YANDA ZAN IYA AMFANI DA HABBATUS SAUDA DOMIN NEMAN LAFIYA
1. Domin karin lafiya: Cokali daya na man habba a hada da zuma cokali daya asha kafin aci abinci sau biyu (2) a rana – dare da rana..
2. Hawan jini: A hada Cokali daya na garin habba dana zuma gangariya.Sa'annan asanya tafarnuwa dakakka amma 'yar kadan. Asha kafin aci abinci na tsawon kwana ashirin (20).
3. Ciwon dasashi da hakori: A tafasa garin habba da ruwan khal (vinegar). Awanke baki dashi.
4. Tsutsar ciki: Asha habba tare da ruwan khal daidai gwargwado.Tana kashe tsutsar ciki sosai.
5. Rashin bacci: Asanya habba cokali daya a cikin kofin shayi asha kafin a kwanta bacci (awa daya kafin a kwanta).
6. Rashin Gani da kyau: A zuba cokali daya (teaspoonful) na man habba a cikin carrot juice asha Kullum har tsawon wata daya.
7. Tari da asma: Ashafa man habba (ko kuma Habba rob) a kirji da dare kafin a kwanta bacci.
|
Tuesday, 21 May 2013
YANDA ZAN IYA AMFANI DA HABBATUS SAUDA DOMIN NEMAN LAFIYA
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment