciwon-sanyi, sabili da babu 'bacteria' mai bada kariya dake hana su shiga ko 'barna. Don haka , idan har lafiyar ki lau kuma kina son tsaftace gabanki toh sai ayi amfani da ruwa , musamman lokacin wanka a tsaftace gaba. Ki guji fesa turare ko wanke gaba da sabili mai kamshi. Idan har lafiyar ki lau kada kiyi amfani da wani abu idan ba ruwa ba. Ki sani cewa farji yana tsaftace kanshi da kanshi a yanayin halittarshi, yana fitar da wani ruwa [secrets fluid] na musamman dake wanke illahirin gaban mace.

> Kayan-sawa na ciki/wandon pant [Under-wears/under-pants] Wasu matan kanyi amfani da wandon pant ko 'skin-tight' kwana da kwanaki ba tare da canzawa ba ko wankewa. Irin wannan halin kazanta na dauda da lema, na bawa cututtuka (Germs) dama su shiga cikin farji su kuma girma cikin 'dan kankanin lokaci har su haddasa ciwon sanyi. Don haka , yana da kyau a canza 'under-wears' wankakku masu tsafta a kowace rana. Idan lokacin zafi ne ko kinyi aiki kuma akwai zufa a jikin ki to sai ki canza wando akalla sau 2 a rana. Kuma yana da kyau ayi amfani da wandon da akayi da auduga [cotton under-wears] domin yana taimakawa wajen tsotse lema da bushewa, sabanin wando da akayi da 'nylon' [nylon under-wear].

> Wajen wanke bayan-gida [Way of cleaning the anus after faeces] Yana daga cikin halayen wasu mata idan sunyi bahaya suna fara wanke dubura sa'annan gabansu, wasu kuma suna hadawa ne duka , wato gabansu da dubura su wanke lokaci daya, wannan ba dabi'a bace ba mai kyau ga mace, domin kuwa idan kika wanke dubura farko sa'annan gabanki ko kika wanke su a lokaci daya toh zaki iya goga ma farjinki wasu cututtuka dake cikin kashi/bayan gida. Don haka , sai a fara wanke farji farko, bayan angama wanke shi da ruwa da kyau to sai a wanke dubura.'Toilet infection' kalma ce da mutane suka kirkira kuma ta samu asali ne daga mummunar dabi'ar wanke dubara tare da farji, wanda wasu ke tunanin shine ke kawo cutar sanyin-mata. Toh saidai dadilan dake kawo cutar sanyin mata suna da yawa kamar dai yanda mu kayi bayani a baya, kuma ita kalmar 'Toilet infection' ba tada muhalli a cikin 'Kamus din likitoci a matsayin sunan cuta. Mutane ne wanda ba ma'aikatan lafiya ba suke amfani da kalmar da nufin 'vaginal infections' ko 'vaginitis' (kalmar da ma'aikatan lafiya suka fi amfani da ita).

> Tsugunni a bandaki [Squatting in toilets] Yin tsugunni a bandakin da mutane da yawa ke amfani dashi nada hadari ga lafiya, musamman bandaki mai dauda da kazanta. Sau da yawa mace zata tsugunna tayi fitsari cikin bandaki sai fitsarinta ya doki kasa yayi tsalle ya fallatso mata ko ya dawo mata tare da wani ruwan dake kwance a kasa ko fitsarin wata macen.Digo daya na fitsarin mai ciwon sanyi zai iya harbar ki da ciwon idan ya fallatso maki ga ga gaba.Don haka, idan zaki yi fitsari kada kiyi inda kowa keyin fitsari a cikin bandaki, ki samu wuri na daban mai tsafta cikin bandakin kuma inda babu ruwa a kwance. Haka kuma kada ki bari gabanki ya taba kasa. Kiyi fitsari a hankali. A yawaita wanke bandaki kullum da dettol ko danginshi 'germicides' masu inganci domin kashe cututtuka.

> Yin amfani da wandon pant na 'kawar ki, yar'uwar ki ko wata mace [Sharing under-wears] Kawar ki, kanwar ki ko wata yar'uwarki mutane ne masu iya kamuwa da cuta. Zai iya kasancewa suna da ciwon-sanyi , don haka idan kina jin cewa kinyarda da ita ko kuma kun zama jini da tsoka toh ki shirya fama da ciwon sanyi da zasu iya harbarki dashi idan kina amfani da wandon su. Koda basu da ciwon , bai kamata ku rinka amfani da pant din junanku ba. Riga kafi yafi magani.

> Rashin kula wajen yin jima'i [Sexual intercourse without care] Yanada matukar muhimmanci ki kiyaye da jin rauni a farji a lokacin saduwa da maigida. Barin gashin gaba ba'a rage shiba da kuma yin jima'i tsawon lokaci ko da karfin tsiya na daga cikin dalilan dake sa mace ta samu rauni a gabanta. Samun rauni ko fashewar fata cikin al'aura na bawa cututtuka kofar shiga jiki su cutar da lafiya da 'infections'.

