SANYI kalma ce mai fadin ma'ana da Malam Bahaushe ke yin amfani da
ita domin yin kokarin bayanan wasu matsalolin lafiya na daban-daban ,
misali , ciwon-sanyin jiki [rheumatism], ciwon sanyin mura [cold and
flu] da ciwon sanyin-mara ko ciwon sanyin-mata [vaginitis] ko ciwon sanyin maza-da-mata
da ake dauka ta hanyar jima'i [STDs/STIs like chlamydia, gonorrhea, syphilis,
genital herpes, HPV etc] da sauransu. Saidai Malam Bahaushe baya kiran
ciwon sida/kanjamau [HIV/AIDS] da ciwon sanyin-mara duk da cewa kau anfi yada
cutar ta jima'i.
Za muyi bayani akan ciwon sanyin-mata ne kadai
[Vaginitis]. Matsalolin ciwon sanyin-mata [vaginitis/vaginal infections
or toilet infections] wasu cututuka ne ko matsaloli dake addabar gaban
mace, wato cututtuka masu sanya kaikayin farji, ko radadin ciwo,
kumburin gaba ko warin gaba , zubar farin ruwa, kurajen farji, zafi
wajen yin fitsari ko wajen yin jima'i da sauransu. Ciwon sanyin-wata
matsala ce dake faruwa ga mata da dama a cikin wasu lokutta na
rayuwarsu. Ana samun wannan cututtuka ko matsaloli sabili da wani sauyin
yanayin jiki da mata ke samu wasu lokutta da kuma sabili da wasu
kwayoyin halittar 'bacteria' da 'fungus' dake zaune cikin al'aurar mace,
haka kuma , mata na iya samun wannan ciwon a lokacin juna-biyu da kuma
shayarwa [during pregnancy and breastfeeding] . Har ila yau, za'a iya
samun ciwon ta hanyar jima'i [vaginal intercouse] da wasu dalilan ko
hanyoyi na daban.
Nau'in ciwukan sanyin-mata suna da yawa, to amma
bincike ya nuna cewa ciwon sanyin-mata nau'i uku ne (3) suka fi addabar
mata da yawa. Za muyi bayani akansu kadai, a takaice insha Allahu, sune
kamar haka: (sunayen su da yaren turanci) 1. 'Yeast infection' 2.
'Bacterial vaginosis' 3. 'Trichomonas'
1. ‘Yeast infection’
('Candidiasis'). Akwai wasu kwayoyin halittun 'fungas' (masu suna
'candida') sune ke haddasa 'Yeat infection'. Su wadannan halittu wanda
kwayar idon mutum baza ta iya ganin suba , saboda kankaantar su saida
taimakon madubin likita ne za'a iya ganin su [microscope] . Halittun
suna rayuwa a wasu wurare cikin jikin mutum kuma adadinsu baya da yawa .
Ana samunsu cikin farji kuma, asali basu cika cutarwa ba.'Candida' suna
san wuri mai gumi, lema da rashin iska domin girma da yaduwa. Idan suka
samu wannan yanayi da suke so toh za suyi yawa su kuma haddasa ciwon
sanyin 'Yeast infection'. Anfi yawan samun irin wannan ciwon sanyi ga
mata da yawa , kusan kashi 75 cikin 100 na mata sun taba samun wannan
ciwon a cikin wasu lokutta na rayuwarsu. Alamomin cutar sun hada da:
zubar farin ruwa mai kauri daga farji, kuraje ko kaikayin farji da kuma
labban farji suyi jawur ko cikin farji.
2. ‘Bacterial vaginosis’ ,
cuta ce dake shafar farji sabili da girman wasu kwayoyin halittun
'bacteria' masu cutarwa dake cikin farji suna rayuwa. Alamonin cutar sun
hada da: zubar ruwa mai 'karnin kifi daga farji, warin sa musamman
lokacin jima'i, ko radadin zafi lokacin fitsari, amma babu kaiyayi cikin
alamomin. Alamomin cutar kuma na iya 'buya.
