Tuesday 21 May 2013

AMFANIN HABBATUS SAUDA

http://worldtruth.tv/wp-content/uploads/2012/06/20110217-136931-black-sesame-seeds-oil.jpgHABBATUS SAUDA (The black seed)

 

 Habbatus sauda ana kiranta da sunaye da dama kamar haka: "Habbatul Baraka" (the blessed seed), Black Cumin, Nigella Sativa, Black Caraway da sauransu. Habbatus sauda nada amfani sosai wajen magance cututtuka da kuma kiwon lafiya, cikin ikon Allah. Ana samun wannan sinadari daga 'ya'yan shukar "Nigella sativa". Shekaru dayawa da suka gabata miliyoyin mutane na kasashen ASIA , MIDDLE EAST da AFRICA sun kasance suna amfani da wannan sinadari mai albarka domin kiwon lafiya da kuma magance cututtuka.

AMFANINTA AKAN LAFIYA (HEALTH BENEFITS):

1. Tana karfafa garkuwar jiki (boosting immune system).

2. Tana gyara al'adar mata ( improving menstruation).

3. Gyara fata daga tamoji (repairing wrinkles on skin).

4. Rage hawan jini (lowering blood pressure).

5. Qarin girman gashi (stimulating hair growth).

6. Yaqi da cututtukan fata (fighting skin diseases: anti-bacterial & anti-fungal).

 7. Kara yawan maniyyi (stimulating sperm producing tissue).

8. Cutsar ciki (worms)

9. Mura da tari (Cold & cough).

10. Asma (asthma) da sauransu.

Allah (S.W.T.) Shine mai maganin cuta. Allah yabamu lafiya. Ameen.

Za'a iya samun wannan sinadari (mai ko gari ) a shagon mu na Muh'd Dikko Rd (opposite K.C.K.), Katsina, Nigeria. Ko kuma a tuntube mu a wannan nambar wayar salula +2348036728702/+2348035716328. Email: madinahislamicmed@gmail.com .Mun gode.

 

 

No comments:

Post a Comment