>Mataki na biyu da zaki iya dauka shine: bayan kin san abunda ke damun ki domin a asibiti an bayyana maki, idan har ya tabbata sanyi ne kuma kin sha magani amma baki samu sauki ba, ko kuma kin samu sauki amma baki warke duka ba yana dawowa, toh zaki iya amfani da wannan taimakon da zamu baki :

Ki samu 'Khal tufah' [Apple cider vinegar] a Islamic Chemist. Ki tafasa ruwa mai yawa yayi zafi, idan yayi 'dumi sai ki samu robar wanka ki juye ruwan ya cika robar, sa'anna ki zuba khal tufah cikin ruwan kimanin adadin kofin shayi [small tea cup] 1 ko 2 cikin robar wankan, sai ki zauna ciki minti 15. Bayan kin tashi daga robar sai ki tsane lemar ruwan dake gabanki da tawul mai kyau ya bushe. Sai ki samu man-kwakwa [coconut oil] da auduga ki goge gabanki, man-kwakwa nada sinadarai masu kashe kwayoyin cuta [ antiviral, antibacterial and antifungal properties] Kiyi amfani da man-kwakwa sau 3 a rana. Za kiyi amfani da Khal tufah kamar yanda mu kayi bayani kullum sau 1 a rana har sai kin samu sauki.
Haka kuma, zaki iya amfani da Tafarnuwa [Garlic]. Ki samu salar tafarnuwa 2 ko 1 ki karkare bawon da ledar ta, kiyi matsi dasu da dare idan zaki kwanta bacci sai da safe ki cire ki yar. Tafarnuwa magani ce mai karfi (kuma 'antibiotic') , itama tana da sinadarai masu kashe cututtuka [antiviral, antibacterial and antifungal properties]. Kuma zaki iya cin tafarnuwa ko amfani da 'capsules' nata, idan zaki iya.
Bugu da kari, zaki iya neman garin Hulba [Fenugreek powder] a Islamic Chemist da zuma (honey) kiyi shayi, ki tasa ruwa ki zuba hulba karamin cokali 1 cikin kofin shayi ki motsa, sai ki sha. Kiyi haka safe da dare, har sai kin samu sauki. Idan mace tana da juna-biyu kada tayi haka sai ta nemi shawarar likitan Islamic Chemist/ likitan asibiti da yasan 'Hulba' ko masani amma babu laifi ga mai shayarwa tayi amfani da hulba, hakan zai kara samar mata da ruwan nono. Masu juna-biyu su guji sha-shayen magunguna ba tare da izinin likita ba. Allah ya taimaka.

Madinah Islamic Medicine: Wannan bayanai Da suka gabata kokarin bincike ne da wallafar Hausa na Madinah Islamic, Katsina. Za'a iya yima bayanan gyara a duk lokacin da bukatar hakan ta taso. Domin neman karin bayani ko gyara, ko kuma neman magungunan Musulunci akan matsalar da wasu:

Kira +2348084028794 

ko email: madinahislamicmed@gmail.com






Thursday, 1 January 2015

Ciwon-Suga ( Diabetes/Diabetes mellitus [DM])- A Takaice

Gabatarwa: Jikin 'dan adam na bukatar wani irin nau'in sinadarin suga (glucose) dake cikin jini domin aiwatar da wasu daga cikin manya-manyan ayyukan da suka shafi lafiyar jikin. Suga (glucose) na bayarda kuzari (energy) ga jikin 'dan adam wanda ake bukata wajen narkarda abinci da kuma rayuwar 'kananan halittun da suka tattaru yawa sukayi ginin jikin 'dan adam ko halittarsa tamkar bululluka [tubali] (cells). Wannan sugan 'glucose' shine makamashin dake bawa jikin 'dan adam kuzari domin rayuwa. Kuma ana samun sa ne daga abincin da muke ci - wato nau'in abinci mai samarda kuzari (carbohydrate), kamar irinsu gero, dawa, masara ,shinkafa da sauransu. Kwalwa (brain), wayoyi ko hanyoyin sadarwar kwalwa a jiki (nerves) da kuma wasu jajayen halittun jini ( developing red blood cells) , duk kaninsu suna amfani da wannan makamashi (glucose) domin samun rayuwa.

Ciwon-suga (diabetes) cutace wadda suga (glucose) dake cikin jini yake haurawa sama - wato suga yayi yawa a cikin jini. Yawansa nada illa ga lafiya. Dalilin yawansa na faruwa ne sabili da jikin mutum baya samarda da wani sinadarin kemical mai suna 'insulin' ( = type 1 diabetes) , ko jikin ne baya amfani da 'insulin' yadda ake so, ko kuma ma jikin baya samar da 'insulin' da kyau [wato isasshe] ( = type 2 diabetes). Idan har babu 'insulin' tofa sugan 'glucose' zai cigaba da taruwa da yawa cikin jini har yayi illa ga lafiya. Sinadarin 'insulin' (a hormone), saifar 'dan adam ce ke samar dashi (pancreas). Amfanin sinadarin 'insulin' shine daukar sugan 'glucose' dake cikin jinin zuwa cikin 'kananan halittun da sukayi ginin jikin 'dan adam (cells) domin samun kuzari gare su da cigaban rayuwa. Idan babu 'insulin' ko baya aiki yanda ake bukata to suga fa zai cigaba da taruwa cikin jini yayi yawa har ya haddasa munanan matsaloli ga lafiya. Sugan zai iya yin illa ga idanu, koda, wasu jijiyoyin jini da kuma wayoyi/hanyoyin sadarwar kwalwa a jiki. Ciwon-suga zai iya haddasa cutar zuciya, mutuwar sashen jiki koma ya jaza yanke kafar marar-lafiyar. Idan ciwon yayi 'karami zai iya haddasa matsalar 'kashi da gabobi, matsalar fata, matsalar narkewar abinci, rashin karfin mazakuta, matsalar hakora da dasashi.  'Type 2 diabetes' ,wato nau'in ciwon-suga na 2 da mukayi bayani (wanda jiki baya amfani da 'insulin' yadda ya dace) shine nau'in ciwon-suga da yafi yawa ga mutane da dama fiye da nau'in ciwon-suga na 1: 'type 1 diabetes' (wanda mu kace jiki baya samarda da sinadarin 'insulin').Alamomin Ciwon Alamomin Ciwon-suga Nau'i na 1 (type 1 diabetes symptoms):
• Yawan jin kishirwa sosai
• Yawan yin fitsari
• Yawan jin yunwa ko gajiya
• Raguwar nauyin mutum ba tare da mutum yayi kokarin ragewar nauyin ba
• Dadewar ciwo/gwambo bai warke ba/warkewa a hankali
• Rashin gani da kyauAwon jini zai iya nuna idan akwai ciwon ko sabanin haka. Idan akwai irin nau'in ciwon , toh mutum zai cigaba da amfani da sinadarin 'insulin' da aka samar a asibiti, za'a bashi sinadarin a asibiti akan 'ka'ida da umarnin 'kwararren likita. Anfi yawan samun 'kananan yara da matasa da irin wannan nau'in ciwon-suga (Juvenile diabetes/Insulin-dependent diabetes)duk dadai cewa zai iya shafar mutane a kowani shekarun su na rayuwa. Alamomin Ciwon-suga Nau'i na 2 (type 2 diabetes symptoms):
• Yawan jin kishirwa sosai
• Yawan yin fitsari
• Yawan jin yunwa ko gajiya
• Raguwar nauyin mutum ba tare da mutum yayi kokarin rage nauyin ba
• Bushewar fata, kaikayin fata
• Mutum yaji kamar ba kafarsa ba ko jin tsira a kafafu
Yin awon jini a asibiti ko wata ingantacciyar cibiyar lafiya zai iya nuna maka ko kana da ciwon suga ko kuma akasin haka. Motsa-jiki (exercise), rage nauyin jiki yanda ya dace dace da koyarwar cikon lafiya, da kuma kula da tsarin cin abinci daya dace da ciwon lafiya, ko shakka babu , zasu taimaka sosai wajen shawo matsalolin lafiya na ciwon-suga. Cututtukan saifa, magunguna, kemikals, kamuwa da wasu cututtukan da gado daga mahaifan mutum na daga cikin dalilin da ake alakantawa da suke haddasa ciwon-suga. Allah ya bamu lafiya. AMEEN.






Sunday, 13 April 2014

Amfanin Man-Zaitun ga Lafiya ( a takaice)

Man-zaitun ( Olive oil/ Olea europea ) wani irin nau'in mai ne da ake samarwa daga 'ya'yan itaciyar zaitun (Olive tree). Ana amfani dashi wajen girki, gyaran fata, magani, hada sabullai da kuma man-fitila ( a gargajiyance). Man-zaitun ana amfani dashi a 'kasashen duniya da dama, musamman kasar Spain, France (Faransa), Italy, Greece (kasar Girka), Syria, Lebanon, Egypt, Libya,Tunisia, Algeria, Morocco da sauransu. Toh amma kasashen da suka fi yawan amfani dashi sune Portugal, Spain, Italy da Greece. Daga shekara ta 2000 zuwa ta 2009, kasashe 3 da suka fi yawan samar dashi sune: 1. Spain 2. Italy 3. Greece. Kasar Syria itace ta 4 , sai mai-bimata kasar Tunisia, a matsayin ta 5.
Sabili da muhimmancin itaciyar zaitun, Allah Madaukakin sarki, Mai -halittu ya ambace ta a cikin Al-Qur'ani Maigirma - Surat At- Tin da Surat An- Nur.
Man-zaitun nada amfanin sosai ga lafiyar 'dan adam. Binciken ilimin kimiyya ya nuna cewa yana da amfani kamar haka:
1. Yana 'karfafa garkuwar jiki ( domin yaki da kwayar cutar biras, bacteriya, fangas (fighting virus, bacteria, fungus etc.) da sauransu. Wadannan cututtuka suke haddasa matsalolin lafiya da dama, kamar irinsu ciwon-anta, tetanus da cin-ruwa.
2. Yana da sinadarai masu bada kariya daga kamuwa da ciwon daji (rich in antioxidant subtances).
3. Kariya daga cututtukan zuciya - yana rage yawan sinadarin kolestirol (reducing high cholesterol) wanda idan yayi yawa a cikin jini yake da illa ga zuciya.
4. Rage hawan jini (reducing high blood pressure).
5. Taimako ga masu ciwon-suga (helping diabetic patients).
6. Kariya daga ciwon jiki (sanyin jiki) dana gabobi (anti-rheumatism & arthritis).
7. Inganta lafiyar zuciya (improving heart's function esp. to older people whose hearts are weak due to aging) musamman ga tsofaffi wanda zuciyar su ta fara rauni wajen aiki saboda tsufa. Yana gyara zuciya da quruciya.
8. Kariya daga ciwon daji dake shagar fata ( protection from skin cancer).
9. Inganta lafiyar qashi. (improving bone health).
10. Inganta lafiyar kwalwa wajen koyon wani abu kamar karatu ko rike karatun, musamman ga manya (improving cognitive function) da sauransu.
Ana iya amfani da man-zaitun kamar haka:
~ Asha cikin babban cokali sau 2 a rana - safe da rana, cokali daya a kowane lokacin.
~ Ayi girki dashi a matsayin man girki ko a zuba cikin abinci bayan girki.
~ Manshafawa kamar sauran man amfani na jiki.
~ Giris ga ma'aurata (sex lubricant). Bugu da kari, zai kuma bada kariya daga cututtuka.
~ Ciwon-kunne, digo 2 ko 3 na man a cikin kunne.
~ Da sauran wasu hanyoyin na inganta lafiya.
Allah Ya bada sa'a.











