Sunday, 13 April 2014
Amfanin Man-Zaitun ga Lafiya ( a takaice)
Sabili da muhimmancin itaciyar zaitun, Allah Madaukakin sarki, Mai -halittu ya ambace ta a cikin Al-Qur'ani Maigirma - Surat At- Tin da Surat An- Nur.
Man-zaitun nada amfanin sosai ga lafiyar 'dan adam. Binciken ilimin kimiyya ya nuna cewa yana da amfani kamar haka:
1. Yana 'karfafa garkuwar jiki ( domin yaki da kwayar cutar biras, bacteriya, fangas (fighting virus, bacteria, fungus etc.) da sauransu. Wadannan cututtuka suke haddasa matsalolin lafiya da dama, kamar irinsu ciwon-anta, tetanus da cin-ruwa.
2. Yana da sinadarai masu bada kariya daga kamuwa da ciwon daji (rich in antioxidant subtances).
3. Kariya daga cututtukan zuciya - yana rage yawan sinadarin kolestirol (reducing high cholesterol) wanda idan yayi yawa a cikin jini yake da illa ga zuciya.
4. Rage hawan jini (reducing high blood pressure).
5. Taimako ga masu ciwon-suga (helping diabetic patients).
6. Kariya daga ciwon jiki (sanyin jiki) dana gabobi (anti-rheumatism & arthritis).
7. Inganta lafiyar zuciya (improving heart's function esp. to older people whose hearts are weak due to aging) musamman ga tsofaffi wanda zuciyar su ta fara rauni wajen aiki saboda tsufa. Yana gyara zuciya da quruciya.
8. Kariya daga ciwon daji dake shagar fata ( protection from skin cancer).
9. Inganta lafiyar qashi. (improving bone health).
10. Inganta lafiyar kwalwa wajen koyon wani abu kamar karatu ko rike karatun, musamman ga manya (improving cognitive function) da sauransu.
Ana iya amfani da man-zaitun kamar haka:
~ Asha cikin babban cokali sau 2 a rana - safe da rana, cokali daya a kowane lokacin.
~ Ayi girki dashi a matsayin man girki ko a zuba cikin abinci bayan girki.
~ Manshafawa kamar sauran man amfani na jiki.
~ Giris ga ma'aurata (sex lubricant). Bugu da kari, zai kuma bada kariya daga cututtuka.
~ Ciwon-kunne, digo 2 ko 3 na man a cikin kunne.
~ Da sauran wasu hanyoyin na inganta lafiya.
Allah Ya bada sa'a.
Monday, 24 March 2014
AMFANIN ZUMA GA LAFIYA (A TAKAICE)
Don haka, zuma nada amfani ga lafiya kamar haka:
1. Tana kashe cutar bakteriya da fangas (bacteria & fungus) da kuma bada kariya daga kamuwa da ciwon-daji. Bincike ya nuna cewa zuma mai duhu-duhu tafi wannan amfanin.
2. Tana warkar da ciwo ko gyambo idan ana shafawa ko sha.
3. Tana taimaka ma mai-mura, tari , atishawa da sauran matsalolin sanyi.
4. Maganin gudawa ce.
5. Maganin gyambon ciki - Ulcer.
6. Tana karfafa garkuwar jiki.
7. Tana rage hadarin kamuwa daga cututtukan zuciya, musamman idan aka hadata da Kirfat (cinnamon).
8. Tana sanya kuzari a jiki.
9. Tana rage nauyin kiba. Shan ruwa mai-`dumi da lemun tsami tare da zuma kafin aci komi da safe zai taimaka wajen rage `kiba.
10. Tana saukaka narkewar abinci ga masu fama da rashin narkewar abinci.
11. Tana rage kumburi mai sanya waje yayi kalar ja da radadin ciwo.
12. Tana kyautata lafiyar kwalwa.
13. Tana gyara fata da rage kurajen fuska (pimples) idan ana shafa ta.
14. Da sauransu.
Saturday, 1 March 2014
KALUBALE GA MA'AURATA - KASHI NA 5
Thursday, 20 February 2014
Fitaccen Maganin Gargajiya na Kasar Sin - Ginseng
Ita kalmar "Ginseng" (furucin kamar haka /'Jinsen/) ta samu ne asali daga kalmar "rénshēn" wanda a yaren Chananci "ren" na nufin "mutum". Gudan kuma bangaren kalmar "shen" na nufin "jijiyoyi ko sauyoyin shuka" ta yanda idan ka hada kalmomin biyu zaka hararo wannan ma'anar, wato "jijiya mai yatsu wacce take kama da kafafuwan mutum." Ginseng sinadari ne da wadannan kasashe suke amfani dashi a matsayin maganin gargajiya tsawon lokaci mai yawa a tarihi , har izuwa yanzu. Akwai wannan sinadari a kasuwanni kuma ana sarrafashi ta hanyoyi daban-daban na zamani, kamar gari, lifton, abun-sha, kofee, sirof, kwayar-magani, da wasu amfanin. Ginseng na daya daga cikin magungunan gargajiya da akafi siya a duniya. Ana fitar dashi zuwa kasashen duniya da dama, wanda harda Najeriya.Ginseng nada tarihi mai-tsawo na amfaninsa wanda tun daga lokacinda aka fara rubuta amfaninsa (farko) a wani kundi lokacin daular "Liang" (Liang Dynasty 220-587 AD) har izuwa yanzu. Abisa wasu bimcike-binciken kimiyya na zamani, sinadarin Ginseng nada amfani sosai ga lafiya ,
kamar haka: 1. Yana sanya kuzari da hana kasala. Mutane da dama sunyi imani da hakan, kuma suna amfani dashi domin biyan wannan bukata.
