Saturday, 28 December 2013

BASIR-MAI-TSIRO

A cikin duburar 'dan adam akwai jijiyoyin jini
wadanda wani lokacin suna samun matsatsi
da talala mai takurasu. A lokacinda suka
samu takurawa da yawa, sai su kumbura.
Kumburin wadannan jijiyoyin jini na kara matsi
da takura a garesu cikin dubura. Dalilin
wannan yanayi marar-dadi ga jijiyoyin, sai
kaga wani tsiro ya fito maka a bakin dubura
wanda jijiyar jinince. Zakaji ciwo, ko kai-kayi
koma zubar jini. Wannan lamari shine Malam
Bahaushe ke kira da BASIR-MAI-TSIRO
(Hemorrhoid/ Pile).
Wasu daga dalilanda ke haddasa shi sune
kamar haka:
1. Gaggawa wajen yin yun'kurin kasaye
abunda dake cikin mutum (kashi). Hakan na
takurama jijiyoyin dubura.

2. Yawan zawo(gudawa) ko 'kin fitowar kashi
maisa yawan tsugunni a ban-daki.
3. Yawan kiba, musamman wajen mara ko
duwawu.

4. Juna-biyu da nakuda (musamman wajen
yunkurin fito da jinjiri daga farji). Yana yima
dubura talala da matsi.

5. Jima'i ta dubura (haramun!). Masu jima'i da
iyalansu ta dubura da mafi yawan 'yan luwadi
na fama da basir mai tsiro.

6.Zama mai tsawo kamar na cikin mota ko na
tela, da sauransu.

7. Matsalolin zuciya kona anta na tsawon
lokaci wanda ka iya jaza talalar jijiyoyin jini.
8. Da sauransu.

Zaka iya maganin rashin fitowar kashi maisa
yawan tsugunni ta hanyar cin 'ya'yan itace da
ganye (fibre foods). Yana da kyau sosai ga
marar-lafiya ya rinka tafasa ruwan zafi ya bari
yayi 'dumi ya gasa basir nashi da auduga ko
kuma ya zauna cikin robar ruwan mai dumi
minti 30 sau 2 a rana, domin samun saukin
ciwo da kumburi. Bayan angama gasawa toh
sai asamu DETTOL a wanke wajen domin
gudun kamuwa da wata bakuwar cuta. Aje
asibiti neman magani. Haka kuma zaka iya
neman taimakon magani daga gare mu. Allah
ya taimaka, Ameen.
Akwai wani irin nau'in basir na cikin ciki maisa
zawo da jini wanda wata cuta ke jazawa ta
daban, wato DYSENTERY a turance. Haka kuma akwai "Fitar-baya" wato RECTAL PROLAPSE za muyi
bayanai akansu insha Allahu anan gaba.

Thursday, 26 December 2013

AMFANIN ZOGALE GA JIKIN 'DAN ADAM

Zogale
(Moringa oleifera) itaciya ce mai ban mamaki dangane
da amfaninta ga lafiyar 'dan adam. Allah
(S.W.T.) yasa albarka da waraka ga
wannan itaciya. Zogale abinci ne mai romon sinadaran lafiya a bayan kasa, baza'a iya kwatanta shiba da sauran ganyaye ta fuskar amfaninsa ga lafiyar 'dan adam. Wannan dalili yasa wasu ke kiransa da suna ITACIYAR RAYUWA ( The tree of life). Ganyen zogale na kunshe da romon
sinadari mai yawa na VITAMIN A (wanda ke
karama idanun 'dan adam lafiya da gani) fiye da
VITAMIN A dake cikin karas har sau 4. Ganyen
zogale haka kuma yana da sinadari mai yawa na
CALCIUM (mai sanya qashi da hakoran 'dan
adam kwari da lafiya) fiye da yawan na cikin madara linki 4. Yana da sinadarin
VITAMIN C (wanda ke karfafa garkuwar jikin 'dan adam domin fada da cututtuka masu kai farmaki ga lafiyar mutum),
yanada wannan sinadarin mai yawa fiye da irin
wannan sinadarin dake cikin lemu har linki 7.
Haka kuma yanada sinadarin PROTEIN (sinadari
mai gina jikin 'dan adam), fiye da na cikin madara sau 2. Bugu da qari, yana da VITAMIN E
(sinari mai gyara fata da lafiyar fata). Masana ilimin kimiyya da bincike akan wannan itaciyar lafiya sun bayyana cewa ZOGALE/ZOGALA nada wadannan magunguna:
-Yana daidaita sukari cikin jini.
-Yana rage hawan-jini
-Yana taimakama mace mai shayarwa da ruwan nono.
-Yana kashe kwayoyin cutar bakteriya (bacteria).
-Yana saukake narkewar abinci a ciki.
-Yana wanke ciki, musamman idan aka cishi kafin aci komai.
-Yana kare lafiyar hanta da koda.
-Yana taimakawa da kuzari ga jikin mutum.
-Yana rage kiba.
-Yana gyara kwalwa.
Da sauransu.