Monday, 24 March 2014

AMFANIN ZUMA GA LAFIYA (A TAKAICE)

Zuma wani irin abinci ne mai zaki kamar shigen suga wanda kudan-zuma ke samarwa daga furen itace ko shuka -wato wani romon sinadari dake cikin furen itace ko shuka da kudan-zuma ke tsotsowa (nectar) domin sarrafa ruwan zuma. Mutane na amfani da zuma a matsayin abinci ko magani. Sabili da muhimmancin zuma, a cikin surorin Alqur'ani maigirma - akwai surah mai sunan kudan zuma - wato Surat An- Nahl. Allah (S.W.A.) ya bayyana mana muhimmancin zuma ga rayuwar 'dan adam a cikin wannan surah " ...waraka ce ga mutane." (An Nahl: 69). Hakika kuma Manzon Allah (S.A.W.) ya bayyana mana muhimmancin ta a wasu hadisai.
Don haka, zuma nada amfani ga lafiya kamar haka:
1. Tana kashe cutar bakteriya da fangas (bacteria & fungus) da kuma bada kariya daga kamuwa da ciwon-daji. Bincike ya nuna cewa zuma mai duhu-duhu tafi wannan amfanin.
2. Tana warkar da ciwo ko gyambo idan ana shafawa ko sha.
3. Tana taimaka ma mai-mura, tari , atishawa da sauran matsalolin sanyi.
4. Maganin gudawa ce.
5. Maganin gyambon ciki - Ulcer.
6. Tana karfafa garkuwar jiki.
7. Tana rage hadarin kamuwa daga cututtukan zuciya, musamman idan aka hadata da Kirfat (cinnamon).
8. Tana sanya kuzari a jiki.
9. Tana rage nauyin kiba. Shan ruwa mai-`dumi da lemun tsami tare da zuma kafin aci komi da safe zai taimaka wajen rage `kiba.
10. Tana saukaka narkewar abinci ga masu fama da rashin narkewar abinci.
11. Tana rage kumburi mai sanya waje yayi kalar ja da radadin ciwo.
12. Tana kyautata lafiyar kwalwa.
13. Tana gyara fata da rage kurajen fuska (pimples) idan ana shafa ta.
14. Da sauransu.












Saturday, 1 March 2014

KALUBALE GA MA'AURATA - KASHI NA 5



GARGADI:
Ba'a yardaba wani yaro ko mutum qasa da shekara sha-takwas (18) ya karanta wadannan bayani ko daya daga cikin shigen jerin irin wadannan bayanai wanda suka gabata. Mai aure ne ko mai shirin yin aure ya kamata ya karanta. Idan shekarun ka/ki basu kaiba kada ka karanta domin doka da tarbiyya sun hana.

GABATARWA
A`dabiance mazaje da dama na cintar kansu cikin wani halin damuwa a duk lokacinda akayi magana dangane da muhimmancin girman al'aura wajen jima'i. Kamfanonin dake samarda kwayoyin magani na girman-mazakuta ko shakka babu suma sun taimaka wajen jefa wannan tsoro cikin zukatan mutane. Wasu kamfanonin ma su kanyi amfani da hotunan batsa na shaidanun mutane masu girman mazakuta domin su jawo hankalin mutane cikin irin wannan tunani: cewa girman al'aurar namiji itace abu mafi muhimmanci wajen saduwa , kuma rashin girmanta na haddasa rashin gamsasshen jima'i ga mace. Sau dayawa sukanyi amfani da wannan dama su sayarda magungunansu da wuri - wato wani sabon salon dubarar kasuwa ne, wanda ta hakan sun sami miliyoyin kudi da mutane.

Sabili da irin wannan barazana, zakaga mutane sun damu sosai akan al'amarin mazakuta , koda kam suna da abunda zasu iya wadatar da matansu (wanda su basu luraba).Muna samun sakonni da yawa (Mails, SMS & Calls) na tambayoyi akan wannan matsala. Saboda yawansu sau dayawa bamu iya karantasu duka kuma mu mayar da amsa. Muna bada hakuri. Don haka zamuyi bayani akan wannan mas'ala daidai gwargwadon abunda muka sani na ilimi. Allah yayi mana jagora.

Minene Adadin Tsawo da Kaurin Al'aurar Baligi ?

Binciken ilimi ya nuna cewa yanayin girman jikin mutum, karanta, tsawo ko kajartar jikin mutum bayada alaka da yanayin girma, tsawo ko gajartar al'aurarsa (kamar yanda wasu ke tunani). Sau da yawa akan samu akasin abunda ake tunani.

Dayawa daga cikin masu binciken kimiyya da nazari akan al'aurar 'dan adam sun raba mutane (baligai) zuwa kaso uku (3): Kason farko (1) sune mutane na tsaka-tsakiya (average) wajen yanayin girman al'aurarsu kuma sune mutanen da akafi yawan samu. Kaso na biyu (2) sune mafi girman al'aura (above average), wato sunfi na tsaka-tsakiya girman mazakuta. Kaso na uku (3) kuma sune na karshe wadanda suke da qasa da abunda kaso na 2 suke dashi (below average), wato masu karantar al'aura.