2. Yana gyara kwalwa domin rike karatu da kuma kyautata hazaqa.
3. Yana qara ruwan-jikin 'dan adam, kamar irin na maniyyi (maza da mata).
4. Yana bayarda rigakafi daga kamuwa da ciwon-daji (kansa), da yardar Allah.
5. Yana taimakawa wajen magance matsalar rashin karfin-maza.
6. Yana maganin ciwon-jiki.
7. Yana qarfafa garkuwar-jiki.
8. Yana rage suga dake cikin jini da yawan sinadarin kolestorol dake cikin jinin.
9. Yana gyara jini da hana saurin tsufan jikin 'dan adam, idan Allah yaso. Yana gyara jiki da
quruciya. Sai a kiyayi cin haram don rayuwa tayi kyau, mutuwa kuma dole ce. Allah yasa mu dace.
10. Da sauransu.
Muna sayarda wannan sinadari a irin sifofin da muka zayyana ana sarrafashi da kuma samar dashi. Mai bukata sai yazo ya siya, a kuma shawarci likita akan yanda ya kamata ayi amfani dashi. Allah ya taimaka.
Medical Disclaimer: I am just a researcher & a herbal practitioner not a professional medical doctor.
Monday, 6 January 2014
ILLAR YAWAN CHOLESTEROL A JIKIN 'DAN ADAM
adam ke amfani dashi domin gudanar da wasu
ayyukan lafiya a cikin jinin mutum. Wasu daga
cikin ayyukan cholesterol a cikin jini sune: 1.
Sauye-sauyen halittar 'dan adam yayin da yake
balaga da kuma sarrafa sha'awar sa. 2. Daidaita
sukari a cikin jini 3. Kare mutum daga daukar
wasu cututtuka (infection) 4. Samarda VITAMIN
D (sinadari maisa 'kwarin 'kashi da hakora) da
sauransu.
Hanta (liver) tana daga cikin ma'aikata ta
gangar jiki dake samar da CHOLESTEROL mai
yawa. Haka kuma abincin da mukeci wanda yake daga dabbobi na samar
dashi (DIETARY CHOLESTEROL).
Wannan
sinadari yafi yawa a cikin abincinmu karmar: kwai
('kwanduwa), hanta, butter, kifi,
nama, madara, mai , kaza da sauransu.
Duk da kasancewar wannan sinadari yana da amfani ga jikin 'dan adam, ba'a so yayi yawa cikin jini. Yawan cholesterol a cikin jinin mutum nada
hadari sosai, yana haddasa cututtukan zuciya.
Cholesterol dai sinadari ne mai danko kamar
kitse. Idan yayi yawa a cikin jini yana likewa a
hanyoyin jini dake daukar jini (artery) zuwa
zuciyar 'dan adam. Faruwar haka na iya
haddasa toshewar fayif din hanyoyin jinin
(plague/atherosclerosis). Idan haka yafaru, yana
jaza matsalolin zuciya kamar haka:
1. Hanyoyin dake kawo jini zuwa zuciya su toshe
(Coronary artery disease). Daga nan sai a samu
"heart attack" (zuciyar mutum ta samu dameji
ko mutum ya mutu).
2. Zuciya ta kasa harba jini zuwa sauran
hanyoyin jini na sauran jikin mutum (heart
failure).
SHAWARWARI
Mutum zai iya rage yawan cholesterol a cikin jininsa
ta hanyar:
1. Motsa jiki (exercise).
2. Cin 'yayan itatuwa da ganye (fruits &
vegetable).
3. Zaka iya amfani da magani domin rage
yawansa (amma da izinin likita ). Haka kuma
yanada kyau mutum yaje asibiti domin a duba
yawan cholesterol a jikin sa, domin yana karuwa yayin
da mutum yake manyanta. Allah yasa mudace.
Ameen.
Wannan hoto da kake gani a sama yana dauke
da bayanan abubuwa biyu kamar haka: Nafarko,
jini yana gudana a cikin fayif din jinin zuciya
(artery) lafiya lau batare da wata matsala ba. Na
biyu, yana nuna yanda cholesterol ya toshe fayif
din jinin (hanyar jini) zuwa zuciya. Cholesterol
shine mai kalar 'dorowa.