Monday, 24 March 2014

AMFANIN ZUMA GA LAFIYA (A TAKAICE)

Zuma wani irin abinci ne mai zaki kamar shigen suga wanda kudan-zuma ke samarwa daga furen itace ko shuka -wato wani romon sinadari dake cikin furen itace ko shuka da kudan-zuma ke tsotsowa (nectar) domin sarrafa ruwan zuma. Mutane na amfani da zuma a matsayin abinci ko magani. Sabili da muhimmancin zuma, a cikin surorin Alqur'ani maigirma - akwai surah mai sunan kudan zuma - wato Surat An- Nahl. Allah (S.W.A.) ya bayyana mana muhimmancin zuma ga rayuwar 'dan adam a cikin wannan surah " ...waraka ce ga mutane." (An Nahl: 69). Hakika kuma Manzon Allah (S.A.W.) ya bayyana mana muhimmancin ta a wasu hadisai.
Don haka, zuma nada amfani ga lafiya kamar haka:
1. Tana kashe cutar bakteriya da fangas (bacteria & fungus) da kuma bada kariya daga kamuwa da ciwon-daji. Bincike ya nuna cewa zuma mai duhu-duhu tafi wannan amfanin.
2. Tana warkar da ciwo ko gyambo idan ana shafawa ko sha.
3. Tana taimaka ma mai-mura, tari , atishawa da sauran matsalolin sanyi.
4. Maganin gudawa ce.
5. Maganin gyambon ciki - Ulcer.
6. Tana karfafa garkuwar jiki.
7. Tana rage hadarin kamuwa daga cututtukan zuciya, musamman idan aka hadata da Kirfat (cinnamon).
8. Tana sanya kuzari a jiki.
9. Tana rage nauyin kiba. Shan ruwa mai-`dumi da lemun tsami tare da zuma kafin aci komi da safe zai taimaka wajen rage `kiba.
10. Tana saukaka narkewar abinci ga masu fama da rashin narkewar abinci.
11. Tana rage kumburi mai sanya waje yayi kalar ja da radadin ciwo.
12. Tana kyautata lafiyar kwalwa.
13. Tana gyara fata da rage kurajen fuska (pimples) idan ana shafa ta.
14. Da sauransu.












Saturday, 1 March 2014

KALUBALE GA MA'AURATA - KASHI NA 5



GARGADI:
Ba'a yardaba wani yaro ko mutum qasa da shekara sha-takwas (18) ya karanta wadannan bayani ko daya daga cikin shigen jerin irin wadannan bayanai wanda suka gabata. Mai aure ne ko mai shirin yin aure ya kamata ya karanta. Idan shekarun ka/ki basu kaiba kada ka karanta domin doka da tarbiyya sun hana.

GABATARWA
A`dabiance mazaje da dama na cintar kansu cikin wani halin damuwa a duk lokacinda akayi magana dangane da muhimmancin girman al'aura wajen jima'i. Kamfanonin dake samarda kwayoyin magani na girman-mazakuta ko shakka babu suma sun taimaka wajen jefa wannan tsoro cikin zukatan mutane. Wasu kamfanonin ma su kanyi amfani da hotunan batsa na shaidanun mutane masu girman mazakuta domin su jawo hankalin mutane cikin irin wannan tunani: cewa girman al'aurar namiji itace abu mafi muhimmanci wajen saduwa , kuma rashin girmanta na haddasa rashin gamsasshen jima'i ga mace. Sau dayawa sukanyi amfani da wannan dama su sayarda magungunansu da wuri - wato wani sabon salon dubarar kasuwa ne, wanda ta hakan sun sami miliyoyin kudi da mutane.

Sabili da irin wannan barazana, zakaga mutane sun damu sosai akan al'amarin mazakuta , koda kam suna da abunda zasu iya wadatar da matansu (wanda su basu luraba).Muna samun sakonni da yawa (Mails, SMS & Calls) na tambayoyi akan wannan matsala. Saboda yawansu sau dayawa bamu iya karantasu duka kuma mu mayar da amsa. Muna bada hakuri. Don haka zamuyi bayani akan wannan mas'ala daidai gwargwadon abunda muka sani na ilimi. Allah yayi mana jagora.