A lokacinda al'aurar mutum baligi take kwance ba a mike ba (flaccid state) tanada kimanin tsawon inci 3 da `digo 5 zuwa kusan inci 4 (3.5- 3.9 inches = 9-10 cm) amma bai kai inci 4 ba, wato inci 3 da `digo 9. Wannan shine yanayin tsawo na mutanen kason farko, wato na tsaka-tsakiya. Kuma shine tsawon da akafi yawan samu a cikin mutane. Inci 4 zuwa sama kuma shine tsawon mazakutar mutanen kaso na 2, wato wanda su kafi mutanen dake cikin kaso na 2 tsawon mazakuta a lokacinda take kwance (flaccid length of penis). Haka kuma, qasa da inci 3 da rabi shine tsawon mazakutar mutanen kaso na 3.

Toh saidai kankantar zakari a lokacinda yake kwance (flaccid length of penis) bashi bane abunda yake nuni da zahirin tsawonsa ba. Domin kuwa zakari na iya mikewa daga kankantarsa zuwa tsawo mai yawa. Hakan kuwa na yawan faruwa ga wasu mutanen.

Mutumin dake cikin kason mutanen farko, a lokacinda zakarinsa ya mike sosai (erect) zakarin nada kimanin tsawon inci 5 da `digo 5 (rabi) zuwa inci 6 da digo 3 (5.5 - 6.3 in = 14-16 cm). Ma'ana mutum wanda keda tsawon zakari na inci 5 da rabi ko inci 6 ko kuma zuwa gidan inci 6 da `digo 3 toh ya fada cikin kason mutanen farko (average). Mutumin dake da sama da wannan adadi kuma ya fada cikin kason mutane na 2, wato mutane masu zakari inci 6 da `digo 4 zuwa sama. Haka kuma, mutumin dake da qasa da inci 5 da rabi wato daga inci 5 da `digo 4 (5.4 in) zuwa qasa ko inci 3 zuwa qasa, toh ya fada cikin kason mutanen karshe (wato mutane na 3) masu karantar zakari.Kauri, fadi ko gwabin zakari kuma (penis thickness, girth, width, or circumference) na kason mutanen farko nada kimanin inci 4 da `digo 7 zuwa gidan inci 5 da `digo 1 (4.7-5.1 in = 12-13 cm). Mafi yawancin mutane suna cikin kason mutane na 2 (average).

Bugu da qari, mutum zai iya zamantowa yana da tsawon mazakuta da ya fada cikin kason farko ko na biyu amma fadi/kaurin mazakutar ya fada cikin kaso na biyu ko na farko ko kuma ma sabanin hakan. Domin kuwa kowani mutum yana da yanayin da Allah Madaukakin-Sarki ya halicce sa na daban. Kuma Allah Mai-Girma da Daukaka  shine Mai halitta mutum yanda Yaso.

Hanyoyin da masu binciken sukabi wajen samun wannan ilimi sune kamar haka: sanya mutane su auno tsawo da kaurin zakarinsu ta hanyar amfanida "ruler " da kuma "tape", wato sunyi amfani da "ruler" wajen awon tsawon zakari da kuma "tape" wajen awon kauri ko fadin al'aura. A wasu binciken kuma ma'aikatan lafiyar ne da kansu suka auna mutanen domin gudun kuskure daga wajen mutane da akan samu wani sa'in.Misali A wani bincike da akayi a Jami'ar Indiyana (Indiana University) mutum dubu-daya-da-dari-shida-da-sitin-da-daya ne (1,661) akayi bincike a kansu, an sanya su su auno tsawo da kaurin al'aurarsu a lokacinda take mike so sai. Ko wanen su kuma ya bayarda sakamakon ta yanar-kizo (internet).

Wadannan bayanai da suka gabata sun samune daga wasu Mujallolin kiwon-lafiya da suka bada rahotanni akan wasu bincike-bincike da aka gabatar akan al'aurar 'dan adam (A study published in Journal of Urology on September 1996 & a study published on December 2000 in International Journal of Impotence Research & others, among many). Wata mujallar kiwon-lafiya ta Birtaniya ( British Journal of Urology in 2007 ) dake nazari da bincike akan al'aurar 'dan adam ta tattaro wadannan rahotannin bincike-binciken da suka gabata, kuma ta kwatanta kamanceceniyar sakamakon rahotannin binciken na daban-daban. Mujallar tayi sharhi akan wadannan rahotanni inda ta fitar da bayani na kimanin adadin tsawo da fadin zakari (da muka bayar) daga bincike-binciken har guda goma-sha biyu (12) na wasu kasashen duniya da dama. Dalilan wadannan bincike-bincike mafi yawanci shine domin a tabbatar da ilimi akan tsawo da kaurin mazakuta tayanda ma'aikatan kiwon- lafiya zasu iya bada shawarwari ga mutane da suke tunanin suna da kananan zakari kuma suke neman mafita daga matsalar daga likitoci.

Wani Mutum ne Zai Iya Gamsar da Iyalinsa?

Sau dayawa mutane da dama nada tunanin cewa al'aurarsu karama ce kuma suna kokonto ko suna gamsar da iyalinsu yanda ya kamata wajen kwanciya . Wannan shine tsoro da yacika zukatan mutane da yawa saboda ganin cewa wasu kan alakanta gamsasshen jima'i da namiji mai girman mazakuta da kuma jin wasu labaran cewa mata sunfi son namiji mai yalwa da sauransu.Abun mamaki kuma shine mafi yawancin masu irin wannan tunanin tsoro ko fargaba sune mutane na cikin kason farko (average men), wato na tsaka-tsakiya masu tsawon zakari inci 5.5 har zuwa gidan 6.3 (da kuma kauri inci 4.7 zuwa inci 5.1). Mafi yawanci irin wadannan mutane su zaka ga basu gamsu da yanayin suba. Mutane kuma na kason karshe (masu karantar mazakuta) dama can sun san matsayin su - sunada karamin zakari.