3. ‘Trichomoniasis ’ : A
cikin cututtukan sanyi da muka yi bayanin su a baya (wato cuta ta 1 da
ta 2) , 'Trichomoniasis' ta 3, itace cutar sanyin-mata da ake yadawa ta
hanyar jima'i ga maza (STD) fiye da sauran a zahiri, wato mace zata iya
harbin mijinta da cutar ko mijin ga matar. Idan ya kasance miji nada
wata mata ko yana neman matan waje masu cutar ko kuma macen ta taba
saduwa da wani mutum mai cutar daya samo cutar daga wata mace, to akwai
yiwuwar ma'aurata su samu cutar koma mafi hadari HIV da wasu cututtukan
jima'i (STDs). Ana kiran 'yar kankanuwar halittar [parasitic organism]
dake sanya wannan cuta da suna 'Trichomonas vaginalis'. Mazaje ba kaso
suke sanin suna da cutar ba kasancewar alamomin cutar basu cika bayyana
ga maza ba. Yawanci sai idan ciwon ya kama matan su suna cikin neman
magani suke gano suna da cutar. Idan anyi sa'a alamomin ciwon sun
bayyana ga maza, ana iya samun alamomi kamar haka: zubar farin-ruwa
kadan, zafi kadan bayan fitsari ko bayan fitar maniyyi. Alamomin cutar
ga mata suna iya kama da ciwon sanyi na 1 da na 2 da muka yi bayani a
sama, ko kuma: zubar ruwa mai launin kore-da-dorawa - mai kumfa da wari,
zafi wajen yin fitsari, rashin jin dadi wajen jima'i. Wannan cuta tana
da hadari ga mace mai juna-biyu ga abunda ke cikinta, musamman idan ba'a
nemi magani ba.
Matakin da Zaki Dauka Idan Har Kinga Alamomin Ciwon-Sanyi
Idan har kina da daya ko biyu daga cikin wadannan alamomin ciwon kai
koma fiye da haka, mataki na farko da zaki dauka shine, ki garzaya zuwa
asibiti ko wata cibiyar lafiya domin neman taimako. A asibiti ne idan
anga kwararriyar likita, musamman 'gynaecologists' wanda suka shahara
akan fagen matsalolin mata , za'a duba matsalar, sa'annan ayi bincike
'lab test' ko da 'microscope' asan abunda ke damun ki a kuma baki
maganin daya dace da shawarwari. Haka kuma , idan anyi binciken kuma an
tabbatar da irin ciwon sanyin dake damun marar lafiyar toh za'a iya zuwa
wannan cibiya tamu mai albarka ta Madinah Islamic Medicine Katsina
domin neman magani/waraka da yardar Allah.
Wasu Halayen Da Zasu Iya Taimakawa Wajen Samun Ciwon Sanyi da Rigakafin su:
> Wajen Tsaftace Gaba [ Vaginal Douching] A cikin farji akwai wasu
kwayoyin halittar 'bacteria' marar sa cutarwa kuma masu amfani (wato
'Normal flora'). Su 'normal flora' suna taimakawa wajen bada kariya ga
farji daga wasu nau'in 'bacteria' na daban masu cutarwa (masu suna
'Bacterial pathogens'). Garin neman kiba akan nemo rama, wasu mata kanyi
amfani da wasu hanyoyi domin tsaftace farji, kamar ta hanyar yin amfani
da sabullan magani, harba magani cikin gaba, ruwan dumi da gishiri ko
dettol domin wanke farji don tsaftacewa ko rigakafi daga 'bacteria' da
zata iya cutarwa. Wadannan abubuwa da ake amfani dasu don rigakafi na
kashe 'bacteria' masu amfani [the normal flora] cikin farji, hakan zaisa
'bacteria' masu cutarwa su samu damar shigowa cikin farji su cutar da
lafiya da ciwon-sanyi, sabili da babu 'bacteria' mai bada kariya dake
hana su shiga ko 'barna. Don haka , idan har lafiyar ki lau kuma kina
son tsaftace gabanki toh sai ayi amfani da ruwa , musamman lokacin wanka
a tsaftace gaba. Ki guji fesa turare ko wanke gaba da sabili mai
kamshi. Idan har lafiyar ki lau kada kiyi amfani da wani abu idan ba
ruwa ba. Ki sani cewa farji yana tsaftace kanshi da kanshi a yanayin
halittarshi, yana fitar da wani ruwa [secrets fluid] na musamman dake
wanke illahirin gaban mace.