Minene Adadin Tsawo da Kaurin Al'aurar Baligi ?

Binciken ilimi ya nuna cewa yanayin girman jikin mutum, karanta, tsawo ko kajartar jikin mutum bayada alaka da yanayin girma, tsawo ko gajartar al'aurarsa (kamar yanda wasu ke tunani). Sau da yawa akan samu akasin abunda ake tunani.

Dayawa daga cikin masu binciken kimiyya da nazari akan al'aurar 'dan adam sun raba mutane (baligai) zuwa kaso uku (3): Kason farko (1) sune mutane na tsaka-tsakiya (average) wajen yanayin girman al'aurarsu kuma sune mutanen da akafi yawan samu. Kaso na biyu (2) sune mafi girman al'aura (above average), wato sunfi na tsaka-tsakiya girman mazakuta. Kaso na uku (3) kuma sune na karshe wadanda suke da qasa da abunda kaso na 2 suke dashi (below average), wato masu karantar al'aura.

A lokacinda al'aurar mutum baligi take kwance ba a mike ba (flaccid state) tanada kimanin tsawon inci 3 da `digo 5 zuwa kusan inci 4 (3.5- 3.9 inches = 9-10 cm) amma bai kai inci 4 ba, wato inci 3 da `digo 9. Wannan shine yanayin tsawo na mutanen kason farko, wato na tsaka-tsakiya. Kuma shine tsawon da akafi yawan samu a cikin mutane. Inci 4 zuwa sama kuma shine tsawon mazakutar mutanen kaso na 2, wato wanda su kafi mutanen dake cikin kaso na 2 tsawon mazakuta a lokacinda take kwance (flaccid length of penis). Haka kuma, qasa da inci 3 da rabi shine tsawon mazakutar mutanen kaso na 3.

Toh saidai kankantar zakari a lokacinda yake kwance (flaccid length of penis) bashi bane abunda yake nuni da zahirin tsawonsa ba. Domin kuwa zakari na iya mikewa daga kankantarsa zuwa tsawo mai yawa. Hakan kuwa na yawan faruwa ga wasu mutanen.

Mutumin dake cikin kason mutanen farko, a lokacinda zakarinsa ya mike sosai (erect) zakarin nada kimanin tsawon inci 5 da `digo 5 (rabi) zuwa inci 6 da digo 3 (5.5 - 6.3 in = 14-16 cm). Ma'ana mutum wanda keda tsawon zakari na inci 5 da rabi ko inci 6 ko kuma zuwa gidan inci 6 da `digo 3 toh ya fada cikin kason mutanen farko (average). Mutumin dake da sama da wannan adadi kuma ya fada cikin kason mutane na 2, wato mutane masu zakari inci 6 da `digo 4 zuwa sama. Haka kuma, mutumin dake da qasa da inci 5 da rabi wato daga inci 5 da `digo 4 (5.4 in) zuwa qasa ko inci 3 zuwa qasa, toh ya fada cikin kason mutanen karshe (wato mutane na 3) masu karantar zakari.Kauri, fadi ko gwabin zakari kuma (penis thickness, girth, width, or circumference) na kason mutanen farko nada kimanin inci 4 da `digo 7 zuwa gidan inci 5 da `digo 1 (4.7-5.1 in = 12-13 cm). Mafi yawancin mutane suna cikin kason mutane na 2 (average).

Bugu da qari, mutum zai iya zamantowa yana da tsawon mazakuta da ya fada cikin kason farko ko na biyu amma fadi/kaurin mazakutar ya fada cikin kaso na biyu ko na farko ko kuma ma sabanin hakan. Domin kuwa kowani mutum yana da yanayin da Allah Madaukakin-Sarki ya halicce sa na daban. Kuma Allah Mai-Girma da Daukaka  shine Mai halitta mutum yanda Yaso.

