Friday, 25 July 2025

🦟 SAURO: Karamin Dodo, Babban Illa — Yadda Zaka Kakkabe Shi Kafin Ya Kai Ka Asibiti!

A lokacin damina a Arewacin Najeriya sauro na yawaita, sauro ba ƙanana ba ne kawai — manyan maqetata ne. Ƙanana ne masu mugunta da fuka-fuki!! Sun zo da shirin shan jini, kawo zazzaɓi, da tura mutane zuwa asibiti.

Amma kai ba marar wayau ba ne! Ga dabarun da zasu hana ka Maleriya kafin sauro su fara shirin taron gaggawa a jikinka:

🔥 1. ƘONA GANYEN BEDI:

Sauro ba su da hakuri da hayakin dogonyaro/bedi. Idan ka kunna busashshen ganyen - yahaqin shi da garwashi, sai kaga  kamar an cewa sauraye  “ku gudu don tsira da rayuwarku" zasu gudu ka huta, kamar sunji ance EFCC na zuwa. Saidai a kiyaye banda yin hayaqi a kusa  da mai asma ko wata cutar numfashi . Kar a bari yayi yawa har ya cutar da mutane ko ya sanya gurbatar iska. 

🍃 2. GANYEN GWAIBA:

Murƙushe sauro da hayaqin ganyen gwaiba ko , ka  zuba ganyen a kusa da taga. Sauro na jin hayaqin ko ganin shi sai su ce “naga wanda ba zan ciza ba yau!”

    🦟 3. IDAN YA RIGA YA CIZA: 

Idan kaji sauro yana kamar muryar tsoho cewa , "Na shana kasa tashi" , to ya riga ya maka barna. Garzaya asibiti a baka magani. Idan ka neme mu , muma sai mun karbi kudin tarar cizon sauro da kabari yayi maka. Kudin Maganinka💸 anan - WhatsApp: 08084028796

🌾 4. CIYAWAR LEMUNGRASS   :

Ciyawar nada ɗan ƙamshi kamar man shafawa. Amma ga sauro, kamar an saki maye ne da baki bude. Ka shuka ko dafa ka yayyafa — sun tafi kenan! Jarraba hayaqin shima.

🌱 5. MAN NA'A-NA'A

Shafa kaɗan a kunne, wuya, ko kafafu , musamman a waje a lokacin hira. Sauro zasu ce “Wallahi mun sha wahala yau!”

💜 6. MAN LEVENDAR (nema a Islamic Chemist):

Kyakkyawan ƙamshi ga kariya daga cizo. Shafa a daki ko bargo  a lokacin hira a waje , Maleriya ba zata samu gurbi ba.

🍊 7. BAWON LEMU BUSASSHE:

Ƙamshi mai dadi da kariya a lokaci guda. Yi hayaqin bawan ko kori mugu a gidanka. 

⚪ 8. GANYEN ICCEN TURARE (CAMPHOR)

 Ƙamshinsa kamar 'yan sanda ne ga sauro — sai su gudu da ƙafafunsu huɗu! Kona shi shima a gida. A kiyaye shima yawan hayaqi da gudun cutar da mutane.

🧹 9. TSAFTA DA RUFE RUWA:

A daina barin ruwa yana kwanciya a ƙasa, kwatoci ko a bude. Sauro suna haihuwa a cikinsu fiye da yadda mutane ke yin selfie. 

🛏️ 10. GIDAN SAURI (NET):

Idan baka da shi, to ka bar ƙofar Maleriya a buɗe. Idan kana da shi — ka kwanta da kwanciyar hankali, har barci yafi daɗi. A nemi Gidan sauro , iyali da kowa ya kwana ciki. Idan sauro ya ganka a ciki shina cewa "Ga kayan marmari Amma basu ciyuwa". Ya tumbin maigida bude a gidan sauro yana sharar numfashi. Gani nan bari.

🩺 KA FI GANI DA IDO: 

Sauro da Maleriya suna wasa da jiki. Idan ba ka kare kanka ba da iyalinka, zaka wayi gari kana ganin allura da drip a asibiti.  

"Idan ka hana cizon yanzu — to ka hana zazzaɓin gobe."

🛡 DOMIN KA KARE KAI:

– Yi amfani da dabaru 2–3 a lokaci guda.  

– Ka fadakar da iyali, ka gaya ma makwabta.  

– Kada a jira sauro su kawo *“invitation”* — ka hana su shigowa gaba ɗaya!

KA TUNA:

Gida mai tsafta, ɗaki mai ƙamshi, da kai mai wayo = Kare Lafiyar Jiki.

