Sunday, 5 May 2019

ALAMOMIN CIWON OLSA


Olsa (القرحة الهضمية /alqurhat alhadmia)  ko "alsa" (peptic ulcer)  wani irin gyambo ne da yake fitowa a ciki ,wato a cikin tumbi ko a jikin ƙaramin  hanjin mutum wanda yake jone da tumbi (stomach) , daga ƙasan tumbin. Idan gyambon yayi ƙamari yakan sa zubar jini  a ciki (internal bleeding). "Gastric ulcer" ko "stomach ulcer"  shine gyambon da yake fitowa a cikin tumbi,  shi kuwa "duodenal ulcer "  gyambo ne da yake fitowa a sashen ƙaramin hanji (duodenum) da yake kusa da tumbin.

ABINDA MASU CIWON OLSA SUKE JI / ALAMOMIN CIWON

- Ciwon ciki
- Rashin son cin abinci
- Ciwon ƙirji ko jin ciwo saman mara
- Jin ƙuna a zuciya (kamar wuta)
-  Rashin narkewar abinci a ciki
- Fitar da "gas" a baki ko yawan gyatsa.    ko
- Amai
- Yawan kasala ko rashin jin dadi
- Rashin son cin abinci mai maiƙo
-  Yin kashi da jini  ko zawo mai ruwa
- Ramewa da sauransu

ABUBU WANDA KE KAWO CIWON OLSA

Mafi yawancin abinda ke haddasa olsa ga mutane shine wani nau'in cuta ce (Helicobacter Pylori/infection) wacce ke harbin mutane da ciwon  , ko yin amfani wasu nau'in magunguna na tsawon lokaci,  musamman magungunan ciwon-jiki da kuma yawan zama da yunwa ko wahalar ƙwalwa (stress). Zaka samu cewa olsa tafi kama manyan mutane,  musamman masu shaye-shayen magungunan ciwon-jiki da kumburi,   irinsu "Ibuprofen", "Diclofenac", "Aspirin " da danginsu. Shi yasa mafi akasari a wannan zamanin zaka ga tsofi da ciwo biyu lokaci daya , wato olsa da ciwon gabobi.

Olsa na faruwa ne a lokacinda wani sinadarin "acid" (gastric acid/gastric juice) mai taimakawa wajen narkarda abinci a ciki ya digo. Idan sinadarin ya ɗigo a tumbi ko hanji , yana cinye wurin ko zaizaye naman a hankali a hankali har sai rauni ya fito. Daga nan sai raunin ya zama gyambo kuma da abinci ya shiga ko taɓa wurin sai mutum yaji wani matsanancin ciwo.  Saboda hakan,  mai olsa najin matsanancin ciwo musamman idan "acid" din yana ƙaruwa fiye da yanda ya dace a jiki. Wani lokacin sai gyambon ya dinga zubar da jini kuma idan marar lafiya yayi amai sai aga jini cikin aman.

ABUBUWA WANDA MAI OLSA YA KAMATA YA GUJE SU

Duk da yake  cewa wani nau'in abinci baya sakawa mutum ciwon olsa, akwai dangin abinci wanda zaya iya sa ciwon  yayi muni ko ciwon yayi tsanani. Daga ɓangare kuda kuma,  akwai kuma abinci wanda zaya iya taimakawa mai olsa domin gyambon yayi saurin warkewa. Don haka, mai olsa ya ƙauracewa wadannan abubuwan domin neman samun lafiya:

- Duk wani abinci mai yaji, saboda zafin yaji na fusata gyambon olsa

- Lemun kwalba, na gwangwani ko na kwali,  musamman mai "gas". Suna sa olsa rashin tausai ga mai ciwon.

-  Abinci mai tsami,  zafi ko sanyi sosai. Suna sanya olsa azabtar da marar lafiya.

- Abinci mai yawan maiko ko soyayye. Suna sanya olsa soyayyar wahalar dakai.

- Gishi ko abinci mai gishiri sosai. Yana sanya olsa zalunci.

- Shan shayi mai "coffee", ko cin goro da duk wani abu mai sinadarin "caffeine". Suna bawa olsa gindin zama domin hanaka zaman lafiya.

- Madara,  musamman ta yogurt. Duk da madara na sanya saukin ciwon olsa, wani lokacin tana sanya ƙaruwar acid dazai sanya ciwon olsa tsananin dadin cutar dakai.  Amna idan aka sha ta da wasu  nau'in magungunan gargajiya  tafi taimakawa.

ABUBUWA WANDA ZASU TAIMAKAWA MAI OLSA DA SAUKIN CIWON

-Cin aiba,  musamman kafin mutum yaci abincin safe , na rana ko na dare.  Duk abincin da za'a
  ci mutum yaci aiba 2 ko 3 kafin yaci abincin. Yana sanya olsa tausayin ka.

- Shan zuma,  cokali biyu sau 2 ko sau 3  a rana. Yana rarrashin olsa da warkar da ita.

- Cin abincin ganye da wasu 'ya'yan itatuwa,  kamar zogale, alayyahu,  kankana da gwanda. Yana hana olsa zalunci da warkar da ita.

- Cin abinci fiye da sau 3 a rana,  amma abinci mai lafiya irin wanda bazai sa ciwon olsa ya   lalace ba. A yawaita cin abinci, sau 5 ko 6 maimakon sau 3 da kake yi a rana, amma ba abinci mai nauyi ba. Abinci wanda zaka dinga ci kadan-kadan kuma akai-akai a rana. Hakan na hana olsa damar ƙuntata maka.

- Samun hutu bayan ka gama cin abinci ko kafin kaci abinci,  na safe,  na rana ko na dare. Hakan na sa olsa raggoncin cutar dakai.

- Cin abinci a hankali da tauna shi sosai kafin hadiyewa. Hakan nasa olsa ta bika a hankali.

- Barin  kwantawa bacci da zaran mutum yaci abinci. A samu awowi kafin a kwanta bacci idan mutum yaci abinci. Hakan nasa olsa bacci daga cutar dakai.

MAGANIN CIWON OLSA
Domin magance ciwon olsa da magani mai inganci sosai domin neman waraka sai a ziyarci cibiyar mu ta MADINAH ISLAMIC MEDICINE dake garin Katsina,  jihar Katsina.

Ko a kira +234808 402 8794 (ko WhatsApp)  domin neman maganin na musamman daga cibiyar mu ta kiwon lafiya ta Musulunci mai albarka da mutane.

Adireshi1: Office branch namu mai address kamar haka:
No. 34 Sabuwar Unguwa Dandagoro - Daura da Solar Walu, Katsina, Jihar Katsina.
Kira: +2348084028794
E-mail: madinahislamicmed@gmail.com

Adreshi 2: Sabon wurin mu:  No. 25 Sokoto Road, Sabuwar Kasuwa ('Yar Kasuwa), Kusa da Gidan Hajiya Azumi.
LIKE our Facebook page domin samun bayanan lafiya irin wadannan masu muhimmanci:
https://m.facebook.com/
MadinahIslamicMedicine/
ref=m_notif&notif_t=like

YI DOWNLOADING APPLICATION (MANHAJA) NAMU ("LIKITAN ISLAMIC CHEMIST" ) A PLAY STORE MAI DAUKE DA BAYANAI MASU MUHIMMANCI IRIN WADANNAN NA SAMA:
https://play.google.com/store/apps/
details?id=com.andromo.dev67983
6.app866696

Wednesday, 24 April 2019

ABUBUWA 3 WANDA MAZA DA MATA SUKA FI DAMUWA AKANSU WANDA BA MATSALA BANE


"Ɗan maraina na ɗaya yafi gudan girma."
"Nonona  guda yafi gudan girma."
"Gabana  baya da girma idan yana kwance sai  idan ya miƙe."

Bincike ya nuna cewa mutane maza da mata nada yawan damuwa dangane da yanayin halittar jikinsu, musamman  ɓangaren jikin mu da ba'a bayyanawa  saboda tsiraici ne . Sabili da al'ada da kunya, mutane najin kunyar su bayyana damuwarsu ga ƴan uwansu dangane da tsiraicinsu da abinda suke gani  na halittarsu wanda suke jin kamar ya sha banban da sauran mutane, wanda kuma suke ganin kamar matsala ce  ko tawayar halittarsu.  Bugu da ƙari, saboda bama tattaunawa tsakanin abokai da 'yan uwa akan  tsiraicin mu, kuma bama ganin tsiraicin juna zaiyi wahala mutum yasan cewa mutane da yawa nada irin damuwarsa , cewa bashi kadai bane  ko bake kadai bace mai  irin wannan damuwar wacce kuma  ba lallai bane matsala ce tare daku ba.

Idan muka tattara wadannan bayanan na ƙorafi a sama , zamu ga cewa ƙorafe-ƙorafen mutane akan abinda yake ci musu tuwo a ƙwarya guda 3 ne kamar haka:

1. Ɗan maraina ɗaya yafi gudan girma
2. Nono ɗaya yafi guda girma
3. Zakarin da baya da girma idan yana kwance sai  idan ya miƙe.

1. Ɗan maraina ɗaya yafi gudan girma:

A yanayin halittar ƴaƴan maraina dama can ɗaya yafi guda girma ga mafi yawancin mutane . Mafi akasari ƙwallon maraina na  dama yafi na haggu girma da kaɗan. Wasu mutanen kuma ƴaƴan maraina nasu  na haggu sunfi na dama girma (the asymmetrical nature of testicles). Wannan ba abinda damuwa bane (it's normal). A lura  idan maraina suka saki, na dama ko na haggu yana saukowa ƙasa kaɗan akan gudan wanda yayi sama kaɗan a jakar maraina, wannan saboda nauyin wanda yafi girma ne. Wanda yayi ƙasa kamar a sikeli shine wanda yafi girma. Amma idan akwai ƙululu daka lura dashi a cikin maraina wanda kake ji idan ka taɓa ko wani curin nama , ko kuwa daga baya ne ka lura cewa ɗan marainanka guda yana ciwo ko yana ta ƙara girma fiye da gudan , ko ya shanye, ko ya canza siga ba kamar gudan ba,  ko kumburi ,  to shine ya kamata ka damu , wato kaje asibiti da wuri ko wata cibiyar lafiya domin bincike da neman magani. Bincika lafiyar  maraina da kanka akai-akai zai taimaka maka domin sanin lafiyarsu da gujewa cutar ciwon daji ko wani ciwo da ka iya shafarsu  ba tare da ka lura ba da wuri. Hakan zai baka damar zuwa asibiti ko wata cibiyar lafiya domin magance  wata matsala kafin ta girma ko tayi maka illa. A kula da lafiyar maraina kyau, sune masana'antar maniyyin namiji domin samun haihuwa, kada a saka wando wanda zai matse su ya cutar dasu  ko a dinga yawan zauna su, musamman idan suna da girma.

2. Nono ɗaya yafi guda girma:

Kamar dai yanda maza suka damu akan lamarin  maraina, basa so ace  daya yafi guda girma , suma mata ba'a barsu baya ba wajen irin wannan damuwa ta rashin sani akan yanayin nonuwa, wato tsoron ko matsala ce cewa nono ɗaya yafi gudan girma. A yanayin halitta , mafi yawancin mata nonansu guda  yafi ɗayan girma ( the asymmetrical nature of breasts) koda kau kaɗan ne ta yanda ba'a iya lura sosai . Nono ɗaya zai iya fin guda girma ko cikowa, ko yanayin  zamansa  a ƙirjin mace yasha banban da gudan. Wannan abune game gari kuma ba abinda damuwa ba. Amma idan ya kasance kina ganin ɗaya daga cikin waɗannan alamomin to kada kiyi wasa, ki garzaya zuwa asibiti domin gano matsalar da magance ta. Alamomin sune: Canjin girman nono or "shape" wanda kika gani baƙo, jin ƙululu ko wuri mai tauri cikin nono fiye da sauran wurare , canjin yanayin fatar nono ko lotsawar nono, kalar ja ga fatar nono, ko ƙuraje akan fatar nono ko  kusa da kan nonon, ko shigewar kan nono ciki, ko canzawar wajen zaman kan nono ko canzawar sigarsa, fitar wani ruwa daga nono ba tare da an matsa ba, jin ciwo/zafi ga nono ko hammata a koda yaushe, kumburi ga hammata da sauransu. Bugu da ƙari, akwai fitar ruwa daga nono wanda baya da nasaba da ciwon daji (kansa) , juna-biyu ko shayarwar mace.

Abin lura anan shine: Mama na canzawa lokacin juna-biyu ko shayarwa, ko  lokacin al'ada (haila) da yaye , don kada canjin yanayin mama yasa ki jin tsoro. A lokacin juna biyu ko shayarwa, misali, akwai  jin ɗan ciwo akan nonuwa, ƙarin girman mama, komawar fatar dake zagaye da kan nono launin baƙa, da kuma samuwar ruwan nono. A lokacin yaye yaro ma , nonuwa na ciwo na wani ɗan lokaci.

 Don haka, yana da kyau sosai mace mai aure,  budurwa ko zawara ta lura  da yanda yanayin mamanta  yake da kuma yanda take jinsa don gudun  matsalolin lafiya da ka iya shafarsa kamar sankarar mama/kansar nono (breast cancer) ko wani ciwo na daban. Sa'annan a kiyayi shafa magunguna ga mama, musamman magungunan  kemical (chemicals) na turawa wanda zamani yazo dasu domin karin girman mama, ko tsaida su tsaye. Suna da hadari ga lafiya. Bugu da ƙari, mace ya kamata ta dinga duba lafiyar mamanta da kanta akai-akai, hakan zaifi sauƙi idan kinje yin wanka a lokacinda jikinki keda santsin ruwa da sabulu , ki dinga laluba mamanki biyu da yatsu domin neman jin ko akwai wani canji a cikin su, ciwo, tauri ko ƙululu da yasha banban da gudan mamanki. Wannan zai taimaka sosai domin ankara da ƙululun ciwon daji (cancerous tumour) da wuri ko wani ƙaululu wanda bana ciwon daji ba (benign/non-cancerous tumour) domin magance matsalar.

3. Zakarin da baya da girma idan yana kwance sai  idan yana miƙe:

 Wannan ƙorafi ne na uku da muka fi samu daga wajen mutane. Ance rashin sani yafi dare duhu inji masu iya magana; wannan zance haka yake. Rashin sani ne yasa zaka ga mutane na tunanin wai matsala ce cewa zakarinsu baya da girma idan yana kwance (flaccid state)  , wai sai ka ga har neman magani suke yi, wai ataimaka masu da magani, amma kuma idan ya miƙe (in erect state)  yana da girma da tsayi sosai. Wannan yanayin halitta ne ba matsala bace Malam. To minene abin damuwa tunda idan ya miƙe yana fitowa da wadatarsa? Masana sun kasa maza gida biyu, a yanayin halittar alƙalummansu , wato (1) SHOWERS da (2) GROWERS a  yaren turanci. (1) SHOWERS sune maza wanda gabansu yana da girma a lokacinda yake kwance  (flaccid state) amma idan ya mike (erect state) baya wuce girmansa na kwance ko baya ƙara girma sosai. (2) GROWERS kuma a gudan ɓangaren, sune wanda zakarinsu baya da girma idan yana kwance (flaccid state) , wani lokacin kamar na yara idan bai tashi ba, amma idan gabansu ya mike (erect state) yana ƙara girma sosai, tsayi da kaurinsa. Wadannan bayanai na nuna cewa SHOWER zakari ne babba a kwance amma baya ƙara girma yanda ake tsammani idan ya mike, shi kuwa GROWER karami ne a kwance amma da zaran ya miƙe zaya bada mamaki dangane da girman da yayi daga ƙaranta, wato tamkar yana shigewa gareji ne kuma ya fito da girma idan ya tashi.

Domin neman ƙarin bayani ko neman magani daya danganci ciwon maraina, mama ko ciwon daji sai a kira 08084028794 (ko WhatsApp). Allah Ya taimaka.

Adreshi1: Office branch namu mai address kamar haka:
No. 34 Sabuwar Unguwa Dandagoro - Daura da Solar Walu, Katsina, Jihar Katsina.
Kira: +2348084028794
E-mail: madinahislamicmed@gmail.com

Sabon wurin mu: Adreshi 2: Sokoto Road, Sabuwar Kasuwa ('Yar Kasuwa), Kusa da Gidan Hajiya Azumi.
LIKE our Facebook page domin samun bayanan lafiya irin wadannan masu muhimmanci:

https://m.facebook.com/MadinahIslamicMedicine/?ref=m_notif&notif_t=like

YI DOWNLOADING APPLICATION (MANHAJA)  NAMU ("LIKITAN ISLAMIC CHEMIST" ) A PLAY STORE MAI DAUKE DA BAYANAI MASU MUHIMMANCI IRIN WADANNAN NA SAMA:

https://play.google.com/store/apps/detailsid=com.andromo.dev679836.app866696



Sunday, 17 February 2019

DALILAI 12 DAKA IYASA MUTUM GANIN JUWA/JIRI DA MAGANI


Ji ko ganin juwa alamace cewa jikinka  na maka magana wacce ba zaka iya ganewa ba, wato jikinka na gaya maka cewa akwai abinda ke damunsa wanda  likita ne kaɗai  zai iya fahimtar maganar domin kuwa kunnuwanka ba zasu iya gane zancen da juwa ke raɗawa likita ba.  Idan ka biyo mu a wannan rubutun da kake karantawa zamu baka aron kunnuwan likita da zaka iya fahimtar zancen da juwa ke raɗawa  likita game da lafiyarka.
---
Juwa ko jiri (dizziness/disequilibrium) , wani yanayi ne marar daɗi wanda mutum ke jin kansa na juyawa zai faɗi saboda ganin sararin da yake zagaye dashi yana juyawa,  wanda hakan nasa  rangaji kamar na maye, koma mutum ya suma ko  ya faɗi,  ko jin kamar mutum yana tashi sama. Idan juwa tana ɗibar mutum yakan ga duniyar da yake a ciki tana jujjuyawa , wanda hakan ba gaskiya bane a zahiri; ƙwalwarsa da idanunsa ne kawai suke yi masa dabo. Juwa ba cuta bace ita karan kanta, saidai wata alama ce da zata iya nunawa mutum wata matsala ko wasu nau'in matsalolin lafiya da mutum yake fuskanta ko shirin fuskanta.
---
Wasu daga cikin dalilan rashin lafiya daka iya haddasa ganin juwa ga mutum sun haɗa da:
---
1. Rashin jini
2. Saukar hawan jini kwatsam (drop in systolic blood pressure)
3. Matsalar zuciya
4. Ƙarancin suga a cikin jini , musamman ga masu ciwon suga.
5. Ciwon kunne
6. Rashin isasshen ruwan-jiki, musamman cikin zafi idan mutum baya shan ruwa isashshe
7. Yawan motsa jiki
8. Wahala ko yunwa matsananciya
9. Nau'in wasu magunguna da mutum ke sha, musamman na ciwon-damuwa da kwantar da hankali.
10. Ciwon kai maisa rashin gani da kyau (migraine).
11. Tsufa da magungunan da tsofi ke sha zasu iya saka ganin juwa
12. Matsalar tsoro da fargaba , da sauran wasu matsalolin da bamu ambata ba.
---
MAGANCE MATSALAR JUWA/JIRI
---
Magance juwa ya danganta da abinda ya haddasa juwar; misali, idan  yunwa ce ke cizonka to cin abinci zai kore ta, idan kuma rashin shan ruwa ne ko wahala to shan  isashshen kofin ruwa akai-akai da hutu mai yawa ya isa  yasa juwa ta rabu da ƙwalwarka data ke matsamawa. Idan kuwa matsalolin lafiya ne kamar na ciwon zuciya ko hawan jini, ciwon kunne ko ƙarancin jini to likita ne zai iya cecenka daga juwa, ta hanyar baka magani , shawarwari  koma ledar jini da za'a jona maka tiyo nata zuwa jikinka domin kashe jiniyar da juwa ke maka cewa baka da isashshen jini a jiki , domin kashe gobarar rashin lafiyarka. Duk wannan  zai faru ne bayan an gano dalilin juwar wanda  aikin likitane da wasu ma'aikatan lafiya. To dai mu taƙaita, ga wasu abubuwa wanda zasu iya magance matsalar juwa:
---
- Shan ruwa mai yawa , musamman a ranar
- Shan citta (ginger), musamman citta ɗanya ko busassa a shayi (tea) ko abinsha (drink), safe da dare koma sau 3 a rana
- Samun isashshen hutu da barci
- Shan lemun zaƙi da yawa ko lemun tsami a shayi
- Cin ganyen alayyahu a abinci
- Cin naman kaza, kifi da gyada
- Shan zobo a shayi ko abin sha , cin ganye, jan-nama, wake, naman kaji, musamman idan rashin jini ne dalilin juwar
- Ganin likita a asibiti ko ƙwararren mai maganin gargajiya

Call +2348084028794
madinahislamicmed@gmail.com
www.madinahislamicmed.blogspot.com