Hanyoyin da masu binciken sukabi wajen samun wannan ilimi sune kamar haka: sanya mutane su auno tsawo da kaurin zakarinsu ta hanyar amfanida "ruler " da kuma "tape", wato sunyi amfani da "ruler" wajen awon tsawon zakari da kuma "tape" wajen awon kauri ko fadin al'aura. A wasu binciken kuma ma'aikatan lafiyar ne da kansu suka auna mutanen domin gudun kuskure daga wajen mutane da akan samu wani sa'in.Misali A wani bincike da akayi a Jami'ar Indiyana (Indiana University) mutum dubu-daya-da-dari-shida-da-sitin-da-daya ne (1,661) akayi bincike a kansu, an sanya su su auno tsawo da kaurin al'aurarsu a lokacinda take mike so sai. Ko wanen su kuma ya bayarda sakamakon ta yanar-kizo (internet).

Wadannan bayanai da suka gabata sun samune daga wasu Mujallolin kiwon-lafiya da suka bada rahotanni akan wasu bincike-bincike da aka gabatar akan al'aurar 'dan adam (A study published in Journal of Urology on September 1996 & a study published on December 2000 in International Journal of Impotence Research & others, among many). Wata mujallar kiwon-lafiya ta Birtaniya ( British Journal of Urology in 2007 ) dake nazari da bincike akan al'aurar 'dan adam ta tattaro wadannan rahotannin bincike-binciken da suka gabata, kuma ta kwatanta kamanceceniyar sakamakon rahotannin binciken na daban-daban. Mujallar tayi sharhi akan wadannan rahotanni inda ta fitar da bayani na kimanin adadin tsawo da fadin zakari (da muka bayar) daga bincike-binciken har guda goma-sha biyu (12) na wasu kasashen duniya da dama. Dalilan wadannan bincike-bincike mafi yawanci shine domin a tabbatar da ilimi akan tsawo da kaurin mazakuta tayanda ma'aikatan kiwon- lafiya zasu iya bada shawarwari ga mutane da suke tunanin suna da kananan zakari kuma suke neman mafita daga matsalar daga likitoci.

Wani Mutum ne Zai Iya Gamsar da Iyalinsa?

Sau dayawa mutane da dama nada tunanin cewa al'aurarsu karama ce kuma suna kokonto ko suna gamsar da iyalinsu yanda ya kamata wajen kwanciya . Wannan shine tsoro da yacika zukatan mutane da yawa saboda ganin cewa wasu kan alakanta gamsasshen jima'i da namiji mai girman mazakuta da kuma jin wasu labaran cewa mata sunfi son namiji mai yalwa da sauransu.Abun mamaki kuma shine mafi yawancin masu irin wannan tunanin tsoro ko fargaba sune mutane na cikin kason farko (average men), wato na tsaka-tsakiya masu tsawon zakari inci 5.5 har zuwa gidan 6.3 (da kuma kauri inci 4.7 zuwa inci 5.1). Mafi yawanci irin wadannan mutane su zaka ga basu gamsu da yanayin suba. Mutane kuma na kason karshe (masu karantar mazakuta) dama can sun san matsayin su - sunada karamin zakari.

Gaskiyar wannan lamari shine: ilimi har ila yau ya nuna cewa , kusan duk mutanen dake cikin kason farko (average men) zasu iya gamsar da iyalinsu wajen jima'i. Dama dai shi jima'i wani abune da yake bukatar dabaru da kwarewa domin gamsar da iyalin mutum. Mutumin dake a kason farko mai dabaru na ilimin jima'i gami da fahimtar iyalinsa akan lamarin jima'i ko shakka babu zai biyama matarsa bukata yanda yakamata kamar yanda mutumin dake dake a kaso na biyu (above average ) ke biyama matarsa bukata yanda ya kamata. Zamantowa a cikin mutanen kaso na 2 sa'a ne domin kuwa mutane a cikin irin wannan kason basu da yawa kamar irin na kason farko. Haka kuma kada kayi mamaki cewa mutumin dake cikin kaso na farko ya gamsar da matarsa sosai fiye da mutumin dake cikin kaso na 2. Ana samun irin wandannan mutane wanda suna da isasshen komi amma basu san yanda za suyi amfani dashi ba, don haka sai mutumin kason farko mai dubara ya fisu abun kirki. Haka kuma, wasu mazajen masu girman al'aura wani sa'in mata na tsogomi da cewa jima'i dasu akwai zafi kasancewar suna da girma da yawa. Bugu da qari, wani sa'in saboda da yawan girman wata mazakutarr sai kaga bata da karfi sosai sai girman kawai.

