YANDA ZAN IYA AMFANI DA HABBATUS SAUDA DOMIN NEMAN LAFIYA
1. Domin karin lafiya: Cokali daya na man habba a hada da zuma cokali daya asha kafin aci abinci sau biyu (2) a rana – dare da rana..
2. Hawan jini: A hada Cokali daya na garin habba dana zuma gangariya.Sa'annan asanya tafarnuwa dakakka amma 'yar kadan. Asha kafin aci abinci na tsawon kwana ashirin (20).
3. Ciwon dasashi da hakori: A tafasa garin habba da ruwan khal (vinegar). Awanke baki dashi.
4. Tsutsar ciki: Asha habba tare da ruwan khal daidai gwargwado.Tana kashe tsutsar ciki sosai.
5. Rashin bacci: Asanya habba cokali daya a cikin kofin shayi asha kafin a kwanta bacci (awa daya kafin a kwanta).
6. Rashin Gani da kyau: A zuba cokali daya (teaspoonful) na man habba a cikin carrot juice asha Kullum har tsawon wata daya.
7. Tari da asma: Ashafa man habba (ko kuma Habba rob) a kirji da dare kafin a kwanta bacci.
|
Tuesday, 21 May 2013
YANDA ZAN IYA AMFANI DA HABBATUS SAUDA DOMIN NEMAN LAFIYA
AMFANIN HABBATUS SAUDA
HABBATUS SAUDA (The black seed)
Habbatus sauda ana kiranta da sunaye da dama kamar haka: "Habbatul Baraka" (the blessed seed), Black Cumin, Nigella Sativa, Black Caraway da sauransu. Habbatus sauda nada amfani sosai wajen magance cututtuka da kuma kiwon lafiya, cikin ikon Allah. Ana samun wannan sinadari daga 'ya'yan shukar "Nigella sativa". Shekaru dayawa da suka gabata miliyoyin mutane na kasashen ASIA , MIDDLE EAST da AFRICA sun kasance suna amfani da wannan sinadari mai albarka domin kiwon lafiya da kuma magance cututtuka. AMFANINTA AKAN LAFIYA (HEALTH BENEFITS): 1. Tana karfafa garkuwar jiki (boosting immune system). 2. Tana gyara al'adar mata ( improving menstruation). 3. Gyara fata daga tamoji (repairing wrinkles on skin). 4. Rage hawan jini (lowering blood pressure). 5. Qarin girman gashi (stimulating hair growth). 6. Yaqi da cututtukan fata (fighting skin diseases: anti-bacterial & anti-fungal). 7. Kara yawan maniyyi (stimulating sperm producing tissue). 8. Cutsar ciki (worms) 9. Mura da tari (Cold & cough). 10. Asma (asthma) da sauransu. Allah (S.W.T.) Shine mai maganin cuta. Allah yabamu lafiya. Ameen. Za'a iya samun wannan sinadari (mai ko gari ) a shagon mu na Muh'd Dikko Rd (opposite K.C.K.), Katsina, Nigeria. Ko kuma a tuntube mu a wannan nambar wayar salula +2348036728702/+2348035716328. Email: madinahislamicmed@gmail.com .Mun gode.
|
Sunday, 19 May 2013
BARKA DA ZUWA SHAFIN MU NA YANAR GIZO
----------
Sent from my Nokia Phone