Sunday, 5 May 2019

ALAMOMIN CIWON OLSA


Olsa (القرحة الهضمية /alqurhat alhadmia)  ko "alsa" (peptic ulcer)  wani irin gyambo ne da yake fitowa a ciki ,wato a cikin tumbi ko a jikin ƙaramin  hanjin mutum wanda yake jone da tumbi (stomach) , daga ƙasan tumbin. Idan gyambon yayi ƙamari yakan sa zubar jini  a ciki (internal bleeding). "Gastric ulcer" ko "stomach ulcer"  shine gyambon da yake fitowa a cikin tumbi,  shi kuwa "duodenal ulcer "  gyambo ne da yake fitowa a sashen ƙaramin hanji (duodenum) da yake kusa da tumbin.

ABINDA MASU CIWON OLSA SUKE JI / ALAMOMIN CIWON

- Ciwon ciki
- Rashin son cin abinci
- Ciwon ƙirji ko jin ciwo saman mara
- Jin ƙuna a zuciya (kamar wuta)
-  Rashin narkewar abinci a ciki
- Fitar da "gas" a baki ko yawan gyatsa.    ko
- Amai
- Yawan kasala ko rashin jin dadi
- Rashin son cin abinci mai maiƙo
-  Yin kashi da jini  ko zawo mai ruwa
- Ramewa da sauransu

ABUBU WANDA KE KAWO CIWON OLSA

Mafi yawancin abinda ke haddasa olsa ga mutane shine wani nau'in cuta ce (Helicobacter Pylori/infection) wacce ke harbin mutane da ciwon  , ko yin amfani wasu nau'in magunguna na tsawon lokaci,  musamman magungunan ciwon-jiki da kuma yawan zama da yunwa ko wahalar ƙwalwa (stress). Zaka samu cewa olsa tafi kama manyan mutane,  musamman masu shaye-shayen magungunan ciwon-jiki da kumburi,   irinsu "Ibuprofen", "Diclofenac", "Aspirin " da danginsu. Shi yasa mafi akasari a wannan zamanin zaka ga tsofi da ciwo biyu lokaci daya , wato olsa da ciwon gabobi.

Olsa na faruwa ne a lokacinda wani sinadarin "acid" (gastric acid/gastric juice) mai taimakawa wajen narkarda abinci a ciki ya digo. Idan sinadarin ya ɗigo a tumbi ko hanji , yana cinye wurin ko zaizaye naman a hankali a hankali har sai rauni ya fito. Daga nan sai raunin ya zama gyambo kuma da abinci ya shiga ko taɓa wurin sai mutum yaji wani matsanancin ciwo.  Saboda hakan,  mai olsa najin matsanancin ciwo musamman idan "acid" din yana ƙaruwa fiye da yanda ya dace a jiki. Wani lokacin sai gyambon ya dinga zubar da jini kuma idan marar lafiya yayi amai sai aga jini cikin aman.

ABUBUWA WANDA MAI OLSA YA KAMATA YA GUJE SU

Duk da yake  cewa wani nau'in abinci baya sakawa mutum ciwon olsa, akwai dangin abinci wanda zaya iya sa ciwon  yayi muni ko ciwon yayi tsanani. Daga ɓangare kuda kuma,  akwai kuma abinci wanda zaya iya taimakawa mai olsa domin gyambon yayi saurin warkewa. Don haka, mai olsa ya ƙauracewa wadannan abubuwan domin neman samun lafiya:

- Duk wani abinci mai yaji, saboda zafin yaji na fusata gyambon olsa

- Lemun kwalba, na gwangwani ko na kwali,  musamman mai "gas". Suna sa olsa rashin tausai ga mai ciwon.

-  Abinci mai tsami,  zafi ko sanyi sosai. Suna sanya olsa azabtar da marar lafiya.

- Abinci mai yawan maiko ko soyayye. Suna sanya olsa soyayyar wahalar dakai.

- Gishi ko abinci mai gishiri sosai. Yana sanya olsa zalunci.

- Shan shayi mai "coffee", ko cin goro da duk wani abu mai sinadarin "caffeine". Suna bawa olsa gindin zama domin hanaka zaman lafiya.

- Madara,  musamman ta yogurt. Duk da madara na sanya saukin ciwon olsa, wani lokacin tana sanya ƙaruwar acid dazai sanya ciwon olsa tsananin dadin cutar dakai.  Amna idan aka sha ta da wasu  nau'in magungunan gargajiya  tafi taimakawa.

ABUBUWA WANDA ZASU TAIMAKAWA MAI OLSA DA SAUKIN CIWON

-Cin aiba,  musamman kafin mutum yaci abincin safe , na rana ko na dare.  Duk abincin da za'a
  ci mutum yaci aiba 2 ko 3 kafin yaci abincin. Yana sanya olsa tausayin ka.

- Shan zuma,  cokali biyu sau 2 ko sau 3  a rana. Yana rarrashin olsa da warkar da ita.

- Cin abincin ganye da wasu 'ya'yan itatuwa,  kamar zogale, alayyahu,  kankana da gwanda. Yana hana olsa zalunci da warkar da ita.

- Cin abinci fiye da sau 3 a rana,  amma abinci mai lafiya irin wanda bazai sa ciwon olsa ya   lalace ba. A yawaita cin abinci, sau 5 ko 6 maimakon sau 3 da kake yi a rana, amma ba abinci mai nauyi ba. Abinci wanda zaka dinga ci kadan-kadan kuma akai-akai a rana. Hakan na hana olsa damar ƙuntata maka.

- Samun hutu bayan ka gama cin abinci ko kafin kaci abinci,  na safe,  na rana ko na dare. Hakan na sa olsa raggoncin cutar dakai.

- Cin abinci a hankali da tauna shi sosai kafin hadiyewa. Hakan nasa olsa ta bika a hankali.

- Barin  kwantawa bacci da zaran mutum yaci abinci. A samu awowi kafin a kwanta bacci idan mutum yaci abinci. Hakan nasa olsa bacci daga cutar dakai.

MAGANIN CIWON OLSA
Domin magance ciwon olsa da magani mai inganci sosai domin neman waraka sai a ziyarci cibiyar mu ta MADINAH ISLAMIC MEDICINE dake garin Katsina,  jihar Katsina.

Ko a kira +234808 402 8794 (ko WhatsApp)  domin neman maganin na musamman daga cibiyar mu ta kiwon lafiya ta Musulunci mai albarka da mutane.

Adireshi1: Office branch namu mai address kamar haka:
No. 34 Sabuwar Unguwa Dandagoro - Daura da Solar Walu, Katsina, Jihar Katsina.
Kira: +2348084028794
E-mail: madinahislamicmed@gmail.com

Adreshi 2: Sabon wurin mu:  No. 25 Sokoto Road, Sabuwar Kasuwa ('Yar Kasuwa), Kusa da Gidan Hajiya Azumi.
LIKE our Facebook page domin samun bayanan lafiya irin wadannan masu muhimmanci:
https://m.facebook.com/
MadinahIslamicMedicine/
ref=m_notif&notif_t=like

YI DOWNLOADING APPLICATION (MANHAJA) NAMU ("LIKITAN ISLAMIC CHEMIST" ) A PLAY STORE MAI DAUKE DA BAYANAI MASU MUHIMMANCI IRIN WADANNAN NA SAMA:
https://play.google.com/store/apps/
details?id=com.andromo.dev67983
6.app866696