Bincike ya nuna cewa mata na cikin kason farko (average women) nada kimanin tsawon farji (zurfi) inci 3 zuwa 4 a lokacinda basu cikin sha'awar jima'i, wato a lokacinda basu kamu ba (un-aroused). Wasu kuma matan nada inci 5 zuwa 7. Amma a lokacin jima'i farji na budewa yana qara tsawo da fadi tamkar roba irinta balo ta yanda zai wadaci ko wani nau'in zakarin daya shige shi. Yi mamakin ikon Allah da cewa ta farji ne ake haihuwar jinjiri yayinda ya bude tamkar roba mai-talala. A yayin saduwa kuma farji na yawaita tsukewa da budewa a lokaci daya (repeatedly) domin ya matse zakari dake kaikawo , don samun guga (friction) dake bada `da
ni'imar jima'i.

Toh wata qila mai-karatu yayi wannan tambayar: Da wata hujjace aka dogara da ita cewa mutum na cikin kason farko zai iya gamsar da iyalinsa wajen saduwa? Hujjar itace, ilimi ya nuna cewa zangon farko na zurfin farjin mace (wato waje-wajen farji daga kofa zuwa ciki har zuwa wajen inci 5 na zurfi a qiyasi) shine wurin jima'i (vagina) mai muhimmanci (baya ga beli) da yafi jin 'dan'danon jima'i a lokacinda zakari ke shiga farji.Dalilin kuwa shine wurin na cunkushe da wasu wayoyin sadarwar qwalwa masu jin ta`bi, wato masu kai sakon jindadi ga qwalwa da suke da yawa sosai (nerve-endings).Wadannan wayoyin sadarwa sune suka tafo har zuwa beli (clitoris) su kayi wata babbar mahada a wajen belin daga karshe. Wajen beli akwai wadannan wayoyin masu yawa tamkar wayoyin lantarki masu kawo wuta mai-karfi. Suna da yawa fiye da dubu takwas a qiyasi (More than 8,000 sensory nerve endings by estimate). Wannan zango daya tafo ya qare da wata boda ta zango na biyu. Zangon na biyu wajen zurfi kuma (cervix ) wajene da bana jima'i ba. Matsatstsen wuri ne da ya fara daga karshen zangon farko ya kuma mika zuwa hanyar mahaifa. Wannan bayanai suna nuna cewa mutum na kason farko nada dama dazai iya biyama iyalinsa bukata idan akayi la'akari da adadin tsawon zakarinsa. Duk kanin wadannan wurare (Vagina & cervix) suna qara tsawo a lokacin da mace ta kamu. Kuma a duk lokacinda maigida yaji matarsa tace ya shege ta da yawa - ba dadi ko tayi masa waigi da hannayenta toh kodai saboda tsawon zakarinsa da ya tabo "cervix" ko kuma saboda bata kamu ba- ma'ana bata cikin sha'awa sosai. Domin kuwa idan bata cikin sha'awa tsakanin zangon farko dana biyu babu nisa- matse suke da juna. Idan akwai sha'awa sosai duk sai su qara budawa da yalwa.

Tsawo ne Yafi Muhimmanci ko Kauri?

A wani bincike mata da yawa sun bada rahotanni cewa kaurin mazakuta yafi gamsarwa akan tsawo. Kaurin al'aurar na miji yafi gugar fatun farji domin samun ni'ima. Mata da yawa suna  nuna cewa sunfi jin zakari ya cika su idan mazakuta nada kauri. Saboda haka akan bada shawara ga mararsa kauri cewa uwargida ta rinka hade kafafunta/cinyoyinta wajen kwanciya domin ta gamsar da kanta da maigidanta.

Minene Mafita?