> Kayan-sawa na ciki/wandon pant
[Under-wears/under-pants] Wasu matan kanyi amfani da wandon pant ko
'skin-tight' kwana da kwanaki ba tare da canzawa ba ko wankewa. Irin
wannan halin kazanta na dauda da lema, na bawa cututtuka (Germs) dama su
shiga cikin farji su kuma girma cikin 'dan kankanin lokaci har su
haddasa ciwon sanyi. Don haka , yana da kyau a canza 'under-wears'
wankakku masu tsafta a kowace rana. Idan lokacin zafi ne ko kinyi aiki
kuma akwai zufa a jikin ki to sai ki canza wando akalla sau 2 a rana.
Kuma yana da kyau ayi amfani da wandon da akayi da auduga [cotton
under-wears] domin yana taimakawa wajen tsotse lema da bushewa, sabanin
wando da akayi da 'nylon' [nylon under-wear].
> Wajen wanke
bayan-gida [Way of cleaning the anus after faeces] Yana daga cikin
halayen wasu mata idan sunyi bahaya suna fara wanke dubura sa'annan
gabansu, wasu kuma suna hadawa ne duka , wato gabansu da dubura su wanke
lokaci daya, wannan ba dabi'a bace ba mai kyau ga mace, domin kuwa idan
kika wanke dubura farko sa'annan gabanki ko kika wanke su a lokaci daya
toh zaki iya goga ma farjinki wasu cututtuka dake cikin kashi/bayan
gida. Don haka , sai a fara wanke farji farko, bayan angama wanke shi da
ruwa da kyau to sai a wanke dubura.'Toilet infection' kalma ce da
mutane suka kirkira kuma ta samu asali ne daga mummunar dabi'ar wanke
dubara tare da farji, wanda wasu ke tunanin shine ke kawo cutar
sanyin-mata. Toh saidai dadilan dake kawo cutar sanyin mata suna da yawa
kamar dai yanda mu kayi bayani a baya, kuma ita kalmar 'Toilet
infection' ba tada muhalli a cikin 'Kamus din likitoci a matsayin sunan
cuta. Mutane ne wanda ba ma'aikatan lafiya ba suke amfani da kalmar da
nufin 'vaginal infections' ko 'vaginitis' (kalmar da ma'aikatan lafiya
suka fi amfani da ita).
> Tsugunni a bandaki [Squatting in
toilets] Yin tsugunni a bandakin da mutane da yawa ke amfani dashi nada
hadari ga lafiya, musamman bandaki mai dauda da kazanta. Sau da yawa
mace zata tsugunna tayi fitsari cikin bandaki sai fitsarinta ya doki
kasa yayi tsalle ya fallatso mata ko ya dawo mata tare da wani ruwan
dake kwance a kasa ko fitsarin wata macen.Digo daya na fitsarin mai
ciwon sanyi zai iya harbar ki da ciwon idan ya fallatso maki ga ga
gaba.Don haka, idan zaki yi fitsari kada kiyi inda kowa keyin fitsari a
cikin bandaki, ki samu wuri na daban mai tsafta cikin bandakin kuma inda
babu ruwa a kwance. Haka kuma kada ki bari gabanki ya taba kasa. Kiyi
fitsari a hankali. A yawaita wanke bandaki kullum da dettol ko danginshi
'germicides' masu inganci domin kashe cututtuka.