Gaskiyar wannan lamari shine: ilimi har ila yau ya nuna cewa , kusan duk mutanen dake cikin kason farko (average men) zasu iya gamsar da iyalinsu wajen jima'i. Dama dai shi jima'i wani abune da yake bukatar dabaru da kwarewa domin gamsar da iyalin mutum. Mutumin dake a kason farko mai dabaru na ilimin jima'i gami da fahimtar iyalinsa akan lamarin jima'i ko shakka babu zai biyama matarsa bukata yanda yakamata kamar yanda mutumin dake dake a kaso na biyu (above average ) ke biyama matarsa bukata yanda ya kamata. Zamantowa a cikin mutanen kaso na 2 sa'a ne domin kuwa mutane a cikin irin wannan kason basu da yawa kamar irin na kason farko. Haka kuma kada kayi mamaki cewa mutumin dake cikin kaso na farko ya gamsar da matarsa sosai fiye da mutumin dake cikin kaso na 2. Ana samun irin wandannan mutane wanda suna da isasshen komi amma basu san yanda za suyi amfani dashi ba, don haka sai mutumin kason farko mai dubara ya fisu abun kirki. Haka kuma, wasu mazajen masu girman al'aura wani sa'in mata na tsogomi da cewa jima'i dasu akwai zafi kasancewar suna da girma da yawa. Bugu da qari, wani sa'in saboda da yawan girman wata mazakutarr sai kaga bata da karfi sosai sai girman kawai.

Bincike ya nuna cewa mata na cikin kason farko (average women) nada kimanin tsawon farji (zurfi) inci 3 zuwa 4 a lokacinda basu cikin sha'awar jima'i, wato a lokacinda basu kamu ba (un-aroused). Wasu kuma matan nada inci 5 zuwa 7. Amma a lokacin jima'i farji na budewa yana qara tsawo da fadi tamkar roba irinta balo ta yanda zai wadaci ko wani nau'in zakarin daya shige shi. Yi mamakin ikon Allah da cewa ta farji ne ake haihuwar jinjiri yayinda ya bude tamkar roba mai-talala. A yayin saduwa kuma farji na yawaita tsukewa da budewa a lokaci daya (repeatedly) domin ya matse zakari dake kaikawo , don samun guga (friction) dake bada `da
ni'imar jima'i.

Toh wata qila mai-karatu yayi wannan tambayar: Da wata hujjace aka dogara da ita cewa mutum na cikin kason farko zai iya gamsar da iyalinsa wajen saduwa? Hujjar itace, ilimi ya nuna cewa zangon farko na zurfin farjin mace (wato waje-wajen farji daga kofa zuwa ciki har zuwa wajen inci 5 na zurfi a qiyasi) shine wurin jima'i (vagina) mai muhimmanci (baya ga beli) da yafi jin 'dan'danon jima'i a lokacinda zakari ke shiga farji.Dalilin kuwa shine wurin na cunkushe da wasu wayoyin sadarwar qwalwa masu jin ta`bi, wato masu kai sakon jindadi ga qwalwa da suke da yawa sosai (nerve-endings).Wadannan wayoyin sadarwa sune suka tafo har zuwa beli (clitoris) su kayi wata babbar mahada a wajen belin daga karshe. Wajen beli akwai wadannan wayoyin masu yawa tamkar wayoyin lantarki masu kawo wuta mai-karfi. Suna da yawa fiye da dubu takwas a qiyasi (More than 8,000 sensory nerve endings by estimate). Wannan zango daya tafo ya qare da wata boda ta zango na biyu. Zangon na biyu wajen zurfi kuma (cervix ) wajene da bana jima'i ba. Matsatstsen wuri ne da ya fara daga karshen zangon farko ya kuma mika zuwa hanyar mahaifa. Wannan bayanai suna nuna cewa mutum na kason farko nada dama dazai iya biyama iyalinsa bukata idan akayi la'akari da adadin tsawon zakarinsa. Duk kanin wadannan wurare (Vagina & cervix) suna qara tsawo a lokacin da mace ta kamu. Kuma a duk lokacinda maigida yaji matarsa tace ya shege ta da yawa - ba dadi ko tayi masa waigi da hannayenta toh kodai saboda tsawon zakarinsa da ya tabo "cervix" ko kuma saboda bata kamu ba- ma'ana bata cikin sha'awa sosai. Domin kuwa idan bata cikin sha'awa tsakanin zangon farko dana biyu babu nisa- matse suke da juna. Idan akwai sha'awa sosai duk sai su qara budawa da yalwa.

Tsawo ne Yafi Muhimmanci ko Kauri?

A wani bincike mata da yawa sun bada rahotanni cewa kaurin mazakuta yafi gamsarwa akan tsawo. Kaurin al'aurar na miji yafi gugar fatun farji domin samun ni'ima. Mata da yawa suna  nuna cewa sunfi jin zakari ya cika su idan mazakuta nada kauri. Saboda haka akan bada shawara ga mararsa kauri cewa uwargida ta rinka hade kafafunta/cinyoyinta wajen kwanciya domin ta gamsar da kanta da maigidanta.

Minene Mafita?

Duk zakarinda ya gaza inci 3 a tsaye (erect) ana kiransa da suna "Micropenis" a turance (wato `dan karamin zakari).Duk mutumin da yake da qasa da abunda ake bukata na tsawo ko kauri yana bukatar ilimin jim'i da wasu dabarun jima'i da zasu taimaka wajen biyama iyalinsa bakin gwargwado. Haka kuma yana bukatar shawarwarin likita kwararre a fannin al'aura. Bugu da qari, akwai hanyoyi na magani, ofireshin (surgery or penile augmentation), famfo (penis pump), qarin-girman zakari da hannu (jelquing/penis exercise) da sauransu na qara girman zakari. Da yawa daga cikin hanyoyin nada hadari ga lafiya wasu lokuttan. Kuma kadan ne daga cikin mutane masu amfani da hanyoyin suke bada rahotan samun nasara idan ka cire magani wanda shima aikinsa ba dindin bane . Kuma kafin mutum yabi daya daga cikin hanyoyin ya zama wajibi yasan hukunci addinin Musulunci akan ko wace hanya - ma'ana haram ne ko halas don gudun sabama Sharia. Don haka sai an tambayi Malaman Sunnah don samun bayani na ilimi (Al-Qur'ani da Hadisi) daga fahimtar magabata. Allah yasa a dace, Ameen.

MEDICAL DISCLAIMER:  
Wanda ya tattaro wadannan bayanai da suka gabata kuma yayi kokarin fassara su a cikin yaren Hausa daga harshen Turanci ba likita bane, Mai- bincikene akan matsalolin lafiya da kuma maganin gargajiya (herbology) irin na Musulunci da kuma na wasu al'adun.Bayanai da mai-bincike ya samo an ciratosu ne daga wasu rubuce-rubuce na wasu masana kiwon lafiya, mujallun kiwon lafiya da kuma yanar-gizo. Mai-bincike yana da kyakkyawar manufar haskakama mutane domin fahimtar wasu matsalolin lafiya da akayi shiru akansu wanda kuma sun dade suna cima mutane tuwo akwarya, domin su ilmanta kuma su nemi shawarwari daga ma'aikatan-lafiya qwararru, don samun mafita daga matsalolinda suka dame su.Wannan bayanai da suka gabata za'a iya yi masu gyara daga qwararru masana kiwon lafiya a duk lokacinda bukatar hakan ta taso domin gudun kuskure da kuma bada gur`bataccen bayani akan matsalolin lafiya. Mun gode.

Domin karin bayani nemi nemi ma'aikatan lafiya qwararru musamman akan al’aura (Urologists) ko kuma bayanai daga wadannan hanyoyi wanda wasu na daga cikin wanda mai-bincike ya ziyarta:

Chen, J.; Gefen, A.; Greenstein, A.;
Matzkin, H.; Elad, D. (2000). "Predicting
penile size during erection". International
Journal of Impotence Research 12 (6): 328333.

Lever, J.; Frederick, D. A.; Peplau,
L. A. (2006). "Does Size Matter? Men's and
Women's Views on Penis Size Across the
Lifespan". Psychology of Men & Masculinity
7 (3): 129.

 Stang, Jamie and Story, Mary.
"Adolescent Growth and Development" .
University of Minnesota. p. 3. Retrieved 26
November 2012.

Wessells, H.; Lue, T. F.;
McAninch, J. W. (1996). "Penile length in
the flaccid and erect states: Guidelines for
penile augmentation". The Journal of
urology 156 (3): 995997.

Wylie, Kevan R.; Eardley, Ian (June
2007). "Penile size and the 'small penis
syndrome'" . British Journal of Urology International 99 (6).

Wikipedia contributors. "Vagina."
Wikipedia, The Free Encyclopedia .
Wikipedia, The Free Encyclopedia, 25
Feb. 2014. Web. 28 Feb. 2014.

Wikipedia contributors. "Clitoris."
Wikipedia, The Free Encyclopedia .
Wikipedia, The Free Encyclopedia, 22
Feb. 2014. Web. 28 Feb. 2014.

Wikipedia contributors. "Human penis
size." Wikipedia, The Free
Encyclopedia . Wikipedia, The Free
Encyclopedia, 26 Feb. 2014. Web. 28
Feb. 2014.

Wikipedia contributors. "Micropenis."
Wikipedia, The Free Encyclopedia .
Wikipedia, The Free Encyclopedia, 31
Dec. 2013. Web. 28 Feb. 2014.

Thursday, 20 February 2014

Fitaccen Maganin Gargajiya na Kasar Sin - Ginseng

Ginseng da yaren turanci ko Rénshēn (人参/人蔘) a yaren Kasar Sin (Chana) , wata irin nau'in shukace mai ganye launin kore da jijiyoyi (sauyoyi) masu tsoka shigen irin na citta a yanayi da launi. Shukace mai tasawa ahankali-ahankali yayinda take girma. Ita wannan shuka ana samun tane kawai a yankin Amerika-ta-Arewa (North America) da yankin Asiya-ta-Gabas (Eastern Asia), kamar irinsu Koriya, Chana ta Arewa-Maso-Gabas, da sauransu. Haka kuma, shukar tana rayuwa ne a yanayin mai sanyi. Kuma tana da nau'i na daban-daban.