YI MANA LIKING KO FOLLOWING PAGE NAMU.

SAURA KUMA MASU SATAR FASAHA SU WALLAFA SUCE NASU NE.

WHATSAPP: 08084028794

🦟 SAURO: Karamin Dodo, Babban Illa — Yadda Zaka Kakkabe Shi Kafin Ya Kai Ka Asibiti!

 🦟 SAURO: Karamin Dodo, Babban Illa — Yadda Zaka Kakkabe Shi Kafin Ya Kai Ka Asibiti!

A lokacin damina a Arewacin Najeriya sauro na yawaita, sauro ba ƙanana ba ne kawai — manyan maqetata ne. Ƙanana ne, amma ‘yan ta’adda ne da fuka-fuki!! Sun zo da shirin shan jini, kawo zazzaɓi, da tura mutane zuwa asibiti.

Amma kai ba marar wayau ba ne! Ga dabarun da zasu hana ka Maleriya kafin sauro su fara shirin taron gaggawa a jikinka:

🔥 1. ƘONA GANYEN BEDI:

Sauro ba su da hakuri da hayakin dogonyaro/bedi. Idan ka kunna busashshen ganyen - yahaqin shi da garwashi, sai kaga  kamar an cewa sauraye  “ku gudu don tsira da rayuwarku" zasu gudu ka huta, kamar sunji ance EFCC na zuwa. Saidai a kiyaye banda yin hayaqi a kusa  da mai asma ko wata cutar numfashi . Kar a bari yayi yawa har ya cutar da mutane ko ya sanya gurbatar iska. 

🍃 2. GANYEN GWAIBA:

Murƙushe sauro da hayaqin ganyen gwaiba ko , ka  zuba ganyen a kusa da taga. Sauro na jin hayaqin ko ganin shi sai su ce “naga wanda ba zan ciza ba yau!”

    🦟 3. IDAN YA RIGA YA CIZA: 

Idan kaji sauro yana kamar muryar tsoho cewa , "Na shana kasa tashi" , to ya riga ya maka barna. Garzaya asibiti a baka magani. Idan ka neme mu , muma sai mun karbi kudin tarar cizon sauro da kabari yayi maka. Kudin Maganinka💸 anan - WhatsApp: 08084028796

🌾 4. CIYAWAR LEMUNGRASS   :

Ciyawar nada ɗan ƙamshi kamar man shafawa. Amma ga sauro, kamar an saki maye ne da baki bude. Ka shuka ko dafa ka yayyafa — sun tafi kenan! Jarraba hayaqin shima.

🌱 5. MAN NA'A-NA'A

Shafa kaɗan a kunne, wuya, ko kafafu , musamman a waje a lokacin hira. Sauro zasu ce “Wallahi mun sha wahala yau!”

💜 6. MAN LEVENDAR (nema a Islamic Chemist):

Kyakkyawan ƙamshi ga kariya daga cizo. Shafa a daki ko bargo  a lokacin hira a waje , Maleriya ba zata samu gurbi ba.

🍊 7. BAWON LEMU BUSASSHE:

Ƙamshi mai dadi da kariya a lokaci guda. Yi hayaqin bawan ko kori mugu a gidanka. 

⚪ 8. GANYEN ICCEN TURARE (CAMPHOR)

 Ƙamshinsa kamar 'yan sanda ne ga sauro — sai su gudu da ƙafafunsu huɗu! Kona shi shima a gida. A kiyaye shima yawan hayaqi da gudun cutar da mutane.

🧹 9. TSAFTA DA RUFE RUWA:

A daina barin ruwa yana kwanciya a ƙasa, kwatoci ko a bude. Sauro suna haihuwa a cikinsu fiye da yadda mutane ke yin selfie. 

🛏️ 10. GIDAN SAURI (NET):

Idan baka da shi, to ka bar ƙofar Maleriya a buɗe. Idan kana da shi — ka kwanta da kwanciyar hankali, har barci yafi daɗi. A nemi Gidan sauro , iyali da kowa ya kwana ciki. Idan sauro ya ganka a ciki shina cewa "Ga kayan marmari Amma basu ciyuwa". Ya tumbin maigida bude a gidan sauro yana sharar numfashi. Gani nan bari.

🩺 KA FI GANI DA IDO: 

Sauro da Maleriya suna wasa da jiki. Idan ba ka kare kanka ba da iyalinka, zaka wayi gari kana ganin allura da drip a asibiti.  

"Idan ka hana cizon yanzu — to ka hana zazzaɓin gobe."

---