Duk zakarinda ya gaza inci 3 a tsaye (erect) ana kiransa da suna "Micropenis" a turance (wato `dan karamin zakari).Duk mutumin da yake da qasa da abunda ake bukata na tsawo ko kauri yana bukatar ilimin jim'i da wasu dabarun jima'i da zasu taimaka wajen biyama iyalinsa bakin gwargwado. Haka kuma yana bukatar shawarwarin likita kwararre a fannin al'aura. Bugu da qari, akwai hanyoyi na magani, ofireshin (surgery or penile augmentation), famfo (penis pump), qarin-girman zakari da hannu (jelquing/penis exercise) da sauransu na qara girman zakari. Da yawa daga cikin hanyoyin nada hadari ga lafiya wasu lokuttan. Kuma kadan ne daga cikin mutane masu amfani da hanyoyin suke bada rahotan samun nasara idan ka cire magani wanda shima aikinsa ba dindin bane . Kuma kafin mutum yabi daya daga cikin hanyoyin ya zama wajibi yasan hukunci addinin Musulunci akan ko wace hanya - ma'ana haram ne ko halas don gudun sabama Sharia. Don haka sai an tambayi Malaman Sunnah don samun bayani na ilimi (Al-Qur'ani da Hadisi) daga fahimtar magabata. Allah yasa a dace, Ameen.

MEDICAL DISCLAIMER:  
Wanda ya tattaro wadannan bayanai da suka gabata kuma yayi kokarin fassara su a cikin yaren Hausa daga harshen Turanci ba likita bane, Mai- bincikene akan matsalolin lafiya da kuma maganin gargajiya (herbology) irin na Musulunci da kuma na wasu al'adun.Bayanai da mai-bincike ya samo an ciratosu ne daga wasu rubuce-rubuce na wasu masana kiwon lafiya, mujallun kiwon lafiya da kuma yanar-gizo. Mai-bincike yana da kyakkyawar manufar haskakama mutane domin fahimtar wasu matsalolin lafiya da akayi shiru akansu wanda kuma sun dade suna cima mutane tuwo akwarya, domin su ilmanta kuma su nemi shawarwari daga ma'aikatan-lafiya qwararru, don samun mafita daga matsalolinda suka dame su.Wannan bayanai da suka gabata za'a iya yi masu gyara daga qwararru masana kiwon lafiya a duk lokacinda bukatar hakan ta taso domin gudun kuskure da kuma bada gur`bataccen bayani akan matsalolin lafiya. Mun gode.

Domin karin bayani nemi nemi ma'aikatan lafiya qwararru musamman akan al’aura (Urologists) ko kuma bayanai daga wadannan hanyoyi wanda wasu na daga cikin wanda mai-bincike ya ziyarta:

Chen, J.; Gefen, A.; Greenstein, A.;
Matzkin, H.; Elad, D. (2000). "Predicting
penile size during erection". International
Journal of Impotence Research 12 (6): 328333.

Lever, J.; Frederick, D. A.; Peplau,
L. A. (2006). "Does Size Matter? Men's and
Women's Views on Penis Size Across the
Lifespan". Psychology of Men & Masculinity
7 (3): 129.

 Stang, Jamie and Story, Mary.
"Adolescent Growth and Development" .
University of Minnesota. p. 3. Retrieved 26
November 2012.

Wessells, H.; Lue, T. F.;
McAninch, J. W. (1996). "Penile length in
the flaccid and erect states: Guidelines for
penile augmentation". The Journal of
urology 156 (3): 995997.

Wylie, Kevan R.; Eardley, Ian (June
2007). "Penile size and the 'small penis
syndrome'" . British Journal of Urology International 99 (6).

Wikipedia contributors. "Vagina."
Wikipedia, The Free Encyclopedia .
Wikipedia, The Free Encyclopedia, 25
Feb. 2014. Web. 28 Feb. 2014.

Wikipedia contributors. "Clitoris."
Wikipedia, The Free Encyclopedia .
Wikipedia, The Free Encyclopedia, 22
Feb. 2014. Web. 28 Feb. 2014.

Wikipedia contributors. "Human penis
size." Wikipedia, The Free
Encyclopedia . Wikipedia, The Free
Encyclopedia, 26 Feb. 2014. Web. 28
Feb. 2014.

Wikipedia contributors. "Micropenis."
Wikipedia, The Free Encyclopedia .
Wikipedia, The Free Encyclopedia, 31
Dec. 2013. Web. 28 Feb. 2014.