Ita kalmar "Ginseng" (furucin kamar haka /'Jinsen/) ta samu ne asali daga kalmar "rénshēn" wanda a yaren Chananci "ren" na nufin "mutum". Gudan kuma bangaren kalmar "shen" na nufin "jijiyoyi ko sauyoyin shuka" ta yanda idan ka hada kalmomin biyu zaka hararo wannan ma'anar, wato "jijiya mai yatsu wacce take kama da kafafuwan mutum." Ginseng sinadari ne da wadannan kasashe suke amfani dashi a matsayin maganin gargajiya tsawon lokaci mai yawa a tarihi , har izuwa yanzu. Akwai wannan sinadari a kasuwanni kuma ana sarrafashi ta hanyoyi daban-daban na zamani, kamar gari, lifton, abun-sha, kofee, sirof, kwayar-magani, da wasu amfanin. Ginseng na daya daga cikin magungunan gargajiya da akafi siya a duniya. Ana fitar dashi zuwa kasashen duniya da dama, wanda harda Najeriya.Ginseng nada tarihi mai-tsawo na amfaninsa wanda tun daga lokacinda aka fara rubuta amfaninsa (farko) a wani kundi lokacin daular "Liang" (Liang Dynasty 220-587 AD) har izuwa yanzu. Abisa wasu bimcike-binciken kimiyya na zamani, sinadarin Ginseng nada amfani sosai ga lafiya ,

kamar haka: 1. Yana sanya kuzari da hana kasala. Mutane da dama sunyi imani da hakan, kuma suna amfani dashi domin biyan wannan bukata.

2. Yana gyara kwalwa domin rike karatu da kuma kyautata hazaqa.

3. Yana qara ruwan-jikin 'dan adam, kamar irin na maniyyi (maza da mata).

4. Yana bayarda rigakafi daga kamuwa da ciwon-daji (kansa), da yardar Allah.

5. Yana taimakawa wajen magance matsalar rashin karfin-maza.

6. Yana maganin ciwon-jiki.

7. Yana qarfafa garkuwar-jiki.

8. Yana rage suga dake cikin jini da yawan sinadarin kolestorol dake cikin jinin.

9. Yana gyara jini da hana saurin tsufan jikin 'dan adam, idan Allah yaso. Yana gyara jiki da

quruciya. Sai a kiyayi cin haram don rayuwa tayi kyau, mutuwa kuma dole ce. Allah yasa mu dace.

10. Da sauransu.

Muna sayarda wannan sinadari a irin sifofin da muka zayyana ana sarrafashi da kuma samar dashi. Mai bukata sai yazo ya siya, a kuma  shawarci likita akan yanda ya kamata ayi amfani dashi.   Allah ya taimaka.

Medical Disclaimer: I am just a researcher & a herbal practitioner not a professional medical  doctor.






Monday, 6 January 2014

ILLAR YAWAN CHOLESTEROL A JIKIN 'DAN ADAM

Cholesterol wani irin sinadari ne da jikin 'dan
adam ke amfani dashi domin gudanar da wasu
ayyukan lafiya a cikin jinin mutum. Wasu daga
cikin ayyukan cholesterol a cikin jini sune: 1.
Sauye-sauyen halittar 'dan adam yayin da yake
balaga da kuma sarrafa sha'awar sa. 2. Daidaita
sukari a cikin jini 3. Kare mutum daga daukar
wasu cututtuka (infection) 4. Samarda VITAMIN
D (sinadari maisa 'kwarin 'kashi da hakora) da
sauransu.

Hanta (liver) tana daga cikin ma'aikata ta
gangar jiki dake samar da CHOLESTEROL mai
yawa. Haka kuma abincin da mukeci wanda yake daga dabbobi na samar
dashi (DIETARY CHOLESTEROL).

Wannan
sinadari yafi yawa a cikin abincinmu karmar: kwai
('kwanduwa), hanta, butter, kifi,
nama, madara, mai , kaza da sauransu.

Duk da kasancewar wannan sinadari yana da amfani ga jikin 'dan adam, ba'a so yayi yawa cikin jini. Yawan cholesterol a cikin jinin mutum nada
hadari sosai, yana haddasa cututtukan zuciya.
Cholesterol dai sinadari ne mai danko kamar
kitse. Idan yayi yawa a cikin jini yana likewa a
hanyoyin jini dake daukar jini (artery) zuwa
zuciyar 'dan adam. Faruwar haka na iya
haddasa toshewar fayif din hanyoyin jinin
(plague/atherosclerosis). Idan haka yafaru, yana
jaza matsalolin zuciya kamar haka:

1. Hanyoyin dake kawo jini zuwa zuciya su toshe
(Coronary artery disease). Daga nan sai a samu
"heart attack" (zuciyar mutum ta samu dameji
ko mutum ya mutu).

2. Zuciya ta kasa harba jini zuwa sauran
hanyoyin jini na sauran jikin mutum (heart
failure).

SHAWARWARI

Mutum zai iya rage yawan cholesterol a cikin jininsa
ta hanyar:

1. Motsa jiki (exercise).
2. Cin 'yayan itatuwa da ganye (fruits &
vegetable).
3. Zaka iya amfani da magani domin rage
yawansa (amma da izinin likita ). Haka kuma
yanada kyau mutum yaje asibiti domin a duba
yawan cholesterol a jikin sa, domin yana karuwa yayin
da mutum yake manyanta. Allah yasa mudace.
Ameen.

Wannan hoto da kake gani a sama yana dauke
da bayanan abubuwa biyu kamar haka: Nafarko,
jini yana gudana a cikin fayif din jinin zuciya
(artery) lafiya lau batare da wata matsala ba. Na
biyu, yana nuna yanda cholesterol ya toshe fayif
din jinin (hanyar jini) zuwa zuciya. Cholesterol
shine mai kalar 'dorowa.