> Yin amfani da
wandon pant na 'kawar ki, yar'uwar ki ko wata mace [Sharing
under-wears] Kawar ki, kanwar ki ko wata yar'uwarki mutane ne masu iya
kamuwa da cuta. Zai iya kasancewa suna da ciwon-sanyi , don haka idan
kina jin cewa kinyarda da ita ko kuma kun zama jini da tsoka toh ki
shirya fama da ciwon sanyi da zasu iya harbarki dashi idan kina amfani
da wandon su. Koda basu da ciwon , bai kamata ku rinka amfani da pant
din junanku ba. Riga kafi yafi magani.
> Rashin kula wajen yin
jima'i [Sexual intercourse without care] Yanada matukar muhimmanci ki
kiyaye da jin rauni a farji a lokacin saduwa da maigida. Barin gashin
gaba ba'a rage shiba da kuma yin jima'i tsawon lokaci ko da karfin tsiya
na daga cikin dalilan dake sa mace ta samu rauni a gabanta. Samun rauni
ko fashewar fata cikin al'aura na bawa cututtuka kofar shiga jiki su
cutar da lafiya da 'infections'.
>Mataki na biyu da zaki iya
dauka shine: bayan kin san abunda ke damun ki domin a asibiti an bayyana
maki, idan har ya tabbata sanyi ne kuma kin sha magani amma baki samu
sauki ba, ko kuma kin samu sauki amma baki warke duka ba yana dawowa,
toh zaki iya amfani da wannan taimakon da zamu baki :
Ki samu 'Khal
tufah' [Apple cider vinegar] a Islamic Chemist. Ki tafasa ruwa mai yawa
yayi zafi, idan yayi 'dumi sai ki samu robar wanka ki juye ruwan ya cika
robar, sa'anna ki zuba khal tufah cikin ruwan kimanin adadin kofin
shayi [small tea cup] 1 ko 2 cikin robar wankan, sai ki zauna ciki minti
15. Bayan kin tashi daga robar sai ki tsane lemar ruwan dake gabanki da
tawul mai kyau ya bushe. Sai ki samu man-kwakwa [coconut oil] da auduga
ki goge gabanki, man-kwakwa nada sinadarai masu kashe kwayoyin cuta [
antiviral, antibacterial and antifungal properties] Kiyi amfani da
man-kwakwa sau 3 a rana. Za kiyi amfani da Khal tufah kamar yanda mu
kayi bayani kullum sau 1 a rana har sai kin samu sauki.
Haka kuma,
zaki iya amfani da Tafarnuwa [Garlic]. Ki samu salar tafarnuwa 2 ko 1 ki
karkare bawon da ledar ta, kiyi matsi dasu da dare idan zaki kwanta
bacci sai da safe ki cire ki yar. Tafarnuwa magani ce mai karfi (kuma
'antibiotic') , itama tana da sinadarai masu kashe cututtuka [antiviral,
antibacterial and antifungal properties]. Kuma zaki iya cin tafarnuwa
ko amfani da 'capsules' nata, idan zaki iya.
Bugu da kari, zaki iya
neman garin Hulba [Fenugreek powder] a Islamic Chemist da zuma (honey)
kiyi shayi, ki tasa ruwa ki zuba hulba karamin cokali 1 cikin kofin
shayi ki motsa, sai ki sha. Kiyi haka safe da dare, har sai kin samu
sauki. Idan mace tana da juna-biyu kada tayi haka sai ta nemi shawarar
likitan Islamic Chemist/ likitan asibiti da yasan 'Hulba' ko masani amma
babu laifi ga mai shayarwa tayi amfani da hulba, hakan zai kara samar
mata da ruwan nono. Masu juna-biyu su guji sha-shayen magunguna ba tare
da izinin likita ba. Allah ya taimaka.
Madinah Islamic Medicine:
Wannan bayanai Da suka gabata kokarin bincike ne da wallafar Hausa na
Madinah Islamic, Katsina. Za'a iya yima bayanan gyara a duk lokacin da
bukatar hakan ta taso. Domin neman karin bayani ko gyara, ko kuma neman
magungunan Musulunci akan matsalar da wasu:
Kira +2348084028794
ko
email: madinahislamicmed@gmail.com